← Book details Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 28

Sashe 13

Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba zato ba tsanmmani ta gan shi a tsaye a kanta. Tashi tayi tsaye cike da mamaki ba ita kaɗai ba sauran ma'aikatan ma suka miƙe tsaye.

"Yalla...."

"Shhhhh... ya isa ba surutu na zo ba. Na zo ne in gaya miki lallai fa maganar mu na nan ba mantawa nayi ba nayi tafiya ne amma na dawo."

Ta juyar da kai gefe ganin yadda kowa su biyu yake kallo. Ta rasa ma me zata ce masa kunya da mamaki duk sun ɗaure ta da jijiyonta. Wani irin kallo yake bin ta da shi wanda shi kan shi bai san yana yi mata ba.

Kayan na sa ta kuma kalla ta ɗan ɓata rai tace "Haba kai kuwa mai babban suna, me yasa kake son saka baƙaƙen kaya musanmman ma shi wannan suit ɗin? Shin ba ka da wasu launukan da kake so bayan baƙi?"

Dariya ta ba shi haka ya saka ya sakar mata murmushi mai ɗauke da sirri,ya gyara tsayuwarsa ya kafa mata idanuwansa irin wanda ake kira da sexy eyes. A hankali ya ƙara matsawa kusa da ita har tana iya jin ƙamshin turarensa mai sanyi da kwantar da hankali.

"Kina son ki san dalili?" Ya tambaye ta a hankali muryarsa cike da nutusuwa.

Ta girgiza mai kai da sauri. Duk sun manta ma a inda suke kuma a tare da wa suke.

"Baƙi launi ne da yake ɓoye komai. In na ce miki komai ina nufin komai. Baƙi na ɓoye rauni, ɓoye sirri. Ni mutum ne da nake son a fahimce ni ba iya ta waje na ba sai dai ta zuciyata."

Ta kasa daina kallonsa ,shiru ya ratsa tsakaninsu. Ta kuma kasa kawar da ganinta daga kan fuskarta. Zuciyarta tayi mata wani irin tsalle. Sai kuma tayi dariya a hankali ,ta ce da shi "To idan ka ce baƙi launin da ke ɓoye sirri ne...to ni me yasa ka faɗa min sirrin naka?"

Matsowa yayi sosai kusa da ita ya ɗan durƙusar da kansa ƙasa daidai saitin kunnenta yace "Saboda ke....Saboda bana son na ɓoye miki komai wanda ya shafe ni."

Ɗan baya tayi kaɗan ta saka idonta a kan fuskarsa tace "Ban..." ya yi saurin katse ta yace "Kar ki tambaye ni dalili ,don nima ban san dalilin ba."

Juyawa tayi ta ga yadda ake kallonsu. Ta yi saurin matsawa da baya ta dabuburce a hankali tace "Mr.Muhammad ana kallon mu fa ,ka je zan fito yanzu".

Kafaɗar sa ya ɗaga yace "Ban damu ba. Zan aiko miki da gayyata ban manta ba dai alƙawarinmu na nan na dinner gobe."

"Akwai aiki fa."

"Zan gayawa Ogan naku ni bani da matsala da hakan."

Ta saki baki tana kallonsa.

"Rufe bakin." ya faɗa a hankali cike da sanyi. Haka ya juya ya fita ya bar ta da tunani.

Tambayar kanta tayi "Me ya faru haka yanzun nan?"

Gabaɗaya sai ta ga idanuwan abokan aikinta a kanta. Fuskewa tayi ta koma ta zauna haɗe da runtse idanuwanta cike da kunya ƙirjinta na bugawa da sauri-sauri.

Bata gama dawowa daidai ba wani ya shigo da katuwar fulawa a tsakiyarta akwai wani ɗan ƙaramin kati. Da wani ƙaramin akwati ya ajiye mata ya juya ya fita.

Da mamaki ta saki baki cikin ranta tace "Me kenan ni Maryamu?"

Smith ne ya taso ya zo inda take yana mata murmushi irin na shaƙiyanci yace "Ooo me yake faruwa ne tsakaninki da wannan hamshaƙin , kar dai daga interview an zarce matakin ILU?"

Ajiye flower ɗin tayi a gefe ta harare shi cikin wasa tace "No, we are just friends."

"Kin tabbata?"

"Na tabbata."

"Amma ki rubuta ki ajiye he is in love with you."

Ta ware masa idanuwanta duka waje tace "Smith...."

Ya ɗaga mata kafaɗa ya tashi daga kan teburin ya koma wurin zaman sa.

Ita kam yau ta ga banu wannan mutumin ya gama da ita kowa da abinda zai ce a kan su, ita kam zuciyarta ma bata daina bugawa da sauri da sauri ba. Amma ba ma wannan ne yanzu ya fi damun ta ba so take suyi magana da Smith.

A gurguje ta ƙarasa aikinta. Smith ta jira a waje. Yana fitowa ya ganta a tsaye da jakar ta a hannu.

"Miss Maryam baki tafi ba?"

"Kai nake jira ai."

Ya kalli agogon hannunsa ƙarfe 8:30pm na dare.

"Dare yayi fa."

"Na sani. Na gayawa Mama zan jima."

"Amma ba kya tsoron ko ana bibiyar ki?"

"Na yarda da ubangijina, Allah Yana tare da ni."

"To muje."

A daidaita sahu suka tara suka tafi. Suna tafe suna hira a nan ne Maryam ta lura da ana bi  n su a wata baƙar mota tinted wuluk.

"Kar ka yi reacting na lura waccar motar bin mu take yi tun daga bakin ofis."

"Haba dai." Ya yi ƙoƙarin juyawa tayi saurin jan hannunsa ya koma ya jingina sosai. Dole suka sauya shawarar haɗuwa a wannan daren a gida ya sauke ta sannan ya wuce. Tana lura da yadda motar ta faka a gefen gidansu kaɗan ta fuske ta shige ciki.

Text tayi masa kan zasu yi magana gobe amma da safe kafin a soma aiki su a haɗu a canteen ɗin cikin ofis ɗin.

Washegari.

Da sassafe ta shirya ta fita saboda zumuɗi da zaƙuwar son ganin Smith.

Sun yi waya da shi har ya isa ma shi. Dama sun tsara kan zai rigata zuwa don ta lura kamar ita ake bibiyar rayuwarta da takunta.

A canteen suka haɗu suka gaisa. Shayi suka fara yin oder da biredi. Suna ci suna hira kamar dai normal hira suke yi a hankali aka dinga samun saura na zuwa.

A hankali cike da murya mai sanyi amma ɗauke da tambayoyi masu nauyi a bakinta.

"Smith ka gaya mini gaskiya,wane ne Paul Stone? Don nayi ƙoƙarin na gano waye shi a nan Global Times ofis amma ban samu komai ba."

Smith ya kalli gefe yana hango yadda mutane ke hada-hada a titi ta taga yake hago su. Sannan ya sauke ajiyar zuciya yace "Paul...Stone.. ba abinda tunanin ki yake hasasho miki ba ne a kan sa. Duk abinda za ki nema a mujjalu,hotuna ,rahotanni,labarai ba za ki samu komai akan sa ba don an goge an shafe babin. Asali ma Paul Stone ba shi ne ainihin sunan sa ba, tsari ne da shiri da aka yi. Paul wani ɗan leƙen asiri ne da aka saka a matsayin ɗan jarida don ya gano wasu abubuwa akan manyan ƙasar nan."

Maryam ta runtse ido,zuciyarta na dokawa.
"To me ya faru da shi? Me ya sa babu wanda ya gan shi ko ya ji ɗuriyarsa tsahon wannan lokacin? Global times ma sun share dukanin wasu rubutunsa,kamar bai taɓa wanzuwa ba?"

Numfashi ya saki mai nauyi,sannan ya juya ya kalli bayan sa da gefe da gefen sa sannan ya juyo ya kalli cikin idanuwan Maryam kaitsaye.
"An ɓatar da shi ne saboda ya gano abinda bai kamata ya gano ba. A binciken da yake yi a kan cin hanci da safarar makamai ,safarar yara mata da kuma almundahanar da mayan shugabanni suke yi wanda a wancan lokacin abin ya zarce tunani da hankali."

"To ya akai ka san ɓatar da shi aka yi?"

"Saƙon ƙarshe da ya turo min kalmomi biyu ne kacal "They Know" Bayan nan da na kira shi ban kuma samun shi ba har yau.

Jikin Maryam yayi sanyi ta kulle idanuwanta. Sai yanzu ta gane dalilin da ya saka aka shafe duk wani bayanan sa a Global Times.

Muryarta na rawa tace da shi "Kenan Paul Stone baya duniyar ne ko kuma a tunaninka ɓoye shi kawai aka yi?"

Smith ya kau da kai,idanuwansa na ɗauke da wasu sirruka masu nauyi wanda baya son fito dasu ɓaro-ɓaro. Nauyin sirrin ya masa yawa ba zai iya ɗagawa shi kaɗai ba. "Miss Maryam,gaskiyar da ta ɓace a tare da Paul zata iya cinye duk wanda ya kusanto ta ko yake ƙoƙarin bayyanata. Idan kika ci gaba da bincike a kai babu mamaki ko ma ince babu wani tazara mai nisa da zata hana kema a shafe babin ki ba a doron ƙasa."

Tuni Maryam ta ji komai ya tsaya mata cak kama tsayuwar kukan agogon bango. Tuni ƙirjinta ya bada wani irin harbi. Yanzu ta gane ɓacewar Paul ba iya labari ko wasan kwaikwayo ba ne ba gargaɗi ne gare ta da ma sauran masu son tono abinda aka birne da jinin mutane da dama.
[9/11, 8:02 PM] Ummulhair S Panisau: RUFAFFEN DUMA
Ummulkhair S Panisau.
Karamci Writers Association.
wattpad:khairi_muhd
Arewabooks:khairatup01
11

Bayan sun gama tattaunawar ne suka shiga ciki. Ya barta da tunani fal cikin ranta. Ta shiga ruɗu ɗayan biyu ne ,ko dai Paul na da rai ɓoye shi aka yi ko kuma ya mutu an shafe babin rayuwarsa. Amma in har yana da wasu ɓoyayyun sirruka to suna ina? A ina ya ɓoyesu? Ita kanta Global Times me ya sa tayi watsi da shi a matsayin sa na ma'aikacinta har aka goge dukanin wani bayanai nasa. Ji kanta ma ya soma yi mata ciwo wannan tunani da ya sako ta a gaba. A gurguje ta gama harhaɗa bayananta don yau da wuri zata tafi gida saboda fitarsu da Muhammad. Tuno shi kawai da tayi sai da taji wani abu ya tsarga mata a rai.

Wajajen la'asar ta gama komai ta tashi ta shiga ainihin ofishin ogan nasu ta nemi izinin tafiya ta ba shi dukanin wasu fayil da ta yi aiki a kan su yau.
*

*

Yaya aka yi kika dawo da wuri yau Maryam?

Mama ba na gaya miki zan fita anjima ba ? Har kin manta wai?

Na manta. Amma da wa za ki fita?

Ina wannan ɗan kasuwan da nake miki bayaninsa Muhamaad Sageer Barau?

Mama ta yi shiru tana kallonta kawai.

Da sauri tace "kar dai kice za ki hana ni ne?na ga kin yi saranda. Kin san dai yanayin aikin mu sai da irin haka, kuma ba wani abu ba ne abinci kawai zamu je ci."

"Na yarda da ke Maryam amma ni uwa ce dole a lokuta da dama nayi ta tuananin ki da lafiyar ki."

"Haka ne Mama. Iya yardar da kika yi da ni kaɗai ta ishe ni kwarin guiwa a rayuwata. Ina son ki Mama."
Chapter 13 · 0% Book details