Sashe 28
Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
"Wannan ba ƙaramin aiki ba ne Dole ne na nemi izini daga hukumar kare hakkin ɗan'adam,da takardu na shige da fice,saboda in tabbatar da ikon shiga gidan. Idan ba haka ba nima zasu iya tsare ni." Faisal ya faɗa.
Muhammad yayi murmushi ya murz zoben sa yace "Na san zaka ce haka daman.Shi yasa da shirina na zo." Ya tura masa wata ƴar ƙaramar jaka yace "Buɗe."
Faisal na buɗe jakar ya ga dukanin wasu abubuwan buƙata da takardu ,da passport ɗinsa da tikitin jirgi da kuɗaɗe da ƙaramar waya. Ya zare idanuwansa yace "Muhammad da saura na a sanin ka."
Muhammad ya ɗaga hannunsa ya ɗora a kan kafaɗar sa yace "Shi yasa na zaɓe ka. A wannan lamarin da kai kaɗai na dogara."
"In sha Allah zamu yi nasara abokina. Sai ka ji ni. Allah Ya dawo da kai lafiya?"
"Amin."
Daga haka suka rabu.
*
Yamma lis ta tashi daga bacci ,saboda ta jima d yin baccin da ta tashi kanta yana yi mata ciwo.Ta dafa kai ta sauko daga kan gadon tana ƙoƙarin tashi daga tsaye. Fitsari take ji hakan ya saka ta shiga banɗaki ta rage mara ta kuskure bakinta ta fito. Jiya aka cire mata bandage ɗin hannun da sauƙi sosai.
Doguwar riga ce a jikinta da hula. Ƙoƙarin fita take yi kuma sai ga Mama ta shigo a ɗan ruɗe.
"Maryam..." kamar bata ma lura ta tashi ba don gadon take kalla kawai.
"Mama gani fa ,lafiya na gan ki a haka?"
"Maryam ƴan sanda a falo!"
Maryam ta ƙara girman idanuwanta tace "ƴan sanda a gidan nan kuma?"
"Suna falo zo muje ke suke nema wai."
"Ni?" Ta tambaya.
"Eh."
Hijabin ta da ke kan bed side drower ta janyo ta saka.
Maryam na fita ta gansu su uku da mace ɗaya cikin kayan gida.
"Lafiya dai Yallaɓai?"
"Maryam Kabir! Mun zo tafiya da ke ne."
"Tafiya da ni ina? A bisa zargin me?"
"Idan mun je kya ji."
"Babu inda zani sai an gaya min laifin da ake tuhumata da shi.Ni fa ƴar jarida ce ba zaku yi min haka...." bata ƙarasa ba ya zaro wata takarda ya nuna mata. Amsa tayi da sauri ta karanta warrent ne daga sama an bada umarnin kamata bisa zargin shigo da ƙwayoyi tana rabawa ƴan mata a ɓoye.
"Bani bace Yallabai sai dai in kuskure aka samu na suna. Bana shan ƙwaya kuma bana raba da ƙwaya...ba ni ba ce."
Ɗan sandan ya haɗe rai ,ya kalli sauran yace "Ku shiga ku duba ko ina na gidan ko za a samu wata shaidar." Suka ƙame mai suka nufi cikin ɗakunan.
Ko ina suka shiga suka dinga ɓaro da abubuwa Maryam na bin su tana hana su amma ba su zo don su tsaya ba.
A cikin dirowa a ka ga wata ƙaramar jaka ana buɗewa sai ga cocaine a ciki.
Marayam ta shiga cikin ruɗu da tashin hankalia.
"Ba nawa ba ne....Yallabai ban san ya...."
Ina suka saurare ta ma. Ankwa aka saka mata aka yo waje da ita.
Mama na kuka tana bayani "Ba nata ba ne ɗazu wata mata ta kawo wai aiko ta aka yi daga gun aikinsu ta kawo mata saƙo , ba nata ba ne..."
Maryam na jin haka ta san cewa shiri ne aka yi don a ga bayanta kuma shirin ya kama da ita.
A hankali tace da Mama "Ki koma Mama,babu abinda zai faru. Shiri ne aka yi don ganin bayana saboda ina son bankaɗo sirrin da zai girgiza kursiyin manya."
Mama ta fashe da kuka tana gani aka tafi da Maryam.
Na kuɗi ne, 9126022777,opay,sani ummulkhair panisau.
Shaidar biya 0906856251.
A telegram.
Arewabooks @Khairatup01