← Book details Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 28

Sashe 9

Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau Asabar ,garin Kaduna cike take da hayaniya. Murtala Square ta yi kaca-kaca da tutocin jam'iyya,da pastoci masu rubuce da kalmonin yabo,da kiɗe-kiɗen waƙoƙi masu ɗauke da taken "Barau ne sabon hasken Kaduna..." jama'a ana sowa ana tafi ana bin waƙar. Jama'a sai tururuwan taruwa suke yi daga kowanne loko da sako. Wasu da rawanin jam'iyya,wasu da riguna masu ɗauke da hoton Alhaji.Barau.

Cikin shiga ta farar shadda ɗinkin babbar riga mai ɗauke da adon sirfani mai ɗaukar ado. Tafiya yake cike da nutsuwa da fara'a a kan fuskar sa. Tafiya yake irin ta jarumi wanda jama'a ke jiran fitowarsa na tsawon shekaru.Sautin ganga da kaho suna ta ɗaukar hankalin mahalarta taron.

Kan kujera ya zauna a saman dandalin da zasu yi taron. Bayan ƴan jawabe-jawabe aka gabatar da shi. Miƙewa yayi tsayi ya ɗaga hannunsa sama . Tuni aka saki wani irin ihu da guɗa daga mata. Bakinsa ya ƙara girma saboda yadda ya ga jama'a sun fito duk don shi hakan ya faranta masa rai sossai.
Hannun dai ya kuma ɗagawa sama duka biyu. Sai kowa yayi tsit baka jin ko tari sai irin kukan yara daga nesa kamar ta jarirai da kuma na yaran da basu fi wattani biyar haka zuwa shidda ba.

"Ƴan uwana jama'ar jihar Kaduna" Ya faɗa muryarsa cike da kwarjini.

"Yau gani a gaban ku a matsayin ɗan takara ,amma fiye da haka na zo muku ne a matsayin ɗan uwa,ɗan ƙasa,ɗan gari,wanda yake son tsaya muku yake kuma son ganin ci gabanmu gabaɗaya daga ni har ku."

Sai jama'a suka amsa da ihu da sowa ana kiran "Barau ! Barau ! Barau!"

Dogon numfashi ya ja,sannan ya fara lissafa alƙawarrukansa cike da salo mai kama da labari ko jan hankali.

"Nan da kuka gan ni kafin na zama Alhaji.Barau. Asalina ɗan talakawa ne,na taso daga cikin talakawa, na san raɗaɗin rashin makaranta. Wallahi idan kuka bani dama,Kaduna za ta zama garin ilimi. Zan gina makarantu a karkara,za mu ɗauki nauyin ƴa'ƴan talakawa,kuma ba wani yaro da zai tsaya a titi yana bara a maimakon karatu." Ya ɗan dakata ya tsaya ya kalli wajen da wasu dattawa ke zaune,ya cigaba da magana.

"Na san da batun rashin lafiya. Na san yadda ake kwana a asibiti babu magani. Na rantse,idan Allah Ya bamu nasara a wannan tafiyar ,babu wata uwa da za ta sake kukan rashin magani saboda rashin abin siyan maganin. Za mu gina asibitoci,za mu kawo likitoci ƙwararru, za mu samar da magunguna kyauta."

Taro ya ɗauki ihu da sowa. Wani matashi daga gefe ya ɗaga hannu yace "Ina da magana."

"Ina sauraron ka samari."

"Batun aikin yi fa ga matasa?"

Alh. Barau ya juya gefe,ya juya hagu,ya juya dama ya kalli matasan nan kaf na cikin taron ,ya ɗaga hannunsa sama yace "Matasa ku sani ku ne garkuwar jihar nan. Za mu buɗe masana'antu,za mu ba ku horo,ku zama masu kasuwanci ba masu jiran aikin gwamnati kawai ba.Matasa za su zama ƙarfin tattalin arziƙin Kaduna!."

Tuni aka koma magana ƙasa-ƙasa cike da ƙus-ƙus. Maganganu suka zama kamar ruwan sama da ya daɗe yana jiran ya zubo.

Ya ci gaba ganin kamar alƙawarukansa na samun ƙarbuwa a zukatan mutane.

"Ku bani dama,ku bani goyon baya,mu kawo ƙarshen yunwa,mu gina Kaduna da hannuwanmu. Talaka shi ne ginshiƙin ƙasa ,kuma ni zan kasance tare da ku daga farko har ƙarshe."

Ganguna suka soma bugu,tururuwar jama'a suka mamaye wajen,mata da maza,dattawa da matasa,suna ɗaga hannayensu suna rera waƙar "Barau 2012! Sabon hasken Kaduna!"

Alhj. Barau da farinciki da walwala ya shiga motarsa yana ta ɓaɓaka dariya. Ya kalli P.A ɗin sa yace "Wato su mutane har yau ba zasu waye su yi tunani mai kyau ba. Kullum da sabon abin da muke cin su da yaƙi su kuma yarda da mu su dangwala mana ƙuri'a. Da ka yi harbi a daidai inda yake musu ciwo shi kenan magana ta ƙare."

Ai Alhaji bana jin ka na san zaka lashe ƙuri'un nan da yardar Allah! Dama ga shi Oga Muhammadu ma yana taimakawa talakawa da matasa sosai ,ko don shi ma zaka samu yadda kake so. Ka yi bacci kayi milo ka ɗaga lemo mai sanyi ka kora babu ja babu haufi Kaduna taka ce wannan karon.

Shi yasa nake son ka P.A ,ka san daidai ka san kuma ta kan siyasa zaka yi albarka mutumin nan.

Suka kyakyata da dariya duka.

*

Ban daga ina ko ta ya aka kawo mini wannan baƙar abayar ba mai cike da ado na duwatsu tana walwali tamkar wanda aka shirya mata tarin duwatsun nan na swarvoski!

Ɗaga rigar nayi na karata da jikina Ya subahanallah! Ta yi nasarar hawa kan farar fatata.

"Tsayin yayi miki?"

Ta juya da sauri ta kalle shi. Bata san yana wurin ba. Ƙasa tayi da kanta tace "Tayi kyau. Na gode!"

Lumshe idanuwansa kawai yayi ya juya sai kuma ya tsaya yace "Abuja zan tafi. Ki yi sauri sai mu sauke ki a gida."

"Babu kowa a gidanmu...."

"Kar ki damu mahifiyar ki an dawo da ita, kuma an gyara dukanin ɓarnar da aka yi muku, sannan na saka muku mai gadi mai kyau. Babu abinda zai faru in sha Allah! Kawai ki kula ki maida hankalinki ki san irin takun da za ki na yi ,ba a kowanne wasa ne ake samun nasara ba."

"Na gode!"
Yayi gaba kawai abin sa.

A gurguje ta shiga tayi wanka ta shirya. Wani flat ɗin takalmi ta gani baƙi shi ma ta saka. Ba tare da ɓata lokaci ba ta fita daga ɗakin ta ja ƙofar ɗakin tayi waje.

Komai tsaf-tsaf.

A bakin mota ta ga direba a tsaye, yana ganinta ya buɗe mata gidan baya ta ɓarin dama ta shiga ta zauna. Ƙamshin turaren sa kawai ta ji ta gano tare zasu yi tafiyar dai kamar yadda ya sanar mata. Tashin motar yayi suka fara tafiya.

Ta wutsiyar ido take kallonsa yadda yayi kyau cikin suits baƙaƙe da farar t-shirt a ciki mai dogon hannu. Agogon hannunsa ma Rolex ne.

Cikin ranta tace "Wai ma mutumin nan baya saka kowanne kaya sai wannan baƙar suit ɗin ne?"

"Kika ce?"

Da sauri ta juya ta kalle shi tana zare idanuwa "Ba dai ya ji ni ba?" Ta tambayi kanta.

Cikin i'ina tace "Ban ce komai ba, ba komai."

"Oh!" Kawai ya faɗa. Ita kuma ta runtse idanuwanta biyu ta ciji leɓɓanta na ƙasa a rai tace "ki nutsu mana Maryam."
[9/12, 9:18 AM] Ummulhair S Panisau: RUFAFFEN DUMA.
Ummulkhair S Panisau.
(Khairatup)
Wattpad:Khairi_Muhd.
Arewabooks:Khairatup01.

Pg8.

"Ban yi tsamanin haka kake ba Wallahi!" Ta faɗa kaifin idanuwanta a kan shi.

Ya juyo da kan sa yana tattare girarsa cike da mamakinta yace "Me kika zata to? Mugun attajiri ? Mai kuɗi masifaffe ko marar zuciya?" Ya tambaye ta kaitsaye.

Dariya tayi ta ce "ku san haka ne. Ni fa tun ran da na fara ganin ka nake mamakin halin ka. Na ɗauka dan a gaban kyamara ne ko kuma don muna interview ne amma sai ka bani mamaki jiya zuwa yau."

Ya maida kansa kan Tab ɗin hannunsa yayi murmushin gefen baki kawai. Yace "kuma yanzu me kika gani?"

Ta yi shiru kawai, zuciyarta na bugawa. Ita fa ƴar jarida ce,aikin ta shi ne ta rubuta, ba ta faɗaɗa zuciyarta ba.

"Yanzu na ga wani babban mutumin da ya bani mamaki."

Daidai nan dereba ya tsayar da mota. A hankali ta ɗaga kai ta kalli ƙofar gidansu lokaci guda ta sauke ajiyar zuciya kuma. Har ta sa hannu zata buɗe ƙofar motar sai ta ji yace da ita "Za ki iya cin abincin daren gobe da ni?"

Ta juya ta kalle shi idauwasu cikin na juna. Bata ji tambayar kamar ta neman yarda ba ta ɗauki tambayar kamar umarni ne yake bata.

Ta ɗauke kai haɗe da buɗe bakinta tana son tayi masa gardama ,sai kuma ta tuna da iyaka tsakaninta da rayuwarta. Sai kuma zuciyarta ta riga ta, bakinta ya buɗe tace "Abinci kawai?"

Ya kalli cikin idanuwanta,bai kawar da kallonsa ba. "Ba yanzu ba,gobe zan aiko direba ya zo ya ɗauke ki."

Daga nan ya yi wa direba alama da ya ja su tafi. Nan suka bar ta da mamaki. Tunani ta soma yi. "Cikin shiru mai cike da nauyi ta fahimci cewa haka soyayya kan fara ba tare da tsawa ko kuma wuta ba,sai dai da tambaya,kallo,da kuma alƙawarin cewa labarin bai ƙare ba tukuna akwai sauran al'amari a gaba." Haka ta ja ƙafar ta zuwa cikin gida.

Tana shiga ta hango Mama zaune kan kujera ta yi zugum!

"Mama.....Mama!"

Mama ta juyo ta ɗago kanta tana kallon fuskar ƴar ta ta. Miƙewa tayi tsaye ta baza mata hannunta biyu tace "Maryama!"

A hankali ta ƙarasa ta shiga cikin hannun ta. Mama ta sa hannu biyu ta rufe ta ruf. Tare suka saki kuka. Aka rasa mai rarrashin ɗan uwansa.

"Mama kiyi haƙuri ,ki yafe min Mama. Ni ce na janyo miki. Ba zan kuma shiga abinda zai saka ki shiga matsala makanmaciyar wannan ba."

"Aa Maryama. Ba laifi ki ba ne. Allah Ya tsara hakan. Alhamdulillahi na dawo cikin kwanciyar hankali da lafiyata. Basu yi min komai ba cikin hukuncin ubangiji."

Maryam ta sauke ajiyar zuciya ta saki Mama. Nan suka zauna suna bawa juna labarin daren jiya.

"Mama baki gane komai ba a wurin da aka ajiye ki?"

"Ban ga komai ba. Hasali ma idanuwana a rufe suke da baƙin ƙyalle. Babu abinda na gani."

"Mama ki tuna ko za ki tuno wani abin da zai iya taimaka min."

"Maryam ina ƙara gaya miki don Allah ki rabu da wannan aikin. Ni gwara ki dinga ɗauko labarai muna ganin ki a akwatin talabijin ba wai ki dinga yin rubutu a kan masu laifi ba. Bani da ƙarfin zuciyar da zai saka na jure rashin ki bayan rashin babanku da yayanki ba."
Chapter 9 · 0% Book details