← Book details Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 28

Sashe 12

Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Akwatin kuɗin ya buɗe ya nuna musu milliyoyin kuɗi,naira da daloli. Jami'an suka kuma kallon junansu da ƙwaɗayin samun su.

Sergent Ya'u yace "Mun ɗauki alwashi Alhaji ko da jininmu zai zuba ,kai ba zaka faɗi ba."

Alhaji ya saki dariya ya yar da karan sigarinsa ya take da ƙafarsa ya murje yace "Wannan ita ce gaskiyar mulki,ƙarfi,kuɗi,da kuma muhimmin tsoro. Sauran duk surutun iska ne."

Daga nan suka watse daga ɗakin duhun.

*

Bai samu ya dawo a ranar ba. Ga shi yayi mata alƙawarin zai kai ta su ci abinci tare. Ajiyar zuciya ya sauke yana taɓe baki ganin kiran mahaifinsa na shigowa a jejere yana ƙin ɗagawa. Wata zuciyar tace da shi "ka ɗaga mana."

Yatsan sa ya saka ya danna amsa kira ya sa a handsfree.

"Muhammad wai yaushe zaka yi hankali ne , kamar ni mutum mai daraja in yi ta kiran ka amma ba zaka ɗaga ba? Kira nawa nayi maka? Aike nawa na yi maka kuma?  saboda ka raina ni baka san darajata ba to don ubanka ba a sauya wa tuwo suna ni nan ni Barau ni ne uban ka ni na haife ka."

Muhammad dai yayi shiru bai iya cewa komai ba tuni daman kan sa ciwo yake yi mai bacci yake ji kwana biyu baya samun isashen bacci. Daga gefen sa ya zaro tissue daga cikin kwallin ya saka ya zuba abar tasa.

"Ina magana kana ji na."

"Me zan yi maka to?" Ya faɗa kan shi tsaye ba tare da wani shayi ba.

"Ka zo ina son ganin ka a gida yau ba gobe ba."

"Yau bana nan sai dai goben."

"Muha..." sai ji yayi ya katse kiran gabaɗaya. Alhaji Barau idan da akwai abinda yake ba shi ciwon kai a rayuwarsa to  Muhammad ne shi ne kaɗai ciwon idon sa. Tsaki yayi ya ajiye hularsa ya zaro sigari ya kunna ta.

Bai san kalar tsanar da na yi masa ba mutumin nan amma yana son ya dinga nuna min isa da iko a kaina. Ba zan taɓa ganin girmansa ba ya riga da ya gama zubar da mutuncinsa a idona.

Wayarsa ya ɗauko ƴar ƙaramar nokia ce ba smartphone bace. Lamba ɗaya ce kawai a cikin wayar an saka "Miss" a ciki. Ya shafa screen ɗin wayar yana kallon sunan tamkar hoton ita Miss ɗin yake kalla. So yake ya kira ta kuma yana tunanin yaya zai yi ya kira ta ɗin ba tare da ta gane shi ne ba. Gabaɗaya kan sa har juya masa yake yi ganin ma baya fahimtar komai abubuwa ne cunkus a cikin ransa.

Kiran Gana ne ya shigo masa ya ɗaga a hankali yace "Ina jin ka ya a kai?"

"Yallabai an kira daga gidan cin abincin nan wai booking ɗin vvip ne ko?"

"Na fasa ka basu kuɗinsu kawai na ɓata musu lokaci da akai."

"An gama." Suna ajiye waya Gana ya kalli wayar yace "Wannan mutumin ko mai murɗaɗɗen hali!"

*

Aiki ya kacame mata yau daman a  ofis da gayya Shehnaz ta bata uban takardu ta yi aiki a kan su don kawai kar ta huta. Ta lura matar bata sonta ma kwata-kwata.

Glass ɗin kan fuskarta ta zare ta ajiye a gefe ta sa hannu ta dafa goshinta. Ajiyar zuciya ta sauke tana jin wani irin ciwon kai ga gajiya ga yunwa. Tsaki tayi ta kuma kallon tulin takardun da suke a gabanta sai ta ji ranta ya kuma ɓaci ma gabaɗaya saboda yawansu sai taga kamar bata ma yi nisa ba da sauran rina a kaba. Juyawa tayi ta kalli ko ina taga babu kowa kamar yadda suka zo kusan lokaci ya fara ja ma. Agogon hannunta ta bi da kallo ta ga dare ya fara ƙarfe tara har da rabi. Miƙewa tayi ta soma tattara komatsanta tana zubawa a cikin jakarta.
Daga baya taji ta mata magana.

"Ina kike shirin zuwa baki kammala aikin da na baki ba Maryam?"

Ta juya ta kalle ta fuska babu annuri ita ma tace da ita "Ma'am dare ya yi ka'idar aikin dama 8-8 ne kuma lokaci yayi ina da right ɗin da zan tafi gida."

"Ba ki da right a ƙarƙashin ikon mu kike har yau."

"Ma'am ,na fahimta amma dole ne in tafi. Bana son tafiyar dare,kuma Mama ma ita kaɗai ce a  gida ba wani isashen lafiya gareta ba. Kuma bani da abun hawa."

"I don't care sai ki kwana."

Maryam a buɗe bakinta da mamakin ta tace "Kamar yaya na kwana? Ko a contract dana yi signing ban ga ance zamu kwana ba."

Tana murza yatsun hannunta tace "I don't care." Ta juya ta yi gaba.

Maryam ta saki baki taji kaman an zare mata laka daga jikinta. Daɓas ta koma ta zauna da bayan kan kujera. Kamar ta yi ihu haka take ji amman babu dama. Tana juyawa gefe tayi tozali da wata tsohuwar jarida anyi rubutu a jiki ƙasan rubutun ma an saka sunan Paul stone. Rubutun kuma a kan tsohon sanata ne "Barau." ta shafa sunan ta kuma maimaita sunan da rubutun.

"Wacce fuska ce a bayan wannan fuskar da ke lullube da fatar akuya?"
[9/10, 8:44 AM] Ummulhair S Panisau: RUFAFFEN DUMA.
Ummulkhair S Panisau.
(Khairatup)
Wattpad:khairi_Muhd.
Arewabooks:khairatup01
pg10.

---------------------

Almakashi ta samo ta yanke wurin. Bata tsaya iya nan ba ta shiga ɗakin da ake ajiye kundin bincike a kan staffs ta soma lalubar sunayen su sai dai hakan zai iya zame mata wahala. Wani abu ne ya faɗo mata a rai takardar da baba maigadi ya bata mai ɗauke da wasu lambobi kuma ya ambaci sunan Paul Stone kafin ya rasu. "Anya babu wata alaƙa tsakanin shi da wannan mutumin ba kuwa? Me yasa Muhammad Sageer yake nuna ƙiyayarsa ƙarara akan mahifinsa ,wacce ce mahaifiyarsa kuma ya akai aka wayi gari da labarin zuciyarta ta buga ? Akwai lauje cikin naɗi kuma akwai tambayoyi fal cikinta. Kafin ta samu amsoshin ta ya zama dole ta fara sanin waye Paul Stone kuma me ya same shi ya ɓace. Kamar Smith ya taɓa ambatar sunan  Paul Stone. A nan ba zata samu abinda take so ba ƙila ma an kwashe komai an lallata."

Fita tayi daga cikin ɗakin ta koma kan kujerar ta zauna. Tana da tarin tambayoyi amma bata da mai amsa mata su. In ta haɗa wannan da wancan sai ta ga akwai alaƙa mai kyawu amma daga ina alaƙar take shi ne bata sani ba. In har tana son yin bankaɗa ya zama dole ta tono matattun da aka birni a baya,ma'ana ta nemo asalin laifuffukan." Bata kuma bi ta kan wancan aikin ba ta tattara kayanta ta fita gudu-gudu ,sauri-sauri.

*

Washegari!

Bata kwanta da wuri ba tana ta aikin bincike. Haka ya saka bata tashi da wuri ba. Ba dan ma Mama ta tashe ta ba yau da sai dai tayi gwangwanin aikin.

Ta gama shirinta ta yi sallama da Mama ko abincin kirki bata ci ba tana can tana ta saƙawa da warwarewa a cikin ranta.

GLOBAL TIMES!
A nan bakin ofishin mai adaidaita sahu ya sauke ta. Ta sallame shi ta shiga ciki. Tun daga gate suke gaisawa da masu gadi da kuma sauran ƙananun staffs kamar ta da kuma manyanta. Laptop ɗinta na manne da ita ƙam-ƙam.

"Sannu da zuwa Miss Maryam Kabir." Harshenta ta fito da shi ta datse harshen da haƙoranta. A hankali ta juya tana murmushi tace "Barka da safiya Ma'am."

"Kinga fuskata tayi kala da wadda safiyar ta tayi mata kyau ko daɗi?"

Ta yi saurin jijjiga mata kai tace "Aa Ma'am."

"In my office now."

"Shit. Yau na shiga uku na taro wasa bani da ƴan kallo."

Smith ta kalla da gefen ido wanda shi ma ita yake kallon. Suna haɗa ido kuwa ya sakar mata murmushi ita ma ta sakar mai  murmushin. Ya ɗaga mata hannu alamar "Hi", ita ma ta maida mai martani ta ɗaga mai hannun.

A ofishin Shehnaz kuwa bayan ta gama sauke mata kwandon bala'i da rashin mutunci iri-iri ta kuma bata wani aikin. Wannan aikin kuma rahoto ne take son taje ta ɗauko akan wani case . Babu yadda ta iya dole haka ta saurara ta gama kuma ta bata haƙuri. Duk wasu muhimman details sai da ta ɗauka sannan ta tafi.

Tana son tayi magana da Smith amma babu lokaci dole sai in taje ta dawo. Haka ya saka ta tsaya a gabansa da jakarta a hannunta.

"Smith ina son muyi magana ni da kai don Allah."

"Amma me ya faru?" Ya tambayeta.

"Ba komai wasu bayanai nake nema kawai kuma na san kai ne kake da amsosshin su. In na dawo dai zamu yi magana."

"Yanzu ina za ki je?!"

"Wani rahato zan ɗauko wa Ma'am Shehnaz. Wai anyi kisa jiya a wani gida wani magidanci ya kashe matarsa."

"Amma that should be covered by Aminu Sule?"

"Nima haka na gani."

Kiyi magana da Yallabai ai ba hurumin ki ba ne wannan."

"Bana son matsla already na karɓi na safe da yawa ban son add up na bacin rai."

"To yayi in kika dawo sai muyi waya da ke."

"Sai na dawo."

Tana zuwa daidai ƙofa kuma peon ya kirata yace taje Ogansu na kiranta. Allah-Allah take yi ace ba zata je wannan ɗauko rahoton ba. Ilai kuwa addu'arta ta amsu Oga ya ba wa Aminu Sule ya tafi. Na dinga yi masa godiya kuwa na koma na zauna. A lokacin kuma smith ya tafi wani aikin.

Tunani ne ya sarƙe ni kan dalilin rashin zuwan Muhammad Sageer. Bayan ta lura shi mutum ne mai cika alƙawari.

Misalin ƙarfe shidda na yamma tana zaune tana wani aikin. Yawancin su ma duk sun dawo daga ayyukan da aka tuttura su. Saboda haka ofishin a cike yake da ma'aikata. Gabaɗaya hankalinta na kan aikin da take yi.

Shi kaɗai ya shigo ofishin na su cike da ƙasaita da isa. Kamar koyaushe cikin shigar da ta zame mai jiki da jini wadda bayan ita ba ya sauya kowacce iriyar kala.
Farar riga ce a ciki mai dogon hannu sai kuma ya ɗora baƙar necktie ,ya ɗora babbar rigar suit ɗin ya saka mai sheƙi da ɗaukar ido.
Chapter 12 · 0% Book details