← Book details Rushewar Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 24

Sashe 5

Rushewar Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ana haka saiga kuma Abba zaiyi tafiya na tsawon shekara guda wanda dagashi sai Mama da yaranta sai Aunty Amarya suka tafi,tunda ya tafi Sharu ya mayar da Ammi kamar wata matarsa don duk lokacin daya so buƙata zaizo wajenta ya sauke wutar sha'awarsa akanta,Shiyasa koda yaushe cikin kuka take da dana sanin auren Abba,haka tun ina ƙarama na taso nake ganin kullum Mahaifiyata cikin zubarda hawaye take,ga dama tun ina ƙarama nake yawan mafarkin yadda nake shan jini da kuma yadda ake bani mutane ina kashewa, wanda wannan kisan idan nayi shi yake sakani cikin shauƙi, haka tunda aka sakani a makaranta nakan fuskanci kyara da kuma tsangwama don acewarsu kalar halittana yayi kama dana Mayu ko Aljannu wannan dalilinne yasa tunda na taso yara da manya ke faɗa mani kalmar mayya wanda a lokacin bansan ma'anar kalmar ba, wani lokacin nakanzo na tamabayi Ammi ta faɗa man ma'anar kalmar mayya saidai tayi murmushin takaici ta kalleni, tunda na fara wayo nake ganin mahaifiyata kullum cikin zubarda hawaye take,ga abinda naɗan fara lura dashi duk ranarda Baba Sharu yazo saiya koromu yace mu fito,daya fito muka shiga zamu iske Ammi na kuka hakan yasa na dinga tunanin ko idan ya shiga dukan Ammi yake shiyasa take kuka, nikam tun ranarda naga ya fito Ammi na kuka na yanke hukuncin da yazo saina laɓe naga miyake yiwa Ammi har take kuka don muddin na kamasa yana dukan Ammi to tabbas saina tanadi duwatsun da zan fasa masa kai dasu,haka washe gari yana dawowa na laɓe ina don inji ko dukanta yake saidai leƙawar da zanyi naci karo ya daɗe mata baki da hanci yana ta shaƙa mata wata Powder wacce yasa jikinta yai laƙwas wata uwar ƙara na ƙwalla wacce ta ankarar da Baba Sharu,ganin hakan ne yasa ya fisgoni ya ɗaga hannunsa da niyyar shararaman sai kuma ya fasa yana mai man gargaɗi akan muddin na faɗa ma wani abinda nagani to saiya saka wuƙa ya yankani ya bada jinina hakama Ammi saiya kasheta, wannan gargaɗin da yayi shine wanda ya tsoratar dani sosai,inaji ina gani ya fice,yana fita na fashe da kuka ina faɗawa jikin Ammi itama hannu tasa tana bubbuga bayana tana son yi man magana amma ta kasa ko kaɗan bata iya buɗe bakinta ji take da tazo yin magana kamar an saka mata zare da Allura an ɗinke, saidai tasan koma miye yanada nasaba da abinda Sharu ya zuba mata tabbas koda zata yafewa kowa duniya to bazata taɓa yafewa Sharu ba,koda Ya Fauzan yazo yaga halinda Ammi ta shiga na rashin magana,hankalinsa ya tashi ga babu abinda yafi ɗaga masa hankali irin kukan da yaga mahaifiyarmu nayi, hakan yasa ya dinga kiran Abba amma ko kaɗan baya samunsa dole yasa ya haƙura haka muka kwana da ita wanda da ƙyar Yaya Fauzan ya lallaɓamu mukayi bacci,shikam da Ammi babu wanda ya runtsa a ranar yanda suka ga rana haka suka ga dare,washe gari ma haka ta yini babu maga,ga wani uban aman jinin da take gundari_gundari,ga Abba ko kaɗan ba'a samun wayoyinsa, haka Ya Fauzan ya sanarda su Baba Sa'adu,amma babu wanda yabi takan abinda ya faɗa kowa ya kama harkar gabansa, haka muka zubawa sarautar Allah ido muna kallo kullum Ammi cikin ciwo take ga ƙafafuwanta dake mata ciwo ko kaɗan bata iya tashi babu magana bata kuma ita tashi,ranar da muka samu wayar Abba muka sanar masa shima babu wani alamar damuwa daya nuna saima cewa da yayi abari idan ya dawo ya neman mata magani,haka muka ƙyale muna kallon mahaifiyarmu cikin wannan hali, tunda abinnan ya faru bamu ƙara ganin Baba Sharu gidanba wanda tunin duniya tsani dukkan wani ɗan uwan Abba don a ganina sune Silar jefa Ammi cikin wannan hali,saidai muna cikin wannan halinne muka nemi Ammi bamu ganta ba, hankalimmu ya sake tashi wanda harda ƴan unguwa aka shiga cigiyarta hakama Abba ya sanya ana nemanta amma ƙasa ko sama har tsawo 3 Month babu Ammi,wanda duk wata kulawarmu ya koma akan ya Fauzan kullum shine yakan zauna ya rarrashemu ga Sadeeq shima da yake tada rigima akaisa wajen Ammi, rana guda aka tsinci gawar mace wacce aka cirewa kai da ƙafafuwa wacce akeda tabbacin ta Ammi ce ranan kowa saida ya shiga matsanancin tashin hankali wanda bazan iya misulta muku shi ba,muna ji muna gani aka kaita makwancinta,tun daga lokacin kuwa Ya Fauzan ya zamto shine ya maye mana gurbin Ammi,ga Abba tunda ya tafi saida ya share shekara da watanni sannan suka dawo

shima Abba tunda ya dawo ya dinga bamu kulawa ta musamman dan saida ya rasa Sajeeda yake jin wata ƙaunarta da ƙaunar yaranta na musamman,hakan yasa koda yaushe ya kanzo ya tare wajemmu yana mai ɗebe man kewar Mahaifiyarmu,saidai wannan kulawar da yake bamu ita ce ta ƙara janyo ƙiyayyar ƴan Uwammu da kuma Matan Abba,wanda ko kaɗan tsakanimmu dasu bamu shiri, haka zalika ina girma lamarina na ƙara ta'azzara don tun mutane basu farga ba har suka fara ganewa cewar lallai duk wanda ya dokeni baya kwana duniyar, don ko a lokacin ni kaina na kashe mutanen da bansan adadinsu ba, tun Mahaifimmu na bamu kulawa har yakai ga ya sauya yaji kuma duk duniya babu waɗanda ya tsana sama damu,haka shima Ya Fauzan kwatsam aka nemesa aka rasa,wanda tun ana saka ran ganinsa har muka fidda,haka muka ci gaba da rayuwa mu kaɗai," nan na zauna na faɗa masu da ta yadda muka taso gidanmu harya kawowa auren biyan bashin da aka mana

dukkansu shiru sukayi Mommy kuwa idan banda kuka babu abinda take yi jin irin jarabawar data samu Æ´ar uwarta wanda koma miye ita ce sanadi,

Da ƙyar muka samu muka rarrashi Mommy tayi shiru, Hameeda ma kukan tausayin rayuwar da mukayi take, Nuraim ma ya ƙara jin wani karsashin ƙara son temakon Raihana,dukda zuciyarsa da take wani bugawa sakamakon jin Raihana nada aure......✍️

*Sakamakon rashin Comment yasa na maida wannan littafin na kuɗi duk wacce take son ci gaba da karantawa ta siya💁‍♀️*

Wannan kenan

*By Mariam sani Riamcool*

*08109554986*
[2/6, 5:51 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA*

*Book 2*

*By Mariam sani Riamcool*

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*

Happy New Year 2024 as we saw 2023. May God bless us with good health. May God open the doors of blessings for us.

*So da na ce bazan yi a kyauta ba sai an biya za'a ci gaba da karantawa,sai kuma jiya naga kun janza kunyi man Comment,shiyasa zan cigaba a kyauta amma dan Allah ku dinga Comment in har bakuyi bazanji daɗin maku Typing ba dan Allah fans ku janza, ku dinga bamu ƙwarin gwiwa,mu munayi don mu nishaɗantar daku da faɗakarwa donmu faranta muku amma kukuma sai ku musguna mana ta hanyar ƙin yin Comment*

*Bismillahirrahmanirrahim*

*Page 72&73*

___________Duk yanda yaso danne abinda ke zuciyarsa kasawa yayi saboda,ace wacce ya daɗe da mafarkin son kasancewa da ita a rayuwa,wacce kullum yake cikin mafarkinta,wacce ya daɗe da cimma burin zama uwar ƴaƴansa tun a mafarkin da yake ganinta, ashe ma duk wannan abun da yake tanada aure shi kam ya zaiyi da zuciyarsa da take yunƙurin tarwatsewa, a hankali wasu siraran hawayen da baisan da zuwansu ba saidai yaji ɗuminsu a kuncinsa a hankali yasa hannu ya ɗaukesu

Tunda ya lula duniyar tunani nake kallonsa harya zuwa lokacin da hawayen suka zubo masa ya share, zuciyata ce ta shiga kokwanto abinda yasaka shi hawayen,sharewa muka ci gaba da hira nida Hameeda da

miƙewa Nuraim yayi ya ce "Mommy zan shiga ciki naɗan kwanta saboda kaina na ɗan sara man ," ya faɗa yana yamitsa fuska

Kallonshi Mommy tayi tana faÉ—in "Son da so nake ka maida Raihana gida kaga saima kaga gidan daganan."

"Hameed ya kaita ko Jabir Mommy ni bazan iya driving ba." Yana gama faÉ—a ya fice, kowa da kallo ya bisa

Yana fita Part ɗinsa ya wuce a hankali ya zo danna door bell ɗin zai shiga saidai cak ya tsaya sakamakon jin maganar da Nafisa ke faɗi, "Shu'aibu Tabbas NURAIM ya ida gano wasu gurɓataccin ayyukan da nakeyi to bazan saurara masa ba wallahi saina kashesa na sadaukar da ruhinsa, Wannan ma abinda yasa na ƙyalesa barinsa nayi naga iya gudun ruwansa,kuma shima yayi yunƙurin tona mani asiri to tabbas saina kashesa naci zuciyarsa nasha jininsa,yanzun ma abinda yasa na raga masa ina son mallakar dukkan wasu Company sa, sannan na aiwatar da ƙudirina akansa, sannan wannan abokin nasa Jabir a yau nake son ku ɓatar man dashi idan da hali ma ina so ku kashesa ku ɓadda gawarsa, saboda na fahimci shine ke taimakawa Nuraim wajen gano miyagun ayyukana, ina son kuma Ku tasgara rayuwar matarsa Ni'imatu kuyi mata yankan,haka zalika yarinyar da kuka ce kunga Nuraim da ita itama da sun fito ku haɗa da ita ku kashe banza, wallahi yanda Nuraim ya fara shiga lammurrana saina mayar da Ahalinsa gawarwaki saina mayar da gidansu gidan zaman makoki,sannan munafukar Uwarsa dake bashi ƙwarin gwiwar bibiyata itama bazata sha ba,sannan shima Abdurrahim da kuka riga kuma kama kada ku barsa ya kubce maku so nake ku haɗa shi da wannan daɗaɗɗen Saurayi ku ƙara gana masu azaba," tana kaiwa nanan ta fashe da dariya tana jan dogon numfashi sannan tace "wallahi Nuraim saina tasgarar da rayuwarka tunda ka taɓoni".

Shikam Nuraim suman tsaye yayi zuciyarsa na tafarfasa da zafi, da sauri ya juya zuwa Part ɗin Mommy don ya tsayar da Jabir dake yunƙurin tafiya shida Raihana, ko Sallama baiyi ba ya shiga Falon yana faɗin "Mommy ina Jabir da Raihana?."

Kallonshi Mommy take tana faÉ—in "Son lafiya naga hankalinka a tashe meya faru? su Jabir kana fita shima ya fita da Raihana don mayarda ita," ta faÉ—a itama hankalinta a tashe
Chapter 5 · 0% Book details