← Book details Rushewar Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 24

Sashe 17

Rushewar Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

washe gari da muka tashi haka muka je Saloon akai mana gyaran kai, mun ɗan jima sannan muka dawo, muna dawowa Mommy ta nuna man lefen da Hamma Nuraim yai man tsayawa nayi da mamaki ina kallon akwatina 16 dake lode da kayayyaki, wai danma lokacin bikin ne ya ƙure shi yasa, nayi farinci sosai da godiya dana dinga zubawa Mommy kamar ba gobe,

ɓangaren Dada kuwa dukda ba wani son auren Raihana da Nuraim take ba haka tayo gayyar ƴan uwa da abokan arziƙi, don Dada tunda Raihana ta shigo gidan ta zubar da makaman yaƙinta, taja mutuncinta ta riƙe, haka yanzu ta bar cin mutuncin Mommy, dukda tana tsoron Raihana bai hanata janta a jikinta ba, don a bikinnan itama sosai take nuna tata bajintar

Nafisa kuwa ita da baƙin ciki ya isheta tuni ta haɗa kayayyakinta tabar ƙasar ta tafi London nan take Nuraim ya buga mata kingin sakin igiya biyun data rage ya ida katseta wanda ba ƙaramin baƙin ciki ta shiga haka yasa ta ƙara ɗaukar aniyar ganin Raihana,

Yau Friday ranar da za'a É—aura aure, zaune nake nayi zugum duk tunanin duniya ya isheni babu abinda nake tunani sama da naga na amso Ammi daga hannun Modibbo, sosai na tuna da ita gabana ke faÉ—uwa ba nida wani burin daya wuce naga, naga bayan Modibbo, ga duk yau yadda na tsinci kaina cikin faÉ—uwar gaba don koya na tuna za'a É—aura mani aure sai naji gaba É—aya bani so, naji gaba É—aya auren ya fice man a rai, shigowar Raheenatu ne yasa ni É—ago da kaina ina kallonta, sosai tayi kyau cikin bugaggiyar shaddar ta wacce taji aiki

Kallona tayi tace "Raihana wai meke damunki na ganki sukuku.?" ƙwalla naji sun cika man ido nace "Raheenatu auren ne bani so wallahi." "kamar ya baki son auren? yanzun dai ki tashi kiyi wanka ki shirya" ta faɗa tana miƙar dani, sannan ta shiga Toilet ta haɗa man ruwan wanka, nayi ina fitowa ta fito man da wani haɗaɗɗen bride material fitted gown ɗauka nayi na shirya cikinsa raina duk babu daɗi, Hameeda ce ta shigo da mai Make up ta zauna ta tsantsara man, ba dan raina yaso ba, sannan tayiwa su Raheenatu, ga yunwa data addabi cikina don koda na tashi ko ruwa ban sha ba haka su Mommy sukai ta fama da naci abinci amma naƙi , saida Mommy tai man Jan ido sannan naɗan tsakura

Photuna ma ba don ina so ba na fito mukayi ansha photuna wanda har saida na gaji haka dai aka ci gaba da hidima, wanda Mommy ko mp ta hana a kunna, da Hameeda sunso ayi wani abin amma fir Mommy ta hana, saidai kawai ƙarfe huɗu da za'ayi Walima

Ɓangaren Nuraim kuwa shar sanye yake cikin wata dakakkiyar shadda sky blue wacce ta ƙara fiddo da tsantsar kyawunsa da cikar haibarsa, fuskarshi sai fitar da annuri take, yau dai Allah zai cika masa mafarkinsa da kuma burinsa na mallakar Raihana wacce ya daɗe yana mafarkin mallakarta, "Nuraim wannan fa ɗoki naka yayi yawa" Jabir ya faɗa yana dariya shima dariyar yayi ya wani juya ido kamar mace yace "Jabir ya san ranka idan banyi ɗokin wannan ranar ba me kake so nayi, dole ne yau na ƙara godewa Allah da zai mallaka min wacce na daɗe da mafarkin samunta a rayuwata, na kuma ci buri akanta, wacce na daɗe da mafarkin zata haifa man gudan jinina"

nan dai Jabir yaci gaba da tsokarnarshi kingin abokansu waɗanda sukai karatu tare suna tare masa, 1:30 nayi Nuraim ya sake shiga wanka ya shirya cikin wata dakakkiyar Shadda fara Sol wacce taji aikin hannu, haka ƴan gidansu da Abokansa su kayi ankon Shadda Ash color suma ba ƙaramin kyau da tsari sukai ba,

ƙarfe 2:30 dai_dai dubbanin mutane suka shaida ɗaurin auren Raihana Nuraddeen Usman da Kuma Muhammad Nuraim Haris Ali, wanda Abba tsabar murna kamar ya zuba ruwa ƙasa yasha, daga wajen ɗaurin auren anci an sha anyi bajinta sosai, sannan suka shigo cikin gida danyi Photuna

lokacin ina É—aki na janza wani haÉ—aÉ—den leshi wanda ya amsa sunansa fari mai ratsin golden, haka zalika aikin dake jikinsa golden ne, kwalliyar aka sake gyara mun wacce nai shar gwanin kyau, Raheenatu ce tace na taso zamuje mu gaisa da abokan ango sannan ayi mana photuna, babu musu na tashi ina yamitsa fuska,

tunda ta fito ya wani kafeta da ido kamar zai cinyeta sosai tayi masa kyau ba ƙarami ba, gani yake kamar ba Raihanarshi ba saboda kyan data ƙara kamar Aljana dan tsabar kyau ji yake kamar ya mayar da ita ciki dan tsananin ƙauna, murmushi mai ma'anoni ya saki yana kawar da fuskarshi

tunda na iso ta ƙasan ido nake kallonshi ganin kyan da Hamma yayi saida zuciyata ta tsinke, cikin kasalalliyar murya na gaishe dashi sannan na gaida kingin, suka amsa suna tsokanata, ina yaƙen dole don bazan kirashi da murmushi ba saboda azabar da nake ji ta daban a jikina

Raheenatu kuwa Abdurrahim ta ƙurawa ido ganin shima mugun kyau ɗin daya zuba "ashe dai baƙaƙe ma akwai masu kyau shidai gashi ɗan baƙi amma akwai kyau ɗin, saidai mugun faɗin ranka ya ƙwareka" ta faɗa a ranta

Abdurrahim ganin yadda Raheenatu ta zuba masa ido yasa shi maka wata jar harara kamar idonsa zasu faɗo, itama hararar ta maka masa tana masa kallon sama da ƙasa sannan ta murguɗa masa baki, ƙwafa yayi yana kauda kanshi "lallai yarinyar nan zan koya miki hankali, yaushe ma kika ga mkwancina da har zata rainani haka hada harara, lallai kuwa zanyi maganinki" ya faɗa yana cije lips ɗinsa na ƙasa

Hameeda ce data lura da duk abinda ke faruwa ta kece da dariya tace "Raheenatu alƙur'an kin tsokano Yaya Abdurrahim ku fara wasan ɓuya dashi, don nasan ba zai ƙyaleki ba"

taɓe baki tayi tace "can shi ta matse mawa da gama ya samu an kalleshi fuska sai kace baƙin ɗuwawu, shi ba wani kyau ba,kawai dai abinda yasa na ɗan kalleshi ne ina son na ƙara gano muninshi ne, gashi kuma na gano" karaf sai a kunne Abdurrahim Zuciyarshi ce tai mashi zafi ji yake da babu mutane babu abinda zai hanashi falla mata maruka lafiyyayyu

Photuna muka sha hadasu Dady da Abba dasu Sadeeq daya shige cikin su Hameed kamar wasu sa'annisa, ansha photuna ba laifi, jin kaina ya ɗan fara sara mun yasa na sulale na haura ina shiga na faɗa kan bed na fashe da kuka ko zan samu salamar ƙuncin da nake jin ya addabi zuciyata a halin yanzu, jin shigowar Mutum ya sani miƙewa zaune ina goge hawayen fuskana

ganin Hamma ne yasa ni haÉ—iye abinda nake ji na sakar masa murmushi, a hankali cikin nutsuwa ya tako har ya iso ya zauna dab dani kafaÉ—unshi na gugar nawa, tallafo fuskana yayi ya kafeni da ido cikin damuwa da kwantar da murya yace "me ya faru dake kike kuka?" "ba komai" na furta wasu hawayen na sake wanke mun fuska, "ba komai kuma kike kuka?" "eh kawai dai naji kukan yazo man ne tunawa da Ammi da nayi"

"Ok ya isa hakanan, kiyi shiru ki daina zubar da hawayenki insha Allah komai yazo ƙarshe Ammi zata dawo garemu da izinin Allah"ya faɗa da sigar rarrashi yana goge man hawayen, "muje na wanke miki fuskanki nasan duk wannan kwalliyar ya isheki amma kafin nan bari na fara rage miki wani nasan ai kina so na rage miki ko?"

shiru nayi ina wasa da yatsun hannuna, wanda Nuraim ya saki murmushi yana ƙara juyo da fuskana ga tashi a hankali ya kai tashi fuskan ga tawa yana goga karan hancinsa ga nawa, wanda muka saki wata nannauyar ajiyar zuciya, a hankali ya kai bakinsa a nawa yana sakar man wani hot kiss wanda saida ya sani shiɗewa cikin salon ƙwarewa ya dinga sarrafani da hot kiss ɗinshi mai wuyar fassarawa wanda yasa ni manta wata damuwata, na ƙarɓi sakon da yake aiko man

saida ya daɗe yana kiss ɗinna sannan ya ƙyaleni yana Murmushi, hatta jan bakina saida ya shanyeshi tass sanna, murmushi ya sakar mani yana kashe mani ido wanda nai saurin janye nawa idanun ina murmushi, da kanshi ya ɗaukeni ya kaini Toilet ya wanke mun kwalliyar, saida ya tabbatar babu damuwa a tattare dani sannan ya fita

Yana fita su Jabir suka ci gaba da tsokarnarshi, ganin jan baki a farar shaddarshi, murmushi kawai yayi yana shafa kanshi

ƙarfe 4:30 pm nayi aka fara walima wadda Mommy ta ɗauko wata shahararriyar Malama, tayi faɗakarwa sosai akan zamantakewar aure,6:00 nayi aka tashi, haka dai aka ci gaba da hidima har 7:00 pm sannan na shirya cikin wata haɗaɗɗiyar lifaya mai kyau na saka sanna aka kaini wani Part wanda Nuraim ya ƙara gyarashi sosai, sosai tsaruwar Falon da mugayen Furniture ɗin da aka zuba a Falon zai birge mutum waɗanda suka kasance Set biyu Milk da brown, har wajen takwas su Aunty Ni'imatu na ƙara kimtsa ko ina ya buge da ƙamshi sannan suka tafi suka barni ni kaɗai, basu daɗe da fita ba su Hamma suka shigo, tsokanata suka fara yi sannan sukai mana nasiha daga ƙarshe suka rufe da addu'a sannan suka tafi

suna fita Nuraim ya ƙara matsowa dab dani yana yaye mayafin lifayar sannan ya ƙurawa fuskana kallo, sadda kaina ƙasa nayi "sarkin kunya da anyi abu sai duƙar da kai ƙasa, tashi muje muyo wanka da Arwalla"

zaro ido nayi nace "Hamma kana nufin a tare zamuyi wanka?" dariya yayi yana shafa kumatuna yace "Yes i mean a taren zamuyi wanka, tashi mu shiga"

ganin zai takura man yasashi tashi ya shiga yayo nashi da wanka da kuma na maganin da aka umarcemu muyi shi, yana fitowa nima na shiga nayo, saidai ina kama ruwa da wani ruwan magani naji faɗowar abu a ƙasana, da sauri na duba naga ko minene hankalina tashe, saidai ganin wata ƙankara_ƙankara yasa gabana faɗuwa tunawa nayi da lokacin dasu Jogu suka saka man ita, hakan yasa na saki nannauyar ajiyar zuciya naci gaba da wankana nayi Alwalla, sannan na zira doguwar rigar dana shiga da ita, na fito a gurguje na ɗan shafa Lotion da turaruka sannan muka tada sallah
Chapter 17 · 0% Book details