Sashe 11
Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shugaban kwamiti daga China yace "Mun amince da shirin ,amma ba za mu baka 50% ba sai dai 40% zamu riƙe 60%. Za ka samu kujerar yanke shawara a majalisar gudanarwa, amma rinjayen ra'ayi zai kasance a hannunmu yake."
Muhammad ya san dama za ayi hakan, kuma hakan yake son ayin saboda samu cikar na shi burin.
Leo yace "Me ka ce Muhammad Deal on?"
Muhammad Ya kalle shi yace "Na ji. In har 40% zai ba ni ikon kare wannan shirin,na amince amma ina da sharaɗi."
"Meye sharaɗin?"
"Sharaɗin shi ne za ku sanya hannun jari wajen gina ɗakunan ajiya a ƙasata musanmman a Lagos da Kano. A karo na farko Najeriya za ta zama cibiyar farko,kafin na ku su biyo baya. Idan kun amince da hakan shi kenan deal on."
Gabaɗaya manyan attajiran suka sa dariya haɗe da tafawa Muhammad. Basirasa da wayonsa suke ƙara cusa shi a cikin su.
Shugaban kwamitin Amuruka yace "Ka yi magana kamar zakin da ya san abincinsa. Mun yarda muna tare da kai ,Muhammad Sageer." Ya kira sunan cike da gwaranci.
A nan suka sanya hannu,aka rufe yarjejeniyar. Muhammad ya san wannan rana ce da za ta canja hanyar kasuwanci a duniya kuma ya yi farinciki da Najeriya zata fara anfanuwa.
Daga nan ya nufi airport don zuwa Cairo wurin Aayan.
[9/10, 8:44 AM] Ummulhair S Panisau: RUFAFFEN DUMA.
Ummulkhair Sani Panisau
(khairatup)
Wattpad:khairi_Muhd
Arewabooks:khairatup01
Pg09
*
Aryan zaune cikin wani ɗakin ƴan sanda,zuciyarsa sai rawa take yi masa.Fitilar farin gilashin da ke kan rufin ɗakin ta ƙara bayyana tsananin gajiyar da yayi. Zufa ke keto masa duk da sanyin na'urar da ke bada sanyi (Ac). Ya jingina hannuwansa da kan teburin ƙarfe,idonsa na cike da kewa da fargabar abinda zai je ya zo.
Jami'in da ake kira da Officer Kareem ya dawo da takarda a hannunsa. Muryarsa ta yi nauyi kamar ana auna kowanne harafi kafin a faɗe shi.
"Lallai ka cika mai sa'a ,matashi, babu wanda ya mutu,babu wanda ya ji ciwo. Amma shagunan da ka buge sun lalace kuma ka yi musu ɓarnar kaya . Mai shagon ya amince kada a kai ka kotu,amma zaka biya tara da kuma kuɗin gyaran shagon. Wannan ce kawai mafitar ka."
Kalmar kuɗi da aka ambata kaɗai ta daki zuciyar Aayan ya ji kamar ya yi ƙarar farincki. Ya ɗaga kai da sauri,yana kallon cikin idon jami'in yace "Zan biya! Zan biya komai....kawai kada ku ci gaba da tsare ni a nan ,ba da gangan nayi hakan ba...na.."
"Ƙarasa mana. Ka sha ƙwaya ne."
Da sauri ya jijjiga kai yace "Aa ban sha komai ba,waya ta na ɗauko da ta faɗa a ƙasa." Ya faɗa yana saurin gyara katobarar da ya so ya aikata.
Jami'in ya ɗora takardar a gaban sa. Adadin kuɗin ya yi masa nauyi sosai.Hannunsa ya yi sanyi ,ya dafe kansa ya koma baya ya jingina da kujerar yana jin komai ya kwace masa.
Jami'in yace da shi "Ya ka koma da baya kuma ?"
"Ina son nayi waya da ƴan gidanmu."
Wani irin makirin murmushi Officer Kareem yayi sannan ya miƙa masa waya.
Daddynsa ya fara kira amma bai ɗaga ba, ya kira Mummy ita kuma bata cikin hayyacinta tana can suna hidimar siyayasa. Ƙarshe dole Ayra ya kira a waya ya sanar mata ita kuma ta sanarwa Muhammad a waya.
*
Da Asuba Muhammad y dira ƙasar Cairo. Daga airport Abdurrahman ya ɗauko shi ya kai shi can caji ofis ɗin.
"Mu je can Abdurrahman."
"Yallabai barka da shigowa."
Hannu kawai ya ɗaga masa.
Isar su ke da wuya suka biya komai da aka caje su na kuɗi. Officer Kareem ya dawo da takardar sakin Aryan Barau. Aryan ya kalla wanda ya jingina da bangon cell ɗin idanuwansa sun yi jajir saboda rashin bacci.
"Ka zama mai ƴanci yanzu. Zaka iya tafiya ko a haka ka koyi darasi, young man. Cairo bata yafiya ga masu tuƙin ganganci. Sai ka kula."
Ya miƙa masa hannu ya saka ya juya ya fita ya bishi a baya.
Suna fita ya ga yayansa. Da sauri ya je kusa da shi ya rungume shi tsam. "Na gode Yaya da gaske na yarda kai ɗin kana son mu da zuciya ɗaya. Iyayena ma kasa saurarta suka yi basu da lokacina amma kai ka baro ayyukan ka ka zo ka cece ni.
Na ji kamar duniya ta kulle ni a daren jiya. Ban san yaya zan biya wannan alherin ba."
Sageer dai yayi shiru ,yana nazarinsa. Daga baya ya buɗe bakinsa yace "Abinda zan so ka biya ni da shi mai sauƙi ne. Ka ɗauki darasi da hakan Aryan ka zama mai hankali. Dukiyarmu ba ta da matsala amma sunanmu shi ne darajar mu. Ina fatan ka fahimce ni?"
Aryan ya lumshe ido yana jin tasirin kalaman Yayan nasa sun kuma tsaya mai a ƙirji. Ya san da cewa wannan daren zai kasance ɗaya daga cikin daren da ba zai taɓa mantawa da su ba,zai ci gaba da tunawa da daren a cikin rayuwarsa.
Juyawa ya yi ya fita daga caji ofis ɗin.
A masaukinsa ya sauke shi ba tare da ya fita ba ya ce da shi "Aiko min Ayra na ganta tafiya zan yi."
"Yaya ba zaka shigo ba?"
Kai ya gyaɗa masa "Ba zan shiga ba."
"Saboda gidan Daddy ne?"
"Ka sani kuma kake tambayata?"
"Amma Ya..."
"Ka kira ta ko na tafi. Na baka minti biyu kacal."
Sarai ya san waye Muhammad Sageer tunda ya ce hakan ce zata kasance ɗin.
Gudu ya saka ya shige ciki. Ayra na ta zarya a falonsu ta gagara bacci. Bata san a wanne hali Aryan yake ciki ba Yaya ya bata umarnin kar ta je ko ina ba darajar ta ba ne ta dinga zuwa caji ofis.
Bata yi tsanmmani ba taji muryar abokin tagwancinta a bayanta ba.
Da saur ta juya tana ganinsa ta saki wani irin kuka.
"Aa kafin nan babban Yaya na waje minti biyu kacal ya bamu don ki fito ya gan ki ko ya tafi."
Ai bata tsaya ma sauraransa ba tayi waje da gudu.
Muhammad bai fita daga cikin motar ba, ya sauke gilashin yana kallonsu kamaninsu basu boyuwa duk da sun kasance a ƴan biyun ma wake da shinkafa ne. Cikin motar ta shiga da sauri ta rungume ɗan uwan nata tace "Yaya you are the best!"
Kanta ya shafa yace "Na baki alhakin saka masa ido, komai yayi in bai miki ba call me."
"Yes Yaya in sha Allahu. Zan na gaya maka nima na gaji da halinsa."
"Na sani."
"Ina tsaye fa ake aibatani." Ya faɗa yana yamutsa fuskarsa.
Murmushi kaɗai Muhammad yayi ya kalli ƙannensa ya ce "Kar ku manta ku ƙannen the Muhammad Sageer ne,mamallakin Maryam Logistics. Ina da matsayi da daraja a faɗin duniya gabaɗaya ba iya Nigeria kaɗai ba. Ku kula."
Suka ba shi tabbacin kiyayewa.
Nan suka yi sallama ya tafi ya bar su da kewa.
Hannunta ta dunƙule ta maka ma Aryan a ciki ya saki ƙara yana dafa cikinsa ya ce "Muguwa meye haka me nayi miki?"
"Ka gama tsorata ni. Na ɗauka na rasa ka ba zan kuma ganin ka ba. Me yasa kake aikata abubuwan da ni nake shiga cikin tashin hankali fiye da kai?Ba ka son ka ga na zauna lafiya kullum da abinda zaka yi daga wannan sai wannan haba Aryan meye haka don Allah?"
"Am sorry." Ya faɗa yana kama kunnen shi biyu yana rarrashinta.
"Babu ruwanka da ni Aryan...."
"Ni da ruwana da ke Ayraa... am sorry ba zan kuma yin wani abu da zai ɓata miki rai ba in sha Allahu."
*
Ba a iya hango cikin ainihin ɗakin,saboda tsananin duhun da yake cikin ɗakin. Fitilar hannu suka kukunna suna kutsawa cikin ɗakin.
Jami'ai ne guda uku cikin shigar kayan ƴan sanda da fitilu a hannunsu suna haskawa kansu hanya. Dsp Makarfi, inspector Tanimu da kuma Sergent Ya'u. Akwatuna ne a gabansu cike da kuɗaɗe da kuma makamai masu silencer.
Alh.Barau ya shigo da takunsa na iko da isa,hannunsa riƙe da sigari.
Alhaji Barau ya soma magana da ƙarfi kamar dai kashedi kamar umarni ko tabbaci.
"Kar ku manta ni nan ni ne mahaɗin rayuwar ku. Ba don ni ba da tuni an sallame ku daga aiki. Abinda nake so daga gare ku shi ne sauƙi ,ku tabbata babu wanda ya ƙara magana kan zamba da na yi a kwangilolin gwamnati. Duk mai ƙoƙarin tona min asiri,ku goge mini babinsa daga duniyar gabaɗaya bana son a samu labarinsa kamar dai saura da suka shuɗe."
Dsp Makarfi yace "Alhaji ai kuwa akwai matsala don kuwa akwai wata ƴar jarida Maryam Kabir tana bin diddigin shirin ka na filin jirgin ruwa. Wannan tsohon akwai abinda ya gaya mata kafin ya mutu. Idan ta samu shaida kuwa ina da tabbacin sai ta lalata mana shirinmu."
Cike da mugun nufi ya zuƙi sigarinsa ya ɗaga girarsa yana fitar da hayaƙi ya kalli Dsp yace "Jaridar da al'umma sun fi son labari mai zafi ai. Sai dai wataƙila a biyo ta wani labarin kuma daban. Na san yanda za ayi. A jawo ta cikin wani sharrin ko kuma a ɗauke ta daga doron ƙasar gabaɗaya. Amma aikin ya kasnace kamar hatsari bana son kuskure a ciki."
"Yallabai ba zai yuwu ba."
A fusace ya juya ya jawo rigar Dsp da ƙarfi ya shaƙe mai wuyan sa da ƙarfi yace "In akwai kalmar da na tsana a rayuwata to to kalmar "Ba zai yuwu ba ce."
"Afuwan Yallabai , tana da babban hannu a kanta."
"Waye?"
"Muhammad Sageer Barau."
A sukwane ya juya yana kallonsa yace "Waye kace?"
"Ɗan ka nake nufi Muhammad."
"Ya aka yi yake da alaƙa da ita ban sani ba?"
"Yallabai bamu da labari."
"Zamu sake shiri Dsp. Duk wanda ya ke son taɓa min suna a faɗin duniyar nan zai gane cewa siyasa ba wasa ba ce ba." Yayi dariya mai zurfi ya kalle su ɗayan bayan ɗaya yace "Ku tuna,ni ba kawai ɗan siyasa ba ne.Ni ne ginshiƙin da ke riƙe da duk abinda kuka mallaka. Idan na faɗi,ku ma kun faɗi. Don haka mu yi aiki tare mu tsira tare,don idan nasara ta zo,dukanmu ne za mu ci nasarar."