← Book details Rushewar Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 24

Sashe 7

Rushewar Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a fusace Sabreen ta ɗaga hannu ta faska mata mari tana ƙara kai mata gula a ciki wacce tasa cikinta yin wani ƙugi tana duƙewa a wajen, kuka su Hajiya Bilkisu da Sabreen suke riris, tuni ƴan unguwar suka cika wajen da Police kowa da abinda yake faɗa donma Police sun tsawata wa mutanen dake ƙoƙarin kashe Rahinatu da bugu, tuni Police suka buga mata Ankwa a hannu suna tasa ƙeyarta ya zuwa Police Station ƴan Jarida da kuma mutane sai ɗaukarta hoto suke, wasu zafafan hawaye masu raɗaɗi da ɗacin zuciya ne suka sabko mata a kumatu tana sadda kanta ƙasa, "Hmmmm rayuwa kenan ashe duk yanda baka
tunanin ƙaddara ita tana nan tana bibiyarka ko kaɗan banyi tunanin rayuwata zata juye daga mai kyau ba ta koma gurɓatacciya, saidai koma miya faru dani ta silar Mahaifimmu ne." ta faɗa zuciyarta na sake tafarfasa

Hajiya Bilkisu kuwa tana can tana kukan munafurci da suman ƙarya, Sabreen ma kukan baikai har zuci ba tunda komai shirinsu ne, haka aka sallaci gawar Alhaji Bashir aka kaisa makwancinsa,

Raheenatu kuwa tana hannu Æ´an sanda suna gana mata azaba sunyi tambayar duniya ta faÉ—a masu me yasa ta kashesa amma sai tace Allah ne shedarta don komi zata ce masu bazasu yarda da ba ita ta kashe Alhaji Bashir ba, shiyasa tun ta jansa kala jikinta duk ya farfashe hannunta kuwa harya samu karaya, idanunta harsun rufe tsabar kumbura da sukayi

.

*Ɓangaren Jogu*

Tsaye yake gaban wani ƙasungumin mummunan halitta mai ban tsoro,ga shima Naseer na kusada shi a zaune da wata kalar murya Jogu ke faɗin "dukda na hau karagar mulkin tsafi a yanzun banida wani ƙarfin ikon da zan iya dawo da mallakar da nayiwa waccan yarinya saboda baƙin ruhin Saddiƙa na a tareda ita, sannan ruhin wacce nake amfani dashi a halin yanzun Saddiƙa ta mayarwa da maishi,ka taimaka man da wani baƙin ikon da zaisa ya zamo kariya a garemu domin hana ɗaukar fansar Uwargijiya."

wani kalar gurnani da nishi wannan baƙin Dodan yayi sannan ya dinga yin wani zance wanda ba'a ganewa, yana gamawa su Naseer suka dubesa a matsanancin tashin hankali suna cewa "ka taimaka ka bamu iko mu kuma munyi maka Alƙawarin kawo maka budurcin mace goma sannan jinin jinjirai goma sannan kawunan tsofi goma indai ka temakemu da baƙin ikonka...........✍️

Love U oll my fans😍

*Aci gaba da Comment ni kuma naci gaba da suɓurɓuɗo maku Typing*

Wannan kenan

*Comment share fisabilillah*

Waɗannan su ne ƙwarin guiwata

*By Riamcool*

*08109554986*
[2/6, 5:51 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA*

*Book 2*

*By Mariam sani Riamcool*

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*

*Bismillahirrahmanirrahim*

*Page* 76&77

_____________✍️wani kalar dariya mai haɗe da gurnani mai tsoratarwa Dodan yayi, wannan ke nufin ya riga da ya amince zai basu baƙin ikon, wata ƙatuwar ajiyar zuciya suka saki gaba ɗayansu

*London*

Zulfa'u ce sanye da wani arnen white jeans daya kamata tsam duk a farfashe, da ƴar ɓingilalliyar Top wacce da kaɗan ta sauka a cibinta,ga gashin dokin data saka a kai ya wani zubo mata har ƙugunta,sai zaƙo_ zaƙon farcen kanti da aka saka mata a hannu sunsha pentin light pink color da kaganta kai bazaka ce tasan wata kalma ta musulunci ba ballantana har akirata da musulma , a hankali tasa hannunta ta buɗe ƙofar wajen ta shiga ciki

haɗaɗɗen eatery ne,wanda wajen babu wasu mutane da yawa,yawancinsu duk turawa ne, tafiya take tana wani murguɗa ƙugu tana girgiza boobs ɗinta,wanda yaja hankalin turawan wajen, kai tsaye wajen wani guy choculate color ta wuce da pipe ɗin shisha dake riƙe a hannunsa yana taja yana fitarda hayaƙi ta hanci ta baki ga wasu ƴam mata suma duk a zaune suna jan shishar, tana zuwa ta faɗa jikin saurayin nan tana sumbatarsa, ta ce "How are You Sweet darling?, two day I missed U over, it is I come coved you," ta faɗa tana sakinsa

wani kallo yai mata irinna Æ´an iska ya ce mata "You know i'm not time always da zan dinga biye miki muna harka kullum kamar wasu dawakai." ya faÉ—a yana jan wani siririn tsaki

wani ƙululun takaici ne ya kama Zulfa'u ganin irin wulaƙancin da Ma'aruf yayi mata gaban su Zeey da Billy, amma saita shanye, itama ta janyo pipe ɗin shisha tana ja,cikin ƴam matan babu wanda ya ce da ita ƙala ganin itama basu tanka ta ba, order Ma'aruf yayi musu suka ci suka sha sannan kowa ya kama gabanshi ya tafo da Zulfa'u dukda fushin da takeyi, haka ya rarrasheta domin yana son ya kashe arna da ita, kai tsaye wani haɗaɗden Hotel suka wuce,suna shiga suka faɗa Toilet sukayi wanka a tare sannan suka fito suka fara baɗalarsu,sun dade sannan Ma'aruf ya sararawa Zulfa'u shima don ta haɗa masa da kuka don ba ƙaramin azaba yake bata ba, saboda bata wani ƙware a harkar ba,duka zuwansu London ta haɗu da Ma'aruf suka fara Soyayya shima ɗan Nigeria ne, amma suna zaune shida Mamanshi da Babansa a London, haka Ma'aruf ya yaudari Zulfa'u harta yarda dashi ta bashi kanta yai amfani da ita, haka ya maida ita kamar wata matarsa,ita kam abinda yasa ta amince ganin yanada maƙuddan kuɗaɗe, shiyasa ta yadda ta buɗe masa gareji yana shiga ciki ya kwashi harka yanda yake so,daganan kuma ya haɗata da su Zee suma abokansa ne na kwalɓewa shi yasa suke adawa da Zulfa'u, kwance sukayi suna maida numfashi, saida Zulfa'u ta huta sannan tayi wanka ta fice gida

Tunda ta shiga take jin kukan Mama ƙasa_ƙasa ida shiga ɗakin tayi kallon Mama tayi yadda ta shaƙe Suhailat tana faɗin "dan Ubanki ki faɗa man waye ya ɗibga miki ciki cikin samarinki masu jajayen kunnuwa kona shaƙeki ki mutu wallahi."

Kuka sosai Suhailat keyi tana faÉ—in "Mama nima kaina bansan waye yayi man ciki ba wallahi saboda inada samarin da muke mu'amala dasu da dama,gashi yanzun cikin ya wuce 5 Month ballantana mu zubar dashi,"

gaban Zulfa'u ne ya faÉ—i itama fa ashe tana É—auke da cikin Ma'aruf,kuma abinda yasa ta barshi don kawai ya aureta ne ko don albarkacin abinda zata haifa, to ashe itama Suhailat na dashi

Sulalewa Mama tayi ta ce "shikenan Suhailat kin ida tona man asiri baya ga wanda Zainab ta tona man ashe dama muguwa itama yaudarata zata yi,na biyewa son zuciya na baro mijina cikin mawuyacin hali don kawai son abin duniya,gashi yanzun bani ga tsuntsu bani ga tarko, abinda naso su Raihana suyi cikin shege sai gashi kune kukayi, yanzun gashi haƙƙinsu dana Nuraddeen na bibiyata,"

haka Mama tayi_tayi Suhailat ta faɗa mata wanda yayi mata ciki amma ta ce itama bata sanshi ba, baƙin ciki goma da gomiya tara ya haɗe mata ga cikin shege ga Aunty Amarya ta yaudareta ta gudu da maƙuddan kuɗaɗe, haka ta zauna ta zurawa sarautar Allah ido, ana nan kuma itama saiga cikin Zulfa'u ya bayyana wanda saida Mama da kanta taje wajen Ma'aruf ta faɗa masa,kuma ya yadda da nashi ne,kuma ya ce aka zubar masa da ciki sai ya ɗaure su,idan ta haifa ta bashi ɗanshi kuma bazai taɓa aurenta ba,daganan ma ya rabu da ita

*Raihana*
tunda na zauna na fara haɗa kayana abinda kaɗai nake buƙata na ɗauka sai dai na rasa ina zan nufa shin a jejin zan tafi koko na tafi wajen Mommy nima naji ɗumin dangin Mahaifiyata,canza shawara nayi na nufi gidan Mommy dukda ba sosai nake gane hanya ba, haka na dinga Tafiya naci uwar tafiya ba kaɗan ba kafin na ƙarasa gidan da baƙar wahala,shiga nazo yi masu gadi suka hana,hakan yasaka ni neman waje na zauna don bazan iya jayayya da Mutum ba,zaune nayi ina jiran ko zanga Motar Nuraim yazo ko Hameed don na shiga amma shiru har 10:pm yayi shiru kakeji ga wajen daya yi tsit baka jin motsin komai

can Asibiti kuwa ba ƙaramin artabu aka sha da Dada ba akan cewa itama fa lallai saita bi Office ɗin likita taji mike faruwa da Nuraim amma aka hanata, koda su Mommy suka shiga Doctor ya kallesu yayi masu ƴa ce "to Alhamdulillahi tunda mun samu damar ceto rayuwarsa yanzun mun riga munyi masa alluran bacci"

godiya su Mommy sukayiwa Doctor sannan suka fito suna fitowa Nafisa ta zo tana kuka ta ce "ya mutu Mommy ko yana raye? dan Allah ki faÉ—a man wane hali yake ciki"

"bai mutu ba Allah ya tseratar dashi daga sharrin miyagu ta faÉ—a tana bankawa Nafisa harara"
gaban Nafisa ne ya faɗi "to taya suka gano nice na shirya komai? amma idan wannan baiyi ba ai akwai wani tarkon harke uwarsa bazan ƙyale ba" ta faɗa tana ficewa daga asibitin gaba ɗaya

Jabir kuwa tun sadda yazo asibiti ya buɗe wayansa yaga message ɗin Nuraim ya faɗa masa duk abinda yaji daga bakin Nafisa shi yasa yaje ya ɗakko su Ni'imatu dasu Mommy, bai ɓoyewa Mommy komai ba ya faɗa mata

koda Mommy taji hankalinta yayi masifar tashi jin har Abdurrahim yana hannunta,saida Jabir ya kwantar mata da hankali kan cewa zai san yanda za'ayi a cetosa daga hannunta,amma ya yanke shawarar su koma É—aya daga cikin gidajen Nuraim wanda Nafisa bata ma san da zamansu ba

ganin dare nayi yasa su Hameeda dasu Dada tahowa gida tunda suka tafo Hameeda taga Raihana zaune waje guda saboda hasken dake wajen yasaka ta ganeta

nikam ina zaune ganin dare nata yi yasaka nama fidda rai da zuwan wani na gidan, tsayuwar Mota naji hakan yasaka ni saurin É—agowa Hameeda ce tazo ta ce "Raihana mi kike yi anan?" "muje ciki zan faÉ—a miki abinda ya maidoni"

shiga nai cikin Motar ina shiga wata tsohuwa tai tsimil ta ce "ke Hameeda a ina kika samo mana wannan Ajnar mai kama da Sajeeda?"Dada ta ƙarashe zancen da jin tsoro dan fa ita kallon Aljana take yiwa Raihana

banza Hameeda tayi mata jikina ne yai sanyi jin abinda ta ce a sanyaye na gaida ita,amsa mani tayi tana yatsina fuska
Chapter 7 · 0% Book details