Sashe 21
Rushewar Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wanka mukayi wanda shi yai mani nima nai masa, wanda sai da ya fara laguda ni tun a can, a tsorace na shirya don ina gudun karya sake, koda muka kwanta nasa ba zai man komai ba amma haka ya zage yai abinsa,wanda na yau ma naji jiki, saida muka tsarkake jikimmu sannan muka kwanta,
*Canada*
Kaykkyawan matashi ne ajin farko ke harhaɗa kayansa tunda hankalinsa ya dawo yake tunanin gida da ƴan uwansa, yake kuma tunanin abinda ya kawo sa ƙasar nan shi dai ba zaice ga taƙa maiman abinda ya kawo shi nan ba saboda ba zai iya tunawa ba, dukkan wani abu nashi da yasan mai muhimmanci ne haka ya tattara ya baro ƙasar sai Nigeria, ganin duk inda ya nufa ana girmamasa saboda zamansa Young millionaire, da ƙyar ya tuna inda suke da zama, hakan yasa shi nufar Goriba road, sai dai tunda ya nufi gidan yaga sauyi da dama, zuciyarsa na masa dukan ukku_ukku yasa shi tunkarar gidan, mai gadin ya miƙawa hannu yace yana son ganin mai gidan tsammaninsa ko su Abba na nan, babu musu mai gadi ya isar da saƙo,wanda ba'a daɗe ba sai ga wani mutum ya fito, da mamaki Fauzan ke kallonsa, mai gadin ya kalla yace "kai cewa fa nayi kayi mani sallama da mai gidan" "bawan Allah to ai nine mai gidan" gaban Fauzan ne ya faɗi yace "ina fa nufin Alhaji Nuraddeen"
mutumen ne ya dafasa yace "kaga ni ban wani san wani Nuraddeen Ali ba, siyen gidan nan, waÉ—anda kake nufi tuni suka tashi"
dafe kansa yayi dake masa ciwo ya ɗaga kan yana shigewa Motarsa, wani iska mai zafin gaske ya furzar yana wa motarsa key, kai tsaye gidan su Baba Sa'adu ya wuce, sosai su kayi mamakin ganinsa, wanda da ƙyar suka ganesa, dukda hantar cikinsu ba ƙaramar kaɗuwa tayi ba ganin yadda Fauzan ɗin ya zama wani attajiri
Jikunnasu a sanyaye suka tarbesa suka tabbatar da lallau Nuraddeen yai musu fintinkau da zarra, babu kamar Sharu shine jikinsa yai sanyi sosai,kamar wani abu bai taɓa faruwa ba haka Fauzan ya nunawa su Sharu, nan suke sanar masa ga dukkan abinda ya faru, hantar cikinsa ba ƙaramar kaɗuwa tayi ba jin abubuwan da suka faru bayan bashi nan, sai dai tabbatar masa da cewar suna Abuja hankalinsa ya kwanta
haka washe gari yabi Flight ya tafi Abuja gidan Modibbo, sai dai tunda yazo get ɗin gidan ya tuna dukkan abinda ya faru dashi da kuma gidan daya gani, da kuma mutumen dake ciki wanda yake masa kallon Mahaifinsa, shine ya kaishi England yayi karatu akan business har Allah ya kawo shi a wannan matakin inda yake da babban Company a can ƙasar Canada, sai dai ganin gidan a ƙargame babu alamar mutane a ciki yasa shi tambaya sai dai abinda aka faɗa masa yai matuƙar kaɗashi, haka yasa aka kaishi inda Modibbo yake, wanda yanzun ya sake birkice musu da ihun da yake
yana ganin Fauzan yayo kanshi da gudu jikinsa duk farfashe da ciwon daya jiwa kansa, cikin ƙaraji yace "Fauzan kada kace gurina kazo ni ba Mahaifinka bane, nine na tsafa kanwarka Raihana sanna kuma na sace Mahaifiyarka na azabtar da ita nai mata ciki muka haifi ɗiya, sannan kaima daga baya na saceka na ɓatar maka da hankali, ƙanwarka Raihana tazo ta gudu da Babanka ka bada cigiyar su a garinnan nasan tana nan ni ɗinnan mugu ne ɗan shan jini ne, idan baku yarda ba kuje gidana kuyi bincike zaku ga kawunan mutane da kayan tsafi, Ihuuu ku ceceni ku kasheni kawai kada ku barni, wallahi kisan gilla zatai manj idan ta dawo, Ihuuu jama'a ni ɗan shan jini ne, idan baku kasheni ba zan kashe kaina na cinye zuciyata" ihuu yake tuɓuru da kururuwa yana ɓarke kayan jikinsa yana cizon kansa sanna yaje ga bango ya dinga buga kansa
Ƙasa tsayuwa Fauzan yayi ya sulale ƙasa yana mayar da numfashi kamar wanda yayi gudun tsere zuciyarsa da ƙarfi take halbawa, miƙewa yayi a zuciye zai nufi inda Modibbo yake ya cakumesa ji yake yau idan bai kawo ƙarshen numfashin Modibbo ba ba zaiji salama ba, da sauri Security ɗin wajen suka riƙesa, suma dukda shock daya kama su, na maganganun Modibbo kuma tabbas akwai ƙamshin gaskiya a maganarsa.............
[2/17, 2:24 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA*
*Book 2*
*By Mariam sani Riamcool*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
Bismillahirrahmanirrahim
*P. 104&105*
____________âœï¸Da huci da raÉ—aÉ—in zuciya Fauzan ya fice ya shiga motarsa yana mayar da numfashi, kai tsaye yaje gidajen Radio da television ya bada cigiyar su da sunayensu, haka kuwa aka watsa a labarai da gidajen rediyo
zaune muke nida Hamma na aza kaina a ciyarsa yana wasa da gashina, nikam na maida hankali da Tv ina kallo dukda,hakanan naji son kamo tashar labarai, ina kamowa Abinda na gani ne ya sani miƙewa zaune, ina ƙara kafe Photon saurayin da ido wanda dukda girma da sauyi da kuma yanayin kuɗi ya zauna a jikinsa hakan bai hanani ganesa ba, cikin ruwan murya na furta "Hamma Fauzan" na faɗa da tsantsar farinciki, shima Hamma fuskanshi ɗauke da farinciki yake hamdala da ƙara godewa Allah, daya haɗa dukkan zuri'arsu waje guda, dama abinda yake so kenan, daman Fauzan da Ammi kawai yake jira, ya kai su Mommy wajen iyayensu waɗanda ya daɗe da gano inda suke a zaune
da maɗaukakin farinciki na yana mayafin Abayar bisa kaina zan nufi Part ɗin Mommy, da gudu, riƙeni Hamma yayi yana zaro ido yace "bi sannu fa karki Mani asara Maybe ko nayi ajiya a ciki" ya faɗa da ƴar dariya
nima dariyar nayi ina maka masa hararan wasa nace "duka yaushe akai auren da zakai ajiyar?" dariya yayi yana kama hannuna muka nufi sashen Mommy
koda muka je suma Falon ya rikice da murna, haka muka ɗunguma mu dukkammu muka nufi inda aka bada Address, koda muka je baya nan saida aka kirashi, a gaggauce yazo wanda faɗin iya kukan da farincikin da mukayi ma ɓata baki ne, shi kanshi Abba sai da ya ƙara kukan farinciki da murna ya kuma Alƙawarta ma kanshi cewar yanzu zai bama su Ammi farincikin da suka rasa a baya,
Dada ita kanta sai da tazo tunda aka gano Ammi tazo ta nemi yafiya tace kuma mafarin barin Ammi gidan Aminiyarta ce tai mata kurciya, Ammi bata nuna mata komai ba ta yafe mata, haka Dada ke nan da nan da Mommy dasu Ammi komai tace FaÉ—ima da Sajeeda,haka da kanta zata zo wajen Mommy ayi fira da jikoki ai raha, koda Fauzan da Nuraim suka haÉ—u ashe sun san juna sosai dan Abokan kasuwanci ne sai dai rashin sani, dukda ga kamanni nan dasu Raihana,
sai da Ammi ta gyagije sosai ƙibarta da haskenta ya dawo sannan Nuraim yace su shirya zai kaisu wani waje, haka dukkammu muka shirya muka shiga motoci na Alfarma,
Raheenatu ce zaune kusa da Abdurrahim, shi kam ya kafeta da yana sakar mata wani lallausan murmushi ita kam juya masa ido tayi tana ƙara masa fari da ido, "My beloved kinyi fa kyau sosai" ƙara juya masa ido tayi tace "really" "yeah" ya furta yana kashe mata ido guda ita kuma ta ɗaga masa gira tana dariya
gyaran murya nayi nace "Yaushe abin nan ya faru bamu sani ba, sai dai kullum mu a gabanmu a dinga Æ´an harare harare irin Alamun baku jituwa to ashe kun É—inke" na faÉ—a ina dariya, shima Nuraim dariyar yake
Sosa kansa yayi yana driving yace "ga tanan ki tambayeta, tun ranar ɗaurin auren ki tace man wai fuskana na kama da baƙin ɗuwawu, wai ba kyau gareni ba hakanan take kallona, to nayi niyya na kafta mata rashin mutunci, to ina zuwa zan karta mata rashin mutunci shine ta kashe man ido wanda gabana ya bada dam tai man kwarjini ke Raihana wallahi sai naji tsoronta nake ji, kawai sai nai mata yaƙen dole na fice, washe gari duk inda na ganta sai ta kashe man ido kuma ta girgiza mani ƴaƴan laushi, wallahi nifa na rasa ganewa, sai kawai na dawo nace mu ƙulla ƙawance tace mani Allah ya sawaƙe ta ƙulla ƙawance da ɗan baƙi kamata, ke dan bani da kuma zuciya da yake zuciyata ba'a ƙirji take ba nazo na dinga binta sai da ƙyar muka ƙulla ƙawance, mu ba soyayya muke ba, yanzu haka komi tace nayi zan iya idan cewa tai na faɗa rami da wannan motar da muke ciki tsab zanyi shahada na faɗa"
dariya dukkammu nace "a ƙawancen ne ta zama your beloved ɗinka?" da sauri Raheenatu tace "suɓutar baki fa yayi,amma ga wadanda suka fiddo soyayyar su fili Yaya Fauzan da Hameeda" dariya nayi nace "ai dukkansu ƙwararri ne"
ganin munzo wata katafariyar unguwa ta manyan masu kuɗin da ƴan siyasa, kan wani ƙerarren gida muka tsaya da motocimmu, horn akayi aka wangale mana ƙaton get ɗin muka shige, tsayawa misalta muku kyan gidan da tsaruwarsa ɓata baki ne don saina cika Page guda ban faɗa muku ba, Dada farkon fitowa tana ƙarewa gidan kallo ta kalli Nuraim tace "kai Nura ko dai ɓatan kai kayi? me ya kaika kawo mu nan gidan wanda kana kallon mala'ikun Jahannamar duniya sunyi mana ƙur da idanu, ga gida tako ina gilashi" dariya dukkammu mu kayi Nuraim yace "Calm down Dada biyoni kuga"
harara Dada ta zabza mashi kamar idonta zasu faÉ—o tace "Nura idan ma zagina kayi nasan matsayin da zan ajiye ka yo idan banda lalata ka wani cemin kom dawon, a'a dawo ba dowon ba" ta faÉ—a tana gyara É—aurin zaninta, banza Nuraim yayi da ita yai gaba muma muka bishi a baya
da sallama ɗauke a bakunanmu muka shiga haɗaɗɗen Falon wanda ƙamshi da sanyi Ac ne ke tashi tako ina, zama mukai sannan Nuraim ya hau sama yace bari yazo, ba'a daɗe ba kuwa sai gashi da wani dattijo wanda fara'a da annurin fuskarsa yaƙi ɗaukewa kallo ɗaya zaka mashi kasan cewa kwarjini da haiba da kamala na tattare dashi, dukda farin gilashin dake manne a idonsa, hakan bai hana mu ganin ƙwalla dake cike tab a idonsa ba