← Book details Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 28

Sashe 21

Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haƙiƙa wannan shi ne abinda jama'a suke tsanmmani daga gare mu, mu tsaya a gaba, mu faɗi gaskiya,mu kare su ko da kuwa hakan na nufin mu sadaukar da kan mu ne.

Maryam Kabir i am falling in love with your personality. Kina burge ni. In sha Allahu za ki kai matakin da kike so, kuma na miki alƙawari duk runtsi ina tare da ke kuma zan tsaya miki duk sanda kike da buƙata ta a kusa da ke ki kira ni in sha Allah zan zo.

A hankali tana murmushi tace "Na sani. Yaya jikin Smith?"

"Yana lafiya. Ya shiga coma amma muna roƙon Allah Ya ba shi lafiya da wuri."

"Allah Ya sa. Ban san me zan faɗa a gun aiki ba. "

"Ki ce baya nan yayi tafiya."

" Ba zasu yara ba. Smith baya wasa da aikinsa bare yayi tafiya unofficially."

"Kar ki damu wannan damuwar taki ma ta zama tawa."

"Na gode!"

*

Maryam ta ɗauko wayarta ta kira DSP Hamza.

"Yallabai! Zan iya saka ka a cikin mutanen da zan yarda da su? Zan iya kallon ka a matsayin ɗan sanda mai kishin ƙasar sa da kuma son gyara goben al'umma gabaɗaya?"

"Maryam Kabir in na ga rahoton ki ko rubutun ki , sai na tuna da mahaifinki Kabir ,mutum mai gaskiya kuma mai son bayyana gaskiya mun yi aiki da shi , kar ki damu ni ba kamar sauran ƴan sanda ba ne nima ina da ƴa'ƴa mata a gabana kuma na san raɗaɗin da iyayen yaran da aka kwashe suke ji."

"Yallabai na gode. Ina da labarin inda aka kai yaran nan. Ina son ka taimake ni don mu ceto su."

"Zan yi duk abinda ya kamata don gani an ceto su."

"Dajin kuyello nan zamu kai farmaki, akwai wani gida a can cikin dajin inda ake kira da farm house kamar yadda shi wannan matashin ya gaya mini na ɓoye maka ne saboda ina tsoron akwai munafukai a cikin ku."

"Zan zaɓi yara na masu amana da na yarda da su. Zamu yi aikin tare amma ki sani sai dai cikin dare zamu iya kai musu farmaki."

"Ina ciki Yallabai zan bada dukanin wata gudunmowa da ta dace a shirye nake da alƙalamina da kuma kyamara ta don ɗaukar rahoton komai mu isarwa duniya."

"Allah Ya bamu nasara."

Daga nan suka ajiye waya.

Ta so ta kira Muhammad sai kuma ta fasa ta bar shi, saboda bata son ta dinga takura masa ko tana shiga cikin lokacin aikinsa. Ta tuna ma ya gaya mata zai kai wa ƴan uwan sa ziyara ya ga halin da suke ciki.

Da dare suka taru a wuri guda don ɗaukar hanya.Hilux guda uku suka ɗauka ,motar sojoji , motar jami'ai da aka shirya da kayan bada kariya da motar asibiti. Dsp Hamza ya bata rigar kariya (bulletproof) ya ce da ita "ki saka za ta taimaka miki."

Suna tafe yana bata bayani.
"Ba za ki biyo mu ciki ba ki tsaya daga baya-baya. Idan kin ga abubuwa ma sun rikice ki rarrafa ki ɓuya. Kada ki ce sai kin tsaya ɗaukar hoto a tsakiyar musayar wuta."

Maryam tayi ƴar dariya kaɗan tace da shi "Na yi alƙawari. Amma zan tabbatar duniya ta ga abinda ya faru."

DSP ne ya soma yin gaba da yaransa kafin sojoji su ma suka afka. Da rarrafe suka fara kutswa a cikin duhun daji. Sautin kukan ƙwaro ya cika sararin samaniya. Maryam na riƙe da kyamarar ta zuciyarta na bugu da sauri-sauri. Ji suka yi DSP Hamza ya ce "ku jira ,ku jira ,ku dakata..."

Kowa ya ƙame a yadda yake. Sai jin harbin bindiga suka yi yana tashi "ta-ta-ta-ta-ta-ta." Wutar bindiga ta cika dajin ,hasken fitilun sojoji kawai ake gani. Ƴan bindigan da ke sansanin suka fara gudu cikin rikicewa. Wasu suka soma maida martani sai dajin ya koma kamar filin yaƙi.

Maryam ta ɓuya a bayan wata bishiya ta durƙusa daga bayan bishiyar ta saita kyamararta ta soma ɗaukar bidiyo. Ta hango wata rumfar katako daga nesa kaɗan a hankali ta dinga rarrafawa har ta isa gun ƴan matan nan ne a cikin rumfar wasu suna kuka wasu kuma sun rikice suna ta ihu jin yadda wuta ke tashi ta ko ina.

Dutse babba ta ɗauka ta soma ƙoƙrin ɓalle kwaɗon da aka kulle ƙofar da ita.

Ɗayan bayan ɗaya suka dinga fitowa daga cikin rumfar, wasu daga cikin sojojin suka yi masu kwanya suka zagayesu suna basu kariya daga harbin maharan.

Sojan yace "ku kwantar da hankalin ku. Kun tsira."

Haɗe hannayensu suka yi suna musu godiya fuskokin su cike da hawayen farinciki. Cike da tausayawa da kuma farinciki Maryam ta ɗauki hoton wannan yanayin. Abin a jinjinawa sojoji da ƴan sanda ne masu gaskiya tuƙuru don ƙasarsu ba don cin hanci ba.

A fili kuwa tace "Wannan ce gaskiyar da ya kamata mutane su gani su kuma shaida irin gwagwarmayar da masu tsaron mu suke sha a yayin da muke kwance a cikin ɗakunanmu cikin kwanciyar hankali duk da haka ana zaginsu ana kuma shakku a kan yadda suke gudanar da ayyukansu."

Daga baya ɗaya daga cikin maharan ya saita bindigarsa yana san kai musu hari . Wani daga can nesa ya hango su ya saita tasa bindigar ya harbe shi a hannu bindigar ta faɗi ƙasa. Ya soma yarfe hannayensa. Nan aka sa mai ankwa.

"Ku ɗaure su, sune mabuɗin masu ruwa da tsaki a wannan aika-aikar."

Bayan an kame su ne aka tara ƴan matan wuri guda aka lissafa su kamar yadda aka gaya musu duk sun cika kuma suna lafiya sai dai a firgice suke. Maryam ta tsaya tana kallonsu ,zuciyarta ta cika da kwanciyar hankali. Hawayen nasara cike da idanuwanta ta kalle su duka yace "Yallabai Allah Ya biya ka da sakamakon alkairi in sha Allahu ba zaka tagayara ba. Ina son gabaɗaya jaruman nan ku tsaya nayi muku hoton tarihi."

DSP yayi murmushi ya kuma sarwa Maryam yace "Kece silar komai, kuma kece kika bani ƙwarin guiwa har na yanke wannan hukuncin amma na sani bayan wannan abin da na yi zan riski nawa tagomashon na transfer daga wannan division ɗin."

Ta san za ayi hakan dama. Sau da dama idan aka samu ɗan sanda mai gaskiya da kishin aikinsa ɗayan biyu ne, ko a kashe shi ko a mai sauyin wurin aiki duk don ba a son mutane su zauna lafiya. Wato in kai ba ɗan iska ba ne ba zasu bar ka hakan nan ba."

"Aikin ki yayi kyau Maryam. Ke ƴar jarida ce mai hazaƙa da jajircewa mai son fito da gaskiya zan iya cewa ma aiki biyu fa kike yi da namu da naku. Keep it up. Amma ki sani ba nan ne ƙarshen labarin ba, akwai labari a gaba don za a sha artabu wurin ganin an ƙubutar da masu laifin."

"Ba zan bari ba Yallabai, ba zan tsaya ba, ban fara don na daina ba alƙalamina shi ne babban makamina. Sai mun fallasa su. Zan kuma ci gaba da rubutawa har sai gaskiya ta fito."

"Da kyau Maryama."

Nan ta musu hoton. Manyan motocin Hilux suka kwashe ƴan matan da aka ceta. Lokacin da suka ɗau hanyar komawa duhun gari na raguwa yayin da alfijir ke ketowa. Wannan daren ya zama daren tarihi ga Maryam da kuma jami'an da suka yi nasarar ceto yaran da aka sace, sannan ya zama tarihi ga mutanen birnin gwari da suke fuskatar barazana.

Koda suka shiga gari da safe Maryam da sauri ta shiga ofishinsu nan ta samu ta yi dogon rubutu mai shiga rai ta kuma bada umarnin a wallafa da hotunan da aka ɗauka ba ta ma jira umarin ogansu ba don ta sani in ta bayar ba za a wallafa ba za a ɓoye abin ne mutane ba zasu san me ya faru ba.

Wannan lamari sai ya jawo cece-kuce a tsakanin al'umma da ma su kan su gidan jaridar GlobalTimes wanda hakan ya sa aka dakatar da Maryam daga aiki na tsahon wata ɗaya ba tare da albashi ba hakan bai dame ta ba tunda dai ta bayyana gaskiya.

DSP Hamza ya gaya mata za a buƙaci shaidar ta a kotu don sun gama tattara komai sunan dai da wancan matashin ya bayar shi su ma suka bayar.

Ta bashi na'am da kuma tabbacin zata bi bayansa zata kuma bada shaida.

Bayan nasarar farmaki da suka samu a dajin kuyello,DSP ya jagoranci binciken lamarin domin samun ainihin mai laifin. Da farko ƙin yin magana suka yi amma dake DSP mutum ne da ya san ta kan aikin sa sai da ya tabbatar da ya sa ogansu ya buɗe baki. DSP kuwa ya girgiza da jin batun saboda manyan sunayen da ya ambata.

"Shehu da Danzaki. Su ne mutanen da muka yiwa wannan aikin."

Ƴan kasuwa ne shahararru. Masu faɗa aji. Wancan karon ma manyan ƴan kasuwar dai aka kama da sa hannu a irin wannan badaƙalar. Ba tare da ɓata lokaci ba ya kira Maryam a waya. Bata yi mamakin jin sunan ba musanmman da ta tuna wancan ma da aka kama su ya ambata. Nan ta gamsar da DSP Hamza babu ƙage a cikin lamarin wancan matashin ma sunayen ya ambata kuma ya bata adireshin dajin sai dai bata faɗa ba saboda rashin hujja kwakwara amma ba yadda za ayi ace mutum biyu su ambaci suna iri ɗaya a ce ba haka ba ne dole akwai wani abin, in ba rami me zai kawo rami?

"Maryam yaya za a ayi yanzu? Kin san dai kaitssaye ba zamu kai musu hari ba.Manyan mutane masu dogon hannu."

"Yallabai zamu yi amfani da dabararsu wurin kama su. Ta hanya mafi sauƙi."

"Yaya kenan?"

"Media!"

"Media?"

xYallabai zan yi amfani da tawa baiwar don ganin sun fito da kan su ba tare da hukuma ta sha wuya ba." Maryam ta faɗa tana murmushi.

"Maryam me za ki yi?"

"Zan yi sanarwa kan an samu shaida da kuma manyan sunayen ƴan kasuwa da ambatar su zai girgiza duniyar kasuwanci."

"Hakan zai haifar miki da haɗari."

"Na sani, amma ai shi aikin nawa na haɗarin ne."

"Maryam."
Chapter 21 · 0% Book details