← Book details Rushewar Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 24

Sashe 20

Rushewar Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Modibbo da jikinsa ke kyarma don ganin Alhaji Naseer a gabansa Jini na shatata, ta cikinsa inda aka tsaga, a hankali wani baƙin hayaƙi ya fito a jikina yana rikiɗewa ya zuwa wata yabiɗaɗɗiyar tsohuwa wadda tasa hantar Modibbo ƙara ƙaɗawa yace "Saddiƙa kiyiwa Allah da Manzonsa ki ƙyaleni don Allah bani son mutuwa yanzun ki taimaka man,ki dubi ƴan uwantakar dake tsakanina dake" wani kalar kuka ta fashe dashi mai gunji da fidda amo, hawayen jini na shatata a kuncinta, tace "Modibbo tuni na yakice wannan ƴan uwantakar da kake ikirari, tuni na fidda kai a layin waɗanda na sani, dukda nasan abinda nayi ne nima na girba harka kasheni, amma ka sani kaima ba zan ƙyaleka ba a tare zamu je can inda ba'a dawowa mu karɓi hukunci" tana gama faɗa ta kece da wata kalar dariya sannan tasa hannu tana shaƙe Naseer wanda idanunsa sukai luhu_luhu kakari yake yana roƙonta amma taƙi sakinsa hakan yasa jinin dake malalowa tasa halshe tana lashewa tana Kallon Modibbo tana gurnani tana wata kalar dariya, saida ta lashe jinin jikinsa tas sannan ta sake shi,zaƙo_zaƙo farcenta ta cakawa Naseer sannan tasa hannunta tana ɓara cikinsa yadda kasan ana fafe cikin dabba haka ta fafe cikin Alhaji Naseer tana dariya haka da hannuwanta tasa tana ƙwalƙwale masa idanu, tana cin ƴan cikin da zuciyarsa, kallon Jogu tayi wanda tsabar firgici tuni ya sume iskar bakinta mai ƙarfi ta hura masa wanda ya sashi farfaɗowa da ihun ceto amma babu wanda yake jinsa, buɗe idanunsa yayi ya kalli Saddiƙa wacce ke cin zuciyar Naseer jini na shatata bakinta jage_jage da jini dariya ta kece da ita tace "Saura kai, kaima bada jimawa zakai irin tasa mutuwar yadda nai masa kai saina linka maka taka biyu" tana gama faɗa ta juyo wajena da siffarta ta Saddiƙa lafiya lau, kallona tayi yadda nima na ƙame waje guda don tsoron daya kamani, hawaye naga na bin kuncinta tace "tace jeki Raihana kiyi rayuwa kamar kowa, ƙarshenshi yazo nida kaina zan ɗau fansata wanda ko ba komai kema zaki ga irin mutuwar da zaiyi" tana gama faɗa bata dawo jikina ba ta ɓace da gawar

nima firgigit na tashi zufa na wanke man jiki ina kyarma wanda hakan ya tada Hamma faɗa jikinsa nayi na fashe da kuka tambayata yake me ya faru amma ba bakin magana ganin haka yasa shi tofa man addu'a wacce ya sani yin shiru ina sauke ajiyar zuciya na koma bacci, da Assuba ko Sallah da zai fita rirriƙesa nayi ina jin tsoro ya fita ya barni hakan yasa shi ja mana Jam'i mukai tare, bayan ya kwantar man da hankali ya ce na faɗa masa abinda ya tsorata ni, kwashe dukkan abinda ya faru nayi na faɗa masa, ƙara kwantar man da hankali yayi,na koma bacci, raina fess na tashi yau sakamakon ganin an kawo ƙarshen ɗaya saura Modibbo

Yauma ƙarfe ɗaya na rana muka shirya harda Baba da Daddy yau muka nufi hanya wanda sai dai kawai naji na faɗa musu sunan garin da zamu je, haka muka dinga tafiya ina nuna musu hanya wanda nima umarni ne naji ana bani, wanda dai_dai wani gida na nuna musu muka tsaya, Daddy ne yaje yaiwa mai gari Sallama suka gaisa sannan yace masa dama suna neman wata baƙuwa ne wacce aka tabbatar masu da tana nan, da farinciki mai gari yace "tabbas haka ne suna nan dama Sajeeda kullum cikin tunani da rashin walwala gashi Allah ya kawo ku cikin sauƙi, ku shiga daga ciki" saida muka shiga aka bamu ruwa muka shiga sannan Mai gari ya shiga gidan yana ƙwalla kiran Sajeeda

da sauri Ammi ta fito daga ɗakin da Hijab sanye a jikinta, "to Alhmdllh Sajeeda ga ƴan uwanki nan da sunzo nemanki don harda wata ƴarki wacce kuke kama mai bilalen ƙwayar ido, ku shiga ku gansu"

gaban Ammi idan banda dukan ukku_ukku babu abinda jin cewar ƴan uwanta kuma ma wai harda ƴarta mai bilalen idanu, to ita ina taga wasu ƴan uwa ma, kodai Modibbo ne ya biyo sahunsu? sai dai kuma abinda ya tsaya mata a rai jin cewar ƴarta mai kama da ita da blue ɗin ido, hakan yasa ta nufi ɗakin zuciyarta na halbawa da sauri........✍️

Wannan kenan

*Comments, Share fisabilillah*

Waɗannan su ne ƙwarin guiwata

*By Riamcool Hasken Royal*

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
[2/17, 2:24 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA*

*Book 2*

*By Mariam sani Riamcool*

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

Bismillahirrahmanirrahim

*P. 102&103*

_________✍️Hakan yasa ta nufi ɗakin zuciyarta na halbawa, ɗaga labulen tayi da sallama ɗauke a bakinta, sai dai sallamar tata maƙalewa tayi saka makon ganin Mommy da sauri zuciyarta ta sake halbawa wanda tai luuu baya ta faɗi, saboda ba ƙaramar razana tayi ba, da gudu su Mommy suka nufota suna kiran sunanta wanda ko motsi, ruwa Mommy ta ɗauko tana yayyafa mata, ta buɗe idanunta tana kallon Mommy wanda nan take ta rufe idanunta zata ƙara sumewa girgizata Mommy tayi tana kuka tace "Sajeeda na roƙeki da girman Allah karki ƙara somewa ki buɗe idanunki nice dai Yaya Fatima, ga kuma ƴarki Raihana" ta faɗa tana kuka

itama Ammi kukan ta fashe dashi ta rungume Mommy tace "Yaya Fatima ashe ina da rabon na sake ganinki? na fidda rayuwa da tsammani sake ganin wani nawa Yaya Fatima"

ƙara ƙanƙameta Mommy tayi tana kuka tace "Sajeeda banyi maki adalci ba, dukkan wata ƙaddara data sameki na dan gantata a kaina, saboda nice silar shigarki cikin ƙuncin rayuwa, nasan da ace ban raboki gaban iyayemmu ba, da baza ki taɓa shiga cikin ƙuncin rayuwar nan ba"

girgiza mata kai Ammi tayi tace "kada kice haka Yaya Fatima can wannan ɗin itace tawa ƙaddara, koda baki taho dani ba nasan saita sameni, komai da kika gani a rubuce yake ki daina danganta hakan daga gareki"

Nima a faƙaice na share hawaye ina ƙara godewa Allah, yau wata nutsuwa ta daban naji tana ratsani da kwanciyar hankali wanda tunda nake a rayuwa ban taɓa jinsu ba, lura da Ammi bata ganni ba yasa nace "Ammi" wanda ya sata saurin kallon inda nake da gudu nazo na rungumeta na fashe mata da kuka itama hawayen take tana bubbuga bayana tare da sake ƙanƙameni kamar wani zai ƙwaceni, ni kam nai luf a jikinta, sosai mukai kuka wanda da ƙyar Nuraim ya rarrashemu daga ni harsu Mommy

Ammi ce ta kira Uwani wacce tunda na ganta na ɗauke kaina wanda kallonta kanshi sake tada man da mikin Modibbo yake, wanda da ƙyar na gaishe da ita, ita kanta kasa sakewa tayi itama don yau zata tattara tabar garin ta koma garinsu Gombe, don Ammi ce dama yasa ta tsaya, Address ta basu ta kuma taya Ammi murna sosai

Wanda ƴan kwanakin da suka yi yasa su shaƙuwa, sallama sukai wanda Nuraim yaiwa mai gari Alkhairai da Sha tara ta arziƙi wanda tsabar murna mai gari kasa godiya yayi, haka cikin kewa suka rabu ana musu fatan Alkahiri

haka muka nufi hanyar gida wanda ina kusa da Ammy ko wane motsi zatai ina kusa a haka har muka isa koda muka je su Raheenatu na Falon Mommy zaune da Sadeeq duk sunyi zugum, wanda idanuwansu ya sauka kan Ammi, murza idanunta Raheenatu ta ƙara yi kar ace gizo suke mata ganin Ammi tsaye ƙara murzasu tayi don tabbatarwa wanda hakan da tayi ya bawa Kowa dariya, ganin da gasken dai sune yasa ta nufi wajenta da gudu tana rungumeta wanda Sadeeq ya rigata isa wajenta sake ƙankamesu Ammi tayi tana murmushi da hawaye, itama Raheenatu hawayen farinciki take da ƙyar ta rabu da Ammi

da kanta Mommy ta haɗa mata ruwan wanka tayi, wata Abaya mai kyau Mommy ta fiddo mata dashi tasa, sannan taci Abinci aka zauna ana firar yaushe rabo,wanda nan Mommy take sanar da ita dukkan abinda ya faru sosai tai murna da farinciki, jin cewar harda aure nayi ga kuma yanzu na dawo nrml kamar kowa wanda tayi farinciki iya farinciki ta ƙara godewa Allah, haka Nuraim duk inda ya matsa tace ya dawo kusa da ita, sai take ganin abin kamar almara ganin dukkammu yanda muka girma,haka zalika ta tausaya mana da dukkan jarabtar da muka gani wanda ta ƙara ƙarfafa man guiwa akan yadda da ƙaddara, ga shinan yanzu sai dai muce komai ya zama labari, haka Abba shima yazo ya dinga neman yafiyar Ammi akan abinda yai mata, don wallahi duka bada saninsa ya aikata mata ba, nuna mashi tayi ba komai ya wuce nan ya roƙi alfarmar ta koma ɗakin aurenta, don yanzun yanda yake jin masifaffiyar ƙaunarta, wanda Ammi itama nata ɓangaren haka yake, babu musu ta Amince ko dan ta ƙara gina rayuwarta wacce za tayi mai cike da farinci, sannan ta bama Mijinta farinciki wanda ya rasa tsawon shekaru

mun daɗe nan sannan muka tafi wanda harda ƙwallata na zira Hijab ɗina naso ace nima ya barni na kwana kusa da Ammi, dariya Raheenatu tayi tana man gwalo tace "bake babu ƙara shiga jikin Ammi, mudai yau muna jikinta maza a tafi gida" harara na banka mata da kunƙuni naima kowa sallama ina wucewa, koda muka je gida ban kulashi ba, Hijab ɗin ya cire man yana jawoni jikinsa yace "wai Habeebty fushin me ake dani?"

turo baki nayi da ƴar shagwaɓa ina doka ƙafafu nace "to ba kaine ba yau ka hanani kwana wajen Ammi ba" Murmushi yayi wanda ya ƙara masa kyawu har dimple ɗinsa na lotsawa wanda ya sani tsaye ina kallonsu hannu nasa dai wajen ina taɓawa, "ko ya burge ki ne?" murmushi nayi ina daga masa kai "kema ai ga naki nan"

"ai bai kai naka ba" na faɗa da ƴar shagwaɓa dariya yayi yace "kin gaji muje muyi wanka mu kwanta" da to na amsa ina cire rigar jikina wanda tunda na cire ya kafeni da ido, zuwa nayi na cire masa nasa kayan sannan nace "muje yau ni zan maka wanka" dariya yayi yace "to kunyar tawa da kike ji ki kaita ina?" dariya nayi nace "ta gudu ai indai kunya ce yanzu ɗaukarni marar ita" dariya yayi yace "haka kika ce?" nace masa "eh mana"
Chapter 20 · 0% Book details