← Book details Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 28

Sashe 23

Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wato yarinyar nan Maryam barazana ce garemu duka. Duk wani tsohon aiki da muka rufe tana bi lallai sai ta tone shi. Ina tsoro kar ta koma kan tsohuwar tashar jirgin nan. In ta je nan ko ta gano wani abu a nan lallai za a samu haɗari. Kowannenmu yana cikin matsala da tashin hankali."

"Shehnaz me kike ganin za ayi?"

"Boss zan iya watsa labaran da take kawowa a matsayin ƙarya zan kuma iya karkatar da hankulan jama'a daga kan batun. Zamu iya cewa ma kamen Danzaki da Shehu kawa shiri ne irin na aikin siyasa da adawa hakan zai iya raba hankulan jama'a."

"Na san za ki iya

"Hon.ka ce wani wani abu mana tuntuni kayi shiru ka kame bakin ka ya kake ganin za ayi?"

"Ni a gani na kar ku nutsa kan batun fito da Danzaki ko Shehu. Saboda yin hakan zai saka shakku da alamar tambaya ga lamarin. Za a samu masu gaskiyar da zasu so tono abin daga tushe in kuwa aka samu idon wasu ko kuma aka samu mutane sun farga hankalinsu kuma ya dawo kan siyasar ƙasa za ku sha mamakin irin kayin da zamu sha."

"Kuma fa ka ce wani abu Hon. Ya kake ganin za ayi?"

"Kafin Paul akwai Abdallah yanzu yana ina?

Akwai paul yana ina yanzu?

Akwai yaron da ya so ya kawo mana hari Yusuf yana ina?

Akwai smith shi ma yana ina?

To ku kwantar da hankalinku wacece wata Maryam? Bata isa ba Wallahi.Wannan fa labarin da jinin mutane bila'adadin fa aka rubuta shi. Ba zamu kashe ta ba amma zamu haɗa ta da wanda zai gama da ita cikin ruwan sanyi."

"Ta ya kenan?" Waziri ya tambaye shi.

"Rayyan! Ta hanyar Rayyan kaɗai zamu ci nasara a kanta. A saka shi ya cusa mata ƙaunarsa a ransa ta yadda zai yi mata illa a zuciya."

"Amma me yasa kake ganin soyayya zata saka ta karaya?"

"Idan kace zaka karya mace da ƙarfi sai ta koma maka jaruma sak. Amma idan ka karya zuciyarta,ka raba ta da ƴancin tunaninta ,ta zama tamkar tsuntsuwa mara fuka-fuki."

"Madallah da Hon. A takaice dai makircin soyayya ya zame mana makami."

Duka suka yi na'am da wannan zancen a haka aka tashi sun yarda sun yi sadaukarwar Danzaki da shehu.

*

Yana zaune cikin mota. Airport za shi duba wasu kaya da za a tura cin. Saƙo ya shigar mai ta wayar sa. Yana dubawa yaga hotuna ne na manyan ƙusoshi manyan mutane wanda dama ya san su. Amma bai san lamarin ya kai haka ba. Iska ya furzar a hankali ya maida wayar ya kulle.

Fita daga cikin motar yayi. Ya isa kusa da wani ba chana suka yi musabaha. Daga ƙarshe suka yi cike-cike suka a hannu suka kuma yin musabaha ciniki ya faɗa.

"Am. Mr. Hong ina neman wata alfarma ne a wurin ka." Muhammad Ya faɗa yana kallonsa. Da ke ya saka wannan machine ɗin a kunne wanda yake translating yaren mutane mabambanta.

"Ina jin ka Mr.Sageer."

"Akwai wani yaro da nake nema. Kuma an gaya mini yana ƙasar ku. Ko na ce magarƙamar ƙasar ku. Ina son a bincika min ko da gaske yana can."

"Ah! Don wannan ba wani abu ba ne, zan zuba yarana kan aikin sai dai ka sani zai ɗauki lokaci. Ka tura min bayanansa kawai zan duba lamarin."

Muhammad ya washe bakinsa yace "Thank you! Mr.Hong."

Daga nan suka yi sallama ya shiga private jet ɗinsa ya tafi.

Muhammad ya zaro wata wayar daban ya yi danne-danne ya maida ta yana murmushi. A fili kuwa cewa yayi "Sauran ƙiris. Samun wannan shi ne zai samar min da matsugunni a cikin wasan yadda ya kamata. Yana kuma ji a jikinsa lamarin ya zo ƙarshe."
[9/12, 10:02 PM] Ummulhair S Panisau: RUFAFFEN DUMA.
Ummulkhair S Panisau.
(Khairatup)

Karamci Writers Association.

Wattpad:khairi_muhd.
Arewabooks:Khairatup01

18.

Wato duk wani sharri a cikin dare ake ƙulla shi.

Sanata Barau ya dawo gida bayan gama taronsu na ƙungiyarsu. Gida ya wuce kaitsaye. A gajiye yake ma yau don yunwa yake ji bai ci komai a can ba gabaɗaya hankalinsa na kan wani lamari da ya shafe na tunanin Maryam ma. A yanzu babban burinsa ya samu ya ƙubuto da Aryan daga Cairo. Labari ya zo mai an sa mai ido kuma ana daf da kama shi a babban magarƙamar ƙasar saboda ta'amali da ƙwayoyi da yake yi.

A fusace yake tafiya cikin sa tiƙi-tiƙi yana haki . Ba wata isashiyar lafiya gare shi ba amma son duniya ya fi mai komai. Hankachief ya saka ya share gumin kan fuskar sa.

Tun daga tsakar falon yake kiran sunan Mujibat. Bata fito ba sai wata mai aikin Hajiyar ce ta fito da gudu tace "Yallabai Hajiya bata nan ta fita ɗazu."

Ko kallonta bai yi ba ya ɗaga mata hannu kawai alamar ta tafi.

Da baya ta koma kafin ta juya ta shige ɓarayinsu.

Wayarsa ya zaro daga aljihunsa. Lambar Muhammad ya danna wa kira ya san zai yi wuya ya ɗaga wayarsa amma ba zai fasa kira ba saboda wannan batun na Aryan ne.

A jejjere yake ganin kiran mahaifinsa na shigowa baya mai irin haka ,dole ya ɗaga wayar amma bai ce komai ba shiru kawai yayi masa yana sauraronsa.

Cikin rai kuwa Alh. Barau cewa yayi "Shegen yaro mai gadon baƙin hali daga uwarsa."

"Don ubanka ba zaka min magana ba ,shegen yaro mai kafirin zuciya."

Muhammad ya karkatar da bakinsa gefe yace "Ina jin ka. Ba kunne ne yake ji ba?"

"Wallahi ba don Aryan ba ,babu abinda zai saka na kira ka."

"Aryan kuma?"

"Akwai matsala. Spy ɗina na can ya kira ni ana shirin kama Aryan a kowanne lokaci."

"Bayan wancan kamen? Wannan karon kuma me yayi?"

"Ta'amalli da ƙwayoyi."

"Innalillahi. Yaron nan baya jin magana Wallahi. Ka bar maganar a hannuna zan saka a ɗauko shi."

"Ba zai dawo ba ka sani."

"Na san yadda zan yi da shi. Ƙani na ne."

"Shi kenan, sai na ji ka."

Ba tare da ya ƙara cewa komai ba ya kashe wayar.

Ayra ya kira ya sanar mata da su shirya zasu dawo Nigeria. Tayi mamakin hakan amma ta lura da muryar yayan nasu akwai damuwa a ciki.

"Yaya,Aryan fa baya nan kwana biyu kenan."

"Na sani. Kada ki damu. Za a zo a kai ki airport zai biyo ki daga baya."

"Yaya akwai wani abin ne?"

"Kiyi abinda nace kawai."

"To Yaya."

Ya ɗauka bayan gargaɗin da yayi mai zai nutsu ashe da sauran rina a kaba. Bai taɓa jin zafin zuciya irin na yau ba ,saboda halin da Aryan ya jefa kan sa ba. Shiru yayi na ɗan lokaci ya zaro tissue daga gefensa ya zubar da abar, daga baya kuma ya ɗauki cingum orbit ya jefa a bakinsa ya soma taunawa. Kujerarsa ya dinga juyawa yana gaba yana baya. Ƙwaƙwalwarsa na aikin tunanin yadda zai yi ya yanke shawarar kiran Abdurrahman.

"Yallabai."

"Abdurrahman kana ina?"

"Ina area."

"Akwai aiki amma a sirrance. Ba na son ayi hayaniya, kuma ba na son Aryan ya gane cewa ni na saka ku. So nake ka sa mutanen ka ku ɗauke shi daga inda yake kaitsaye ku kai shi airort za ku samu Ayra a can tana tare da passport ɗinsa. A saka shi a wheelchair a matsayin mara lafiya inda hali ma a shaƙa mai magani ya fita daga cikin hayyacinsa."..

"Za ayi Yallabai."

"Amma Yallabai yana ina?"

"Aikin ku ne nemo shi Abdurrahman me amfanin ka in ni daga nan zan maka komai?"

"Afuwa Yallabai."

Bayan ya ajiye wayar. Ya sauke ajiyar zuciya. Ita kaɗai ce hanyar da zai bi don cetan Aryan daga jami'an Narcotics na can.

CAIRO

Aryan ya fito daga hotel ɗin da ya ke zaune kwana biyu, yana sanya wayarsa a cikin aljihun rigarsa. Da shirin zuwa wani party ya fito dama abokan sa na jiransa a can already. Ko kaɗan bai san ana leƙensa ba.

A bakin motarsa ya tsaya yana ƙoƙarin buɗe motar ya ga inuwar mutane a bayansa a sukwane ya juya ya gansu su uku fuskokinsu a kulle. Bayansu farar hilux ce da suka zo da ita,suka kewaye shi.

"su waye ku?"

"Mu daga embassy muke an aiko mu ne don tafiya da kai. Akwai matsala a visar ka zamu kai ka airport yanzu a samu tsaiko."

Ya buɗe baki yace "Waye ya turo ku? Wacce matsala kuma? Ban yarda da ku ba."

"Ka kalli uniform ɗin mu mana."

"Ban gamsu ba."

"Kada kayi gardama Aryan."

"Ba fa zan bi ku...." Bai yi aune ba kawai ya ji sun shaƙa mai abu ta baya ya sulale ya faɗi a kafaɗar ɗayansu.

Cikin mintuna kaɗan suka sauya mai kaya suka saka shi a cikin mota. Tuni anyi takardu na rashin lafiya da sa hannun likitoci don ba dawa a airport.

Abdurrahman ya turawa Muhammad saƙon "Mission accomplished." Zamu tabbatar da cewa an saka shi a cikin jirgin kafin mu tafi.

"Aikin ku yayi kyau. Ka duba account ɗin ka ku raba."

Kwanaki biyu basu yi wani dogon tattaunawa da Miss ba. Ayyuka sun yi mai yawa kamar yadda ya ga sun mata yawa. Ya gani a labarai tana kan wani case ne. Shi abinda yake ba shi mamaki da ita yadda take zaƙewa zaƙulo abubuwa ita ba ƴar sanda ba,ƙaramar ƴar jarida ta zama bomb,ta zama dodon manyan mutane sai tono ramuka take yi.

Kasa jurewa yayi dole ya kira layin nata. Yayi ta kira bata ɗaga ba hakan ya sa ya gane cewa bata kusa ko kuma ta kuma shiga wata cakwakiyar. "Miss! Ba kya jin magana." Ya faɗa da murmushi kwance a kan fuskar sa.

*

KOTU!
KADUNA.

Kotun babban birnin Kaduna a cike take maƙil. Jama'a sun yi cincirindo har waje. Ƴan jarida na ta ɗaukar hotuna ,kyamarorin kafafen watsa labarai na ta walƙiya.
Motar ƴan sanda ce ta shigo harabar. Bayan tayi faking aka fito da Alh.Danzaki da Alh.Shehu ,hannayensu ɗaure da ankwa. Duk da suna da wani ƙwarin guiwa a ransu ,kallon raini suke bin jama'a da ƴansanda da shi don sun na ganin kamar Boss zai iya buga wani wasan kafin a soma shari'ar wataƙila ma an kama Maryam an ɓoye ko kuma a kashe su a hanyarsu ta zuwa kotu.
Chapter 23 · 0% Book details