← Book details Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 28

Sashe 26

Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali tace "Yaya mai jiki?"

Matar tace "Alhamdulillahi da sauƙi za a ce. Yaya naki jikin?"

"Alhamdulillahi! Bai farfaɗo ba?"

"Gamu nan dai muna ta addu'a Allah Ya tashi kafaɗunsa, in kuma ba na tashi ba ne Allah Ya ba shi ikon wucewa lafiya."

Jiki a sanyaye ta isa kusa da gadon. Lallai lamarin ubangiji sai shi. Mutumin da kafin yau a tsaye yake , cikin ƙoshin lafiya. Yana magana,yana numfashi kamar kowa ba shi da wata matsala ta ciwo yau ga shi samɓal a kwance bai ma san waye a kan sa ba. Tabbas duk wanda bai ji tsoron Allah ba yana tare da wahala a rayuwa.

Lifeline mashine ɗin take bi da kallo, yadda yake aikin sa. Ta sauke ajiyar zuciya ta soma magana ita kaɗai. "Dsp Allah Ya tashi kafaɗun ka, Allah Ya tona asirin masu hannu a ciki. Allah Ya yi maka sassauci a ciwon da yake damun ka." Suka amsa da "Amin."

A hankali ta juya ta kalli iyalin Dsp ta ga karaya a cikin idanuwansu kamar dai sun cire tsanmmani da tashin sa ni kaina in za a tambaye ni zan faɗa Dsp kamar ba zai tashi ba. "Huh!" Ta sauke ajiyar zuciya.

Har ta koma ɗaki tana wasi-wasi.

Muhammad ya koma ya zauna ya kunna laptop ɗin sa yana aiki a ciki. Kusan yanzu a nan yake wuni yana gadinta.

Mama na dawowa ta cika da farincikin jin ɗiyarta ta tashi kuma babu wata matsala ita iya hakan ma ya yi mata daɗi.

"Sannu Maryam, sannu Yaya kike ji yanzu? Yaya jikin naki?"

"Mama da sauƙi. Mama kin rame iya kwana ɗaya kawai?"

"Ba za ki gane me uwa take ji in ta haihu ba sai ranar da kika haifa a sannan ne za ki san cewa Mama ta sha fama da zullumi a rai."

"Kiyi haƙuri Mama. Na miki alƙawarin in na gano abinda nake son ganowa zan ajiye aikin."

"Maryam yanzu nake son ki ajiye ba sai wani lokaci ba."

"Mama ki yi haƙuri ki ƙara bani dama ki ƙara min uzuri ,Mama ba zan yafewa kaina ba muddin na haƙura na koma gefe ina kallo."

"Maryam an gaya miki ke kaɗai akwai abinda za ki iya yi ne a kai? Kin isa ki sauya system ɗin da kika tashi kiga a haka yake? Babu abinda zai canja...."

"Amman zan zama sanadin kwanciyar hankali na wani lokacin kuma za a rage mugun iri a ƙasata."

Mama ta kalli Muhammad muryarta na rawa tana son tayi kuka tace "Kana jin ta ko? Ka na ganin irin taurin kan ta , ban isa na gaya mata ta ji ba. Bana son aikin nan ,bana so bana so,ni na yafe ta haƙura..."

Muhammad ya miƙe tsaye ya soma lallashin Mama.

"Mama kiyi haƙuri don Allah ki daina asarar da hawayen ki. Zata ajiye aiki in dai aiki ne zata ajiye ki daina kuka."

Maryam ta kalle shi da baki a buɗe da kuma mamaki wai zata ajiye aiki a kan wannan abin ne zata ajiye aiki? Ba zai yiwu ba ,aikin nan rayuwarta ne ba zata iya barin sa ba.

"Kana gani fa harbin ta aka yi , da ya zo da ƙarar kwana shi kenan yau zaman makoki muke da kwanan ta ɗaya a kabari. Kullum yarinyar nan in ta fita ina cike da tsoron me zai same ta, bana samun sukuni har sai na ga ta shigo ciki. Gaskiya bana son aikin nan idan kuma ban isa da ke ba Maryam kije ki ci gaba."

A wannan gaɓar sai Maryam ta zaɓi da ta yi shiru gudun kar ta kuma ɓatawa mahaifiyarta rai. Ta bari akan zata karɓi hutu zuwa lokacin da zata warke kuma zuciyar Mama tayi sanyi tukunna."

Wata Nas ce ta shigo da sauri tace "Muhammad Sageer ka yi sauri ka zo mara lafiya na son magana da kai da gaggawa jikinsa ya tsananta."

Ba iya Muhammad ba hatta Maryam bata san lokacin da ta diro daga kan gadon ta bi shi ba.
[9/12, 10:02 PM] Ummulhair S Panisau: RUFAFFEN DUMA
Ummulkhair S Panisau
(Khairatup)
Karamci Writers Association.
Wattpad:Khairi_Muhd.
Arewabooks:Khairatup01

20

Muhammad kaɗai aka bari ya shiga saboda shi ya buƙaci da ya gani.

Maryam ta kalli a gefe a jikin bango,hannayen ta a rungume da ƙirjinta, hawayenta basu daina zuba ba. Yaran na kalla na ga sun ji jigum sun tsugunna kawai daga su sai Allah su ka san me suke ji a wannan lokacin. Ina jin yadda suke ji saboda tuno da lokacin da na ga gawar mahaifina kwance a gabana samɓal baya ko motsi ina ta ba shi hannuna ya kama amma bai kama ba har yau na kasa cire hoton sa a cikin idanuwana ba. Nima tuni ƙwalla ta zubo min zuciyata sai bugu take yi kamar zata fashe ta fito waje tsoro nake ji bana son ya mutu bana son ya mutu." Haka ta dinga maimaitawa.

Sai zarya take yi daga nan zuwa can Muhammad ya jima a ciki kafin ya fito ya kalli matar Dsp yace "ku shiga yana son ganinku." Da sauri nace da shi "Ni fa?"

"Bayan sun fito."

Ji yake yi kamar ya jawo ta jikinsa ya lallaɓata ta daina kukan ,yana ganin yadda jikinta ke rawa saboda fargaba, ya lura bata iya rikicewa ba sam-sam. Idanuwansa na kan ta da duk wani motsi nata. Allah-Allah take yi a ce ta shiga.

Jim kaɗan suka fito suna kuka duk su ukun.

A fili Maryam ta soma salati. "la'ilaha illallahu muhammadar rasulilahi.Wayyo Allah kaicona kar ku ce min jikin yayi tsanani har haka?"

Matar tace mata "ki je."

Da sauri ta shige ciki.

A hankali ta ke tafiya ganin yadda lokaci guda kamaninsa suka sauya. Da murmushin ƙarfin hali yake kallonta, hannunsa ya saka ya sauke oxygen ɗin yana son yayi magana amma yana kokawa da numfashinsa.

Da sauri Maryam ta isa kusa da shi duk da tsikon da hannunta yake yi mata hakan bai hana ta saki kukan da ya maƙale mata a cikin maƙogwaron ta ba.

"Ka yafe min don Allah! Nice sila ni na jawo maka hakan da baka karɓi case ɗin ba da ba haka ba. Ka yafe min?"

"Maryam ni da ke musulmai ne, mun san kaddara kuma mun san dole ne mu yarda da ita, to haka ma mutuwa dole ce babu fashi sai mun je inda magabatanmu suka tafi. Bana jin komai dan zan....koma ga....mahallicina lokaci na ne yayi kwana ne ya ƙare ko basu harbe ni ba yau zan ta.... tari ya sarƙe shi fiye da na baya.

"Kayi shiru ka daina magana." Ta ce da shi.

Ya gyaɗa mata kai cike da ciwo yace "Maryam ki nutsu ki maida hankalinki. Ƙasa na da buƙatar ki. Tana buƙatar taimakon ki da agajin ki. Maryam akwai abubuwa da suke faruwa da gayya don kawai a ɗauke hankalin talakawa daga kan su. Maryam...." sai kuma yayi shiru ya ɗora hannunsa a kan ƙirjinsa yana jin wani irin ciwo.

Da sauri ta matsa gaban shi da kyau tace "Yallabai ka yi shiru don Allah."

"Maryam,na san mahaifin ki Kabir mutum ne mai gaskiya da son tona gaskiya. Akwai abinda ya sani ya kuma tattara bayanansu a wancan lokacin na sani kuma ni na shirya masa yadda zai yi ya samu nasara a kan su , kuma yayi bincike mai kyau. Amma sun fi mu wayo da saurin shiri a ranar suka kashe shi da haɗin bakin wani aminin sa ana kiransa da Abdallah Umar. "

Da sauri ta tari numfashinsa tace "Ban taɓa jin sunan sa ba a ina yake? Ina zan same shi don Allah?"

Na'urar asibitin ke bada sautin beep (din,din,din...)

A hankali ya ci gaba da magana. "Abdallah ya ci amanarsa ya kuma kwashe dukanin wasu shaidu da bayanai kafin mu kai ga samun mahaifinki a lokacin, tun daga ranar ba a kuma ganinsa ba har yau. Babu inda ban sa yarana su nemo shi ba amma basu same shi ba na fi zargin ko a kashe shi ko kuma an sauya masa ƙasa ko kuma ya canja suna da rayuwa a wani wurin. Na jima ina son na sanar miki da hakan sai dai ban samu wata ƙwaƙwarar hujja ba, har yau ina kan bincike sai dai na gayawa matata wani abu zata baki saƙo ki duba kuma ki bibiya. Wan ki Yusuf ma ba ɓata yayi ba yana....yana....naa...." sai tari ya sarƙe shi tuni numfashinsa ya dinga sama da ƙasa ya kasa furta komai tana kallon yadda yake kokawa da numfashinsa har san da ya dinga faɗar kalmar shahada a hankali tana kuka tana taya shi maimaitawa.

Can kuma sai na'urar ta yi ƙara mai tsawo ta daina harbawa kamar baya.

Maryam ta fashe da kuka ta haɗa kai da gadon ta saki kuka.

Sauran ne suka shiga ciki.Matar Yallabai Hamza ta sa kuka ita da yaranta ta durƙusa a ƙasa ta kama ƙafar mijinta.

Duk da raɗaɗin da kafaɗarta take yi sai ta ji bata ma jin komai. Komai ta daina gane masa fuskarsa take kallo. A fili kuwa tace "Shi kenan, Yallabai ya mutu saboda gaskiya,duniya ba zata manta da sadaukarwar da kayi a banza ba."

Ɗankwalinta ta saka ta kulle mai fuska. A wannan lokacin ta kuma ƙurtawa a ranta ,duk tsanani da wahala,zafi,ruwa ,iska ba zata tsaya ba sai ta gama abinda ta fara.

Yallabai ya tafi amma ya bar ta da zullumi da tunanin abu biyu na farko "waye Abdallah Umar da ya ambata a matsayin aminin mahaifinsa da ya daɓa masa wuƙa a baya? Ina kuma Yusuf yake? Tsabar tunani da gajiya bata san lokacin da jiri ya kwashe ta ba sai ji aka yi ita ma tim ta faɗi a ƙasa.

Daidai lokacin da Muhammad ya shigo da sauri ya koma ya kira Nas guda biyu suka zo suka kamata aka maida ta ɗakinta.

Tuni labari ya fita akan rasuwar Dsp Hamza a asibiti.
Haka aka gama duk wasu cike-cike aka miƙa shi ga iyalinsa. Muhammad ya tsaya musu kan komai har aka samu aka kai shi gidansa na gaskiya.

Tabbas dukanin wani mai rai sai ya ɗanɗani mutuwa!.

*
Chapter 26 · 0% Book details