Sashe 25
Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Likitan ya fito da farar riga a jikinsa yana cire handgloves ya gyara zaman gilashinsa.
Nas ta miƙa masa takardu. Akwai alamun gajiya akan fuskarsa,sai dai ganin yadda iyalan masu jiyan ya saka ya saki murmushin kwantar da hankali. Dukansu miƙewa suka yi tsaye suna jiran ƙarin bayani amma na alkairi ba na sharri ba.
"Alhamdu lillahi, muna miƙa godiya ga Allah da ya bamu nasara wurin shawo kan matsalar.
Dsp na samun kulawa sosai yana fitas da numfashinsa yadda ya kamata ba kamar sanda suka zo ba.Mun yi nasarar cire musu harsashin duka su biyun. Maryam dama kafaɗarta harsahin ya same ta sai kuma shock da ta shiga. Zamu bar su under observation na tsawon awa ashirin da huɗu."
Matar Dsp tace "Likita ka tabbata mijina zai tashi?"
"Hajiya mu aikin mu shi ne ceton rai amma rayawa ko kashewa ta Allah ce. Mun dai yi amfani da dukanin wata kimiya don ganin sun samu lafiya. Ku ci gaba da addu'a."
Mama ta share hawayenta tana godewa Allah.
Ƴan jarida dake gefe sun ɗauki rahoton likita da hotunan mutanen wurin don tura rahoton gaggawa ga gidajen radiyo da talabijin.
Inspecto Aliyu Sa'ad yace "Alhamdu lillahi, lallai Allah Ya kare su. Wannan aikin namu aiki ne da sai da addu'ar al'umma da ta iyaye gabaɗaya."
Muhammad da ke gefe kuwa ya jingina da bango,zuciyar sa na bugu da sauri, ajiyar zuciya ya sauke ta farinciki da shafin Maryam bai zama labari ba.Maryam tana raye."
*
Zaune yake a falonsa. Falon da duhu kasancewar ya kashe dukanin fitilun ciki. Hannunsa a kan haɓarsa yana kallon talabijin.
_An tabbatar da cewa Dsp Hamza da Maryam suna cikin ƙoshin lafiya,amma za a barsu under observation na tsawon awa 24._
A fusace ya yi wulli da remote ɗin ya miƙe tsaye. Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke sannan ya fara magana shi kaɗai cike da murya me nuni da ƙiyayya.
"Na kashe kuɗi, na tsara dabaru don ganin bayan wannan yarinyar amma duk a banza, wato ba zasu mutu ba musanmman ma wannan ƴar jaridar. Dsp ma yana raye , Maryam na numfashi..." Kujerar bayansa yayi cilli da ita ta doku da garu.
"Ba zan tsaya ba. Kuma ba zan bari su fito da rai ba. Tashin Hamza barazana ce a gare ni da daula ta, iko na zai taɓu, mulkina zai taɓu mutunci na zai zube komai zai fita daga cikin rayuwata. Rayuwar da na kai tsayin lokaci ina gina ta fitowarsu daga asibiti daidai yake da tonuwar sirrina a duniya." Ya faɗa a fili yana naushin iska.
*
Washegari!
A hankali idanuwan ta ke motsi alamun suna ƙoƙarin buɗewa ne. A hankali ɗan yatsan ta ya motsa. Muhammad da ke tsaye a kanta ya kuma matsawa jikin gadon. A hankali ta buɗe idon sai kuma ta rutse da sauri saboda hasken da ya shigar mata a bazata. Bayan kaman sakan biyu sai ta kuma buɗewa a hankali tana ganin komai dishi-dishi kafin ta buɗe su tar. Ba ta yi zata ba Muhammad ta gani a gabanta a tsaye yana kallonta. Allurar bata gama sakinta ba hakan ya saka da ta yi ƙoƙarin tashi ta koma da baya ta kwanta ta ɗan saki ƴar ƙara. "Arh!"
"Miss. Maryam! Yau dai ga taurin kan ki ya ja miki kwanciya a gadon asibiti,harbin ki fa aka yi, harsashi da aka cire daga kafaɗar ki gashi nan hannun naki ya samu matsala an ɗaure miki. Ina fatan kin yi farinciki da hakan don dama kin san hakan zata iya kasancewa da ke."
Maryam ta ambaci sunan Allah a hankali tace "Ya Salam!Bani da lafiya fa amma kake yi min faɗa."
A hanali ya tafa hannayensa biyu amma basu bada wani sauti ba. "Sannu Miss, ashe dai bakin bai mutu ba?"
"Ba zai mutu ba."
Kujera ya jawo ya zauna a kai yana kallonta wannan karon babu wasa a kan fuskarsa.
"Miss ,ba wasa nake ba. Da gaske nake wannan karon. Babu ruwanki da wani binciken tsohuwar tasha,ko Paul Stone ,ko inspecto Sameer ko garkuwa da mutane bare a kai ga ba da shaida a kotu. Baki ga halin da muka shiga ba jiya. Ba ki ga Mama yadda ta shiga ainihin tashin hankali ba.Miss ki ajiye makaman yaƙin ki. Ba ma son mu rasa ki. Da ace harsashin ba taɓa ki yayi ya fita ba da ba wannan maganar muke yi a nan ba ni da ke."
A hankali cike da murya mai jinya tace "Ba zan iya yin shiru ba Muhammad.Ba zan kuma ja da baya ba. In na mutu kwana ne ya ƙare, ba zan gudu don iya wannan ƴar barazanar ba."
Ya dalla mata harara yace "Na ji kamar kin ce ƴar barazana? Baki da hankali."
Murmushi tayi. Sai a lokacin ta tuna harda Dsp ba ita kaɗai bace.
"Muhammad ina Dsp?"
"Yana ɗaya ɗakin. Ya fita daga haɗari kamar ke dai."
"Basu da imani kuma basu da tsoro. A cikin mutane fa kafin mu gane me yake faruwa har sun kuma kai mana wani harin."
"Wanda ya riga ka bacci zai riga ka tashi."
"Amma..."
Yatsan sa ya saka akan labbansa yace "Shhhh! Koma ki kwanta kin tashi za ki dame mu da magana ki ki ki."
Ta zumburi bakinta gaba ta yi mai kalar tausayi.
Ya kama kunnensa ɗaya yace "Sorry."
Ta gyaɗa masa kai kawai.
"Ina son na ga Dsp."
"Bai farka ba ai."
"Eh duk da haka ina son na ga yanayin jikinsa."
"Ki bari na tambayi likita in ya amince sai na kai ki da kaina."
"Muhammad..."
"Maryam..."
Sai kawai tayi shiru don ta ga alama ba zai bar ta ba.
Tashi yayi tsaye yace "Bari na je na gayawa likita kin tashi har za ki ma iya kai naushi."
Murmushi kawai tayi mai. Yana fita ta dafa hannun mai ciwo tana cije baki kaɗan saboda azabar zafi.
Muhammad bai dawo ba sai da likita. Bai samu Mama ba bata nan ta koma gida ta yi wanka ta ɗan huta.
A hankali likitan ya saki murmushi yana kallon hannun yadda aka naɗe shi da bandage a hankali. Muhammad ya zagaya gefen ta ya tsaya hannunsa rungume a kan ƙirjinsa. Yana kallon likitan da Maryam calmly.
"Sannu Maryam." Likitan ya faɗa yana murmushi.
Maryam ta juya idanuwanta a hankali kafin tace da shi "Alhamdulillahi. Na ji sauƙi ma."
"Ashe kece ma likitar?"
Ta ɓata rai.
Ya zaro wayarsa daga aljihunsa ,shi ma ya basar kamar ba shi ne yayi maganar ba.
Vidio recording ya shiga ya saita saitin Maryam da yadda take yamutsa fuska duk don fa kar a taɓa mata hannun ne take cewa wai ta warke.
"Likita ka gaya mai ya daina yi mini vidio. Bana so."
Likita ya ja hannun a hankali kaɗan yana son ya ga ko ya koma. Ta saki ƙara tace "Wayyo Allah!"
"Kar ki damu dislocation ne ai. Zai warware da sauri." Har wata guntuwar ƙwalla sai da ta zubo mata. Muhammad yayi murmushi mai sauti yaca "Ashe jarumai ma na kuka? Serves you right. In halin ki ne gobe ma ki ƙara."
Ta zabga mai harara.
Yace da ita "Ai ina jindaɗin ganin yadda kike complain ɗin nan. Kin ga ina ɗaukar miki shaidar kin ji jiki nan gaba zan nuna miki in kika cika min baki. Wannan fa tarihi ne."
Likitan yayi dariya yace"Yana da kyau ,zai taimaka miki ki tuna yadda kika yi jarumta. Jiya dama mun yi miki X-ray kamar yadda na faɗa gocewar ƙashi ne kawai,amma an mayar miki da shi daidai,saidai dole ne mu ci gaba da kula da ke da lura da hannun har zuwa gobe."
A hankali ta kalle shi tace"likita bayan wannan babu wani abun dai ko?"
Zaunawa yayi a hankali yace "Aa , babu babban haɗari. Amma saboda bullet ɗin ya taɓa naman wurin da jijiyoyi ya wuce ,muna son mu tabbatar babu infection kuma zafin ya ragu sosai kafin mu sallame ki."
Muhammad ya katse musu maganar ya na tattare girarsa a wuri guda ya ɓata rai yace "Kin ji ko? Ke dai ki huta kawai, ki daina damuwa , na sani ke ma kin fi bullet ɗin ƙarfi amma for now dai ki bar kan ki ya huta."
A hankali ta zumɓuri bakinta kuma lokaci guda ta saki murmuashin gefen baki taca "Ka ga fa,ni dai sai na hana a dinga bari kana shigowa tunda damuna zaka na yi."
Ya nuna kansa da yatsan sa yace "Kuma wai ni? The Muhammad Sageer?"
Ta maka mai harara.
Shi dai likitan dariya sukw ta ba shi. "Kun burge ni. Kada ki damu Maryam ƙyale shi. Ke da vidion ma zai saki nishaɗi ne in kika kalla kika ga yadda kike matsw ƙwalla kina ɗan ihu. Kinga kuma dama ana son mai jinya yana dariya. Zan aiko Nas ta kawo miki hot pack don ya taimaka miki wajen rage raɗaɗi."
Maryam ta sauke ajiyar zuciya tana murmushi tace "Na gamsu kuma na samu ƙwarin guiwa yanzu."
"Ki huta sosai,ki sha ruwa.Idan Allah ya so gobe sai mu sallame ki."
Muhammad yayi zooming kan fuskarta sosai musanmman don ya ɗauki murmushinta sosai,shi ma cike da annashuwa ya saki murmushin. Likita yayi musu sallama ya fita daga ɗakin.
"Don Allah Muhammad yaya jikin Dsp? Da gaske ina son na gan shi. Saboda ni ne aka yi masa haka, duk wanda ya raɓe ni sai wani abu ya same shi, ka taimake ni ka kai ni in gan shi don Allah!"
Ya lumshe manyan idanuwansa masu rikitar da mutum. Sai kuma ya mike tsaye ya fita. Har ta cire rai kuma sai ga shi ya shigo tare da Nas a bayansa. Tayi masa kallon tuhuma.
Ya ce da ita ga ta nan zata raka ki. Amma likita yace minti biyu ma ya wadatar da ke ki gan shi baya son hayaniya.
Da sauri ta gyaɗa kai ta yarda. Nas ta taimaka mata wurin tashi suka raka ta ɗakin da Dsp yake a kwance. Suna shiga ta ga matar Dsp a zaune kan kujera tana kallon mijinta. Ga ƴarsa da ɗansa duk sun yi zugum tuni zuciyarta ta karye. Ta zama bata da wata laka ta gama sa wa a ranta ita duk wanda ya raɓe ta sai abu ya same shi.