Sashe 6
Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Akwai haraba mai fili da faɗi. Falon babba ne ,an shinfiɗa tiles masu sheƙin fari da ruwan toka. A tsakiya kuwa akwai ƙaramar rijiya ta ado (fountain) mai fitar da ruwa a hankali,abin ya ƙara wa wurin nutsuwa.
Falon ya kasance na zamani,kujeru masu launin ruwan madara da aka yi musu ɗinki cikin tsari. Babban Tv ne manne a bangon falon an zagaye shi da shelves masu ɗauke da litattafai da kayan ado. Hasken fitilu masu launin zinariya a rataye da chandeier mai walƙiya.
Ɗakunan barci kuwa,kowanne an yi masa ado da salo daban-daban. Babban ɗakin Sageer kuwa gadon ɗakinsa king size ne mai farin zanin gado,labulayen masu duhu ne domin suna hana hasken rana shiga.
Kitchen ɗin ma na zamani ne ,gabaɗaya an yi da turmi mai sheƙin baƙi da farin granite. Kayan girki kuwa duk na zamani ne. Microwave,oven,da fridge babba.
Bayan gidan kuma akwai ƙaramin wuri na hutawa inda aka gina katanga. Akwai kujeru na roba tare da tsire-tsiren ado. Wannan wurin shi ne wurin da Sageer kan zauna idan yana son yin tunani shi kaɗai.
[9/9, 11:27 PM] Ummulhair S Panisau: RUFAFFEN DUMA.
Ummulhair S Panisau.
(Khairatup)
Wattpad:khairi_Muhd.
Arewabooks:Khairatup01
5
Ruwa ya bata. Ya lura har lokacin jikinta bai bar rawa ba. Sai haki take yi.
Amsar kofin tayi ta sha ruwan hannunta sai kyarma yake yi.
"Ki nutsu Miss Maryam. Ba abinda zai faru kina hannu mai kyau."
Kai ta gyaɗa masa tace "Mamana, sun ɗauke min Mama ,ban san a wane hali take ciki ba. Bana son na rasa ta."
Zaunawa yayi a gefenta. A hankali ya anshi kofin yace "Ki nutsu babu abinda zai faru in sha Allahu. Amma su waye suke bibiyar ki ? Kuma me kika yi suke bibiyar ki? Ku fa ƴan jarida kun iya shiga abu mai hatsari amma in aka far muku kun fi kowa tsoro. Me yasa kike yin abinda zai shafi lafiyar ki da kuma ta na kusa da ke?"
"Ban yi komai ba. Aikina ne na bankaɗo laifuka na kuma fito da gaskiya."
"Well! Serves you right. Yanzu fargaba ma kaɗai ta ishe ki ina gaskiyar ina ƙaryar?"
"Kana namiji amma kana tsoro?"
Dariyar gefen baki yayi yace "Ba tsoro nake ba ina kiyaye lafiyata ne. Ina da buƙatar na kasance lafiya. Saboda akwai dubban al'umma da suke samu su ciyar da iyalinsu ta ƙarƙashina. In na jawo wa kaina maƙiya bayan wanda nake da su ai za a samu matsala. Wani wasan ba a buɗe ake yin shi ba, ta ƙarkashin ƙasa ake yin sa. Ina fata kin gane ko kina buƙatar ƙarin bayani?"
"Ban fahimta ba."
"Miss Maryam! Bani da lokacin ɓatawa. Zan kwanta za ki iya zama a nan na kwana biyu har a gyara gidanku sannan zan saka a binciko miki mahaifiyar ki."
"Ta yaya zaka nemo ta?"
"Ki ka sani ko na san su?"
Ta zaro idanunta waje sosai ta na matsawa baya cike da tsoro a cikin ranta kuwa cewa tayi "Kar dai na yi gudun gara?"
Murmushin dai da ya saba yayi yace "Come on wasa nake yi."
Wani ɗaki ya nuna mata daga gefe yace "Za ki iya sauka a nan." Daga nan ya wuce ya bar ta a wurin.
Takardar ta jawo wannan tashin hankalin ta ciro daga aljihun rigarta ta ƙare mata kallo. Hango fuskar Baba maigadi tayi a cikin takardar tuni ta runtse idanuwanta gam har a lokacin tana jin jinin shi a jikinta.
"Su waye wannan ? Me suke so ? Su waye Paul Stone da Insp.Sameer Ibrahim.? Idan ina son sanin abin da yake faruwa dole ne na san su waye su kuma meye mafarin komai." Da wannan shawarar ta kwanta bacci.
*
Ɗakin taron a ɗinke yake da manyan mutane sanannu a idon duniya bakiɗaya. Ɗakin a cike yake da nauyi da kuma hasken fitilu na ruwan zinare yana walkiya. Tagogi da labulaye duk a rufe suke kun san dai bango ma yana da kunne. Teburi ne mai faɗi zageye da shahararun mutane masu ji da kan su. Ƴan siyasa ,ƴan kasuwa,ƴan jarida,tare da ƴan sanda.
Ƴan siyasa fuskokinsu ɗauke da murmushi mai ɗauke da siyasa ,kowanne na kallon ɗan uwansa da idanuwa tamkar ƴan adawa.
Ɗaya daga cikinsu ya yi gyaran murya,yana kallon kowa cikin nutsuwa. "Mun taru a nan domin mu tabbatar da cewa kasuwancin mu na makamai zai ci gaba da gudana ba tare da wata tawaya ko tsangwama ba. Dukaninmu a nan mun san me muke nema wato "Kuɗi ,iko,da kuma kariya daga bincike."
"Sanata Shamsu Waziri me ka zo da shi?"
Sanata Waziri ,mutum ne da jama'a suke gani a matsayin jagora na gari mai kuma kishin ƙasa ,amma a zahirin gaskiya shi ne ginshikin wannan taron na cin amanar ƙasa. Ya ɗauki gillas ɗin da aka zuba masa giya a ciki ya kurɓa yana murmushi cike da makirci yace "Dole ne mu daidaita. Gwamnati na neman ƙarin kuɗaɗe,jaridu na neman labarai ,ƴan sanda suna neman rabo. Yanzu ba mu da lokacin wasa ,duk wanda ya karya doka ko yarjejeniyar da muka kafa,zai iya shiga cikin jerin mutanen da za a iya kawar da su a doron duniya."
Daga gefensa wani ya saki dariya yace "Mutuwa ko rayuwa,duk ciniki ne. Amma muna da buƙatar tabbatar da cewa jama'a a waje suna ganin wannan taron a matsayin tattaunawar tattalin arziƙi ba wani abun daban ba."
"Alhaji Ma'aruf ka faɗi magana mai kyau. Ka san kuwa yanzu an fara sa wa lamuran ƙasa idanu?" Cewar Tanimu Gata kwamishinan ƴan sanda.
A nan dai suka ci gaba da tattaunawa a kan abubuwan da suka shige musu kai.Musanmman ma da suke zargin wani ɗan jarida da ya saka musu idanu.
Paul stone da ya jiƙe jagab da gumi a cikin drowar da ya ɓuya ya ji cikinsa ya ɗuri ruwa kenan sun fara zargin yana sa musu ido kenan. Ƴar ƙaramar kyamararsa ya maida cikin wata ƙaramar jakarsa da ya gama ɗaukarsu a hoto ba tare da sun sani ba.
Takardar ya kalla yana tunanin wannan ba iya taron yadda za a shigo da makamai ba ne makomar ƙasar ce gabaɗaya.
Bayan kowa ya fita da mintina talatin ya fito daga maɓoyarsa. Ta inda ya salallaɓo ya shigo ta nan ya koma. Yana fita ya saka facing cap ya sa face mask amma a sauke kan haɓarsa ya saka baƙin gilashi. Jakarsa ya gyarawa zama a kafaɗarsa ya kuma karya kwana yana karya kwanar kuwa ya ci karo da wani yaron Ogansu.
"Yallaɓai Paul me kake yi a nan?"
Paul ya haɗiyi yawu da ƙyar ya fuske yace "Na zo na gana da wani ne. Me kake yi a nan?"
"Tare muke da Oga. Yau sun yi wani meeting ne."
"Okey. Bara na tafi sai mun haɗu a ofis." Ya faɗa yana raɓarsa ya wuce.
Bin sa yayi da kallo bai yarda da shi ba. Hakan ya saka ya zaro wayarsa ya soma kiran Ogansu.
*
Paul Stone na fita kuwa ya san cewa akwai matsala asirinsa ba zai rufu ba zasu zarge shi. Wayar sa ya zaro ya kira amininsa Smith sai aka yi rashin sa'a Smith bai ɗaga wayar ba. Sau uku yana kiran Smith amma bai ɗaga ba sai ya tura masa da saƙo. "Akwai babban al'amari da ake shiryawa a kan ƙasata da talakawanta ina buƙatar taimakon ka Smith." Ya tura masa da saƙon. Sai dai tun kafin ya tsallaka wurin motarsa wata farar mota bus ta sha gabansa aka ɗauke shi aka sa shi a ciki.
Daga wannan ranar babu wanda ya ƙara ganin Paul bare a san me ya same shi.
"Yallaɓai Waziri!" Firgit yayi ya dawo cikin hayyacinsa ya juya ga babban yaronsa.
"Ka tabbatar da cewa Paul Stone ba ya raye?" Ya jefa mai tambayar kaitsaye.
"Yallaɓai me yasa ka tambaya?"
"Abubuwa ne na ga suna son su rincaɓe mana gabaɗaya. Akwai wani abu da bama gani kuma yana kusa da mu."
"Yallaɓai kamar saura shi ma babu shi. Ka kwantar da hankalin ka."
Zaunawa Sanata Waziri yayi ya ɗora ƙafarsa ɗaya a kan ɗaya ya zari sigari guda ɗaya ya saka baki ya kunna yayi mata zuƙa ɗaya. Kusan minti biyu bai kuma cewa komai ba sai daga ƙarshe yace "Kuɗi da jini,ɗaya suke."
"Wannan haka yake Yallaɓai."
"Me ya kawo ka?"
"Akwai saƙo ne daga Boss."
"Boss?"
"Ƙwarai Yallaɓai.!'"
"Me ya faru?"
"Akwai wata ƙura da take son kunnowa ne."
"Wai ƙurar nan ba zata bar mu haka ba? Kar fa a zo ayi ƙurar da zata kwashe mu gabaɗaya."
"Ah haba dai Yallaɓai wannan ƙurar ƙarama ce ba zata yi wuyar lafarwa ba. Ɗankwali ce."
Ya fashe da wata iriyar dariya yana kallon yaronsa Teemo yace "Teemo gaskiya ne a gayawa Boss wannan ɗankwalin na sharar datti ne kada ya damu ko Bangis ma ya isa yayi maganin ta."
"An gama Yallaɓai. Na barka lafiya."
Ya ɗaga mai hannu kawai ya zaro wayarsa.
"Akwai wata ƙaramar ƙura da ta taso kuma ance min daga ɓarin ku ne. Ina son ayi min maganinta da gaggawa."
Daga ɗaya ɓarin yace "Yallaɓai ai ina shirin kiran ka ,ka kira ni. Saƙon Boss ya iso mini kuma ina kan aiki a kai. Sai dai fa tayi ɓatan dabo amma akwai asawarta a hannunmu."
"Ni kuma sai nake ganin a saki asawar ta ta. Zamu haɗa mata babban shiri a sauƙaƙe zamu gama da ita. Amma ba ta wannan hanyar ba idanuwan jama'a ya fara dawowa kan mu kar kashe-kashen yayi yawa. A sannu ake taku. Ina fata ka gane?"
"Na fahimta, zan kira Gata yanzu sai ka ji mu."
*
Gata na kwance a wani ɗakin otal gefensa budurwa ce sun gama sheƙe ayarsu. Yana ganin wayarsa ta fara haske ya tunkuɗa budurwar daga gefensa yayi mata nuni da hanyar waje. Ta kalli jikinta da mugun mamaki da tunanin ta yaya zata fita a haka babu wasu cikakkun kaya a jikinta?
Bai ɗaga wayar ba, ya kalle ta yana zare mata idanuwa ya yi mata nuni da hanyar waje ya ɗebi kayanta ya watsa mata tare da jefa mata bandir ɗin kuɗi a kan fuskarta.
A fusace ta rarumi kayan da kuɗin tana gunguni ta fice waje. Tashi yayi ya maida ƙofar ya rufe ya ja labule ya koma kan kujera ya zauna.