← Book details Rushewar Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 24

Sashe 22

Rushewar Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mommy da Ammi kuwa tunda yake sakkowa daga Step ɗin benen suka kafe Mahaifin nasu da ido wanda ƙwalla suma ta cika musu,ido miƙewa dukkansu sukayi suna nufar Mahaifin nasu wanda shima tunda suka nufo shi, su yake kallo, da hanzarinsa ya ida sakkowa suka faɗa jikinsa suna fashe masa da matsanancin kuka, wanda Dattijuwar dake bayansu itama batai ƙasa a guiwa ba ta haɗesu su dukkansu, ta rungume tana kuka, rasa mai rarrashin su akai saida suka fidda tsohon mikin dake zukatansu sannan Abbi ya rarrashesu da ƙyar aka zauna ana sake gaisawa, nan Nuraim ya gabatarwa Abbi kowa da kowa wanda sai da yayi hawayen farinciki ganin zuri'a guda duk tashi ce

"Alhmdllh ban san da wane baki zan godewa Mahalliccina ba akan ni'imar da yai man wanda a da ban ganota sai a yanzu, wanda ada nayiwa Ubangiji shishigi ya gwada mani iyakata, wanda dukkan abinda ya faru inada hannu dumu dumu a ciki, sai dai shi kuskure babu wanda baya aikata sa, to muna roƙon Allah ya yafe mana, Fatima na yafe muku ku dukkanku Allah yayi Albarka" ya faɗa da yalwataccen murmushi akan fuskarshi

duk girman su Mommy bai hana su kwanciya jikin Mahaifiyarsu ba, ita kuwa Alexandera wacce ta koma A'ishatu a yanzu sai shafa kansu take tana sa musu Albarka
[2/17, 2:24 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA*

*Book 2*

*By Mariam sani Riamcool*

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

Bismillahirrahmanirrahim

Last page

*P.106&107*

____________✍️ Sosai akayi fira da raha akai wasa da dariya,kowa ka ganin fuskarsa cike take da annashuwa da Annuri,haka ranar Abbi yace dukkammu dasu Mommy zamu kwana

Dada kuwa mamaki ne ya kasheta ganin gidan su Mommy da kuma ganin yadda suke da maƙuddan kuɗaɗe,amma ta baro gaban iyayenta ta biyo ɗanta, kuma ta shuka mata rashin mutunci ta bata wahala, sosai jikinta ya ƙara yin sanyi ta kuma ƙara neman yafiyar su Mommy

haka shima Dady ɓangarensa jikinsa yai sanyi sosai, yayi nadamar abinda ya aikata mata, yanzu kuwa zai ririta matarsa tamkar tsoka ɗaya a miya,

ranar haka muka kwana,sosai na tashi da kewar mijina,

washe gari sai wajen Ishsha'i sannan muka bar gidansu Mommy, wanda Abbi yace a ƙara barin su Raheenatu dasu Sadeeq, haka muka barsu muka dawo gida

dukda a gajiye muka dawo hakan bai hana mu murzar juna ba, sai da muka tsarkake jikunnammu sannan muka kwanta,

Kamar yadda ya saba hauka tuɓuru da kukan jinjirai marassa daɗi haka yake ji duk yayi baƙi ya lalace shi kaɗai yasan kalar azabar da yake sha, wacce da ita da mutuwa basu da maraba, jin wani Mugun iska ya ɗaga shi sama ana kecewa da wata kalar sheɗaniyar dariya wacce ta ƙara rikirtar dashi,ihu da kururuwa yake na neman ceto amma ina babu wanda ke jinsa, haka wannan iska ya dinga gudu dashi yana ihu, har ya kaishi dokar dajin da baka jin sautin komai sai wasu kalar dariyoyi dake tashi da kuma wasu kalar kuka marassa dadin sauraro, wata muguwar tsawa aka buga da walƙiya wacce, tasa wasu yara suka bayyana, suna dariya suna nufosa, nan take ya gane yaran da yakewa fyaɗe ne kuma ya kashe su ta hanyar tsafi,

da wata kalar murya Æ´ar yarinyar tace "jamu É—au fancarmu jamu kaceka kamar yadda ka kacemu jamu lalata maka da caccan jiki kamar yadda ka lalata mana kafin ka kacemu" ta faÉ—a tana fashewa da wani kalar kuka mai firgita mai sauraro

wata kalar dariya Uwargijiya ta sheƙe da ita tana faɗin "Modibbo na fasa kasheka da hannuna waɗannan sun isheka,iyakata na tsaya nai kallo idan sun gama dakai mu tafi tare"

kuka ya fashe dashi yana roƙonsu akan su ƙyalesa amma ina haka yaran nan suka fara azabtar dashi ta hanyar cire masa Jarumarsa, wacce yai lalata dasu, wani ihu da kururuwa ya ƙara saki, sannan zaƙoƙon farcen hannunsu suka cakawa idonsa nan take jini ya malalo saida suka ƙwalƙwale masa ido sannan suka ɓara cikinsa suna ciccire kayan cikinsa haka suka masa yaga_yaga kai daban ƙafa daban duk sunyiwa kayan cikinsa daban_daban, sai da sukai masa kisan wulaƙanci, naman jikinsa duk sun mashi gutsin_gutsin, haka suka ɗaukesa suka nufi inda suka ɗaukosa suka ajiye,suna sowa da murna suka ɓace harda Saddiƙa Uwargijiya

A firgice na miƙe ina sharce zufar data wanke man fuska, hamdala da godiyar Allah nayi daya gwadawa Modibbo ƙarshensa ya kuma kawo ƙarshen zaluncisa, a hankali na sauko daga kan gadon Arwalla na ɗauro na dinga salla ina ƙara godewa Allah,

saida nayi sallar Asubah sannan na koma wani kalar bacci mai daɗin gaske na ɗaukata, sai wajen 12 na tashi na gyara gidana tsaf ko ina na ƙamshi lungu da saƙo, sannan nai girki, wanka na shiga nayo nazo na shirya cikin wata haɗaɗɗiyar shadda pink color wacce tasha aiki, sosai naci kwalliya sai kace wacce zata gidan biki, sai uban ƙamshi nake zubawa, kallo na kunna, naje tashar labarai, ganin ana hasko gawar Modibbo wacce akaiwa gutsin_gutsin, wacce ana bada labarin abinda aka gani a gidansa, waɗanda mutane da dama sunyi ala wadai da halinsa, da ƙyar aka samu wasu suka haƙa rami a gidan nasa aka birnesa, jikina ne yai sanyi laƙwas, tsoron duniya dana mahaliccina na ƙara shigata,

Hamma ne ya shigo,wanda tunda ya shigo yake tazbihi ga Allah daya mallaka masa wannan haÉ—aÉ—É—iyar kyauta, wani sassanyan murmushi yake aiko man dashi wanda nima ban kasa a gwiwa ba na aika masa da nawa ina tashi na rungumesa ina dariya, shima haka É—aukana yayi cak yana juyi dani, sannan ya ajiye ni,

bedroom muka shige na temaka masa ya cire kayan sannan nace masa muje na temaka masa yai wanka, "No kada ki ɓata kwalliyarki ban moreta ba barshi da kaina zanyi, sannan nazo na bada tukuici" ya faɗa yana kashe man ido guda dariya na saki ina kai masa dukan wasa a chest ɗinsa

shigewa yayi toilet ni kuma na miƙe na zaɓo masa wasu haɗaɗdin ƙananan kaya waɗanda nasan zasu matuƙar amsar jikinsa,ina nan zaune ya fito, ni da kaina na shafa masa lotion da kaya na saka masa, turare ya ɗauka yana fesa jikinsa dashi, wanda naji tukar amai Toilet na faɗa da gudu ina sheƙashi kamar zan juye hanjin cikina, a rikice ya shugo yana man sannu, da kanshi ya wanke man baki ina daɗe hanci sannan ya gyara, wajen bedroom ɗin na fita saboda jin ƙamshin turaren, Falo na fita na faɗa bisa 3 seater ina kwanciya, jin fitowarsa yasa na marerece fuska nace "Baby dan Allah kaje ka cire kayan ka wanke jikinka turaren nan ya fita, wallahi shi ya sani Amai" na faɗa kamar nayi kuka

da matsanancin farinciki yace man "da gaske" "eh mana" na faɗa kamar zanyi kuka, juyawa yayi saida ya sake wani wanka kamar zai canja fatar jikinsa sannan wasu kayan ya janza ya fito fuskarshi ɗauke da Annuri, da sauri ya nufo wajena yana shafa cikina yace "ashe dai da gaske nayi ajiyar" kallonshi nayi da mamaki nace "ban fahimta ba" "ba zaki fahimta ba tashi muje Hospital" ya faɗa yana miƙar dani

"wallahi Baby nifa lafiyana ƙalau" na faɗa ina raurau da idanu, bai bi ta kaina ba haka ya ɗauko man mayafi na yafa muka tafi, koda muka je Doctor yai mana ƴan gwaje_gwaje ya tabbatar da ina ɗauke da juna biyu na tsawon sati ukku wanda nan take Nuraim saboda tsabar daɗi ya ɗaukeni yana juyi dani har hawayen farinciki saida yayi sannan yaiwa Doctor ɗin gwaggwaɓar kyauta, nima kaina nayi farinciki sosai

haka muka taho, wajajen shaƙatawa ya kaini wanda mun daɗe muna yawo sannan muka dawo, Part ɗin Mommy muka sauka wanda Nuraim ya sanar dasu ba ƙaramin farinciki sukai ba wanda kamar su zuba ruwa ƙasa susha dan murna, nikam kunya duk ta isheni

saida muka jima sannan muka nufi namu Part É—in wanda muna komawa shi da kanshi yai mani wanka ya shiryani tsaf, ko Abincin kirki bai iya ci ba saboda tsabar murna

hannuna ya ɗauka yana damƙa mani yace in buɗe,ina buɗewa naga wata haɗaɗɗiyar Iphone 15, tsalle na doka ina faɗawa jikinsa da murna, zaro ido yayi yace "bi sannu fa kada ki mani asara" dariya nayi na shiga kwarara masa godiya har saida ya haɗe bakimmu waje guda sannan nai tsit, cikin wani irin salo yau nake tsosar lips ɗinsa na ƙasa, shima cikin salo da ƙwarewa ya dinga aika man da hot kiss, da ƙyar na zille ina saka wayar a chage sannan na dawo muka dasa daga inda aka tsaya,sosai na zage na faranta wa Mijina wanda nasha saka Albarka,

haka muka dinga gudanar da rayuwarmu cikin farinciki da wanda su Raheenatu tuni sunyi nisa a soyayya ita da Abdurrahim Hameeda kuma da Yaya Fauzan, ganin ko wane a shirye yasa aka saka rana bada jimawa ba, Ammi ma tuni an mayar da aurensu da Abba wanda Yaya Fauzan ya gina musu katafaren gida anan Abuja ya zuba musu ma'aikata da dalla_dallan Motoci sannan ya bawa Abba wani baban Company sa, Nuraim ma wani Company nashi ya damƙawa Abba a matsayin kyauta wanda Abba arziƙinsa yanzu ya linku, babain sabuwar soyayya suka gina da Ammi haka Abba ya zage yake bata kulawa, ga duk Sati ake zuwa gidan iyayen su Mommy wanda ba abinda zamu ce a yanzu sai dai godiyar Allah dan family ɗimmu yanzu cike yake
Farinciki, wanda kamar ba'a taɓa fuskantar wani ƙalubalen rayuwa ba, dukkan rayuwarmu data rushe yanzu ta ginu ciki ƙarko da aminci
Chapter 22 · 0% Book details