← Book details Rushewar Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 24

Sashe 2

Rushewar Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kallonta Nuraim yayi yana sakin Murmushi yake faɗin "to Alhamdulillahi da Allah Ubangiji ya bayyanar mana daku cikin sauƙi,ashe dukma ana kusa,yanzun ina Ammin tamu take?."

hawaye na sake sharewa ina faÉ—in "Ammi yanzun bata tare damu ta tafi ta barmu.....," "ina Sajeeda ta tafi? Kardai kice man Sajeeda mutuwa tayi don Allah,kada ki faÉ—a man kalmar da bazan iya É—auka ba," Mommy ta faÉ—a a kiÉ—ime,kallonta nayi wasu sabbin hawayen na saken bin kuncina, "ko zamu iya sanin tarihinki da abinda ya samu Ammi?," Hameed dake zaune ya faÉ—a,kallonshi nayi ina É—aga masa kai sannan na ce,

*WAIWAYE*

"Asalin mahaifina ɗan Niger ne,mahaifansa Safiyya da Usman Toro sune suka haifi Abba,waɗanda dukkansu bazan iya kiransu dana kirki ba,saboda dukkansu sun kasance masu zubar da jinin Al'umma ta hanyar tsafi,saboda Juwala Safiyya itama ba ƙaramar matsafiya bace don tafi Toro iya tsafi saboda ƙwarewarta a tsafi ma yasa Toro auren Juwala,koda sukayi aure basu wani daɗe ba Allah ya azurta su da samun ɗansu na farko Baba Sa'adu,daganan kuma sai Baba Sharu daganan kuma sai ta samu ciki, wanda Toro a lokacinne ya ce zai ƙara aure,Juwala bata wani damu ba saboda ita ba wani miji bane a gabanta abinda tasa a gaba kawai shine harkarta ta tsafi,koda aka auro Aishatu itama dai ba wata ta kirkin Toro ya auro ba saboda itama cikin ƴan ƙungiyarsa ta tsafi ce ya auro,ga rashin imani a zuciyarta,haka dai Juwala da A'ishatu sukayita zaman doya da manja dan babu mai shiga harkar wani a haka dai Juwala ta haifi Baba Khabir bayan ta haifeshi ne ta ƙara samun wani cikin wanda itama ashe Aishatu na dashi,saida Aishatu ta haifi Baba Nazeer wato Modibbo,sannan itama Juwala ta sake haihuwar Abba Wanda aka raɗa ma suna Nuraddeen,da ganan kuma ta ƙara samun ciki wanda Toro ya ce shifa ya gaji da haihuwar da take masa hakanan wanda ya hassala zuciyar Juwala har takai ga sunyi gagarumin faɗa,wanda takai ga Toro sakin Juwala, daganan ne ita kuma Juwala tayi zuciya ta ce ko ƴaƴanta bazata sake waiwaya ba kamar yadda tabar cikin Mahaifiyarta ita kuma haka zata bar ƴaƴanta da Toro,wanda wannan abu ba ƙaramin farinciki yasa Aishatu ba,haka Juwala tai nesa da Toro taje taci gaba da rainon cikinta,har Allah yasa ta haifi ɗanta Baba Sule, lokacin itama Aishatu nada ciki,bayan watanni sai gashi Allah ya azurtata da ƴarta mace Saddeƙa,haka yaran Juwala suka tashi babu wani mai kula dasu don Aishatu bata wani shiga sha'aninsu Nuraddeen ne kaɗai ta ɗauka tamkar ɗanta wanda ya taso komai a wajenta yakeyi,hakan yasa sukayi muguwar shaƙuwa tsakanin Nuraddeen da kuma Modibbo wanda suka taso cikin ƙaunar junansu,wanda ko wanda suke ciki guda basa masa ƙaunar da Modibbo ke masa,hasali ma su basu wani damu da ƙanen nasu ba,kowa sha'anin gabansa yake,haka Toro yaci gaba da koyawa yaransa harkar tsafi,wanda Modibbo da Nuraddeen,suka feɗare masa suka ce sam su bazasu koyi tsafi ba,wanda Aishatu ta goyi bayansu,wanda da kanta ta saka su makarantar boko,suka ci gaba da karatu,saidai kuma ƴarta Saddiƙa tun tana ƙaramar yarinya ta kasance wata feɗararrar yarinya marar tausayi da Imani,wanda ta samu farin jini sosai a wajen Toro da kuma su Baba Sa'adu wanda a hankali suka fara koya mata harkar tsafi tun tana ƴar ƙaramarta,wanda ba ƙaramin ɗaci zuciyoyin su Nuraddeen da Modibbo sukayi ba ganin kalar gurɓatacciyar Rayuwar da ƴan uwansu Da Mahaifinsu suka ɗora masu ƙanwar tasu wanda babu yadda basuyi ba akan suga sun dakatar da ƙudirin Mahaifinsu,saidai abin yaci tura, Saddiƙa kuwa ganin Modibbo da Nuraddeen sun takura mata yasa tai masu wata muguwar tsana, wanda suma ko kaɗan basa jituwa da ita ko kaɗan,don ko Mahaifiyarta Aishatu ta gagara,kullum Aishatu cikin baƙincikin ganin halinda ƴarta ke ciki take, Saddiƙa kuwa kullum lamarin nata ta'azzara yake,haka su Sharu Khabir Sa'adu suka taso cikin gurɓatacciyar Rayuwa,wanda kowane a cikinsu burinsu bai wuce ace sun gaji Mahaifinsu ko Mahaifiyarsu Juwala,ganin Saddiƙa tai musu fintinkau a harkar tsafin yasa suka saduda,sai kuma Sharu ya biyo bayanta ganin hakane yasa Saddiƙa kula Sharu suna tsafikansu a tare,wanda har takai sun fara ajiye baƙaƙen Aljannu da kuma ƙananun Dodanni tsafi, lokacinne kuma Nuraddeen ya gaji da halayyar ƴan uwanshi ya tattara nashi ya nashi ya bar ƙasar Niger gaba ɗaya,wanda babu yadda baiyi da Modibbo ba su taho tare amma ya ƙiya,dole yasa shi barin ƙasar Niger ya komo Kano da zama wanda ya bazama neman ilimin boko dana Arabi, ganin zaman baiyi masa ne yasaka shi zuwa kasuwanni yana dako don ya samu ɗan abinda zai saka ma cikinsa,a haka har ya samu wani shago yana zama ana biyansa...........✍️

*Wannan kenan*

Comments Share fisabilillah

Wadannan su ne ƙwarin guiwata

*By Mariam sani RIAMCOOL*

*08209554986*
[2/6, 5:51 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA*

*Book 2*

*By Mariam sani Riamcool*

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*

*Bismillahirrahmanirrahim*

*Page* 66&67

____________✍️ "Cikin hukuncin Ubangiji yana zama yana samun abinda zaici har ya dan dunga samun na kashewa,a haka yaci gaba da zama shago shima a hankali Allah ya bashi ikon nashi nakansa,yana nan Kano da zama yaji gaba ɗaya garin Kano ya fice masa a rai,dole yasa ya tattara yanashi_yanashi ya bar garin Kano ya koma Katsina da zama,nan ma ya buɗe shagon yana zama kuma yana karatunsa a Funtuwa,bayan ya kammala karatunsa ne a makarantarsu ya haɗu da Safara'u,suka ƙulla soyayya,har Allah Ubangiji ya bashi ikon aurenta,suka zauna anan Unguwar yari, saidai Safara'u tanada wani boɗaɗɗen hali wanda baza ka taɓa gane mata ba,sai ka zauna da ita,tunda Nuraddeen ya aureta ta fitineshi da masifa da jaraba,komai ya kawo mata bata godewa saidai rainuwa,gashi ta riga da ta rainashi bata jin maganarsa ko kaɗan,shi kuma gashi dama can bai iya masifa ba shiru_shiru yake,koda ta ishesa da masifa saidai kawai ya fice ya bar mata gidan, haka ya dinga rayuwar ƙunci da Safara'u, koda ta ishesa ya yanke hukuncin ƙara aure ko zai huta da jarabarta,haka ya shiga neman auren ƴar maƙwabcinsa Karime har aka bashi ita,ranar da Safara'u taji zai ƙara aure ba ƙaramin tashin hankali akayi ba don tayi rantsuwa ta maya ta ce duk ranarda aka kawo Karime sai an ɗauki gawarta

haka aka ɗaura mashi aure da Karime yarinya nutsatstsiya bata da kwaramniya ko kaɗan,hakan yasa Nuraddeen jin daɗin zama da Karime,ana nan kwatsam wata rana saiga wata matashiyar budurwa ta shigo wujiga_wujiga tana neman temako,ganin halinda Matashiyar nan take ciki ne yasa Karime Temakonta,ta bata abinci da kuma masaukin da zata kwanta,koda Nuraddeen ya dawo saiga Safara'u ta fito tana masifar an kawo masu Aljana cikin gida an girke to wallahi kodai ta fita ko kuma ita ta tafi ta bar musu gidan, Nuraddeen da baisan kan zancen ba ya tambayi,Karime abinda ya faru,nan ta zauna ta faɗa masa kan temakon da tayi ne, Karime yasa ta kirawo masa budurwar,tunda ta fito ya kafeta da idanu,ganin tsantsar kyawu kamar Aljana don koshi kansa bai yarda da cewar Mutum bace yafi yarda da cewar Aljana ce,koda ta fito ya tambayi sunanta,cikin gurɓatacciyar hausarta ta ce masa sunanta Sajeeda kuma ita batada kowa iyayenta hatsari sukayi duk sun mutu gashi ita bata san kowa a Nigeria ba

Sosai Nuraddeen da Karime suka ji tausayinta, Nuraddeen ya bata É—aki guda a cikin gidansa donta zauna,saidai Safara'u tunda taga Sajeeda take jin wani uban haushinta,haka komai na gidan sai tace Sajeeda ita zatayi shi hatta da wankin kayanta Sajeeda keyi,saidai ita Sajeeda bata wani damu ba saboda tayi bautar da tafi wannan,koda Safara'u taga wannan bautar da take yi mata bata damuwa,sai tajanza ta dawo horata da yunwa da kuma gori da cin mutumci,Karime na gani ba halin yin magana don itama Safara'u bata raga mata ba,me gidanma kanshi ba wani taga masa tayi ba shiyasa kowa yake binta a sannu

Tunda Sajeeda taga abinda Safara'u ke mata ta yanke hukuncin guduwa tabar gidan don bazata iya zama a gidan ba ko don horon yunwar da Safara'u ke mata,saidai da tazo guduwa saita fasa,don tasan ta gudu duk aikin da take yi zai dawo kan Karime,ga Karime ba lafiya gareta ba yanzun,hakan yasa ta haƙura da guduwar ta zauna,ana nan kwatsam sai ciki ya ɓullowa Karime wanda Safara'u taji zafi da haushin samunsa ta bazama bin bokaye da malamai,don ganin cikin jikin Karime ya zube amma sai Allah bai yarda ba,saidai Karime kullum cikin zubda jini take,wanda anyi maganin har an gaji ga kullum cikin ciwo take,haka cikin jikinta ya isa haihuwa amma shiru babu haihuwa har yakai shekara bata haihu ba,kullum cikin magani ake,ana haka wata rana saiga naƙuda ta taso gadan_gadan,koda Karime tazo haihuwa da tayi wani motsi sai gaɓar jikinta ta kare, koda akaga abinda ke faruwa aka yanke yi mata C S kawai,haka Nuraddeen da Sajeeda suna ji suna gani akayi mata tiyata,anyi nasarar fiddo jaririyar saidai abin mamaki itama kamar yadda mahaifiyarta ta kare itama haka Jaririyar gaɓɓan jikinta suka kare, haka Karime tasa aka kirawo mata Nuraddeen da kuma Sajeeda koda suka zo ta ɗauki hannayensu ta haɗa ta ce don Allah Nuraddeen yayi mata Alƙawarin auren Sajeeda don tasan ko bayan ba ranta Sajeeda ita ce zata maye masa gurbinta,ya temaka ya ɗaukar mata wannan Alƙawarin ko ba komai zata mutu cikin farinciki.

Tunda Sajeeda taga yanayin da Karime take taketa faman kuka,bata ida shiga tashin hankali ba saida Karime ta ce ta auri Nuraddeen, taya zata auri Nuraddeen? mutumin da ko gaishesa tayi da ƙyar yake amsa mata,kuma gani take idan ta auri Nuraddeen kamar taci amanar Karime,kallonta Sajeeda tayi tana faɗin "don Allah Karime ki janye wannan alƙawarin don bazan iya cin amanarki ba na aurar miki miji," ta faɗa tana sakin kuka

Murmushi Karime tayi mata tana faɗin "Sajeeda in har kina son na mutu cikin farinciki don Allah ku cika man ƙudirina ku auri junanku,don nasan ke kaɗaice Macen da Nuraddeen zai samu kwanciyar hankali,ki taimaka ki cika man wannan mafarkin nawa dana daɗe ina son ganin ya cika,"

Kama hannunta Nuraddeen yayi yana faÉ—in "Karimatu bama zaki mutu ba insha Allah,bana son kina wannan zancen,"
Chapter 2 · 0% Book details