Sashe 20
Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin sa'a tana fita ta samu adaidaita sahu , suna tafe zuciyarta na bugawa da sauri kamar ana kaɗa mata gangi. Wannan ba ƙaramin ci gaba ba ne a wurin ta. In har da gaske yaron da aka kama na da sa hannu a wannan harin da aka kai Birin Gwari to tabbas zasu san su waye silar hakan.
A hanyar ta na zuwa station ɗin ta ga kiran Muhammad ya shigo mata da sauri ta ɗaga.
"Miss kina ina ne?"
"Ina hanya zan je station akan wannan case ɗin."
"Kina da buƙata ta a wurin?"
"In dai baka komai zan so ka kasance a wurin."
"Zan zo na same ki a wurin nan da mintuna goma sha biyu haka. Wannan wata dama ce da ba za mu bari ta kubce mana ba."
Suka ajiye waya.
Dsp ya tarbe ta da fuska mai nuni da lamarin na da muhimmanci sosai.
Maryam muje ciki ,zo ki gan shi. Ya faɗa yana nuna mata wani matashin saurayi wanda shekarunsa basu wuce talatin ba, hannunsa ɗaure da ankwa. Idanuwansa cike ta tsoro,gumi da yake zubo masa yake kamar wanda ya yi gudun awanni.
"Ya bada wani bayani ne DSP?"
DSP ya gyaɗa mata kai. Ya nuna mata wuri ta zauna tana kallon saurayin.
"Bai faɗi komai ba amma yace da shi a cikin maharan ,sannan akwai sunayen da ya sani amma yana tsoron ya faɗa su kashe shi."
Da sauri Maryam ta ja kujerar ta gaban DSP tace "Yallabai in ku ka ba shi tsaro da kariya zai faɗa. Ina son ka bani damar yin magana da shi a ƙebance."
DSP ya tafi tunani kafin yace "Zan baki mintuna goma sha biyar kawai. Amma ki sani ,abubuwan da zai gaya miki zasu iya tada jijiyar wuya ga mutane da yawa."
Maryam ta gyaɗa masa kai da sauri tace "Na sani! Kuma na shirya."
Maryam ta shiga ɗakin binciken inda aka maida mai laifin. Zaunawa tayi tana kallonsa da kyau. Recoder ɗinta ta kunna ta ajiye a ƙasa daga gefe.
"Sunan ka?" Ta tambaye shi cike da murya mai laushi.
"Kabiru." Ya amsa kaitsaye muryarsa na rawa.
"Me yasa?"
"Ni dai ba ni da niyyar cutar da kowa.Na yi aikin ne saboda ina cikin talauci da yunwa. Ban ma san abinda zamu yi kenan ba."
"Ya akai ka shiga tawagar?"
"Wani abokina ne ya kira ni. Yace min wanda ya ɗauke mu aikin babban mutum ne."
"Yaya sunan sa?"
Shiru Kabiru yayi jikinsa na rawa cike da tsoro.
"Look! Kabiru idan ka faɗi gaskiya zaka ceci yara da yawa da aka rabasu da iyayensu. Kai kan ka na san kana da na sanin aikata wannan ɓarnar.ka sa kan ka a matsayin iyaye da yayye da ƙanne na waɗan da aka sata yaya zaka ji in kai ne?"
Kabiru ya kalle ta idanuwansa na fitar da ƙwalla. A hankali yace "Bana son na rasa raina ta wannan hanyar ban taɓa yi ba sai wannan karon ,yaran sun bani tausayi, na kasa daina ganin fuskokinsu cike da roƙo da hawaye da neman taimako. Madam,ina da yaƙinin ba wai iya satar ba ne akwai wani abu da ake shiryawa wanda hakan zai ɗauke hankulan jama'a da hukuma daga wani babban laifi da ake son kaddamarwa."
"Amma me yasa ka kawo kan ka gaban hukuma?"
"Saboda na san ko na faɗa sai sun kashe ni ko ban faɗa ba ma zasu kashe ni, don na san yanzu sun samu labarin kamanin da aka yi kuma suna shirin yadda zasu kawar dani daga doron ƙasa don kar na tona musu asiri. Madam ki kula da duk wani da kike ganin ki yarda da shi zai kyautu ki yarda da iya kan ki kawai."
"Kabiru ka yarda da Allah. In sha Allahu babu abinda zai same ka. Ƴan sanda zasu baka kariya."
Murmushin gefen baki yayi ya ɗauke kai yace "Madam, ƴan sanda,ƴan jarida,ƴan siyasa duk akwai ɓata gari a cikinsu. Ke ma don na yarda da ke ne da shi DSP ɗin ne yasa zan gaya muku kuma na san ko ba ni zaku yi ƙoƙarin banƙaɗo gaskiya."
"Na gode."
"Alhaji Tukur , da kuma Alhaji Ɗanzaki,da wasu guda biyu wanda ban riƙe sunayensu ba. Amma suna da yawa ba mutum ɗaya ko biyu ba ne, mutane ne da dama."
"Ya akai ka san sune?"
"Sune suke kawo mana kuɗi. Aikin mu kawai shi ne mu sato yaran mu kai su wani gida wanda ake kira da "Farm House".
Da sauri Maryam ta zaro wata takarda daga aljihunta zanen taswira ne. "Zaka iya nuna inda Farm House ɗin yake a nan?"
Ya kalli taswirar da kyau, ya kuma jinkirta a nutse a hankali ya nuna wata hanyar wani ƙauye mai nisa da gari sosai. Da sauri Maryam ta sa biro tayi circling ɗin wurin ta cusa a jakarta gudun kar wani ya gani.
Tana fita ta ce da DSP sun gama magana. Kuma su cika alƙawarin ba shi kariya har a yanke mai hukunci. Ya so ya ji ko ya gaya mata wani abun amma ta ƙi sanar masa da komai.
Tana fita ta ci karo da motar Muhammad daga tsallake yana jiranta. A gajiye ta isa wurin motar ta buɗe ta shiga gidan baya don ta ga kamar akwai direba yau.
"Sannu Miss."
"Yauwa."
"Akwai bayani ne?"
Ta kalli direbansa ta kalle shi. Yace "Oh! Journalist Madam na manta privacy. Za ki ci abinci?"
"Aa a maida ni Global Times."
"Aa zamu je mu ci abinci ne. Nima dawowa ta kenan."
"Ina kaje?"
"Akwai kayana da suka zo naje clearance ne."
"Oh!"
Ya gayawa Direba inda zai kai su.
[9/12, 10:02 PM] Ummulhair S Panisau: RUFAFFEN DUMA.
Ummulkhair S Panisau.
(Khairatup)
Karamci Writers Association.
Wattpad:khairi_muhd.
Arewabooks:khairatup01
16.
Bayan sun gama cin abincin ne ya kalle ta da kyau. Yana son ya ce wani abun amma sai ya tsaya nazartar fuskarta kamar tana da abinda take son ta faɗa ko wani abu da yake damun ta.
"Me nayi kake kallona haka?"
"Ina kallon abubuwa da dama a fuskar ki ne. Ki gaya min wataƙila za ki samu ragin wani abun."
Ajiyar zuciya ta sauke,ta janyo gilashin ruwa ta sha sannan ta ajiye tace "Muhammad kawai ina mamakin yadda masu aikin jarida suka maida aikin kamar hanyar samun kuɗi kawai. Abin yana damuna a rai Wallahi.
Ya gyara zamansa yace "Ba iya aikin ku ba ne. Har ma da mu namu ƴan kasuwa akwai ɓata gari masu kasuwanci amma a gefe ba iya kasuwancin ba ne."
"Ka san waye ɗan jarida a idanun talaka?"
"Sai kin faɗa."
"Kafin nan ka bani amsa ka san waye jarumi a idan talaka?" Ta faɗa cikin murya mai sanyi.
Muhammad ya ɗaga girarsa yace "Jarumi? Kina nufin jarumin film?"
Ta yi murmushi. '"Jarumi a nan na nufin journalist (ɗan jarida). Mutum ne da ake gani tamkar ido da kunne na al'umma. Shi ne yake shan wahala, ya ke shiga rikici , ya raba dare da rana kawai don ya tona gaskiya,ya kawo wa jama'a abinda yake faruwa a zahiri wanda bai sani ba."
Muhammad ya lumshe ido ,yana jindaɗin yadda take fasalta ma'anar.
"Mutane , suna sa ran jarumi ya zama marar tsoro. Suna sa ran zai faɗi gaskiya ko da ba ta da daɗi, komai zafin ta kuwa. Ɗan jarida kada ya sayar da labari saboda kuɗi,kada ya karkatar da gaskiya saboda wani mai mulki." Ta gyara zama idanuwanta cike da ɗokin magana. "Ga talaka ɗan jarida shi ne muryar su. Idan gwamnati ta yi kuskure,shi ne ya ke anƙarar dasu,idan wani babban mutum mai ji ta kuɗi ya take haƙƙin talak,shi ya ke ɗaukar hoto ko rahoto ya saka a jarida.Jama'a suna son kyautata masa zaton ya kasance mai gaskiya,mai adalci,kuma mai jajircewa har ma idan hakan na iya jefa shi cikin haɗari."
"Na gane nufin ki Miss. Aikin jarida ba aiki ne na wasa ba."
Dariyar taƙaici tayi sannan tace "Ba aikin wasa ba ne.Aiki ne da ke iya sa wa ka zama jarumi, ko kuma ka zama maƙiyi ga gaskiya. Mutane suna son su dogara ga mu, mu kuma zama haske a cikin duhu,idan muka gaza kuma mu bar su a duhu."
Maryam ta sauke ajiyar zuciya ,ta ɗan ja numfashi ta sauke ajiyar zuciya ta ci gaba da magana.
"Ka san hatsarin da muke ciki? Kana kallon dai Smith akan gaskiya aka so kai shi lahira. Jarumi na gaskiya baya samun bacci mai daɗi.Yana fuskantar barazanar kira daga mutane don barazana ko tsoratar wa, yana fuskantar tsangwama daga masu mulki, wani lokacin har hari ake kai masa na rai."
"Ko a karan kan ki sau nawa aka biyo ki za a kashe kina neman taimakona" ya faɗa yana dariya ita ma dariyar tayi. Akwai wanda ba ka sani ba bamu san juna ba lokacin.
"Bani labari."
"Akwai lokacin da na gano wani babban cin hanci akan aikin titi, na yi bincike na kuma fitar da labarin. Da daddare bayan na taho gida wata mota ta tsaya a gabana aka jefo mini wata takarda ,wasiƙa ce an gaya min in na sake na kuma zurfafa bincike a kan lamarin sai na rasa raina. Amma ban tsaya ba sai da na saka kama wannan mutumin hakan ya saka a rage mini matsayi ni kuma na gwammaci na sauya wurin aiki na dawo nan Global Times a matsyain ƙaramar ma'aikaciya."
"Lallai kin jima kina wasa da rayuwar ki."
"Jarumi na gaske ya san cewa gaskiya ta fi tsoro girma. Jama'a suna tsanmmanin za ka yi tsayin daka saboda su. Idan kuma muka gudu fa? Me zai rage musu? Babu wanda zai ji muryoyinsu." Da zuciya ɗaya take maganar kamar tana rera waƙar gwagwarmaya.
Mutane suna son mu zama muryarsu,ta ƙara ,amma wasu lokutan wannan muryar ce ke jawo mana bala'i. Amman duk da haka, sai mun tsaya tsayin daka mun kai musu labari na gaskiya.Domin idan muka yi shiru, duhu zai mamaye komai.
Muhammad.....Na jima da gane cewa dole ne na bawa kaina ƙwarin guiwa saboda aikin jarida ba kawai rubutu ba ne gwagwarmaya ce da gaskiya da tsoro da kuma cetar rayuka.