Sashe 7
Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ranka ya daɗe afuwa ina banɗaki ne."
"Ba tambaye ka ba duk da na san babu wani banɗaki da kake ciki. Ina da labarin komai a kan waɗanda suke a ƙarkashi na. Kana can kana hutawa dai. Amma kar ka manta a harƙalar mu dole ne kayi taka tsan-tsan,saboda gudun set up."
"Afuwa Ranka ya daɗe zan kula."
"Better."
"Ranka ya daɗe wani abun ne ya taso?"
"An gaya mini an kama mahaifiyar wata ƴar jarida?"
"Haka ne Yallaɓai."
"A maida ita gidan ta. Wasa ya sauya dole ne ma taƙun wasan ya sauya. Ku jira umarni na gaba kawai."
"An gama Yallabai, yadda kuka ce hakan za ayi."
Suka ajiye waya.
*
"No! Kar ka damu. Shawo kan ta ba zai zame mini babban aiki ba sai dai yadda zan shigo da ita cikin wasan ba tare da ta sani ba shi ne nazarin da nake yi."
"A tunanin ka hakan zai saka ka samu abinda kake so?"
"Tun a karon farko da na gan ta na gane cewa ita ce zata iya yi mini aikina ba tare da wani garada ba sai dai akwai hatsari a hakan. Kai ka san su waye su da kuma ƙarfin su."
"Muhammad! Gaskiya ka bi ta tawa ka sauya shawara."
"In na riga da na yanke shawara kai ma ka sani bana kuma sauraran kaina bare kuma kai."
"Hmm! Ka sake tunani dai ita mace ce."
"Zan zame mata garkuwa!"
"Muhammad anya kuwa iya aikin ka ke so ayi maka?"
"Kar ka shiga inda ba haka ba ne. Kuma kai ka san koma meye zan yi don na ga ƙarshen su."
"To me yasa kai ba zaka yi ba?"
"Saboda idanuwansu na kaina."
"Ita ma ai ta shigo cikin kafcen nasu,neman ranta fa suke."
"Faisal kai aminina ne kuma na yarda da kai. Ina son ka yarda da ni nima babu abinda zan bari ya same ta nayi maka wannan alƙawarin."
"Na yarda da kai amma ina tsoro."
"Tsoro dole ne,amma rama cuta gun macuci bai zama illa ba."
"Ba a iya kada kai a magana. Allah Ya sa wannan plan ɗin ya ci."
"In Sha Allah."
"Kar na manta, Nimra na neman ka."
"Faisal..."
"Ba ruwana fa ni kawai ɗan saƙo ne."
"Ka gaya mata bana nan, in na dawo zan neme ta."
"Muha..." bai ba shi damar ƙarasawa ba ya kashe kwamfutar. Ya koma ya jingina da kujera yana jin kan sa yana mai ciwo. Ya gaji amma in yana son ya cimma maufarsa dole ne ya yi duk abinda zai yi don ya samu matsaya. Dawowar Nimra cikin rayuwarsa zai iya haifar masa da matsaltsalu marasa iyaka. Tashi yayi ya ɗauko pcm ya sha. Yana tsaye jikin tagar ɗakinsa iska na kaɗa mai labule kamar dai akwai hadari a garin. Idanuwansa suka sauka a kan Maryam zaune a wurin hutawarsa. Ta cukuikuye kanta wuri guda ta cure a kan kujera ta dunƙule.
Bayan ta yake kallo da kyau. Fara ce sosai kuma tana da gashi. Baya son yayi hakan amma hakan shi ne kaɗai mafitarsa. Wasu lokutan kana haɗuwa da mutane baka shirya ba, sai dai zuwan wasu alkairi ne a rayuwar ka da kai da shi baki ɗaya. Zuwan Miss Maryam ba haka kawai ba ne... tunainsa ne ya katse yayin da wata ƙaramar wayarsa tayi ƙara din! din! din. Alamun saƙo ya shigo masa sai harba ja da kore take yi.
"Mayya. Wannan yarinyar ba zata bar ni ba Wallahi."
Yana zuwa ya kunna wayar.
"Na san kana nan kuma kana jin wannan saƙon a halin yanzu. Avoiding ɗina kake yi da gayya, ni kuma ka sani suna na Nimra naci a jinina yake. Ko ka kira ni ko na zo gidan na ka."
Murmushi yayi ya ajiye wayar ya koma bakin tagar ya ga har a lokacin tana nan. Yanke hukuncin zuwa ya zauna ya yi. Yana son ya san wacece ita.
[9/9, 11:27 PM] Ummulhair S Panisau: RUFAFFEN DUMA.
Ummulkhair S Panisau.
(khairatup)
Wattpad:Khairi_muhd.
Arewabooks:Khairatup01
6
"Hmm! Da alamu dai daren bai yi miki nisa ba, ko dai yanayin ne yayi miki daɗi har ya sa kika zaɓi ki zauna a nan?"
Juyowa tayi a hankali ta kalle shi. Ta saki murmushi a ƙasan ranta tana jin daɗin yadda take gaban allon kwaikwayon ta the Muhammad Sageer!.
"Kin kuma tafiya wata duniyar ne?"
Ta jijiga masa kai tayi tana yaƙe. Kan ɗaya daga cikin kujerar ya zauna yana kallonta yace "In ba za ki damu ba zan iya taya ki zama a nan?"
"Oh! Bismillah ka zauna."
Zaunawa yayi.Ta ƙura mai ido tana nazarin sauƙin halinsa.Tana mamakin yadda yake iya zama da ita bayan matsayinsu ba ɗaya ba ne.
"A wancan ranar kin yi min tambayoyi game da ni. Yau nima ina son na yi miki tambayoyi in ba za ki damu ba."
"Ina sauraron ka."
"Me ya sa suka biyo ki?"
Tayi ɗan murmushi ta gyara zaman ta tana kallonsa tace "Ni ƴar jarida ce. Ba kuskure nayi ba don na shiga gonarsu. Ko da yake ni ƴar ƙaramar ƴar jarida ce ,ina yin aikin ne da dukanin rayuwata. Sun biyo ni saboda wani abin su da yake a hannuna."
"Ba kya tsoron su kashe ki?"
"Da ina tsoro da ba zan shiga aikin jarida ba."
Ya ɗan ɗaga girarsa ya ci gaba "Ƴar ƙaramar ƴar jarida ce ke amma masu bibiyar ki manyan miyagu ne masu hatsari, ko da yake ba sai na gaya miki ba tunda yau kin gani da idanuwanki da ace ban zo ba da wataƙila yanzu kin zama gawa."
A hankali ta kalle shi tace "Adalci baya zuwa cikin sauƙi, Idan muka yi shiru,gaskiya zata mutu don tsoro. Ba laifi ba ne don na fuskanci hatsari ,laifin shi ne na san gaskiyar na kuma take ta da takalmina na wuce saboda ina tsoron kar na rasa raina!. In dai fuskantar hatsarina za hana zalunci yin ƙarfi , to zan zaɓi shiga hatsarin a koyaushe."
"Kina da jarumta,akwai wuta a kalmomin ki sosai, Da ace wasu ne bake ba da tuni yau sun tsorata da abin da ya faru da ke a yau,da har aikin ma sai sun yi watsi da shi. Amma ke na ga kamar kin riƙe littafin ki kamar takobi."
"Shi ne takobina. Kalmomi na iya, sun fi harsashi idan ta kasance an rubuta ta da gaskiya."
"Miss Maryam. Ina son sanin wace ce ke? Ina nufin ina son ƙarin haske a kan ki. Ina son sanin me ya ja hankalin ki har kika zaɓi wannan hanyar? Me yasa kike son kashe kan ki saboda samo labaran da zasu iya zama ajalin ki?"
Tuni yaga yanayin ta ya sauya. Muryar ta tayi ƙasa idanuwanta suka cika taf da hawaye.
"Am sorry! In ba kya son ki gaya min ba dole ba ne amma,don Allah kar kiyi kuka."
"Na taso ina ganin yadda zalunci ya cinye min mutanen da nake so. Mahifina....ya rasa rayuwwar sa ne saboda gaskiya.Tun daga lokacin na yi wa kaina alƙawarin sai na ɗora daga inda ya tsaya. Ko da a yau ni kaɗai ce muryar da ta rage na sani na kuma yi imanin cewa murya ɗaya kaɗai zata iya girgiza tsaunuka idan ta yi ƙarfi."
"Haka ne! Amma me ya faru?"
Na taso gidan rufin asiri, mahaifina ɗan jarida ne wanda a wancan lokacin an san da shi saboda ƙwazon sa ,sai dai ƙwazon na sa ya ja masa durƙushe wa daga abokan harkarsa. Mutum ne mai bin didigin gaskiya da kuma taimakawa wanda aka zalunta. Ni Maryam tun da na taso nake jin karatun riƙe gaskiya daga bakin mahaifina. Mu biyu kacal ya haifa da ni da yayana Yusuf. Na shaida yadda talakawa ke shan wahala saboda rashin adalci. Mahaifina Kabir Umar ya shahara wajen rubuce-rubucen gaskiya da fallasa masu cin hanci da rashawa. Akwai wani babban bincike da Baba yake yi wanda ya gano wani babban sirri akan wani ɗan siyasa mai ƙarfi wanda ya mallaki ikon da ya fi na ƙasa. Ɗan siyasar nan yana amfani da ƙarfin iko da kuɗi wajen cin zarafin mutane da satar kuɗin gwamnati. Akwai wani haramttacen kasuwanci da yake yi wanda ƙasa bata sani ba. Mahaifina ne ya fara wallafa bayanai gam da shi, yana shirin buga cikakken rahoton da zai girgiza ƙasa da duniyar wannan ɗan siyasar sai suka yi nasara a kan shi. Kafin rahoton ya kai ga jama'a ,aka soma yi masa barazana,daga baya kuma aka shirya masa ƙulalliya. Ranar da zai buga labarin ,ranar yayi haɗarin mota ya rasu. Ni na san wannan shiri ne ba haɗari ba ne kashe shi aka yi don a ɓoye gaskiya. Ƴan sanda su ka ƙi yin bincike, suka ce babu case ai haɗari ne da ya faru a gaban kowa. Na san Baba ya fita da takardu da recordings amma ba a samu ko ɗaya a jikin shi ba? Shin ina suka tafi? Na san ba haɗari ba ne an rufe bakinsa ne ta hanyar kawar da numfashinsa ,a ƙoƙarinsa na tona wata gaskiya. Wannan lamarin ya tsaye mini a rai kuma ya bar mini tabo a rai.Tunanin jinin mahaifina da aka zubar saboda gaskiya shi ya zame mini kuzari da ƙwarin guiwa. Na ɗaukar wa kai na alƙawarin zan ɗora daga inda Baba ya tsaya. Wannan ne ya saka na yi karatun jarida na zama ƴar jarida. Ban shiga don neman suna ko kuɗi ba,sai don ci gaba da gwagwarmaya da kuma yaƙar rashin adalci.
"To shi ɗan'uwan naki fa yana ina ban ni kin ce komai akan sa ba?."
Hawayen da take ta ƙoƙarin dannewa sai da suka zubo mata. Da sauri ta juyar da kanta gefe ta sa hannu ta share hawayen ta.
"Am sorry! Don Allah kiyi haƙuri ,ki daina kuka. Wallahi bana son na ga mace tana kuka.Ba zan ƙara tambayar ki komai ba."
"Bamu san inda yake ba. Wayar gari muka yi babu shi. Tsahon shekara bakwai kenan mun saka a ranmu shi ma ya rasu."
"Haka kawai sai ya ɓata? Ƙasa ce ta janye shi ko kuma sama ne ya haɗiye shi da za a ce ba a gan shi ba?"
Murmushi tayi don yadda yayi maganar ma dariya ya bata. Da dukanin zuciyarsa yayi maganar.