← Book details Rushewar Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 24

Sashe 6

Rushewar Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baiyi magana ba ya juya da sauri ya shiga Mota ya jata da gudun tsiya yana tunanin ta ina zai fara ga Abdurrahim gasu Jabir ga Ni'imatu, wani irin gudu yake shararawa kai kace zai tashi sama, saidai wata ƙatuwar Mota dayaga tana yo kansa gadan_gadan hankalinsa ya tashi, haka yaita ƙoƙarin kauce mata amma saida ta cimmasa da mugun gudu ta kawo ma motarsa karo wacce ta birkice da Nuraim daketa ambatar sunan Allah, motar na bige ta Nuraim ta wuce a tsiyace,

Tun sanda su Raihana suka fito Jabir zai kaita wata mota ta dinga binsu ta baya sai daga baya Jabir ya lura da binsun da akeyi, gudu ya ƙara ma motarsa,saidai duk iya gudunsa saida suka cimma sa da wata motar tasha gabansa,da sauri ya taka birki yana ambatar sunan Allah, wani baƙin ƙaton mutum baƙi mummuna ya fito, yana zuwa ya buɗe yana fisgo ni da ƙarfi sannan ya ɗaga hannu ya sharara man marin da saida bakina ya fashe, sannan ya fiddo Jabir daga Motar yana saitasa da bindiga, dukkan waɗancan na cikin motar suka fito sannan ɗaya daga cikinsu ya matso yana bugawa Jabir ƙasan bindigarsa, wanda yasa tsakiyar kansa fashewa yana zubar da jini, nikam wannan jinin dana gani shine yasa kaina wani irin juyawa a hankali naji zuciyata na sauyawa tana komawa ya zuwa ta rashin imani, ji nake tsaf zan iya cin mutum a ɗanyensa, sannan na kora da jininsa, ga gangar jikina data fara janzawa ji nake kamar anyi man musayar wata, da sauri na gartsa wa mutumin nan cizo a hannu sannan na shaƙesa ina kafa masa wani cizon a wuya ina zuƙar jininsa ina jin wani manɗon daɗi da garɗi, da sauri wannan wani yazo yana fizgoni da ƙarfin tsiya, saidai ina juyowa dukkanninsu kowa ya tsorata, ganin yadda yanayin halittana ta fara janzawa yazuwa wata halittara ta ban ga haƙorana da baki da sukayi jage_ jage da jini.........✍️

*Wannan kenan Comment Share fisabilillah*

Waɗannan su ne ƙwarin guiwata

*By Riamcool*

*08109554986*
[2/6, 5:51 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA*

*Book 2*

*By Mariam sani Riamcool*

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*

*Bismillahirrahmanirrahim*

*Page* 74&75

___________✍️Da wata kalar murya mai fidda amo da sauti take faɗin "duk wanda yai ƙoƙarin taɓa man makamin fansata bazan taɓa ƙyalesa ba, ku tabbatar da dukkanku babu wanda zai tsira bare ya sha, wallahi dukkanku saina kashe ku, kamar yanda kuka so kashe man makamina, saidai ku zaɓi mutum guda wanda zan tura yakaiwa wacce ta aiko ku saƙo."

dukkansu tsit sukayi jukunnan su duk sun jiƙe da zufa da fitsari ko wane jikinsa idan banda kyarma babu abinda jikinsa yake, Jabir kanshi shima matsanancin tsoro ya kamasa, lallai be yarda da Raihana mutum bace, ganin babu wanda yai magana a cikinsu yasa duk ta dinga binsu ɗaya bayan ɗaya tana zuƙe jinanansu, sai mutum ɗaya data bari shima tuni ya suma a wajen, ina gamawa naji wata juwa na neman yada ni ƙasa da sauri na dafe motar dake kusa dani ina ƙoƙarin amboton Allah amma zuciyata da bakina sun mani nauyin furtawa, a hankali na sulale ƙasa ina fashewa da kukan dana saba, ni kaina na kasa tantace wace kalar halitta ce ni da zan maida jinanan mutane ruwan shana, Jabir ne ya matso a ɗaɗɗare yana rarrashina da ƙyar na samu na miƙe ina ciro mayafin abayar na goge jinin daya ɓata man fuska da hannuwa, sannan na shiga motar Jabir yaja, yana parking a ƙofar gidan Alhaji Muttak'a na fito ina masa godiya na shige,

Ina shigewa nayi saurin lulllub'e fuskana ina tafiya karo naji naci da mutum da sauri na juyo da fuskana, ina kallon Alhaji Muttak'a dana ɓata masa farar shadda da jini, shima a razane yake kallona da ƙyar ya haɗiye wani yawu daya tokare masa maƙoshi, sannan ya ce "Raihana kije na sakeki saki ukku ki gafarceni akan abinda nayi maki amma dan Allah dan annabi ina roƙonƙi da girman Allah da Manzonsa ki ƙyaleni da rayuwata da rayuwar iyalina, nasan tabbas ke ce kika kashe Aslam bana fatan ki ƙara ɗaukan rayuwan wani iyalin nawa,kinga kinsha jinin iyalina biyu to kinga kamar kinsha nawa ne, yanzun ki faɗa man dukkan abinda kike buƙata zan baki." ya faɗa yana fashewa da kukan daya daɗe da riƙewa

wani banzan kallo na masa ina sakar masa wani Miskilin Murmushin daya saka ƴan hanjin cikinsa kaɗawa, kafin na kafesa da idanuna masu ƙara razana sa,tun zufa ta fara tsatsafo masa a jiki, saida na tabbatar ya razana sannan na kaɗa kaina ina wucesa, kai tsaye Side ɗina na wuce ina shiga na sauke wata nannauyar ajiyar zuciya sakin da Alhaji Muttak'a yai man ji nake kamar anyi man Albishir da gidan Aljanna, ji nake dukkan wani nauyin daya danne zuciyata ya ragu, wani kalar farinciki na tsinci kaina a ciki, saidai matsalar ɗaya ce yanzun "nikam ina zan dosa?," na tambayi kaina don bana son ƙara shiga cikin Al'umma ballantana na ɗauki rayuwan wani shiyasa zan nisanci mutane na koma a jeji da zama don hakan shine zai fiye mani Alkhairi

*Nuraim* kuwa tunda motarsa ta birkice kansa ya bugu sosai har yai sanadiyar tsagewa jini na malala a hankali tsiraran mutanen dake wajen suka fara kawo temakon gaggawa wanda da ƙyar aka samu damar cirosa daga cikin motar babu alamar numfashi a tare dashi, ga kansa dake ta zubarda jini, da sauri aka ɗaukesa aka nufi asibiti dashi, kai tsaye Emergency room aka shiga dashi, wayar da aka zaro daga Aljihunsa aka fara duba Number ɗinda ya kira ta ƙarshe ita ce aka kira,

lokacin Jabir yana tuƙi saida akai masa kusan 3 miss call sannan ya lura don kwata_kwata hankalinsa baya tare dashi, zaro wayan yayi yana dubawa yaga Number Nuraim da sauri ya danna kira, yana kira aka ɗauka yaji ana cewa mai wayar ne yai Accident idan ɗan uwansa ne yazo ana buƙatarsa, "Innnalilahi wa'inna ilaihirraji'un," shine abinda Jabir ke maimaitawa hankali a tashe yace su faɗa masa wane asibiti ne, nan suka faɗa masa, da sauri ya datse kiran gabansa idan banda dukan ukku_ukku babu abinda yake tabbas ko tantama baya yi wannan shirine aka shirya masu shida Nuraim shi an tura kashesa shi kuma Nuraim an haɗa masa hatsari, da hanzari ya nufi Hospital ɗin

Kafin kace me su Mommy sun shigo suma hankalinsu ba'a kwance ba ciki kuwa harda Nafisat dake kukan munafurci, saidai tana ganin Jabir gabanta ya faÉ—i "to shi ya akayi wannan bai mutu ba? shida naso ace ya riga Nuraim mutuwa." ta tambayi kanta

sun daɗe nan zaune kowa jirin_jirin zuciyoyin nata bugawa ba barema Mommy wacce dauriya kawai take Hameeda kuwa sarkin rashin dauriya tuni take kuka,ga wani babban tashin hankalinnasu anata kiran wayar Abdurrahim tana ringing amma ba'a ɗauka ba, Dada ce ta shigo da gudu daga ita sai bujen tsahhi na ciki, zane a hannu tanata sharɓan hawaye, Baba Salihu da Mama Sharifa nata rarrashinta, tana zuwa ta faɗa jikin Mommy ta sake fashewa da wani matsanancin kuka tana faɗin "Faɗima ki faɗa man me ya samu Nura ake faman ɓoye man kardai ki ce man mutuwa yayi," da sauri Mommy ta ɗagota itama hawayen nata na ƙoƙarin zubowa tai ƙoƙarin dannewa ta ce "Dada Nuraim ba mutuwa yayi ba hatsari ne yayi ki kwantar da hankalinki insha Allah zai tashi."

Doctor ne ya fito yanata faman sharce zufa da hanzari Dada ta miƙe tana cewa "kai likita ya jikin Jikan nawa da sauƙi dai ko." wata zufar ya sake sharewa fuskarsa ɗauke da matsananciyar damuwa ya kalli Dada yana faɗin "Iya tabbas Allah shine ke rayawa kuma ya kashe wanda yaso babu abinda zance maku saidai haƙuri domin kuwa Allah........," bai ida ƙarasawa ba Dada tai tsallen ƴan bori ta cakumo kwalar likita tana falla masa mari sannan ta ce "kai likitan nasara ƙwalbatin ubanka nace, kada ka kuskura ka tunzura zuciyata na ci buhun ubanka yanzun, yoo dama ai munsan Allah shike rayawa kuma ya kashe wanda yaso, to kada ka kuskura ka ida hassala zuciyata yanzunnan nai maka abinda babu daɗi, harda wani cemin Iya, ka faɗa man wane ɗan tsako na taɓa ƙyanƙyashewa harda zaka kirani iya." ta faɗa tana sakin huci kamar wata kumurcin Maciji, Baba Salihu ne yazo ya dinga bama Dada baki da haƙuri harta saki likitan da ya fara jin azaba duk idanunsa sunyo waje saboda Dada ba ƙaramin shaƙarsa tayi ba, haƙuri su Mommy suka bashi, sannan ya ce su biyoshi Office don Dada bazata bari suyi magana a tsanake ba

*Raheenatu*

duƙe take tana kuka da wuƙa a hannunta ga Alhaji Bashir kwance cikin jini wata kalar ƙara ta ƙwalla tana girgiza kai,da sauri aka banko ɗakin ana shugowa saidai turus Hajiya Bilkisu tayi tana yadda Cup glas ɗin dake hannunta hankali a tashe ta kalli Raheenatu hawaye na zubowa take faɗin "Raheenatu kashe man miji kika yi, meya aikata miki da zaki kashesa? shan ƙwayar ki harya kai ga kisan kai, to wallahi yanda kika kashesa nima saina kasheki," ta faɗa tana nufo wajen Raheenatu a fusace wuƙar dake hannun Raheenatu ta amsa zata caka mata,kamar an wullo Sabreen tai saurin zuwa tasha gaban Hajiya Bilkisu tana riƙe hannunta ta ce "me kike shirin aikatawa ne? so kike kema a kasheki ne ki bari doka tayi aiki akanta."

Wani kalar matsanancin kuka mai ban tausayi Raheenatu ta fashe dashi tana faÉ—in "wallahi bani ce na kashe miki Miji ba, taya kike tunanin zan kashesa? amma Allah ne shedata."
Chapter 6 · 0% Book details