Sashe 3
Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A lokacin da yanke shawarar fara jigilar kaya ta iyafot sai ya yanke shawarar shiga harkar jiragen sama. Bai dogara da kuɗin ubansa ba wannan kuɗin halak ɗinsa ne kuma guminsa. Ya yi hulɗa da bankuna da manyan abokai masu zuba hannun jari, ya kafa kamfaninsa "Maryam Air & Logistics."
Shekarun da suka biyo baya,kamfaninsa ya bunƙasa,ya zama mai jigilar kaya daga Nigeria zuwa Dubai,London,da new York. Ya kuma buɗe sashen jiragen haya na alfarma (private jets) ga gwamnnati,kamfanoni da masu kuɗi. Abinda Muhammad ya sani kawai shi ne "Mahifinsa ya bar masa suna da alƙa ne kawai,amma ba ya son yayi dogaro da su." Duk lokacin da aka ce "Sannu ɗan Sanata mai neman kujerar gwamna" sai yayi murmushi yace "Eh,amma yanzu haka zaku ce Muhammad Sageer ,wanda ya kafa sunan sa da kansa."
A yau duniya ta san shi a matsayin ɗaya daga cikin ƴan kasuwan Afirka mafiya tasiri,ba wai saboda mahaifinsa ba, amma saboda ƙwazonsa ,hangen nesansa ,da kuma dagiyarsa.
Wannan shi ne Muhammad Sageer.
*
Alhaji Barau ya lumshe idanuwansa yayin da ya zuƙi sigari . "Ba su san komai ba. Su dai talakawa suna kallon abinda muke shirya musu. A fili,zan yi alƙawarin makarantu, asibitoci, aikin yi... amma a asirce ,zan ci gaba da ciyar da kaina ne da nawa iyalin da mutane na." Ya faɗa yana fashewa da dariya.
Cike da murya da ke nuni da rauni Barrister Ado ya kalli Alhaji Barau yace "Alhaji kana da tabbacin ba za a iya gano abubuwan da suka shuɗe a baya ba? Kana sane da cewa akwai takardu da suke nuni da rawar da ka taka a harkar kuɗaɗen da aka samu na haram?"
Dariya yayi mai sanyi ya kuma zuƙar sigarinsa ya kalli Barrister yace "Kai Ado baka gane waye ni ba har yau ko? Kai na lura har yau baka ma san mece ce siyasa ba? To saurare ni da kyau. Siyasa da kake gani bata da tsarki. Duk wanda ya hau mulki yana da irin nasa ɓoyayyen sirrin.Abinda ya rage kawai shi ne wanda ya fi iya lullube shi da kyau. Nan da ka gan ni abinda na fi iyawa shi ne na fi kowa iya rufe gaskiya."
"Amman yanzu zaka fito neman takarar gwamna. Wannan matsayi ya fi na baya nauyi. Abinda ka aikata a baya zai iya taso maka."
"Kai Ado! Saurara min Kabir kawai nake shayi kuma na riga da na yi maganinsa." Hannunsa ya saka ya buga teburin da ke gaban sa da hannunsa.
"Na gina alaƙa da manya daga kan kotu,ƴan sanda,daga masu rubuta labarai (ƴan jarida.) Duk wanda ya yi yunƙurin tona mini asiri,zan kashe shi kamar yadda ake kashe labari kafin ya fito. Da zarar na hau kuma,duk wanda ya san gaskiya,ya zama abokin shiru kawai."
"Ka tuna ,jama'a suna iya ɗaga murya idan suka ji tsoron talauci da rashin adalci."
Wani irin murmushi ya saki mai cike da makirci. Sannan yace "Jama'a? Jama'ar da zan iya siyan su? da na siyi zuciyarsu da taliya ko buhun shinkafa,kai har dubu ɗaya ma na gama da muryoyinsu. Kai alƙawarin ruwa a borehole kaɗai ya isa su dangwala min ƙuri'unsu. Abinda nake tsoro kawai shi ne abokan hammaya da suka fi ni dabara wajen buga wasan ɓoye."
Barrista dai shiru yayi cikin ransa kuwa tunanin irin makirci da shu'umancin Sanata Barau ya ishe shi. Amma meye nasa? Jakar kuɗin da aka ajiye masa a gefen teburin ya ɗauka. La'adarsa kenan ta cin hanci da rashawa. In dai zai same su zai zama bawa ga mai ba shi su.
*
"Maryam dole na tafa miki na kuma sara miki bisa wannan ƙoƙarin da kika yi. Global times na alfahari da ke a matsayin ma'aikaciyar ta."
A fusace aka buɗe ƙofar aka turo ta da ƙarfi. Shehnaz ce ta shigo a fusace tana kallon ƴan ɗakin.
"Me kenan Shehnaz?"
"Tambaya ta ma kake yi? Baka san me ya faru ba? Baka san me ka yi ba? Taya zaka ba wa wannan yarinyar damar da tawa ce? Ta ya ya zaka bata damata nace?"
Maryam gefe ta koma ta tsaya kawai. Kowa ya san Shehnaz. Bata son kowa ya fita ko ya ture gwamnatin ta.
"Ya isa ki nutsu! Ba daga ni ba ne. Daga sama ne aka turo da saƙon a aika junior reporter sai na ga Maryam ce ta dace da na aika. Tana da ƙwazo."
Ta juya ta kalli Maryam ido cikin ido sai kuma tayi tsaki tace "Ba ku kyauta min ba, na jima ina burin na samu damar da zan yi hira da Muhamamd Sageer ka sani kuma amma shi ne sa'i ɗaya zaka bawa wannan yarinyar damata. Baku kyauta min ba Wallahi."
Yallabai ya kalli Maryam ya mata alama da ta fita ta basu wuri. Ta ajiye mai kayan aikin da rikoda ɗin ta fice waje ta bar su tana mamakin halin Shehnaz."
"Ta iso kenan?"
"Taya ka sani?"
"Saboda na san za ayi hakan. Coffe?"
"Ina da buƙata kam don kaina har ya soma ciwo saboda wannan ƴar hayaniyar."
Ya ja mata kujera ta zauna sannan ya aika peon da ya kawo musu coffe mai zafi.
Hannunta ta saka tana shafa goshinta. Sai dai ƙasan ranta kuwa cike yake da farinciki. Idanuwansa masu kaifi da haske take ganin suna gilma mata. Da sauri ta rintse ido tace a fili a hankali "Maryam ya haka ne?"
"Me kika ce?" Smith ya tambaye ta.
"Ba komai."
"Well. Ya hirar ta kasance?"
"Smith ba zaka gane ba Wallahi. In nace zan faɗa zaka ce ina exaggrating ne. Inda mutunci da isa mutum ne to tabbas zasu zo a siffar Muhammad ne. Mutum ne mai sauƙin kai ba kamar yadda ake faɗa ba a gari. Ni da na gan shi na zauna da shi nayi hira da shi ni zan gaya maka halinsa."
"woww! Tsaya haka Miss. Ba za dai ki san hallayensa ba , kin san dai wanda ya nuna miki. Na sha gaya miki mutane na da fuskoki da dama,wanda suke iya controlling ɗin kansu wajen nuna different faces ɗinsu. Ina fata kin fahimce ni?"
"Ban san naka karatun ba, amma ni wanda na sani shi ne i saw a different man with class and elegance."
Suna zaune peon ya kawo musu Coffe ɗin.
[9/9, 11:27 PM] Ummulhair S Panisau: RUFAFFAN DUMA.
Ummulkhair S Panisau.
(khairatup)
@Wattpad:khairi_Muhd.
@Arewabooks:khairatup01.
03.
*
Fayil ɗin ya ɗauko da gaggawa. Buɗe fayil ɗin DPO yayi. Ya na nazarin fayil ɗin. A jikin fayil ɗin an maƙala hoton tashar jirgin, wani ɗan zane da ya yi alamar ƙofa a jikin bango da ba ta shiga tsarin ginin ba."
"Haruna."
"Sir!"
"Me ka sani game da wannan tafiyar?"
Cike da rawar murya yace "Sir ya rubuta mana cewa yana jin ƙarar takun tafiyar mutum amma baya ganin kowa a cikin ɗakin. Ya bi sautin inda yake jin kuka jikin wata ƙofa na tsaya zan shiga idan ban dawo ba...." a iya nan saƙon nasa ya tsaya.
DPO ya ɗora hannunsa a kan teburin yace "Iya abinda ya rubuto kenan ka fin ya ɓace?"
"Iya abinda ya aiko kenan."
"Ka je zan sake neman ka.A ci gaba da bincike."
"An gama Yallaɓai."
Wani jami'in ne ya shigo ya sara shi ma yace "An sami motar Insp.Sameer a bakin titi kusa da dajin tsohuwar tasha.Kujerar a cike take da ruwa. Kuma babu kowa a ciki. Sai wannan takardar da aka yi rubutu a jiki."
"Me aka rubuta?"
"Inspector Sameer ya shiga inda bai kamata ya shiga ba...kamar sauran ma wannan mai gaskiyar ya tafi."
DPO ya yi shiru cikin nazari daga bisani ya ƙarbi takardar ya ajiye a cikin fayil ɗin. Ya sallame shi ya fita.
Dariya ya kece da ita bayan fitar sa yace "Ba a haifi wanda ya isa ya ja da mu ba."
*
Haske mai sheƙi daga Burj khalifa ya watso ta cikin gilashin tagar ɗakin taro na otal ɗin Burj Al Arab, inda manyan ƴan kasuwa daga turai ta gabas ta tsakiya suka hallara. A cikin ɗakin,ana tattaunawa akan yarjejeniyar jigilar kaya tsakanin kamfanonin duniya. A gefe ɗaya ,akwai ƴan kasuwa daga China;Amuruka;Dubai;New york amma duk da haka idanuwan kowa na kan mutum guda ɗaya "Muhammad Sageer." Daga Nigeria.
Murmushi mai ɗauke da nutsuwa yayi yace "Na gode. Hakan shi ne manufata ba wai kawai jigilar kaya ba,har da gina gada tsakanin Afirka da Gabas ta tsakiya. Dubai ta dogara da kasuwanci, Najeriya ta dogara da albarkatun ƙasa. Idan muka haɗa su, duka bangarorin za su ci gajiyar hakan sosai."
Wayarsa ya buɗe ,ya nuna musu tsarin jiragen cargo jets ɗinsa da ke kan hanyar sabon filin jirgi a Kaduna. "Mun fara da kai kaya daga Kaduna zuwa London da Dubai. Amma a cikin shekara biyu masu zuwa,burina shi ne ganin jiragenmu suna sauka a kowanne babban birni a duniya."
Ƴan kasuwar suka yi jinjina. Wani daga cikin manyan masu zuba jari yace "Ka fara daga ƙasa,daga Kaduna...amma yanzu kana nan a Dubai kana tattaunawa da mu. Wannan abin koyi ne a gare mu."
Muhammad yayi murmushi a karo na ba adadi murmushin na daga cikin al'adarsa ne. Idanuwansa na haska cikin ɗakin. "Na fara da abubuwa ƙanana,amma burina bai taɓa kasncewa ƙarami ba. Na san idan ba mu haɗa Afirika da duniya ba ,ba za mu taɓa samun damar mu ba. Wannan shi ne burina,kuma hakan zan yi."
Lokacin da aka gama taron ,wani ɗan jaridar Forbes Middle East ya same shi a bakin ƙofa yace "Mr. Muhammad,wannan ne farkon gina daular ku ta duniya?"
Muhammad ya ɗan tsaya ,ya kalli fitilun Dubai da ke haskawa a bayan gilashin ɗakin taron. Cike da kwarjini da ƙwarin guiwa ya kalle shi yace "Wannan ba farkon ba ne ,wannan shi ne ci gaba. Kuma ku jira ku ga inda zan kai wannan tafiyar." Yana gama maganar ya sa kai ya fice daga ɗakin taron. Ya bar ɗan jarida ba baki a buɗe yana jinjina iko na Muhammmd Sageer ƙaraminsu babbansu.