Sashe 5
Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Idan kina son ki ci gaba da aikin nan ki daina duba inda ba a ƙarasa shi ba. Gaskiyar da kike nema ba ta da tsira. Ki duba yadda aka yi da Paul Stone,da kuma inspector Sameer...
Maryam ta ɗan ja da baya, amma kafin ta iya cewa komai sai mai motar ya ja da gudu ta ɓace cikin hayaniyar titi.
Hannunta na rawa ta saka hannu cikin jaka ta zaro rikoda ɗinta. Abin mamaki tana jin sautin hirarta da Shehnaz da suka yi a ofishin daidai yadda suka yi.
"Wani ne ya na jin duk abinda nake yi..!" Ta furta a fili a hankali,zuciyarta sai harbawa take yi kamar ana harbi. A gefe,wani tsohon mutumi ne a tsaye a gefen hanya yana kallonta. Kallo ɗaya Maryam tayi mai ta gane shi. "Wannan ai shi ne tsohon maigadin da nake nema. Shi ne ya gaya mini faɗuwar ginin nan shiri ne." Da sauri ta ƙarasa wajensa tace "Baba,don Allah,ka sake gaya min gaskiyar abinda ka sani kafin su gano ka."
Baba maigadi ya kalli dama da hagu,murya na rawa yace "Ƴata...rufaffayiyar ƙofar da kika gani a cikin hoton nan ba ƙofa bace kawai...ƙofar kabari ce da aka ɓoye gaskiya a cikinta.Kuma duk wanda ya kusanci ƙofar nan bai taɓa dawowa da rai ba."
Maryam na ƙoƙarin sake tambayarsa suka ji kukan mota hayaƙi na tashi a bayan su. Wani mutum ya fito daga motar da sauri ya nufi wurin. Cikin sauri Baba maigadi ya riƙe hannun Maryam cike da firgici yace "Ki gudu ƴata! Ki gudu kafin su same ni da ke. Basu da imani basu da tausayi. Wannan labari ne da aka soma rubuta shi da jinin mutane kuma ba a san ranar da za a rufe labarin ba. Bana son ki rasa ranki baki nemo ainihin labarin ba..."
"Aa Baba tare zamu gudu ga ofishin mu nan ba zan bar ka..." bata ƙarasa ba mutumin ya zaro bindiga daga aljihunsa ya yi nufin harbi. A tsorace Maryam ta duƙa ,sai jin ƙarar harbi ta yi ya karaɗe titi. Mutane suka firfito suna guduwa,wasu na ihu, Maryam ta ɗaga kai tana gani Baba Maigadi ya faɗi ƙasa jini na fita daga ƙirjinsa. Hannunsa ya saka cikin aljhunsa ya miƙa mata. Wani lissafi ne da aka rubuta a cikin takardar. "Ki ...ki..je..ki nemo fayil ɗin nan a tsohon ofishin jirgi...akwai takardu..sunan Boss..za ki ..." Bai kai ga ƙarasawa ba, idanuwansa ya tsaya cak. Maryam ta ƙara dafa shi tana kuka. "Baba! Baba! Innalillahi wa inna illahir raju'un.Wannan wanne irin abu ne haka da rayukan mutane suke salwanta a kai? Waye Wannan Boss ɗin? Me ake ɓoyewa haka?"
Juyawa tayi tana kallon gefe da gefen ta sai ta hango mutumin da yayi harbin na ƙoƙarin tunkaro inda take ,sai kuma ya ga motoci sun tsaya da mutane sun fara tururuwa a wurin ,ga mutane suna ihu. Tuni ya juya ya saka facing cap ya shige motar sa ya ɓace daga wurin.
Takardar da Baba ya bata tayi saurin cukuikuyewa ta saka a cikin aljihun rigarta jikinta duk jini da hannunta harda gefen fuskarta. Miƙewa tsaye tayi tana kallon gawar Baba maigadi da ya tafi da sirri mai girma zuciyarta na tafarfasa tare da ɗaukar alwashin koda duniya zata zama gabaɗaya maƙiyanta sai ta bankaɗo Rufaffen Dumar da ake son binnewa. Sai ta nemo waye Bosss,sai gaskiya tayi halinta.
Daga gefe taji kamar ƙarar flash an ɗauki hotonta sai kuma ta juya taga babu kowa a wurin.
Wani saurayi ne daban ya ɗauki hotonta ba tare da ta sani ba.
Tuni ƴan sanda suka soma fareti a wurin.
Ofishin ƴan sanda aka tafi da Maryam don ta bada shaida kan abinda ta gani.
Ta gayawa ƴan sanda komai da ya faru a kan idanta amma bata nuna musu ta san Baba Maigadi ba. Bayan ƴan shige-shige aka rabu da ita ta tafi.
Kafin ta fita ta karɓi duk wani abu da yake nata. Bata daina ganin fuskar Baba Maigadi ba. Tana ganin sa kwance cikin jini tuni ta runtse idanuwanta biyu da ƙarfi cike da tsoro da kuma fargaba.
Smith ne ya kai ta gida suka yi sallama. Sai dai tana shiga cikin gidan sai taji ƙofar a buɗe nata mukullin ta mayar ta shiga ciki. Tana taka ƙafafuwanta taji ta taka abu kasancewar da duhu dole ta lalubi makunin fitila ta kunna. Falon nasu ta gani kaca-kaca an musu ɓarna sosai. Baki ta buɗe ta saki jakar ta a ƙasa ta soma kiran sunan Mama! Mama! Ba wani lungu da bata duba ba amma bata ga Mama ba hankalinta ya kuma tashi ta saki kuka. So take yi ma ta sauya kayanta amma ina tashin hankalin rashin Mama ya fi mata komai a halin da take ciki yanzu.
Tsugunnawa tayi ta saki kuka tana magana ita kaɗai "Mama kina ina don Allah ?Mama kece kaɗai gatana a duniyar nan bayan Baba da Yaya Yusuf kece na ke kalla kawai na ji hankalina ya kwanta Mama zan haukace..."
Ji tayi kamar an shigo cikin gidan ana ta dirgowa tuni ta haɗiyi yawu makwat idanuwanta suka firfito waje. Wayarta ta soma laluba amma ina bata gani ba dole ta tashi ta isa inda ta yarda jakarta ta buɗe ta ɗauko wayar bata kai ga buɗe wayar ba ta ga inuwar mutum a kanta. Hannu na rawa ta ɗaga kanta sama a hankali cike da tsoro da tashin hankali. Majiya ƙarfi ne tika-tikan maza a gabanta sun kai su biyar ko wanne da makami a hannunsa. Yawu ta haɗiya da ƙyar har maƙogwaronta na motsi.
Waya ɗaya daga cikinsu ya miƙa mata. Hannu na ƙyarma ta karɓa ta kara a kunnenta.
"Idan kina son ki rayu kamar kowa ki cire hannun ki daga cikin wannan wasan. Ana buga wasan nan tun kan a haife ki ne. Da yawa sun so su kawo ƙarshen wasan amma sun rasa ran su a maimakon wasan ya zo ƙarshe. In kina son ki ga mahaifiyar ki cikin ƙoshin lafiya ki bamu abinda maigadi ya baki."
"Bai bani komai ba. Ku dawo min da mahaifiyata bata yi muku komai ba."
"Kiyi abinda na ce kawai. Hakan ita ce kaɗai hanyar tsirar ki."
"Bai bani komai ba,bai gaya...."
"Maida masa wayar."
Ta miƙa mai wayar ya kara a kunnensa.
Ya kalle ni ya kalli yaransa suka kalle ni ɗayansu yace "Tashi muje."
Haka na tashi da ƙyar na fita nice a gaba su a bayana suna biye dani. Na gama ayyanawa guduwa zan yi na tsira daga garesu. Ba zasu yiwa Mama komai ba har sai sun mallaki abinsu da ke hannuna ni kuma ba zan basu ba. Wayata na gyarawa zama a cikin riga ta na waiga a hankali na faki idansu na arta a guje. Bayana su ma suka biyo da gudu.
"Kada ki taɓa sayar da gaskiyar ki Mamana. Gaskiya tafi komai a duniya." Kalmomin mahaifinta ta tuna ta kuma ƙarawa ƙafafuwanta iska.
Gudu take yi cikin duhu,zuciyarta na harbawa da tsananin firgici.Hannunta na rawa ta rikice,tana jin kamar duk titin ya haɗu da ita. Fitilun motoci na haskawa a kanta,amma zuciyarta ta kasa tsaida gudu. Bata yi zata ba kawai ta ji ta bugu da abin da bata san meye shi ba. Faɗuwa ƙasa tayi tana maida numfashi. A cikin firgici ta ji ƙarar cin burki.
Ƙofar motar aka buɗe da sauri, jin muryar tayi kamar ta taɓa ji amman ta manta a inda san ta.
"Miss Maryam." Ya faɗa cike da mamaki.
Ɗaga kanta tayi da mamaki ,idanuwanta suka sauka akan fuskar sa. A hankali tace "Muhammad Sageer."
"Subahanallahi, me ya faru da ke kika tsinci kan ki a wannan yanayin haka?"
"Sun kashe shi..sun kashe Baba mai gadi..a gabana suka kashe shi nma zasu kashe ni...kashe ni zasu yi." Ta faɗa murya na rawa tana girgiza kai tana nuna bayanta.
Kallonta yayi sosai,zuciyarsa na gane irin hatsarin da take ciki. Bai sake yi mata wata tambayar ba ya sa hannunsa mai laushi ya kamo hannunta ya ɗaga ta sama sosai ya riƙe mata hannun ganin bata da ƙwari. Dereban sa ya buɗe masa gidan baya ya saka ta a ciki shi ma ya zagaya ya zauna a gefenta.
"Muje Ya'u kar mu tsaya a nan akwai hatsari."
"An gama yallaɓai."
Tsayawa tayi cak tana kallonsa na wasu daƙiƙu,kamar tana duba ko zai iya zame mata aminttacen katanga a wannan rikicin. Sai ta tuna da yadda ya taɓa gaya mata bayan gama interveiw ɗinsu;"Gaskiya komai tsadar ta,ta fi kyau a tsare fiye da a rufe ta da ƙarya." Zuciyarta ta ɗan lafa daga bugun da take yi.Ba tare da ta sake jajjaya ba tayi shiru tayi luff abinta ajikin kujerar ta kwanta.
Muhammad Sageer ya kalle ta ,ta gefen ido,zuciyarsa cike fal da tarin tambayoyi amma ya san ba zai samu amsoshinsu yanzu ba.
*
"Ta gudu boss. Bamu yi nasarar kamata ba. Kuma mun duba ko ina a gidansu bamu samu komai ba."
Wanda aka kira da Boss ɗin kuwa ya saki wani irin ihu yana wurgi da duk abinda ya zo gabansa.
"Sai na kashe ku idan baku yi wani abu akan wannan ƴar ƙaramar yarinyar ba. ƴar ƙarama da ita tana son ta shiga cikin kunnena ta hana ni bacci? Ba zan yarda ba, ba zan laminci haka ba."
"Kayi haƙuri Boss ka ƙara min lokaci. Zamu samo maka ita."
"Ba ita ce a gabana yanzu ba. Duk waɗan da kuka san sun san wani sirri bisa wannan aikin nake so a hallaka min su bana son su rayu suga safiyar gobe. Ku ɓace min daga nan."
"An gama Yallaɓai."
*
Gidansa suka nufa dama daga tafiya ya dawo.
Gidan Sageer na cikin ɗaya daga cikin unguwa mai nutsuwa,kusa da manyan tituna amma ba cike da hayaniya ba. Fentin bangon gidan fari ne mai sheƙi ,sai wasu layuka da aka zana da launin kore a ƙasan bangon da ya bambanta gidan da sauran gidajen unguwar.
Kofar shiga gidan babba ce,an yi ta da ƙarfen zamani mai haske,aka rataya masa ƙararawar tsaro (security bell). Kusa da ƙofar akwai ƙaramin lambu mai cike da furanni zuma-zuma,tulips da roses da suke ba wa gidan ƙamshi da kyan gani.