← Book details Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 28

Sashe 2

Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai kuwa ba musu ta amsa ta shaye tas sannan ta ji ta fara dawowa daidai. Wuri ta samu ta zauna ta buɗe littafinta ta kalle shi.

"Na gode da ka amince da wannan hirar.Zan yi ta a takaice cikin mintunan da ka bani."

"Zan so hakan ina sauri ne. Yawanci mutan su kan so su karɓi awaani don jin tarihina. Ni kuma da kika gan ni bani da lokacin ɓatawa. Sai dai ke mintuna sha goma ne suka rage miki. Kin san ni SD bana wasa da lokacina."

Oh! Haka ne. Ta faɗa da sauri. Ta kunna na'urar rikodi,ga biro a hannunta. "Zan fara kai tsaye.Duniya tana ganin Muhammad Sageer Barau  a matsayin hamshakin mai kuɗi ,mai dabaru ,mai gina dauloli ,wanda bai dogara da mahaifinsa ba ya nemi na kansa ya kuma kafa kan sa da kansa. Amma waye kai idan aka kashe waɗanan fitilun taron? Ma'ana a bayan fage? Ina nufin idan kyamarorin suka daina ɗaukar hoto?"

Ya jingina da kujerarsa,yana kallonta da ido mai zurfi kamar yana nazarinta. "Wannan tambayar..." sai kuma yayi shiru daga bisani kuma a hankali yace"Miss Maryam,wannan tambayr na iya zama mai haɗari. Kuma wataƙila ita ce tambaya mafi ban sha'awa da aka taɓa yi min a wannan shekarar."

Maryam ta gyara na'urar rikodi,idanuwanta na bin kowanne motsi na Muhammad.

"Da farko mutane suna ganin ka a matsayin mutum mai nasara,amma duk nasara tana da tushe. Mene ne farkon tafiyar ka zuwa kasuwanci?"

MUHAMMAD ya murmusa ,ya jingina da kujerarsa yace "Kaduna ce ta fara wannan tafiyar."

"Ban gane ba."

"Ina nufin na fara ne da ƙananun jari a cikin kasuwar kurmi market. Amma abinda ya bambanta ni da sauran ina da hagen nesa ne ina ganin dama a inda wasu basa ganin komai."

"Abin burgewa." Inji Maryam. Ta yi rubutu da sauri. "Amma me yasa baka yin amfani da dukiya ko shura ta mahaifinka. Kamar yadda muka sani shi ma sahahararen ɗan kasuwa ne kuma babban ɗan siyasa?"

"Bana son duniya ta san ni da wannan ɗan Barau Abubakar Muhammad ne na fi son duniya ta san ni da asalin ni kaina."

"Gwanin burgewa."

"Wanne ƙalubale ne mafi girma a wurin ka a wannan lokacin?"

Ya ɗan murmusa ya ɗauke kan sa daga kallonta ya mai da kai gurin taga yace "Ƙalubale? Duk lokacin a kake farawa daga ƙasa,mutane suna ganin kana ƙara ƙarancin ilimi ko ƙwarewa.Amma gaskiyar magana dagewa ya fi ko wanne jari da kuɗi."

Miss Maryam ta ɗan yi shiru tana nazarin kalmominsa. Daga bisani ta ci gaba."Yadda mutane ke ganin ka a duniya a matsayin mutum mai ɗaukaka da kasuwanci a ƙasashen waje ,yaya kake haɗa hakan da rayuwar ka a gida?"

Ya kuma murmusawa. Mamaki ma yake bata ashe yana da fara'a saɓanin yadda taji ana cewa ba shi da fara'a.

"Ko wanne yanki na rayuwata yana da muhimmanci.Ba wai kawai kasuwanci ba ne a gabana,amma mutane ko na ce al'umma ,da kuma darajar abinda nake yi hakan na bani cikakken jin daɗi da kwanciyar hankali."

Ta ɗaga kai ta kalle shi da kyau. Mutum mai ƙarfin hali amma mai sauƙin kai a lokaci guda. "Shin akwai wani abu da kake son duniya ta sani game da kai amma bata sani ba?"

Ya ɗan yi shiru kamar ba zai yi magana ba sai kuma yace "Eh ,akwai abubuwa da yawa. Amma mafi muhimmanci shi ne duk abinda kake gani a waje ,akwai aiki tuƙuru da sadaukarwa a baya domin duk nasara ba ta zuwa da sauƙi."

"Aure fa?"

"Sai dai ko nan gaba. Yanzu dai bana wannan tunanin."

"Budurwa fa?"

"Bani da lokacin ɓatawa a soyayya."

Maryam tayi murmushi ta kalli na'urar rikoda tace "To zan iya cewa minti goma sha biyar sun  yi ƙaranci sosai don yin hira da kai."

Muhammad ya kalli agogon hannunsa ,sannan ya yi murmushi mai kama da wani sirri. "Minti goma sha biyar sun yi miki kaɗan?."

"Da zaka ƙara min minti biyar ina da sauran tambayoyi a kan labbana."

"Na baki."
[9/9, 11:27 PM] Ummulhair S Panisau: https://chat.whatsapp.com/LXssYE0TSMQ6ejpXDQe5zx?mode=ems_copy_t

RUFAFFAN DUMA.
Ummulkhair S Panisau.
(Khairatup)
2

*

Tuni Maryam taji girma da ƙima na Muhammad ya kama ta.

"Koda duniya ta san ka a matsayin ɗan kasuwa mai nasara,akwai abubuwan da suke sa ka farinciki wanda bamu sani ba? In akwai meye sirrin?"

"Farinciki na gaske... yana zuwa ne daga ganin mutanen da ka ke taimaka musu don ganin sun cimma burinsu. Ba daga iya jari ko gidauniya kawai ba,amma daga gina mutane,daga ganin mutane suna bunƙasa saboda abinda ka taimaka musu da shi. Wannan shi ne ainihin farinciki a wurina."

"Zan iya cewa kai mutum ne mai zuciya mai kyau a bayan hoto na wadata da iko?"

Kai tsaye ya kalle ta ,idanuwansa na haskawa "Za ki iya faɗa Miss Maryam...amma ki sani ba kowa ne yake ganin hakan kamar yadda kike gani ba. Wannan hirar na ji daɗinta ban taɓa yin irin ta ba. Wannan ita ce hirar da take da muhimmancin nuna gaskiya a bayyane."

Ita Wallahi muryarsa daɗin sauraro take yi mata. Sautin muryarsa mai daɗin ɗanɗano mai kama da sirdi.

"Ka taɓa jin tsoro ko fargaba a lokacin da kake kasuwanci?"

Agogonsa ya kalla yana murmushi yace "mintuna ashiri kaɗai ba zasu isa na baki tarihina ba. Amma dai duk wanda ya fara daga ƙasa dole ne ya ji tsoro. Amma abin da ya bambanta ni da saura shi ne yadda na juya tsoron zuwa ƙarfina."

Maryam shiru tayi tana kallon fuskar sa, tana ganin ƙarfin hali da kwarjini,amma kuma mutum mai sauƙin kai da tausayi.

"Akwai wani abu...ina jin akwai ƙarin zurfi a tare da kai,wani abu da mutane ba sa ganin sa a tattare da kai?"

Murmushi yayi mai ban sha'awa yace "Miss Maryam, kowa na iya ganin waje na a rayuwa,amma kuma sirrin zuciyata yana ga waɗanda suka da mu da ni da gaske. Kuma zan iya cewa yanzu,kina cikin waɗanda zasu iya ganin ɗanɗano na gaskiyata."

Zuciyar Maryam ta soma bugu da sauri "Me yake nufi kenan?"ta tambayi kan ta. Sai ta ga kamar abin na son ya wuce tambayoyin jarida kawai, ba iya hirar aiki bace kamar dai wata iriyar alaƙa ke son ginuwa a hankali cikin hankali.

Gani tayi ya miƙe tsaye ya gyara zaman rigarsa ya ɗauki wayarsa yace "Na gode. Lokacin ki ya cika. Amma wata rana zamu kammala abinda muka soma. Naji daɗin haɗuwa da ke Miss Maryam. Kin burge ni da alamu za ki kai wani mataki babba a nan gaba. P.A zai sallame ki na bar ki lafiya." Yana gama faɗa ya juya ya fita ya bar ta  zaune jigum tana tambayar kanta "Me ya faru yanzun nan?"

A kan idonta Muhammad ya fice daga ɗakin ya bar ta da ƙamshin sa ya bar ta da tunaninsa. Mutane na masa kallon mutum mai girman kai da ɗagawa amma yau ita tayi tozali da sabon Muhammad ne ba wanda take ji ana zancensa ba sai dai a fuskar mutumin da ta gani ido da ido.

Ta tattara kayanta ta fita ita ma. Nan ta haɗu da team ɗinta suka ɗauki hayar komawa can Global times office. Ita kam yau ta gama zama wata a gidan a matsyinta na Junior reporter yau an bata babban aiki ita ko a iya haka jarida ta biyata.

*

"Muhammad, fatan yarinyar bata wuce ka'ida ba?"

"No bata wuce ba hasalima ta burge ni,ƙwarin guiwarta ya yi min da kuma yadda take yin komai cikin nutsuwa. Bata damu da sanin personal life ɗina ba wannan ya saka na ji daɗin hirar da ita don kuwa komai mun yi shi ne  a kan kasuwanci.Ta iya aikinta zata kai wani babban mataki a gaba bata da tsoro."

"Da kyau!Ance junior reporter ce wannan ne karo na farko da aka bata irin wannan aikin."

Murmushi yayi yana gyara links ɗinsa yace "Ta burge ni ayi mata sallama mai kyau."

P.A M.Gana kuwa ya jinjina wa Maryam da kwazonta don kuwa in har Muhammad ya nanata kwazon mutum ko ya karya ka'idarsa tabbas ba ƙaramin burge shi yayi ba. Muhammad mahaifin ka ya kira ɗazu yace ka neme shi."

Nan da nan ya sauya fuskar sa annuri da walwalar kai suka kau. A lokaci guda ya ji wani irin ɓacin rai ya ziyarce shi tuni ya lalubo baƙin gilashinsa ya saka ya kame ya haɗe rai ya maida kai bisa titi."

P.A ma sai ya kama kan sa don ya lura ba tun yanzu ba Muhammad baya son ana danganta shi da Sanata Barau. Ko me yasa? An rasa gane dalilin.

Muhammad Sageer Barau.
Ya taso a gidan wadata da suna. Mahaifinsa ,Sanata Barau Muhammad ,ya yi Sanata a garin Kaduna ,kuma yayi a garin Abuja. Duk kuwa wanda ya san Barau zai ga kamar cewa girma da kuma kwanciyar hankalin Muhammad zai zo masa da sauƙi  saboda arziƙi da  iko na mahaifinsa.Amma sai shi Muhammad ya ɗauki tasa tsanin rayuwar daban a yadda yake son ya yi rayuwarsa ba tare da dukiyar mahaifinsa ba. Akwai wata ƙulalliya tsakaninsa da mahaifinsa wanda hakan ya ja labule tsakaninsa da shi. Duk da kuwa duniya bata san da haka ba daga uban sai ɗan sai Allah,sai makusantan su na jiki.

Tun yana saurayi ,ya ƙudurta a ransa ba zai jingina da mahaifinsa ba, Saboda kar ma duniya ta dangata dukanin wata nasara da zai samu da shi,saboda haka ya ƙudurta a ransa zai kafa kansa da kansa da ikon Allah.

Ya fara da ƙananun kasuwanci musanmman a kurmi market daga baya kuma da ya kammala karatunsa sai ya ji yana son ya buɗe wani ƙaramin kamfani na jigilar kaya a Kaduna da motoci guda biyu kacal da zasu dinga ɗaukar kaya daga kasuwar kurmi zuwa shagunan Kaduna da Kano. Duk wanda ya gan shi a lokacin ba ya iya yarda cewa shi ɗin ɗan tsohon Sanata ne,Domin kuwa yana aikinsa ne da kansa a ofishinsa ɗan matsakaici. Yana tsara kwangilarsa,yana kuma tattaunawa da direbobinsa.

Bayan wasu shekaru ya ƙara faɗaɗa kasuwancinsa zuwa jigilar kaya tsakanin jahohi. Baya jin kunyar zuwa kasuwa da kansa, yana tattaunawa da ƴan kasuwa ,yana kuma nazartar buƙatunsu.
Chapter 2 · 0% Book details