← Book details Rushewar Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 24

Sashe 11

Rushewar Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hannuna na miƙa mata da ƙarfin gaske ta riƙeshi kam sannan cikin muryanta mai daɗin sauraro take raira wata kalar waƙa mai daɗin sauraro wacce ta saka jikina tsima, daga bisani kuma tai tsit tana shesheƙar kuka,tana ƙara matsa hannuna, ƙara ɗago fuskata nayi ina kallonta a dai_dai lokacin itama ta ɗago da tata fuskar tana sakar mani murmushi, kallonta nake sosai ganin yadda take masifar kama da Abba har murmushin da tayi sai nake ganin tamkar Abba ne yayi shi

"wacece ke" tambayar data fito daga bakina kenan ina sake dubanta, nuni tayi man dana zauna, zama nayi sannan ta ƙara matse hannuna kam tana kallona ta ce " Raihana ba zaki sanni ba saboda na kasance mai son zuciya,ni ɗin sam ba tagari ba ce,na kasance mai zaluntar al'umma, saboda son zuciyata nabar mijina da ƴaƴana, tabbas da ace na kasance tare da ƴaƴana da ko kaɗan bazan taɓa bari ki shiga wannan rayuwar ba" ta faɗa tana mai sake zubar da hawayen nadama

Sosai Tsohuwar ta bani tausayi, hannuwana na saka ina share mata hawayen, zoben dake hannunta naga ta ciro ta kamo hannuna ta saka mani ta ce "Raihana ga wannan shine zobena, wato zoben JUWALA, kije ki riƙe zaiyi maki amfani sosai"

"dama ke ce Juwala? Maman Abba, kina raye ne dan naga ke bakiyi kama da ruhi ba, yanayinki ya tabbatar mani da É—aureki aka yi na tsawon shekaru" na faÉ—a ina sake kafeta da idona

"Tabbas ni ba matatta bace ina raye ban mutu ba, saidai tsawon shekaru 20 na kasance É—aure anan saboda wani gagarumin laifi dana aikata wanda aka yanke man shekara 20 a ma'adanan ruhika"

"To amma me yasa kika gayyato ni anan"

"saboda ina buƙatar na taimaki jinina sannan ina buƙatar ki taimaki Mahaifinki da ɗan uwanki saboda suna a hannu macucin Mutum azzalumi, wanda shine wanda ya lalata miki rayuwa,shine wanda ya sace mahaifiyarki yake azabtar da rayuwarta, Mahaifiyarki na raye tabbas ba Mutuwa tayi ba, a halin yanzun dukkan Alhakin ceton rayukansu suna a wuyanki, zoben dana baki shine zai baki damar tunkararsa,sannan ruhin Saddiƙa da aka cire maki shi zai ƙara taimaka miki"

ko kaÉ—an banyi mamakin jin cewar Ammi na raye ba,saboda dama can ni ban yadda da mutuwa tayi ba, "amma ta ina zan gane mutumin da kika faÉ—a, waye shi? a cikin su Baba Sa'adu"

"ko kaɗan baya cikin su Sa'adu, wanda kuka yarda dashi kuka aminta dashi,shine ya daɗe yana cin dunduniyarku,kuma ba kowa bane face Modibbo,shine Jogu ɗin da kika sani,wanda yake ɓoye maki murya da kuma fuska"

cikin tsananin ruÉ—ewa na tashi ina faÉ—in "Wallahi ba dai Modibbo ba ki sake tunani, nasan ko kaÉ—an Baba Modibbo bazai kasance mai zaluntar mu ba, saidai ciki na tabbata Sharu ko Sa'adu"

"cikin daka tsawa ta ce tabbas kinyi wawan tunani,abinda na faɗa miki shine gaskiya, fitar da ita daganan ka mayar mata da baƙin ruhinta" ta faɗa da alamun ɓacin rai

magana nazo yi mata amma wannan halittar ya daka man tsawa yana fizgoni ya jefar dani a wajen yana fesa mani wani turare, ruhin da aka cire shine ya dinga dawowa, har ya shige a jikina,niko sai burburwar azaba nake,

zafin ranar da naji yana dukana shine ya saka ni ware idona a hankali harna buɗesu duka,miƙewa nayi da mamaki ganina kwance cikin dokar daji, "kenan dukkan abinda ya faru jiya da daddare da gaske ne?" na tambayi kaina

da mamaki na ida miƙewa tsaye duban jikina nayi na ganni daga ni sai ƴar ɓigilar rigar bacci wacce na saka ta Hameeda, a hankali na buɗe bakina ina karanto wasu ɗalasiman tsafi waɗanda zasu mayar dani gida, ina gamawa na buɗe idona na ganni bedroom,murmushi na saki ina shigewa Toilet dan yin wanka da kuma Arwalla,

ɓangaren Mommy da Hameeda sai sintiri suke saboda tunda Hameeda ta tashi bata ga Raihana a inda ta kwanta ba har tai sallar asuba ta koma bacci, koda ta tashi wajen 11:30 bata ganta ba, ga Nuraim ya fita Office an kira wayarshi bata shiga, Mommy ce ta kalli Hameeda ta ce "kodai ki ƙara zuwa ɗakin ki duba"

da to Hameeda ta amsa tana hawan sama zuwa bedroom d'inta, tana shiga taji ƙaran ruwa hakan ya sakata sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, zama tayi bakin bed ɗin tana jiran fitowar Raihana,

fitowa nayi É—aure da towel, kallon Hameeda nayi dake zaune na sakar mata Murmushi, hararan wasa tayi min tana faÉ—in wai ina kika je ne? nake ta faman nemanki har hankalimmu ya tashi nida su Mommy"

cikin yanayin damuwa na dubeta na ce mata zan faɗa mata inda naje, shiru tayi bata sake tambayana ba, cikin kayan da su Mommy suka siya man na ɗauko wata haɗaɗɗiyar gown baƙa mai kyau wacce taci adon white stone, na saka sosai tayi man kyau, lotion na ɗan murza da turaruka na saka Hijab ina kabbara Sallah, ina sallamewa istigfari kaɗai nayi ko salati banyi ba na miƙe,ina cire Hijab ɗin

"amma me yasa baki Addu'a Raihanatu? Hameeda ta tambaye ni, kallonta nayi ban ɓoye mata komai ba na faɗa mata ƙwalla ta share ta ce "Raihana Allah ya fitar dake daga wannan halin, idan kin gama ki safko ƙasa kici abinci, kuma Hamma Nuraim ya ce ƙarfe 2:00 zai dawo zaku je wani wuri dashi da Mommy"

da to na amsa mata na ce ta jira ni mu fita tare, gyara gashina nayi nai parking ɗinshi, ko powder ban shafa ba na ɗauki veil ɗin nayi roning ɗinshi, feshe jikina nayi da turaruka, ɓata fusaka Hameeda tayi ta ce "haba Raihana kalli fa ko Powder baki shafa ba naga baki son shafa powder,to gaskiya ki shafa" ta faɗa tana turo baki

dariya nayi nace "to Æ´ar uwar Raheenatu" itama dariya tayi ta ce "ni kam naso naga Raheenatu É—innan" murmushi nayi na shafa powder da É—an kwalli sai lip gloss,muka sabko

Mommy muka samu zaune ta zuba tagumi, tana ganimmu ta saki wata nannauyan ajiyar zuciya, ta ce "Ƴar Mommy ina kika shige ne kika tayar mana da hankali"

"Mommy yunwa nake ji idan na ci abinci zan faɗa maki" na faɗa ina mai nufar dinning nida Hameeda, sosai na zage na narƙi abinci har Hameeda na man dariyar mugun cin da nayi

Mommy kam sosai take jin daɗin yadda Raihana ta ƙara sakewa da su yadda kasan tayi wasu shekaru a wajensu, don kullum tana maƙale jikin Mommy duk yadda Raihana bata da ɗimi ta zauna kusa da Mommy sai tayi mata surutu, Murmushi Mommy tayi ta ce "ƴar Mommy zo ki faɗa mana inda kika ɓuya muke ta nemanki"

babu abinda na ɓoye mata na faɗa mata dukkan abinda ya faru dani harna gwada mata zoben dake hannuna, sosai Mommy ta shiga damuwa,kuma wani ɓangaren tayi farincikin jin cewar ƴar uwarta na raye, amma jin cewar hannun mugun mutumin da take shine yafi ɗagar mata da hankali , ganin damuwar data shiga shine ya saka ni kwantar mata da hankali akan cewar zan ceto rayuwarta insha Allah

bayan munyi sallar Azahar sai ga Hamma Nuraim dashi da Abdurrahim sun shigo, jugum_jugum suka samemu suna tambayar mu abinda ya samemu mukayi sukuku, kamar yadda na faÉ—awa Mommy haka itama ta faÉ—a musu, kwantar mata da hankali sukayi

ko cin Abinci Nuraim bai tsaya yi muka tafi wajen Baba......✍️

wanna kenan

*Comment, Share fisabilillah*

Waɗannan su ne ƙwarin guiwata

*By Riamcool Hasken Royal star✨🌟💫✨💫*

*08109554986*
[2/6, 5:51 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA*

*Book 2*

*By Mariam sani Riamcool*

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*

*Bismillahirrahmanirrahim*

*Page* 86&87

____________Gudu yake shararawa sosai don tunda yaji abinda ya faru da Raihana yau hankalinsa ya sake tashi da lamarinta, babu abinda yake so sama da yaga Raihana ta fita daga cikin wannan rayuwan, da tunane_ tunane ya ratsa dajin yaci gaba da gudu

nikam ina ganin ya shiga dajin kaina yai wani irin sara man a hankali na lumshe idona bacci na ɗaukana, kwanciyar Mommy ta ƙara gyarawa Raihana jikinta yai sanyi ƙalau, a haka har suka isa cikin ƙungurmin dajin parking Nuraim yayi ya fito, sannan Mommy ta fito, tana kallon inda suke, ganin Raihana na bacci yasashi ɗauko ruwa a hankali yana shafa mata a fuska, a hankali na dinga buɗe idona harna waresu duka akanshi, miƙewa nayi na kalleshi ina turo masa ɗan mitsilin bakina, dan haushin tadawar da yayi man naji, kafeni yai da ido yana ƙara haɗe ranshi, wai irin karma ta fara rainashi tun yanzun ƙara shima ya ɗan ja mata aji, da hannu yai mani alamar dana fito

fitowa nayi ina ƙara jin haushin haɗe man ran da yayi, ƙara turo bakina nayi ina wucewa wajen Mommy, "ƴar Mommy lafiya dai ko, ko wani abun Hamman naki yayi maki?" Mommy ta tambaya da kulawa

kallonshi nayi sannan na kalli Mommy na ce "Mommy babu abinda yai man kawai baccin ne ban ƙoshi dashi bane, kuma mamadin ya ɗan bubbuga man ƙafa amma saiya shafa man ruwan a fuska" na faɗa a ɗan shagwaɓe

yanayin yanda tayi maganar yasa shi jin wani yar, ga É—an bakinta da take turowa duk sai ta sakashi shiga cikin wani kalar yanayi, cikin kasalalliyar murya yace "muje Mommy"

shiga gaba yayi muka dinga binshi wajen baka jin motsin komai saina tsuntsaye da kaɗawar ganyen itatuwa, haka muka dinga tafiya a ƙasa har muka iso wani kogo, wanda kallonshi da nayi saida ya saka kaina juyawa, Hamma Nuraim ne ya fara shiga, sannan
muma muka shiga wani kalar ƙamshin turare ne wanda a take ya ƙara hautsina man kai, waje muka samu muka zauna ina ƙara ƙura ma Dattijon dana gani ido, da sauri na janye idona daga kansa, gabana na wani irin bugawa, sadda kaina ƙasa nayi na gaishesa a ladabce, amsa mani yayi da murmushi a fuskarsa
Chapter 11 · 0% Book details