Sashe 24
Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alƙali na shiga kowa ya miƙe tsaye.
Alƙali ya zauna ,sannan saura suka zauna.
Aka karanta jawabi kan laifikun da ake tuhumarsu da shi.
"Shirya garkuwa da mutane.
Tsoratar da jama'a.
Kai hari ofishin ƴan sanda."
DSP aka kira ya tsaya a wurin bada shaida (Witness box) ya kora bayanin komai tun daga farkon yadda aka yi garkuwa da yara da kuma yadda suka shiga dajin kuyello don ceto su da kama ƴan bindigar da aka yi har suka faɗi wanda ya aiko su.
Alƙali ya buƙaci a soma kawo shaidu.
Kasancewar Maryam ce shaida ta farko ita aka soma kira. Miƙewa tayi ita ma ta shiga cikin witness box ɗin ta tsaya haɗe da ɗan risinar da kai a gaban alƙali na nuna girmamawa.
Lauya: "kina da hujjar cewa waɗanan mutanen su ke da hannu a kan wancan lamarin na garkuwa da mutanr a ƙauyen Birnin Gwari?"
Maryam ta numfasa tace "Ina da hujja. Ni ƴar jarida ce ,sunana Maryam Kabir ina ɗaya daga cikin mutanen da suka maida labarin kwashe yaran da aka yi da muhimmanci , a matsayina na ƴar jarida nayi tambayoyi ga mutane kala-kala kuma na samu bayanai. A daren ne ɗaya daga cikinsu ya kawo kan sa wurin hukuma aka kira ni kuma aka yi masa tambayoyi, shi ne ya gaya mana inda aka kai yaran dajin Kuyello ana kiran gidan da aka ajiye su da White House.....komai ta gaya musu da ta sani har shiga sansaninsu da suka yi. Ta miƙa masa wata ƙaramar rikoda da akwai muryoyin masu laifin a ciki. Sannan ta bada vidio na yaƙin da aka yi kafin aka kwato yaran daga wurinsu da yadda aka kama su harda tona asirinsu da aka yi."
Lauya "zata iya yiwuwa ai ,haɗa wa aka yi. Ki tuna ke fa ƴar jarida ce za ki iya yin wasa da hankalin mu."
Maryam tayi murmushi ta san za ayi hakan dama.Ta juya ta kalli alƙali ta ci gaba da magana.
"Ya mai girma mai shari'a na san lauyan waɗanda ake ƙara daman zai ce haka shi yasa ban kawo ba sai da shaidar tacewa daga manyan da suka san harkar yadda ake tantance ainihin muryoyi ma'ana ba wadda aka ɗora ba ce. Muryoyinsu ne na aslali. Bayan ni a wurin akwai DSP Hamza akwai kuma inspector Aliyu Sa'ad. Kotu zata iya bada wa aje a tantance."
Jama'a suka saka dariya. Alƙali ya daka guduma bisa tebur ɗinsa yace "Ayi shiru."
Lauya "Za ki iya tafiya. Ya mai girma mai shari'a ina son kotu ta bani damar kirawo DSP Hamza."
Alƙali "Kotu ta baka dama."
Lauya "DSP Bismillah!"
DSP Hamza ya fito a karo na biyu ya tsaya ya kuma yin rantsuwar zai faɗi gaskiyar da ya sani.
Lauya"Shin a wannan atisayen da ka yi akwai sanin manya a ciki ko kuma kai ne kayi gaban kan ka da kan ka don ka samu isashen lokaci wurin shirya wannan wasan kwaikwayon?"
DSP "Ban jira ba saboda babu lokaci, ina tsoron kar su sauya musu maɓoya."
Lauya "ka taka doka kenan?"
"Ban taka doka ba aikina nayi a matsayina na ɗan sanda wanda hakkina ne kare lafiyar jama'a da lafiyarsu da dukiyarsu."
Lauya " Me ye dalilin ka na tafiya da ƴar jarida mace?"
"Saboda ta kawo labaran da kan ta. Aikin ta ne ta nunawa al'umma abubuwan da suke faruwa a bayan idanunsu hakan ba laifi ba ne."
Lauya "An ce anyi musayar wuta tsakani,to da ace an harɓi ɗaya daga cikin ƴan matan fa? Baka ganin kayi wasa da rayukanasu suma?"
DSP "Babu wanda aka rasa kuma su suka fara buɗe mana wuta kafin muka maida martani mu ma."
Jama'a (tafi).
Alƙali (Gargaɗi.)
Dsp "Ya mai shari'a ina son kotu ta bani dama na kawo makaman da aka kai mana farmaki a daren da aka samu ƴan matan."
Alƙali "Kotu ta baka dama."
Yaran DSP suka shigo da bindigun da aka kama a jikinsu ,da kuma wayoyi da aka samu bayanan kira da saƙonni daga Danzaki. Daga baya kuma aka shigo da Dattijo shugaban ƴan bindiga.
Tuni idanuwan Danzaki suka firfito waje da ya fara jin sanyi kamar zasu iya sha. Amma ganin shugaban sai ya ji yau kam ramin ƙarya ya ƙure musu.
Lauyan Gwamnati "Dattijo za ka iya gaya mana gaskiyar abinda ka sani?"
Dattijo "Ni ne shugaban su. Ni da yarana ne muka yi wannan aikin, sai dai da fari ba a kama ni ba sai a kuskure na biyu da muka kai hari caji ofis."
Lauyan Gwamnati "Su waye suka saka ka aikin zaka iya gane su ka nuna wa kotu su in suna nan?"
Dattijo "Gasu nan a gurfane da Alh.Danzaki da Alh.Shehu. Sune suka saka mu kai hari caji ofis mu kashe yaran da aka kama saboda kar su bada sheda akan su. Sai aka yi rashin sa'a mu ma aka kama mu."
Lauya "Mun gode. Ya mai shari'a i rest my case."
Alƙali "Defence Lawyer baka da wani abin cewa?"
Lauyan ya miƙe ya duƙa yace "Ya mai shari'a ina da tambaya ga Dattijo."
"Kotu ta baka dama."
"Dattijo taya ya aka baka aikin kwamushen yaran ,da har kake ikirarin Alh.Danzaki ne ya baka aikin, meye hujjar ka?"
Dattijo "Ya gayyace mu gidansa na GRA, da mu da su muka yi magana su biyun nan ga su nan." Ya nuna su da hannunsa sanan ya ci gaba.
"Ya bamu aikin mu kwaso yaran ,bamu da niyan karbar kudin fansa dama za a kai su kasashen ketere ne a sayar dasu."
Jama'a (aka soma ƙus-ƙus ,hayaniya ta ƙaure a ciki. Alƙali ya yi gargaɗi aka yi shiru."
Bayan tattara bayanai aka miƙawa alƙali ya sanar da hukuncin da ya yanke.
Alƙali "Danzaki da Shehu,bisa shaidun a aka gabatar,kotu ta same ku da laifi a akan dukanin tuhume-tuhumen. Kotu ta yanke muku zama a gidan kaso na shekaru talatin a gidan yari tare da horo mai tsanani." Ya maka gudumarsa ya miƙe tsaye.
Jama'a sun jinjina wa wannan shari'ar da aka yi ba tare da son rai ko siyasa ba. Ba a duba iko da arziƙ ta mutane biyun da duniya ta shaida dukiya da matsayinsu ba aka yanke musu hukunci lallai adalci yana na nan tafe,shari'a ta soma yin adalci tsakanin talkawa da masu kuɗi.
Maryam ta fita tana jin wani sanyi na ratsa ta.
Dsp ya ce da ita "Maryam mun gode da gudunmowar da kika bamu har muka kai ƙarshen wannan case ɗin. Wannan zai zama babban tarihin da Kaduna ba zata manta ba."
Maryam ta ɗaga masa baban yatsanta alamar jinjina tana dariya tace "Allah Ya taimaki waɗanda suka yi sadaukarwa domin gaskiya. Na ji daɗin yin aiki da kai Yallabai. Kai mai gaskiya ne. Ina fatan wani aikin ya kuma zuwa da zamu yi tare."
"Ina tsoron sanar miki ba zai yiwu ba iya tarayar kenan."
"Me yasa Yallabai?"
"Yau aka aiko mini da takardar transfer ɗita an sauya min wurin aiki zuwa Zamfara."
Maryam ta fito da idanuwanta waje tace "Na san za ayi hakan,amma ban da wuri haka ba."
"A hakan ma na gode. Tunda mun kai ƙarshen lamarin."
"Allah Ya baka yawan rai."
"Amin ɗiyata Maryam. Allah Ya miki albarka ya kiyaye ki. Ya jiƙan Kabir Abdallah."
"Amin."
Aka fito da Danzaki da Shehu suka kalli DSP da Maryam suka yi kwafa aka wuce da su.
"Kallon gargaɗi ne wannan". Inji Maryam.
"Maryam mu bar....."
Sautin abu kawai suka ji ya daki ƙirjin DSP ji kake tush harbi ne. DSP ya dafe ƙirjinsa yana ƙoƙarin faɗuwa ƙasa tuni jini ya fallasa a kan fuska da jikin Maryam. Ta saki ihu tana ƙoƙarin juyawa ita ma ta samu nata rabon sai dai ita a kafaɗa aka same ta.
Tuni harabar ta hautsine da ihun jama'a.
Tuni kafafen yaɗa labarai suka soma sakin labarin.
_Breaking news._
_An kai hari a harabar kotu bayan yanke hukuncin da aka yi ga Shahararrun ƴan kasauwan nan Danzaki da Shehu, an harbi Dsp Hamza da ƴar jarida Maryam da ta zama shaida ga shari'ar. Daga wata majiyar kuwa harin na da nasaba da shari'ar manyan ƴan kasuwa da ƴan siyasa da ake tuhuma._
Muhammad na ɗakin taro a ofishin sa Gana ya kira shi ya sanar masa da harin da aka kai wa Maryam a take ya saki salati yace "Gana suna ina yanzu? How bad is it?"
"Babu masaniya an kwashe su dai an tafi da su asibiti."
"Gana ina zuwa ka kula kafin na iso.
[9/12, 10:02 PM] Ummulhair S Panisau: RUFAFFEN DUMA.
Ummulkair S Panisau.
(Khairatup)
Karamci Writers Association
Wattpad;khairi_muhd
Arewabooks:khairatup01
19
Tuni garin Kaduna ya cika da haya-haya ana ta magaganu. An rasa su waye suka yi harbin tamkar waɗanda ƙasa ta tsage suka shige ciki haka aka neme su aka rasa. Jami'an tsaro kan su ya ɗau caji. An shiga da su cikin ɗakin tiyata. Kowa jiran fitowar likita yake yi.
Jama'a da dama na roƙon Allah Ya tashi kafaɗun Maryam da Dsp saboda mutane ne nagari kuma akan gaskiyarsu aka kwantar da su.
Mama hawayenta basu daina zuba ba. Ta kasa magana sai hawaye. Da ɗaya da ɗaya ta ga ciwo da raɗaɗin rashi. Da farko mijinta wanda ya fita lafiya sai gawa aka kawo mata, na biyu Yusuf daga fita har yau ba a kuma ji daga gare shi ba , Maryam ɗin da yanzu take gani tana jindaɗi ita ma an sabauta mata ita.
Gani tayi an miƙa mata handkacief.Ɗaga kan ta tayi sama. Matashin saurayi ta gani fari tas bafulatani. Handkachief ɗin ya kuma miƙa mata.
"Mama ki share hawayen ki. Maryam da Dsp na buƙatar addu'a ne in sha Allahu babu abinda zai same su kiyi imani."
Mama ta gyaɗa kai tana share hawayenta da hadkacief ɗin da ya ke fitas da ƙamshi mai sanyaya rai.
Gefe ya koma ya tsaya da wani ɗan sanda suna tattaunawa kan lamarin. A nan yake gaya masa ana kan binciken masu sa hannu a abin.
Muhammad ya cije leɓɓensa na ƙasa ya juya kawai.Hannayensa ya zura cikin aljihunsa ya kafa idanunsa akan ƙofar ɗakin tiyata.
*
*
BARAU DIKKO TEACHING HOSPITAL.
Harabar asibitin cike yake maƙil da ƴan jarida, ƴan sanda da tsirarun jama'a masu san ganin faɗan ƙarshe.