← Book details Rushewar Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 24

Sashe 15

Rushewar Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shima washe haƙora yayi yana mai jin daɗin sauka da Raheenatu tayi, kallonshi tayi tace "i will go up, when you go home and call me" tana gama faɗa ta wuce saida tazo hawa step ɗin benen ta juyo tana girgiza mishi boobs tana faɗin "ka gani ka gani ƙwalelanka,ka gani ka gani ƙwalelanka, haka taita girgijewa tana hautsina ma Elejon tunani, dariya ta kece da ita tana faɗin "kaji ɗan banza daga ganin lafiyayyin ƴaƴa na motsi har ka haukace" gwalo tayi mashi ta haura sama da gudu tana dariya

shafa kanshi Elejon yayi yana yana dariyar halayyar Raheenatu shidai ba ƙaramin birgeshi take ba, ga wata zazzafar ƙaunar da sonta daya riga ya kamashi, lumshe idanunsa yayi yana shafa ɗan gemunsa, ya fice

Raheenatu na shiga ta faÉ—a kan gado tana mai sake lumshe idonta, ita kanta tasan Elejon na sonta amma saidai koda ya musulunta bazata iya aurensa ba saboda wani dalili nata na daban, dukda bawai itama bata sosnshi ba, saboda babu macen da zata ga Elejon tace bata sonshi, a hankali ta furzar da iskar bakinta, tana tunanin yadda rayuwa ta sauya mata, tana fatan kamar yadda tata rayuwar ta sauya ta Raihana itama ta sauya, duk lokacin data tuna Ahalinta takan tsinci kanta cikin damuwa sosai,

*RAIHANA*

A hankali na miƙe jiki ba ƙwari na nufi inda Sadeeq yake, bacci na iske ya kwashesa, hannu nasa ina bubbuga ƙafaɗarsa, "tashi ka ɗauki Abba mu tafi" na faɗa ina ficewa, bayana ya biyo yana ɗaukar Abba, rufe idona nayi na riƙe hannun Sadeeq, bamu buɗe idonmu a ko ina ba sai gidan Mommy, kai tsaye wani ɗaki nakai su Part ɗin Mommy, Ni kuma na haura sama ina shiga, na faɗa bisa bed ɗin ina maida numfashi, ji nake duk jikina yayi man tsami, kiraye_kirayen Sallah asuba yasa na miƙe na shiga Toilet nayi wanka sannan na ɗoro Alwalla, Sallah nayi saidai yau naji da sauƙi babu azabar nan da nake ji, ina gamawa na tada Hameeda tayi Sallah, har Azkar na ɗan taɓa har gari ya waye, sannan na kwanta ina kwanciya bacci mai nauyin gaske ya ɗauke ni, wanda sai 12:00pm na tashi, shima saida Hameeda ta tadani wai Hamma yace ta tadani inyi Break, wanka na shiga nayo, nai shirina tsaf sannan, sanye nake da Arabian gown wacce taji adon Stone na fito sai walwali nake,

a hankali na sauko inata zuba ƙamashi, kafeta da ido Nuraim yayi yana jin kamar ya hadiyeta ciki don ƙaunarta, Murmushi na sakar mashi ina ƙarasowa na zauna kusa da Mommy, gaida ita nayi, ta amsa da murmushi

Kallon Hamma nayi ina gaida shi, da fara'a a fuskarsa ya amsa yana nuna min abinci "kije kiyi Break kar yunwa ta kamaki naga bakya son cin abinci" ya faÉ—a yana kauda kanshi gefe

Da to na amsa ina miƙewa na nufi dinning Abinci kaɗan na ɗan ci, na miƙe, "ina zakije baki karasa kingin ba? maza zauna sai kin cinye shi" ya faɗa yana nufo inda nake, ganin haka yasa Mommy tashi ta haura sama, da kallo nabi Mommy kamar zanyi kuka, "maza kici wannan abincin da kika ɗan ci shine kinci abinci" , turo bakina nayi kamar na fashe mashi da kuka nace na ƙoshi fa Hamma"

shima kamar yadda nayi haka ya turo bakin yana faÉ—in "sai kinci da yawa fa" ya faÉ—a da salon da nayi maganar, dariya na kece da ita ganin yadda yayi

"Spoon ɗin ya ɗauka yana ebo Abincin yace "buɗe bakin" buɗewa nayi ya bani ina ci ina yamitsa fuska a haka ya dinga danna min abinci, saida ya tabbatar na ƙoshi sannan ya ƙyaleni da kanshi ya bani ruwa nasha, "ko kefa amma ki zauna kina wasa da cikinki, bakya son cin Abinci"

shiru nayi ina wasa da zoben dake hannuna daga bisani kuma na yamitsa fuska ina ƙara turo baki nace " kaga Hamma ka mini ɗure abinci da yawa cikina duk ya cunkushe da ƙyar fa nake fitar da numfashi" na faɗa a shagwaɓe

Lumshe idanunsa yayi yana jin wani yanayi a tare dashi don shi duk lokacin da Raihana ta turo mashi bakin nan gaba ɗaya hautsina masa lissafi take, yarasa me yasa ko dai da gayya take masa hakan, kiran sunanshi da tayi ne yasa shi saita nutsuwarsa yana kafeni da idanunsa masu ƙara narkar dani a duk lokacin dana haɗa ido dashi

hannuna ya kalla yana taɓa zoben dake walwali a hannun yace "a ina kika samu zobe mai kyau haka ne?"

murmushi nayi ina ƙara shafa zoben nace "Yayana ne ya bani shi" haɗe fuska yayi yace "wane yayan ?" "YAYA FAUZAN" na bashi amsa a taƙaice, "ɗan gidanku ne?" "eh mana"

"kuma shine zoben har yanzun bai miki kaɗan ba?" Ya faɗa da son jin ƙarin zance, shiru nayi shima share zancen yayi, miƙewa nayi nace zanje wajen Mommy ina son faɗa mata wani abu, kai kawai ya ɗaga min yana bina da kallo

Koda naje gun Mommy na zauna na faɗa mata dukkan abinda ya wakana, hamdala tayi tana min faɗa akan me ban faɗa mata ba, Nuraim ta kira ta faɗa masa komai, babu ɓata lokaci suka nufi inda Abba yake, dukkansu saida suka tausaya mashi, donma wai nan da sauƙi, tunda har magana yana yi tunda na shiga ya kafeni da ido yana hawaye a hankali ya miƙo man hannunshi da nufin nazo yana kiran sunana, jiki babu ƙwari na nufi wajenshi a hankali ya buɗe baki yace "Raihana tabbas na fidda tsammani da rayuwa, sai gashi a lokacin da banyi tsammanin ba kin kawo man ɗauki, nasan ni kaina banyiwa rayuwarku inganci ba, dukda ƙarfina a kafi abin na mini ciwo Raihana ta yadda na kasa baku kulawa,ni har gobe bani ganin laifinki Raihana tunda ba yin kanki bace, hasalima duk wata matsala data sameki a ta sanadina ne, na gaza Bama mahaifiyarki kulawar data dace, harta koma ga mahaliccimmu, haka zalika kuma ban ma rayuwarku inganci ba, wadanda naso su na ririta sune suka guje suka yunƙurin guntule kingin rayuwar data rage man, waɗanda naƙi na tozarta sune suka tarairayeni a lokacin da jarabta ta saman" kuka sosai Abba yake nima kukan nake, da ƙyar mukayi shiru da bada bakin su Mommy, daga bisani kuma aka ɗauki Abba zuwa asibiti don a ƙara duba lafiyar shi, muna zuwa aka amsheshi aka bashi gado,

Saida Abba yayi watanni a Hospital suna bashi kulawa ya murmure yanzun ya fara maida jikinshi, sosai yake janmmu a jikibsa wanda koda yaushe muna tare, haka zalika har nayi kwanaki da gama Iddah, sosai Baba ke ƙara shiryani nida Nuraim wanda ranar Juma'a za'a ɗaura auren.........✍️

Wannan kenan

*Comments, Share fisabilillah*

Wadannan su ne ƙwarin guiwata

*By Riamcool Hasken Royal*

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
[2/9, 2:09 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA*

Book 2

By Mariam sani Riamcool

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

Bismillahirrahmanirrahim

Page 94&95

______________✍️Dukda bikin ba wani dogon lokaci aka saka ba, amma babu laifi ana shirye_shirye, haka Mommy ta zage tana gyara Raihana, ciki da waje, fatar nan tata sai sheƙi take tayi kyau sosai abinta, Nuraim kuwa sai rawar ƙafa yake da rawar kai akan Raihana,

Abba kuwa jiki ya ƙara murmurewa an sallame shi a Hospital, harya fara maida jikinsa, sosai yake jammu a jikinsa,ga Lagos Nuraim ya bada cigiyar Raheenatu, don yadda Abba ya damu akan son ganin Raheenatu, haka zalika ya riga daya saka damuwar Ammi a ranshi ganin tana hannun Baba Modibbo,

zaune nake Mommy ta tasa ni gaba akan sai nasha wani magani wanda Baba ya bada aban, kurɓa ɗaya nai mashi naji Brain ɗina na neman juyawa, ga kuma wani Azababben ciwon kai lokaci guda daya rufeni, kallon Mommy nayi ina ƙwal_ƙwal da idanu alamun zanyi kuka nace "Mommy don Allah na barshi hakanan tunda na kurɓa, wallahi bakiji yadda Brain ɗina ke juyawa ba, ga kaina dake wani irin sara man,kuma fa ga lalle da zamuje ayi mana" na faɗa kamar na fashe mata da kuka

Nuraim dake tsaye bakin ƙofar tun ɗazun ya harɗe hannuwansa a ƙirji yana kallonta don tunda Mommy ta saka aka fara gyara Raihana gaba ɗaya ta hanashi ganinta, ta ɓoyeta, gaba ɗaya cikin kwana biyun daya yayi bai ganta ba, ya shiga cikin wani yanayi, yanzuma da Mommy ta shigo ɗakin ta mance bata kulle ba shiysa harya samu damar shigowa, kallonta yake sosai don daga ita sai wata ƴar ɓingilalliyar riga wacce ta bayyana halittun ƙirjinta waɗanda suka cika fam dasu sunyi tsaye, ga fatar jikinta dake sheƙi sosai ta ƙara ja da haske tayi ɓulɓul, a hankali ya tako harya iso daf da ita, Cup ɗinda ke hannuna ya amsa yana ɓata fuska yace

"Mommy tunda har kanta na ciwo daga shanshi kamata yayi ki ƙyaleta tunda ta sha"
sake da baki Mommy ke kallonshi don ita batama san da shigowarsa ba, sai yanzun "bazan ƙyaleta hakanan ba saifa ta shanye tas sannan, kai da kanka kasan fa muhimmancin maganin nan" Mommy ta faɗa tana amsar Cup ɗin dake hannunsa, da ƙyar na shanye shi, ina matsar ƙwalla

lallashina Hamma ya dinga yi, "idan kin gama ƙwallar ƴar Mommy sai ki tashi kiyi wanka kuje ayi maki lallen" Mommy ta faɗa

Cikin ɓata fuska Nuraim ya kalli Mommy yace "Mommy ina kuma zata tafi, a hakan yadda tayi kyau ɗinna? gaskiya Mommy ta zauna mai lallen tazo da kanta tayi mata, bani son wani koda ɗan yatsanta ya kalla, Mommy, bare tayi ɓulɓul da ita sai sheƙi take kuma ta fita, tunda na tabbata ta fita sai wani ya kalleta, nifa ko Abdurrahim ban son ya kalleta bare kuma wani na daban, Uhmm Uhmm ta zauna nida kaina zan aika a ɗauko mai lallen" Nuraim ya ƙarashe zance da ƙara haɗe fuska
Chapter 15 · 0% Book details