← Book details Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 28

Sashe 14

Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai kawai ta gyaɗa mata ta shige cikin ɗakinta.
*

Abinda bai taɓa yi ba yau shi yake yi wato zaɓo kaya fiye da sau biyu ko uku. Gasu nan kan gado ya rasa wanda zai saka ya ga ya kwanta mai a rai. Ƙarshe hannu ya harɗe wuri guda yana kallon kayan kamar dai kayan ne zasu zaɓi kan su da kan su. Tunowa yayi tana da burin ta gan shi da wasu kalar kayan bayan baƙaƙe bai da kuma wasu sai dai akwai wata guda da a wancan lokacin da Nimra ta ba shi a matsayin kyautar birthday ɗinsa bai taɓa sakata ba saboda baya son wata kalar bayan baƙi. Hannu ya saka ya zaro wata suit ɗin kalar fara amma irin off white ɗin nan rigar ciki shuɗiya ce mai sanyi. Takalman sa na fata ya saka kalar dark brown. Sai ga Muhammad na taje gashin sa ya gyara shi cike da tsari gwanin ban sha'awa,ya feshe jikinsa da turare tuni wajen ya ɗauki ƙamshi.

Shi kan shi direban sa yau sai da ya sha mamakin ganin wannan sauyin a wurin ubangidan nasa.

koda suka isa hotel ɗin bai fito ba yana kallon farfajiyar hotel ɗin da fitilu suka haska shi tar gwanin ban sha'awa. Ganin lokaci ya soma ja ya saka ya fito cikin baƙin gilashi ya tsaya a jikin ƙofar hannunsa ɗaya cikin aljihunsa ɗayan kuma yana duba agogo ko wani muhimmin meeting bai taɓa jin kalar abinda yake ji a yau ba. Kana ganinsa ka san jiran wani abu muhimmi yake yi fiye da duk wani abu da ya gabata a rayuwarsa ta baya. Shi kan shi tambayar kansa yake yi anya kuwa lafiyarsa ƙalau kuwa? Ya rasa sunan abinda yake damunsa a kwanakin nan tun bayan haɗuwarsa da Miss Maryam da ya ɗauka don sunan mahaifiyarsa ne da yake so ya sa take burge shi amma yanzu ya fara ji a ransa wannan yanayin ya wuce yadda yake tsanmani. Kamar ance ɗago ya ɗaga kansa sama idanuwansa basu sauka a ko ina ba sai a kan fuskar Maryam zuciyarsa ya ji ta buga sau biyu tamkar an busa ƙaho. Wani murmushin da bai shirya ba ya bayyana a kan fuskarsa,murmushin da bai taɓa kula da cewa shi ma ya iya irin sa ba.

Maryam ta ƙaraso,ƙafufuwanta sanye da heels ɗin da ta saka silver colour. Ba wasu kaya ta saka na tashin hankali ko nuna tsiraci ba. Aa atampa ce ta saka ɗinkin captan ta saka silver heels da mayafinta shi ma kalar takalmin ƙafarta amma fari. Kalar zanen atampar jikinta. Ta kafa ɗauri wanda ya hau kan fuskarta yayi mata kyau ainun. Jan jambaki da shafa ta kuma zizara kwalli ta dai yi kyau daidai da nata,daman gata fara. Wani ne ya tsaya yana kallonta yace "Ma Sha Allah!" Karafa akan kunnen Muhammad ya ko juya ya sauke masa wani irin kallo sai ga shi ya gane Muhammad ya bar wurin da sauri.

Kallonta yayi yana murmushi yace "Miss Maryam sai na gan ki kamar wata character da kika fito daga cikin wani labari a littafin da ba a rubuta shi ba ma."

Dariya tayi tana son kare kanta tace "kai kuma kamar wanda ka saba da irin waɗannan labaran ba. Ka ga kuwa yadda kalar nan ta yi maka kyau fiye da wadda ka nacewa sak ka fito kamar dai ɗan kasuwa na Hollywood."

Tare suka yi dariya dukan su, sannan ya nuna mata hanya yace "Bismillah."

A cikin hotel ɗin kuwa fitilu ne masu kama da launin zinare suna saukowa daga saman rufin suka bada wani irin ado abin sha'awa. ƙamshin turaren wardi da vanilla na ratsawa ta cikin iskar wurin, kiɗan piano mai laushi da motsa zuciya kamar waƙar soyayya mai bada kalmomi masu sanyaya rai.

Wurin cin abincin cike yake da mutane ba laifi don babban waje ne ,kowa ka gani da mata ko budurwarsa. Duk da hakan Muhammad baya ganin kowa Miss Maryam kaɗai yake kalla.

Ya ja mata kujera ta zauna tace "Na gode."

Kujerar Maryam na kusa da taga,inda za ta iya kallon fitilun wurin daga nesa. Muhammad ya zauna a gabanta,ya miƙa mata gilas ɗin ruwan inibi ta amsa ta ajiye a gabanta kafin ya ɗaga nasa ya kurɓa.

A hankali yace "Yau ba mun zo don cin abinci kawai ba ne, mun zo ne don mu buɗe sabon babi na rayuwar mu ne."

Maryam tayi shiru na ɗan lokaci,idanuwanta suka cika da wani irin haske da ba ta san daga ina ya fito ba. A zuciyarta kuwa cewa tayi "Idan wannan ba soyayya ba ce, to me cece?"

Ya tafa hannunsa yace "Ina kika tafi?"

Ta yi murmushi tace "Ni fa wurin nan ya yi min kyau."

Aka miƙo musu menu. Ya duba da annuri saman fuskarsa yace "Me za a kawo miki?"

Wasa take da yatsun hannunta. "Ka zaɓar mana."

Shi ya zaɓar musu abincin da za a kawo musu.

Tattaunawa suka soma yi a tsakaninsu. Magana suke yi akan abunuwan yau da kullum makaranta,aiki,kasuwanci,masu laifi da abokan arziƙi.

Nan ta jefe shi da tambayar da bai yi zata ba.

Ina son na san me yasa ka gayyace ni cin abinci tare da kai ba tare da mun san juna sosai ba? Ba ka ganin hakan zai saka abokan hammayar ka su samu nasara a kan ka ko abin suka akan hakan ?"

"Abokan hamaya? Basa gabana ban ma san da su ba saboda ban shiga kasuwanci don na kara da kowa ba. Na shiga ne don kaina ,don gobena don kuma na kusa da ni su samu abin yi da kuma tallafawa kan su. Don an gan ni da ke sai ya zama wani tashin hankali? Ko dai kina tsoron kar a haɗa ki da ni? kar ace akwai wata alaƙa a tsakaninmu ni da ke?"

"Ba haka nake nufi ba. Kai babban mutum ne. Kana da shura kuma kana da ƙima da aji a idon duniya gabaɗaya. Ka san mutane...."

"Ki daina damuwa da mutane dama su sana'arsu ce yin surutu. Bana damuwa da zantkansu da ace ina damuwa da tuni na mutu don baƙinciki."

"Saboda me?"

"Saboda ana cewa na ƙi aure wataƙila ina cikin wata ƙungiya ne. Ko kuma ina aikata alfasha a bayan fage tunda ba na kwana a gidan mahaifina. kin san me ?" Ya tambayeta yana tsareta da ido.

Tace da shi "aa sai ka faɗa."

"I care no more. Na daina damuwa da me za a ce a kaina. k
Duk wanda zai ce ya jima bai ce ɗin ba."

Ta sakar mai murmushi kawai.

Jingina yayi da kujerar ya tsaya yana kallonta kawai. Cikin idanuwanta yake kalla da nutsuwa. A hankali ciki-ciki kamar mai yin raɗa ya ji tace "Maryam,akwai wani abu da nake jin ban fahimta ba a tsakanin mu...."

Shiru tayi zuciyarta na bugu. Amma ta yi murmushi kawai tace "kai dai ka iya zaro magana Wallahi."

"Na bar ta."

Hira suka ci gaba da yi. Kowannensu na ɓoye da wata zuciyar ta daban da suka kasa fassara ta. Komai da suka yi oder ɗinsa ya ƙare abinda bai ƙare musu ba kawai shi ne jindaɗin kasancewa tare.

Tare suka jera suka fito suna hira suna dariya ana kallonsu. Wasu ma sun ɗauki hotuna a ɓoye.

Tafiya suke amma kowannensu na jin kamar akwai wani abu da bai faɗa ba sai dai sun bar wa zuciyarsu a matsayin sirrin na zuciyarsu.

A gida suka sauketa da ta fita yace "Miss Maryam na gode da lokacin ki,ba zan taɓa mantawa da wannan ranar ba."

"Nima na gode!."

"Sai da safe,ki gaishe da Mama." Ya faɗa yana miƙa mata wata ledar yace "Mama za ki bawa kice mata in ji ɗanta Muhammadu Sageer."

Tayi dariya ta amsa tace "Shi kenan zan gaya mata sai da safe Allah Ya tsare hanya amin."

Ya amsa shi ma da amin.

Nimra kwance a ɗakinta akan gado. Idanta a kan wayarta da ke haske da wani hoto da ya kulle mata zuciya gabaɗaya. A jikin hoton Muhammad ne da Maryam zaune a wani katafaren hotel suna cin abinci suna yi wa jun dariya. A hankali tace "Ko dai wannan shi ne dalilin da ya sa ya canja min gabaɗaya bayan waccar maganar?" Ji tayi ma numfashinta ya tsaya cak na ɗan lokaci, sannan ta lumshe ido,zuciyarta cike da wani irin raɗaɗin kishin da wuce misali.

Ƙawarta Fadila ce ta turo mata da hoton ta watsapp ɗauke da jimla ɗaya "Ga abinda kika jima kina tambayar kan ki me yasa...ga dailin nan yanzu." Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci Nimra ta miƙe tsaye ta fita daga cikin hayyacin ta. Zuciyarta na raya mata kar ta bar wannan maganar haka ta ɗauki mataki kafin lokaci ya ƙara ƙure mata.

"Koma wacce wannan zata gane bata fi ni komai ba,kuma zan koya mata darasin da ba zata taɓa mantawa da shi ba." Ta faɗa muryarta cike da tsawa da kuma rawar zuciya.

Tuni muguwar ƙwaƙwalwarta ta fara lissafo mata dabaru iri-iri. Ba ta ga wannan a matsayin babbar barazana a soyayyar ta da Muhammad da ta riga ta ɗaure ta gama ta riƙe ta a cikin rayuwarta ba.

Dare ya ja sosai amma Nimra bata iya bacci ba. Ta jawo littafin rubutunta ta fara rubutu a ciki.

Washegari da safe,ta farka a makare amma abin farko da ta yi shi ne kiran Farida da ta shaida mata wannan labarin da ya hana mata sukuni.

Tana ɗaga wayar tace "Ina son a nemo min wacce yarinyar nan kuma ina ne gidansu."

"ki nutsu mana Nimra na san halinki da kyau yanzu sai kiyi abinda zai zubar miki da mutunci da ma na Daddy ga shi kina gani zaɓe ya taho."

Dariya mai sanyi Nimra tayi tace "Farida wannan ba magana ba ce ta mutunci. Wannan magana ce ta mallaka,magana ce ta Muhammad nawa ne mallakina ne,kuma ita yarinyar da take son shigowa rayuwar mu dole ne in nuna mata bata kai ba,bata kuma isa ta shiga tsakaninmu ba. Muhammad rayuwata ne."

"To na ji bani awa biyu zuwa uku zan sa a binciko miki ainihin wacce ce ita."

"Ina jiran ki Farida, ina tsakanin rayuwa da mutuwa ne."
Chapter 14 · 0% Book details