← Book details Rushewar Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 24

Sashe 19

Rushewar Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kallonsu mai gari yayi da tausayawa yace musu ba damuwa nan yasa aka basu masauki sannan yasa aka kai masu ruwan wanka,saida sukai wanka sosai sukai salloli , ko abinci da aka aiko musu dashi basu ci ba saboda kowa da abinda ke damunsa, Uwani kwana tayi kuka saida Ammi tai ƙarfin halin rarrashinta

haka suka zauna a garin cikinsu kowa da abinda ya damesa, ga mai gari ya sa aka dinga ma Ammi magani,(kunsan maganin Fulani ) cikin ikon Allah ta dawo Nml wannan baƙin da rama da tayi duk ya fara ɓacewa ta ɗan ciko gashi suna samun kulawa wajen mai gari ba laifi, hakan yasa hankalinta fara dawowa jikinta,

*Ɓangare guda kuwa*

tunda aka kai Hajiya Bilkisu Asibiti suka ƙi amsarta yasa ƴan aikin zuwa Police Station ɗin suka zo, sannan aka amsheta lokacin ta galabaitu ga bata a hayyacinta ma, sun duddubata sukai mata ɗinki, sannan ƴan aikin suka kira mai ɗori ya ɗora ƙafar data kare, saida ta share kusan wata guda sannan ta fara dawowa hayyacinta wanda tana tashi da sunan Sabreen ta tashi, sallamarta Doctor yayi ganin ta samu sauƙi, hakan yasa ta tattara ta koma gida, gashi tunda abin ya sameta ba taga ko mutum ɗaya a cikin ƙawayenta ba, hakan ya sata zuwa gidajensu, sai dai a cikinsu dak wurin wanda taje da kalar tarbar da zai mata a wulaƙance, kamar ma basu santa ba, don Turai gwadawa ma tai ita bata santa ba

jiki ba ƙwari ta dawo gida tasha kuka kamar ranta zai fita, wanda sai a lokacin tayi da nasani halayenta da biyewa ƙawayen banza, harta lalata rayiwarta da kanta, gashi lokacin da duniya ta juya mata baya, suma sun juya mata nasu bayan, wanda hada ƙarin cin mutunci da suka haɗa mata, wanda sune suka zuga ta ta kashe mijinta, Kuka sosai take

Sabreen kuwa tunda Bobbos ya tafi da ita yake gana mata azaba kala da kala, wanda kullum sai yayi amfani da ita ya kai sau ukku, sannan ya bama yaranshi su shana suma, sosai ta koɗe ta lalace, wanda saboda tsananin lalacewa kai baka ce Sabreen bace.........✍️

Wannan kenan

*Comments, Share fisabilillah*

Waɗannan su ne ƙwarin guiwata

By Riamcool Hasken Royal star

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
[2/14, 12:29 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA*

*Book 2*

*By Mariam sani Riamcool*

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

Bismillahirrahmanirrahim

*P.100&101*

__________✍️Sosai Sabreen ta wahaltu kullum cikin kuka da ciwo, da dana sanin halayen Mahaifiyarta, wacce koma minene ita ce silar, komai kuma muddin ta kuɓuta tayi Alƙawarin zata shiryu ta gyara halayenta, kullum cikin kuka da takaici take

*Raihana*

Sai ƙarfe 11 na buɗe idona naga Hamma baya nan miƙa nayi na miƙe Toilet na shiga nayi wanka na fito daure da towel lotion na shafa sannan na ɗan shafa powder da kwalli sai lip gloss dana shafa, wata riga Italiono gown mai shape sosai da buɗaɗen wuya Red color wanda rabin ƙirjina duk a waje yake, sosai rigar ta amshi jikina feshe jikina nayi da haɗaɗdun turaruka

jin yunwa yasa na nufi dinning don nasan Mommy ce zata aiko dashi, zama nayi naci nai nak sannan naɗan gyara gidan dukda ba ɓaci yai ba sosai amma haka na zage na gyara shi tas, ko ina ya fito tsaf ƙamshi tako ina, kwanciya nayi kan ɗaya daga cikin kujerun Falon,

jin ana danna door bell ya sani miƙewa na buɗe su Raheenatu ne da Hameeda, da farinciki na tarbesu sannan muka zauna muka sha fira sun ɗan jima sannan suka ce zasu tafi, harara na aikawa Hameeda nace "nan da nan ɗin shine kike cewa wai zaku tafi ga baki ga hanci"

dariya tayi tace "ke Wallahi Mommy tace karmu daɗe muzo mu gano mata lafiyarki, to kuma mun ganki garas kike" dariya nayi suna miƙewa suka fice wayar Raheenatu na amsa ko ta ɗan rage man kewa, zama nayi naita game

har Hamma ya dawo koda ya dawo yace na saka Hijab zamu je gurin Baba ni dashi da Mommy muka je, koda muka je yauma ya ƙara miƙo man ruwa a ƙwarya yace na kalleta sannan na rufe idona, yadda yace nayi hakan nayi,

Kallo ɗaya zaka masa kasan cewar duk a razane yake hankalinsa ba'a jikinsa yake ba, duba da yadda ya zurawa waje guda ido babu abinda yake kira idan banda Sajeeda ta dawo masa da kayansa haka daga bisani kuma zaki ga ya toshe kunnensa yana ihuu da kururuwa yana su ƙyalesa bai son su ɗau fansa, wanda wannan ihun ne ya janyo masu gadin asibitin Mahaukatan zuwa suka rirriƙesa sukai masa allura, laƙwas yayi ya kwanta, sai dai ko yanayin baccin daya kwashesa zai tabbatar maka da cewar ba'a tsanake yake yinsa ba duba da yanayin yadda yake zabura ya shura ƙafafu, dariya na kece da ita ina buɗe idanuna, kallon Baba nayi na faɗa masa dukkan abinda ke faruwa wasu ruwan ya sake bani na wanke fuskana sannan yace na rufe idona, yadda ya umarceni haka nayi na rufe idon nawa,

Kamar koda yaushe zaune take ta rabka uban tagumi tana sana'ar tata wato Tunani wacce ta zame mata al'ada kullum tunani shine abokin firarta, "haba Sajeeda wai sau nawa zance miki ki daina tunanin nan tunda har Allah ya kuɓutar dake miye na kuma tunani, kita Addu'a insha Allah, Allah zai haɗaki da ƴaƴanki duka, kuma Fauzan nasan ko wace ƙasa yake ki bari nida kaina zan samo miki shi, nasan dana kirasa zai ɗauka" sauke ajiyar zuciya Ammi tayi tana share hawaye tace "tunanina ɗaya ne Uwani ya zanyi da Amal?"

idan ta Amal karki damu ai ƙaddara ce babu kan wanda bata hawa, koni zan iya riƙe miki Amal a hannuna zan bata kulawa fiye da kowa bazan taɓa bari tasan cewar bani na haifeta ba" girgiza kai kawai Ammi tayi tana miƙewa don ita kaɗai tasan kalar baƙin ciki da takaicin da take ciki, a fakaice Uwani ta share hawayenta itama tana miƙewa

buɗe idona nayi ina sauke ajiyar zuciya, na faɗawa Baba duk yanda akai "To Alhmdllh da Allah ya kuɓutar da ita a hannunsa sannan ya fara girbar abinda ya shuka ana tun kafin yaje can, yanzu abinda nake so daku gobe ku dawo zamu rangaɗa mu duka muje can, nasan ke tsaf zaki kaimu wajen da take" ɗaga masa kai nayi sannan mukai sallama muka koma

muna komawa na gwada ya barni wajen Mommy ko nafi samun sauƙin abinda nake ji don ganin Mahaifiyata saida ya tada man da tsohon mikin Jogu, koda Raheenatu ta tambaye mu inda naje, na faɗa mata dukkan abinda ke faruwa, sosai ta kaɗu da jin zancen cewar wai Ammi na raye, tayi kuka sosai wanda har zazzaɓi ya rufeta, saida nai Ishsha'i sannan na koma gida ban daɗe da kwanciya ba bacci ya ɗauke ni wanda na kwanta da son kaiwa Jogu ziyara,

kwance yake wanda yayi nisa cikin tunanika tun lokacin dasu Uwani suka gudu yake kwance yana buga ƙofar ɗakin yana surutai, wanda ya jawo hankalin Security ɗin gidan suka ɓalle ƙofar ganinsa a haka ya tada masa hankali suka kaishi Asibiti wanda yayi kusan wata sannan ya warke sai dai tunda ya warke da ihun kiran Sajeeda ta bashi zobe ya tashi, wanda kuma duk rufe idon da zaiyi haka zaiga wasu kalar Halittu da jinane a jikinsu sunzo suna zasu ɗau fansa haka zai tashi ya zura da gudu yana karku ɗau fansa, wanda bilhaƙƙi da gaske yake ganinsu, Mutane kuma na ganin ya haukace hakan yasa aka kaishi gidan Mahaukata ana bashi magunguna da da Allurai, wanda suka ƙara birkita masa ƙwalwa, ga abin nashi babu sauƙi, wanda shi dai ya san da hankalinsa, Naseer ma wajensa kusan haka abin yake dan tun lokacin da Zoben nan ya bar hannun Jogu shima komai nasa ya lalace, duka ƴan ƙungiyar su ta tagayyara komai nasu ya lalace, wanda da dama a cikinsu duk sunyi Mutuwar wulaƙanci wanda aka rasa wanda ke ma ƴan ƙungiyar su kisan gilla

Alhaji Naseer ganin abinda ya faru da Abokinsa ya tabbatar da shima bazai tsira ba, kullum da zillimi yake kwanciya, a hankali shima ya fara ganin Halittun da Jogu ke gani wanda suke binsa kullum da Jinane a jikunnasu suna dariya suna kuka don harda Saddiƙa yake gani wacce tafi tsorata sa da siffofin halittu da dama, gashi kullum da azabar da take gana masa, wanda nan akai tsammanin shima ya zare don saida takai shima ana mashi Allurar Mahaukata da bashi magunguna

Jogu yayi nisa cikin wannan tunanin yaji dirar abu a gabansa, rufe idonsa yayi don baya son yai tozali da mummunan abinda ke gabansa don ya tabbatar koma miye a gabansa bana Alkhairi bane, sai dai da sauri ya buÉ—e idon nasa saka makon ganin abubuwan da suka kusan bugar masa da zuciya

Idanunsa ya sauke akan Raihana wacce tai tsaye waje guda tana kallonsa, tana sakar masa wani Miskilin Murmushi wanda ya hautsina masa lissafi, daga bisani kuma ta haɗe rai tan tunkarosa ja da baya ya ke "Raihana ki taimaka kiyi mani rai don Allah nasan nida kaina banyiwa rayuwarki adalci ba, nine sanadin ɓata rayuwarki amma ko don darajar ɗan uwan Mahaifinki ki ƙyaleni kada ki kasheni, ki barni da bala'in dake tattare dani" ya faɗa yana fashewa da wani kalar matsanancin kuka

dariya na fashe da ita ina tunkarosa da wata kalar murya mai fita biyu nace "Jogu wallahi sai kayi Mutuwar wulaƙanci wanda ko arziƙin Sallah ba zaka samu ba ina tabbatar maka da sai dai Namun daji sun cinye gangar jikinka sannan kan Abokinka Naseer zaka fara ganin kisan gillar da zan mashi a gabanka" na faɗa wanda nidai bani ce ke Maganar ba sai dai inga bakina na motsi kawai wanda na tabbata da Ruhin dake jikina ne ke wannan maganar
Chapter 19 · 0% Book details