Sashe 27
Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan anyi sadakar uku Muhammad ya shiga wani aiki ka'in da na'in wani nauyi aka ɗora masa a kai kuma ya zame masa dole ya sauke nauyin.
Ta hanyar abokan hulɗarsa ya samu lambar wanda zai zame masa tsanin wuce wancan hanyar. Wayar yake kalla da kyau yana kallon lambar kamar wani abu yake son gane abu a jiki.
Maryam ce ta faɗo masa a rai. An sallame ta jiya da yamma kuma bai je ya duba ta ba hasali ma aikawa yayi aka maida su gida kuma bai kirata ba. Baya son ta kuma shiga wata rigimar a cikin wannan ɗan tsukun lokacin, so yake yi yayi nasarar hana ta dukanin wasu bincike har sai ya samu abinda shi yake so,shi yasa yayi amfani da Mama wurin ganin an danne ta na tsahon lokaci. Da kansa ya nemar mata hutu a Global Times duk da bai sanar mata ba.
Iska ya fitar mai ɗumi. Tunanin wanda zai bawa aikin yake yi amma kafin nan sai ya samu tabbacin abinda yake zargi tukunna.
Da ƙwarin guiwa ya ɗaga wayar ya saka ta a kunnensa yana jin tana riging adadin yadda zuciyarsa ke bugu daga can ɓarin aka ce "Hello!"
Sai da ya lumshe idanuwansa tukunna ya amsa.
"Wannan layin wayar prison ɗin NSAWAM ne?"
"Nan ne."
"Yallabai ina son wasu bayanai ne akan wani bawan Allah ɗanuwanmu ne da ake zargin yana can na tsahon shekaru."
"Waye shi?" Mutumin ya tambaye shi kaitsaye.
"Yusuf Kabir."
Sai mutumin yayi shiru kuma bai kashe wayar ba.
"Zan biya ka ko nawa kake so? Amma ka gaya min shin da gaske akwai shi a nan.?"
Mutumin yace "Ba zan ce maka komai ba sai ka zo ka bani kafin alƙalami tukunna."
Muhammad yace "Zan zo amma ka sani komai zaka gaya min."
"Yaushe zaka zo?"
"Ni ina Nigeria ne zan zo wani satin."
"Shi kenan in zaka zo ka gaya min zan gaya maka ta yadda zamu haɗu."
"Na gode." Ya faɗa ya kashe wayar.
Muhammad yayi shiru na tsahon wani lokaci mutum ɗaya kawai zai aika yayi mai wannan aikin ba tare da an samu matsala ko zargi ba. Ba kowa ba ne sai Aminin sa "Faisal."
*
Mama na ɓare mata lemon ɓawo a kan kujera . Ta miƙa mata sai taga bata amsa ba, ɗaga kanta tayi ta kalle ta sai ta ga ba ma ita take kallo ba wani gun daban take kalla.
"Maryam! Yaya dai,tunanin me kike yi ne haka?"
"Abdallah Umar."
"Me kika ce?"Mama ta faɗa cike da mamaki da razanin inda ta ji sunan.
"Mama waye shi? A ina yake?"
"Ban san shi ba, nima yau na taɓa jin sunan a ina kika san shi?"
Maryam ta kalli Mama da kyau sannan tace "Mama kin sani, kin san shi. Abdallah Umar aminin Baba ne tare aka san su. Kin ga kuwa babu yadda za ayi ki ce ba ki san jama'ar da Baba yake mu'amala da su ba.
Mama ta miƙe tsaye tace "Maryam wato ba za ki daina wannan bankaɗe-bankaɗen ba ko?"
"Mama kin sani ba zan huta ba har sai na kai ƙarshen abin. Duk da na yarda zan daina aikin a baya saboda ke,amma yanzu zuciyata ta kasa bani goyon bayan na haƙura da wannan abin musanmman da ya daganci Babana da ɗanuwa na. Mama kada ki tauye ni ki janye kalaman ki a kaina da aikina."
Mama ta ja gauron numfashi. Kamar zata ce wani abu sai kuma ta fasa ta juya kawai ta shige ciki.
"Mam! Mama! Mama! Rashin maganar ki ba zai kawo mana mafita ba. Ki gaya min waye shi? Don ina son na san me ya faru a wancan lokacin?" Maryam ta faɗa da ƙarfi da kuma karaya a muryarta.
Wannan abinda da Mama tayi ya kuma tabbatar mata da cewa ta san mutumin da ake magana a kai wato "Abdallah Umar."
"Hello! Faisal kana ta ina ne?"
"Ya akai?"
"Ina son ganin ka ne ,akwai wani abu kuma da kai kaɗai na yarda."
"Bana kusa yanzu. Ina Kotu akwai ƙarar da zamu kara yanzu."
"Yaushe zaka neme ni?"
"Muhammad meye ne?"
"Wani casen ne nake son na kawo ƙarshen sa. Ka ɗauka ina da buƙatar taimakon ka.Zai iya kasancewa ma zaka tsaya mana a kan case ɗin."
"A ina ne?"
"Ghana!"
"Kai! Wai kai baka da kai ne? Har can ka kai Muhammad me kayi wannan karon kuma?" Ya faɗa ƙufule.
"Ka san dai ba zan sa ka a cikin matsala ba ko? In ka kawo ƙarshen abun fa ka taimake ni ne shi ne tsanin da zan samu abinda nake so."
"Me kake so?"
"Faisal..."
"Muhammad kar ka ce min saboda ita kake yi?"
Muhammad ya masa shiru.
"Muhammad baka da hankali. So kake ni da kai mu nutse a cikin ruwa. Ba zan maka ba."
"Faisal ba don zan tafi Chaina ba ni zan je, Abdurrahman na sa shi wani aikin.kai ne kaɗai ka rage min ka sani."
"Muhammad zan kira ka in na fito,lokaci ya ƙure min."
"Aa tsaya ka bani amsa, za kai yi ko ba za ka yi ba?"
Sai da Faisal ya sauke ajiyar zuciya yace "Muhammad ka sani sarai cewa babu abinda zaka tambaye ni na kasa yi maka,shi yasa kake sako ni a abinda ba zan iya ce maka aa ba. Zamu gauraya da kai. In na fito zan shigo yaushe zaka tafi?"
"Ƙarfe ɗaya na dare."
"Kai ni fa ina Abuja?"
"Huh! Ta nan zan tashi ai zan zo na same ka. Kayi zaman ka in na zo sai mu tattauna."
"Shi kenan ina jiran ka."
Suka ajiye waya. Ba zai gayawa Maryam komai ba har sai ya gano me ya faru har Yusuf ya isa ƙasar Ghana.
*
"Assalamu alaikum!"
"Wa'alaikum salam!"
Mama ta faɗa tana fitowa daga cikin ɗakinta. Bata gane matar ba ,duk da haka ta yi mata iso ta zauna a falo. Ta kawo mata ruwa sannan ta zauna.
Matar ta sha ruwan ta ajiye a kan tebur sannan tace "Ba ki gani ne ba ko Mama ?"
"Ban gane ki ba kuwa baiwar Allah! Yaya gida?"
"Alhamdu lillahi! Na zo wurin Maryam ne."
"Ayya! Maryam kuwa bacci take yi, da yake akwai wasu magunguna da in ta sha su sai bacci ya kwashe ta."
"Allah sarki! Yaya jikin nata?"
"Jiki da sauƙi sosai."
Sai tayi shiru. Sai kuma tace "Mama dama saƙo ne aka aiko da shi."
"Daga ina?"
"Can ofishin su. Ogarsu ce tace a kawo mata ta duba sai ta kira ta."
"To shi kenan za a bata na gode."
Matar ta tashi ta ce "Mama zan koma, Allah Ya sauwake ,Ya sa zakkar jiki Ya kiyaye na gaba."
"Amin-Amin!"
Mama na ɗaukar jakar ta shigar da ita ɗakin Maryam. Akwai wata ƙaramar dirowarta da take ajiye tarkace a wurin da zummar in ta tashi zata gaya mata. Kallon yadda take baccin sadidan kawai take yi ,da gayya ta ce a saka mata maganin bacci don ta dinga hutawa. Ta ja ƙofar ta koma kitchen.
*
ABUJA.
Muhammad na isa suka yi waya da Faisal ya gaya masa inda yake ya je ya same shi.
Tafawa suka yi suna dariya. Kan kujera suka koma suka zauna suna dariya irin ta aminai.
"Muhammadu Sageeru babban mutum."
"Faisal kenan yaya case ɗin?"
"Case Alhamdu lillahi duk da an ɗaga ƙarar."
"Allah bada sa'a. Amma ba wannan ba kana ji na?"
"Ina jin ka."
"Na samu bayani akan yayan Maryam ,Yusuf wanda aka nema aka rasa tsahon shekaru bakwai kenan."
"Ni fa abinda ban gane ba a nan shi ne dalilin da ya sa ka damu sai ka shiga wannan abin."
"Faisal ba zan ɓoye maka ba wannan ita ce hanyar da nake son na samu kan Maryam da ita. Idan na dawo mata da ɗanuwanta zata yarda ta aure ni ,ni kuma in na aure ta zan san yadda na sa tayi amfani da iliminta wurin wancan aikin da muka jima muna jiran tonuwarsa."
Faisal ya kafa masa idanuwansa.
"Faisal ba zan cuce ta ba,amma tabbas ina da buƙatar taimakonta ta bayan fage."
"Muhammad na jima da sanin kai baka da hankali amma yau na tabbatar. Ba wani don manufa ka farka daga baccin da kake yi, son ta kake yi."
"So?"
"Ƙwarai,son ta kake yi."
"Me yasa zaka ce son ta nake yi?"
"Saboda yadda kake damuwa da lamarinta, baka lura ka canja ba? Kira nawa aka min kan rashin halartar taron da aka yi a Amurka akan kasuwancin da kuke son kafa shi ta haɗin guiwa? Ko ka je? Ba kana can kana jinyar ta a asibiti ba? Ka kai ta kun ci abinci, ka daina sauraron Nimra kana kafa-kafa da ita, baka minti kaɗan baka yi tunanin ta ba ko ƙarya nayi maka?"
Muhammad ya koma da baya ya jingina da kujerar ya lumshe idanuwansa.
"Muhammad ka yarda sonta kake yi."
"Na ji ina son ta. Sai me?"
"Hakan nake son ji dama. Son ta kake yi ba wani tausayi ko amfani da ita ka daina gayawa kan ka ƙarya ,kana raina wa kan ka hankali."
"Na daina."
"Yauwa yanzu ne zan taimaka maka."
"Mugu kawai."
Faisal ya sa dariya.
Muhammad ya matsa kusa da Faisal sosai yace "Nsawam prison,Ghana. Sun tsare shi a can a matsayin ɗan leƙen asirin da suke zargi.Kuma abin mamakin shi ne ba a taɓa kai shi kotu ba bare a yi zaman shari'ar. Again babu wani rubuttacen bayani da ya tabbatar da laifinsa.
Ko a nan muna da case mai ƙarfi, Wannan babban laifi ne tsare mutum na tsawon shekaru ba tare da shiri'a ba... hakan ya saɓawa dokokin ƙasa da ƙasa.
Wannan ne dalilin da ya sa na zo maka.Kai lauya ne mai kare hakkin jama'a. Ka tafi Ghana a hukumance ,kamar kana neman wani ɗan ƙasa da aka tsare ba a bisa ka'ida ba. Hakan ne zai baka damar shiga gidan yari a tare da an zargi wani abu ba. Akwai wani ma'aikaci a can zaka kai masa kuɗi zai nuna maka hanya mun gama magana da shi zan baka lambar wayarsa.