← Book details Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 28

Sashe 15

Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Burin Nimra shi ne ta soki Maryam ta hanyar da ko a gaba zata ji tsoron kusantar Muhammad gabaɗaya.

Cikin ƙanƙanin lokaci aka gano mata wace ce Maryam da wurin aikinta ma.
*

Zaune take kan kujerarta tana aiki tuƙuru wasu takardu take dubawa. Peon ne ya kawo mata wani ƙaramin kwalli nannaɗe da wani ƙyalle mai kyau. A ranta ta ɗauka kyauta ce aka kawo mata ko kuma ma Muhammad ne ya aiko mata da shi. Buɗewa tayi a hankali wani hoto ta hango ko da ta zaro hoton ita ce da Muhammad a wurin cin abincin nan a hotel san da suka je cin abincin nan,tare da wata ƙaramar wasiƙa da aka yi rubutu da jan alƙalami.

"kada ki kuskura ki sake kusantar wanda ba na ki ba. Wannan farkon gargaɗi ne."

Maryam ta tsaya cak! Tana juya takardar a hannunta zuciyarta ta buga da ƙarfi. Ba ta san daga inda wannan saƙon ya fito ba,amma ta fahimci kamar akwai wata inuwa da ta riga ta fara bin sawunta."

Hoton ta jujuya da kyau ta ajiye a gefe, ta sa hannu ta kama haɓarta ta shiga tunani wacce wannan take mata barazana da wannan hoton? Tsaki tayi ma ta ajiye batun a gefe ita yanzu so take yi ta je gidan Paul ba za a rasa samun wani bayani daga gidan sa ba ko da baya nan amma ai ba za a rasa wata tsohuwar ajiya ba amma shin Smith zai kai ta gidan Paul ɗin?

Akwai haɗari ta sani amma dole sai tayi don wannan lamarin an soma shi ne tun kan ta san kan ta ma.
[9/11, 8:02 PM] Ummulhair S Panisau: RUFAFFEN DUMA
Ummulkhair S Paisau.
(khairatup)
Wattpad:khairi_muhd
arewabooks:khairatup01
12

*

Cafe ɗin cikin ofishin ta shiga ta zauna dama ta turawa Smith saƙon ya same ta a nan. Ta buɗe littafin rubutun ta amma ta kasa rubuta ko da kalma guda a ciki sai wasa take yi da biron hannunta kamar yadda zuciyarta ke kai komo.

Smith ya sa hannunsa biyu ya tafa a kan fuskarta, a dan firgice ta juyo tana kallon sa. "Ka bani tsoro Smith."

Zaunawa yayi yana dariya . "Wasa nake miki naga kin nutsa can kina tunani. Me kike nazari ne?

"Paul Stone!"

Ya kalle ta da kyau kafin yace "Wai baki haƙura ba Maryam?"

"Kai ma ka san ba zan haƙura ba ai."

"Maryam why sai ni?"

"Saboda wannan fuskar taka tana gaya min akwai sauran bayanin da baka gama gaya mini ba."

"Maryam a halin yanzu bacci ya kamata kiyi don da ganin cikin ƙwayar idanuwanki baki bacci ba kwana biyu."

"Ban rufe su ba,kuma ba zan rufe ba sai ka gaya min abinda nake son ji."

"Maryam bamu da komai sai inuwa kawai."

"Smith abokina,ba zamu ci gaba da bin inuwa kawai ba. In har mu na son sanin ainihin abinda ya faru da Paul dole ne sai mun je wurin da za mu samu amsar tambayoyin mu."

Ya ɗaga gira ya kallon ta. "Wanne wuri kenan?"

"Gidansa."ta faɗa tana kallon cikin idanuwansa. "Ina son ka kai ni can gidansa. Ina son na ga kayan aikinsa,kwamfutarsa,teburinsa,takardunsa...."

"Maryam kin haukace? Kina gaya mana mu kai kan mu gidan zaki ne. Ba kya tsoron masu bibiyarmu su samu galaba a kan mu?"

"Ban damu ba. Na shigo aikin nan ba don ina tsoro ba sai don ina son na bayyana gaskiya."

"Maryam..."

"Smith don Allah. Ina ji a jikina akwai abinda zamu samu."

"Ina tsoro."

"Ba komai ina tare da kai."

"Yaushe?"

"Cikin dare."

Ajiyar zuciya ya sauke ya na kallonta ya kuma ɗauke kan sa ya ce ban san gidansa ba amma akwai abokinsa Godwin zan same shi ya gaya min kwatancen sai na gaya miki muje amma ba yau ba."

"Kana ganin zamu iya yarda da wani bayan kan mu?"

"Zamu iya ɗaukar risk."

"Alright zamu yi. Ina son na shiga rayuwarsa kamar yadda ya bari. Paul yana kan wani babban abu ne kafin ya ɓata. Idan kuma mun ce zamu bibiyi rahotannin hukuma ba zamu samu komai ba don a ko ina akwai azzalumai."

*

Smith ya lullube fuskarsa da facemask baƙi ,ya sanya baƙin gilashi ya rufe idanuwansa. Wayarsa ya zaro daga aljihunsa ƴar ƙaramar keypad ya danna wata lamba ya kira ana dagawa yace "Ina bakin shagon."

Ban san me aka ce masa ba dai ya shiga shagon. Ya tarar da wanda ya je gani kan kujerar roba ,yana shan sigari,yana wasa da wayarsa.

"Good afternon" smith ya faɗa cikin nutsuwa,ya zauna ya zame gilashinsa ya ajiye a gefe kan teburin.

Godwin ya ɗago a hankali,yana kallon Smith daga ƙasa zuwa sama yana tantance shi. Sannan yace "Afternoon. Waye kai?"

"Smith.ina neman wani ne da ake kira paul Stone. An gaya min kai da shi aminai ne."

Wani murmushi mai cike da raini Godwin ya saki. Ya maimaita sunan "Paul Stone? Hmm..tsohon abokin ne amma me yasa kake tambaya?"

Smith ya jinjina kan sa,ya ciro littafin sa na rubutu ya yi rubutu ya kalli Godwin yace "Ina son ka bani adireshin sa ne kawai."

Godwin ya kwantar da sigarinsa,ya jingina da kujera yana shafa gemunsa yace "kai ɗan sanda ne?"

"Aa." Smith ya amsa da sauri. "Ni ɗan jarida ne. Ina bincike ne a kan Paul ne saboda gudunmowar da ya bawa jarida ina son mutane su san shi."

Godwin yayi shiru na ƴan daƙiƙu,sai ya yi murmushi wanda bai kai zuci ba. "Paul baya son baƙi....amma... sai ya lumshe ido sai kuma ya ce "For a little token,zan iya gaya maka inda yake da zama a wancan lokacin."

Tuntuni dama Smith ya gane Godwin ba aminin arziƙi ba ne don akwai ma'anoni a cikin maganganunsa. Yana jin akwai almar tambaya akan Godwin.

"Baka da matsala,zamu baka ko nawa kake so." Ya faɗa cikin dabara.

Cikin magana irin ta area boys ya kalli Smith da turanci yace masa "look my friend be careful where you dig. Paul's enemies are not the kind you want to meet. Even me." Yayi dariyar mugunta ya ci gaba "i dey protect myself."

Smith ya gane ya shigo cikin wata cakwakiya shi ma. Yana cikin yanayin da zai iya kawo mai haɗari. Amma haka ya kalli Godwin cikin ido yace "I'll take my chances . Kawai ka gaya min adireshin."

Godwin ya ɗaga kafaɗa yace masa "Rubuta." Ya gaya masa adireshin shi kuma ya rubuta a cikin littafin na sa. Godwin ya ce da shi "Gashi nan na baka. Amma kar kace ban gaya maka ba."

Smith ya miƙe zuciyarsa na bugawa . Yana jin wannan adireshin zai kai su ga wata gaskiyar da suke nema ko kuma cikin haɗarin da basu taba zata ba.Ya bashi kuɗi kamar yadda ya buƙata.

DARE
10:00PM

Smith da Maryam na daga gefe a tsaye daga can ɗaya ɓarin na titi suna kallon ƙofar gidan Smith. Dare ne baka jin komai sai kukan karnuka da kuma hasken fitilu unguwar ma babu mutane sosai shiru layin.

Smith ya kalli Maryam yace "Maryam kin shirya?"

Ta gyaɗa mai kai tace "Muje."

"Da zarar fa mun shiga ba gudu ba ja da baya."

Duk da zuciyarta na bugawa kamar ana buga ganga sai da tace da shi "Na shirya."
Smith ya fitar da maɓallin kwaɗo ya ɓalle ƙofar. Ƙarar buɗe ƙofar tayi wani irin ƙara mai sanyi da ya sanya suka ji ɗan tsoro kaɗan suka kalli juna.

Suna shiga ciki Maryam ta kunna fitilar wayar ta ganin cikin da duhu. Gidan a cike yake da ƙura ga yana ta ko ina. Tari ta yi ta sa hannu ta toshe bakinta tana kallon bagon falon. A hankali ta isa kusa da teburin Paul akwai laptop a kai wadda ta sha ƙura.

"Anya kuwa Smith sun san da wannan laptop ɗin kuwa?,Murya na rawa ta ce Smith ka kunna mu gani.

Smith ya matsa ya kunna laptop ɗin. Tana gama kamowa ya ga hakan nan ana rubutu a jiki an sa masa "WHO ARE YOU?"

Maryam ta yi baya da sauri ,zuciyarta tayi wani ɗan tsalle . Smith...wannan...waye ya rubu..."

"Calm down ba wani abu ba ne. Laptop ɗin is hacked suna yin haka hackers ana kallonmu. Bamu da isashen lokaci muyi sauri muyi abinda zamu iya mu tafi kafin a zo a same mu.

"Haka ne." Nan suka dinga tonu takardu tsofaffi fila-fila suka yi wa ma'ajiyar Paul har ta sare sai kuma ta buɗe dirowa ta hango wata takarda da wani hoto. Ta jawo ta riƙe a hannunta tace "Smith zo ka gani wannan hoton tsofaffin manyan ƴan kasuwan nan ne kamar da kuma Sana...." tayi shiru jin kamar motsi bayan nasu a ciki gidan.

Smith ya tsaya cak ya na kallon inda suka ji ƙarar ya kalli Maryam da tuni idanuwanta sun firfito waje tana kallonsa a tsorace.

Hannunsa ya saka ya sa a kan bakin sa alamar tayi shiru kar ta yi magana.

Takardar da hoton ta nannaɗe ta cusa a cikin rigarta da sauri.

"Smith."

"Ki tsaya a nan."

"Aa kar ka bar ni a nan ni kaɗai Smith mu je tare..." wani ƙarar sautin ta kuma ji sai gata a gaban Smith da sauri ta riƙe hannunsa gam-gam.

Smith ɗin ma a tsorace yake amma haka ya dake ya sa hannunsa biyu kan bakinsa alamar kar ta kuma magana.

Inuwa suka gani ta bayyana a cikin ɗakin, ba a ganin fuskar amma mutum ne a tsaye kakkaura da shi.

Maryam ta saki wayarta a ƙasa don tsoro ta saki ihu.

Smith ya ce "Maryam!"

Tsugunnawa tayi ƙasa ta ɗauki wayar hannunta na rawa ta kuma kunna ftilar amma bata ga kowa ba suka kuma haskawa.

"Smith mu tafi don Allah."

Smith yace "Maryam tsaya ba kya jin warin gas na tashi?"

Idanuwanta ta kwalalo waje tace "Am sorry Smith ni na jawo maka."

"Maryam mu fita daga nan."

Basu kai ga fita ba aka kashe fitilar dake haska ragowar wurin tuni duhu ya lullube ko ina. Maryam na iya jiyo bugun zuciyarta a kunnen ta. Sai kawai ta ji ihu daga sama. Smith ya yi tsalle ya kare ta,yayi da wani abu mai kaifi ya bugi bango.
Chapter 15 · 0% Book details