← Book details Rushewar Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 24

Sashe 24

Rushewar Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read

driving nake cikin jin daɗi wanda nida Hamma ne na amshi Driving ɗin don bana son Driver ya tuƙamu yau, Abilkhairi ne riƙe a hannunsa ya kafe Raihana da idanu wacce take jin waƙar Zinoleesky a hankali tana ɗan rausayawa dariya yayi yace "Habibte bi a hankali damu kada ki ɓarar damu nan" dariya kawai nayi ina ci gaba da Driving ɗin har muka isa wani ƙaton shopping mall wanda na ɗan tsitstsinci abinda nake buƙata sannan muka nufi wani waje na shaƙatawa wanda wajen baro wajen ne naji an kira sunana wanda cak na tsaya ina juyowa ganin Alhaji Muttak'a wanda na ƙarasa wajensa muka gaisa a mutunce sannan ya tambayeni nayi aure na faɗa masa harma da yara nan na gabatar masa da Nuraim wanda yake ta haɗe fuska, murna sosai Alhaji Muttak'a ya tayani wanda yayi mamakin mashahurin mai kuɗin data aura wato Nuraim, sannan daga gani daɗi da kwanciyar hankali ya zauna mata

Koda muka koma gida da ƙyar na lallaaho Nuraim ya saki fuskanshi daga nan kuma muka faɗa farantawa junammu rai, a hankali rayuwa taci gaba da tafiya cikin jin daɗi da kwanciyar hankali wanda ba abinda zance da Allah sai godiya tabbas na yarda da cewa mahaƙurci mawadaci na yadda da zalunci baya nasara akan gaskiya haka kuma mai haƙuri yana tare da Allah,danni sai dai nace Alhamdulillahi komai nawa ya warware Rayuwata data Rushe ta ginu, babu abinda zance da Mijina sai godiya dan shine matakin dukkan wata Nasara tawa, ni kam sai dai nace Alhamdulillahi

Alhamdulillahi nima dai nace to duka_duka anan na kawo ƙarshen littatafin Rushewar Rayuwa Abinda ke ciki Allah ya bamu ikon Amfani dashi, insha Allah sai mun haɗe ahy sabon zazzafan littafina *BAYAN WUYA* hmm akwai cakwakwiya iya cakwakiya a ciki fatan zaku biyoni kamar yadda kuka biyon a RUSHEWAR RAYUWA, ina godiya mai tarin yawa ga wadanda suka biyoni a wannan littafin much love oll ku sani ba zan taɓa mancewa daku ba ina godiya
Chapter 24 · 0% Book details