← Book details Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 28

Sashe 4

Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*
Gidan ba mai girma ba ne sosai ɗan matsakaici ne daidai zaman rufin asiri.  A tsakiyar falon Maryam ce a zaune ta baza takardu da hotuna da rikodar  tana nazari. Kunnenta na ɓarin dama fensiri ne a maƙale. Daga gefe ta hango wani hoto da ta ɗauka a wayarta lokacin da ta shiga harabar wani tsohon gini da ya faɗo a kan wasu bayin Allah. Waɗanda aka tono su daga ƙarkashin ƙasa.Bayan dogon nazari ta lura da hannun ɗaya daga cikinsu yayi ja kamar an ɗaure shi da igiya har ya bar shati. Ɗayan kuma a ƙafa ɗayan kuma an rufe masa baki. A fili tace "Waɗanda gini ya faɗo musu meye alaƙarsu kuma da irin waɗanan shatin?" Akwai lauje cikin naɗi duk yadda aka yi ana ƙoƙarin ɓoye wani sirrin ne ,wani babban al'amari ake shiryawa. Littafinta ta janyo ta zaro bironta daga bayan kunnenta na hagu ta soma yin rubutu a cikin takarda,tana haɗa bayanan da ta samo. Akwai wani mai gadi tsoho ne ,ya sanar mata da cewa wannan faɗuwar ginin da mutuwar waɗanan bayin Allahn shiri ne daga manyan ƴan ƙasa don su ɓoye wani abu. Tsohon ya tsere amma ya bar ta da lallube a cikin duhu.

"Idan har na bar wannan labarin ya tafi a haka, to tabbas na ci amanar ƙasa. Ya kamata na shiga na fita na nemo gaskiya na bayyanawa duniya su ma waɗanan bayin Allahn na kwato musu haƙƙinsu.

Wayarta ce ta ɗauki ƙara. Ta sa hannu ta ɗauka, "Maryam ya aka yi baki kawo min rahoton ki na wancan satin ba?"

Tuni Maryam ta saitu. Madam Shehnaz ce fa a waya babbar Editer ɗin su.

"Gobe zan kawo miki. Na samu babban labari."

"Good." Kawai ta faɗa ta kashe wayar.

Wayar ta bi da kallo na wasu sakanni ,zuciyarta na bugawa kamar gangi. Daga nan ta jingina da kujera ta ɗora hannuwata bisa fuskarta ta saki ajiyar zuciya. Wani abu ya gifta mata a ƴan sakanin da ta kulle idanuwanta. Tuni ta buɗe tana sauke ajiyar zuciya a jejere. Akwai abubuwan da suka cunkushe mata a ƙirji,suka kuma zauna mata a kwakwalwarta wanda ta kasa manta su bare ta daina ganin gilmawar hotunansu a cikin idanuwanta. Ba zata manta da zaluncin da aka yi musu ba kuma ba zata ja da baya wajen neman hanyar ɗaukar fansa ba. Ba kuma zata sauke ƙudurinta na fito da gaskiya fili ba,ko da kuwa hakan zai iya jawo mata haɗari.

  Mama ce ta shigo falon ta kalle ta tace "Wasa-wasa kin maida gidan nan wani ƙaramin ofishin ki. Don Allah dubi yadda kika barbaza min takardu da hotuna a tsakar falo. Kamar a kan ki aka fara aikin jarida."

"Mama...na fa lura ba kya son nayi aikin nan."

"So nake yi ki fitar da miji kiyi aure ki manta da wannan aikin kiyi zamanki a ɗakin ki kema. Sa'aninki duk suna ɗakunansu ke kina nan kina fama da biro da takardu da hotuna."

"Mamaaaaaaaa...." ta faɗa tana jan sunan ta da ƙarfi.

"Ke kika sani. Tashi za ki yi ki gyaran falo ,can ki koma ciki ki ƙarata nima nan marking zan yi wa yara.

"Mama na san Abba yana alfahari da ni."

Mama ta tsaya cak tana kallon ƴar ta Maryam tuni idanuwanta suka ciko da hawaye. Wani lokaci na rayuwarsu ya dawo mata sabo fil ba ta manta ba kuma ba zata taɓa mantawa ba ciwo ne da mantuwar shi daga gareta sai dai ranar da ƙasa ta rufe mata ido kawai.

"Kiyi haƙuri Mama,bana so ki manta saboda kar ki manta da raɗaɗin abin da aka yi mana. Tunowar ki da zubar ƙwallar ki a kai shi ne karfina da ƙwarin guiwata."

"Maryam babu kyau wasa da wuta."

"Mama wata wutar kota ƙona ka ba zaka ƙone ba sai dai ita ta salamce."

"Maryam ke kaɗai na ke gani nake jin sanyi a cikin raina. Bana son ki shiga wasan da zamu zo muna wayyo Allah!"

"Mama Abba ya koya mini yin yaƙi da ƙarya. Ya koya min bin hanyar gaskiya da kuma jarumta. Ba zan manta da duk wata koyarwar sa ba ."

"Shi kenan Maryam.Allah Ya yi miki albarka ,Ya tsare min ke."

"Amin Mama. Addu'arki kaɗai nake so daman."

"Kullum tana tare da ke."

Ta rungume Mama ta gefe tana share nata hawayen.

*

Washegari da ƙwarin guiwarta ta shiga ofishin Shehnaz Ahmad,Matashiyar budurwa mai ji da iko,shekarunta ba zasu haurawa talatin da shidda ba amma ta kai wani matsayi da mataki mai girma a harkar jarida. Shehnaz Ahmad allon kwaikwayo ce ga ƴan jarida masu tasowa saboda ƙwarewarta a aiki. Ana shakkarta sosai ta iya manipulating ɗin labari ta fuskar da in ka saurara sai ka gamsu da hakan ne. Su ƴan jarida za a iya kiransu da idon al'umma gabaɗaya (media) abinda ta wallafa ko ta kawo shi ake yarda da shi. Global times ofishin jarida ne da ake ammana da labaransu.

Ɗakin a cike yake da tsofaffin jaridu, da kuma hotunan tarukan gwamnnati a kyaututtukan da suka ci saboda rubuce-rubucensu.

Maryam ta ajiye  fayil ɗinda ta haɗa a gaban teburin ta. Cikin takunkumin numfashi tace "Ga rahotan nan Ma'am na kammala. Wannan ba ƙaramin lamari ba ne da za a bar shi , da alamu ba natural death ba ne sai da aka musu izaya sannan aka kashe su aka kai su nan aka sauke musu ginin a kai don a nunawa mutane cewa hatsari ne. Hakan na nuni da wani ɓoƴayyen al'amari da ake ɓoyewa. Akwai sa hannun manya a ciki musanmman ƴan siyasa...." Shehnaz ta ɗaga mata hannu alamar ya isa. Fayil ɗin ta ɗauko da sauri,ta lumshe idanuwanta na ƴan sakanni kafin ta buɗesu tace "Kin burge ni. Ban damu da na san ƙananan ma'aikatan ba amma ke kam kin saka na san fuskar ki na kuma riƙe sunanki dama na gaya miki ba zan tuna ki hakan nan ba dole sai kin yi wani babban abu tukunna. Kin iya aikin jarida da kyau. Amma wannan rahoton ba za mu iya wallafa shi a jardar mu ba. Akwai barazana mai girma ga Global Times muddin muka wallafa wannan labarin, yin hakan zai rusa mana mutuncin gidan nan."

Tuni idanuwan Maryam suk cika da hawayen bakinciki. "Amma Madam ,meye manufarmu a matsayin ƴan jarida in har ba za mu tona gaskiya ba? Wanne daraja  za mu yi? Wannan kujerar da kike kai bata da amfani tunda zamu fara rufe ido akan gaskiya saboda tsoro."

Shehnaz ta bugi teburin da ƙarfi tace "Ke har kin isa ina magana kin suka na? Yaushe kika zo gidan?  Ko don kin ga Yallabai na ɗaure miki ƙugu shi yasa kike jin ke wata ce?   Ƴar ƙaramar alhaki ce ke yarinya yaushe kika shigo aikin? Har yau baki san komai ba? Wa ya ce miki aikin gaskiya kawai muke yi? Saurara da kyau aikin jarida da kike gani kasuwanci ne muna sayar da abinda muka san zai kawo mana kuɗi ne kawai. Ke ma don kuɗi kike aikin."

Maryam ta saki baki tana ganin ikon Allah!
"Kenan jininsu ya tafi a banza?"

"Maryam, ki saurare ni da kyau wasu lokutan dutse muke ɗauka muke ɗorawa a kan ƙirjin mu don mu aiwatar da wasu abubuwan ko yanke wani hukunci. Na san gaskiyar kike nema ,amma mutanen nan sun wuce duk yadda kike tunani kafin ke anyi wasu bayan ke ma za ayi wasu,duk da haka babu abinda zai sauya na ɓoye gaskiya. An taɓa ɓatar mana abokin aikin mu Paul Stone a kan irin wannan binciken. Idan kika ci gaba , za ki iya rasa rayuwarki. Kuma babu wanda zai kare ki."

"Ba don na ɓoye gaskiya na shiga aikin jarida ba, ba kuma don na ɓoye gaskiya na zaɓi fannin laifuka ba (crime reportig). Idan ba zaku wallafa ba zan samu wata hanyar ,idan kuwa gaskiya ta ɓuya saboda tsoro,to ni ma zan so na mutu a kan neman gaskiyar,fiye da in rayu cikin shiru."

Ta sa hannu ta tattare fayil ɗin ta fice daga cikin ofishin, zuciyarta cike da ƙudiri  a ƙasan ranta, cewa wannan ranar ta shiga cikin yaƙin gaskiya wanda rayuwarta ce farashin sa.

Shehnaz ta bi ƙofar da kallo ta yi ƙwafa haɗe da ɗaukar wayarta ta soma kiran wata lamba. Jim kaɗan aka ɗaga kiran ta ce.
  "Da alamu tarihi zai maimaita kan sa. An samu sabuwar ƴar balaja'un da take ƙoƙarin shiga gonar boss. Yanzu dai na hanata amma ban san iyakacin lokacin zan dinga danne ta ba wannan mai zafi ce da taurin kai. Ya kamata ku ɗan taƙaita na wasu ƴan kwanaki da alamu akwai idanuwa bisa kan mu.Akwai yuwuwar tarwatsewar nakiya muddin muka kuma yin wani laifin. Saboda haka a taka a sannu."

Ban san me aka ce daga ɗaya ɓarin ba sai kawai tayi murmushi ta kashe wayar.

"Dubunki sun zo kuma sun tafi ,amma babu abinda ya girgiza sarautar Boss."
[9/9, 11:27 PM] Ummulhair S Panisau: RUFAFFAN DUMA.
Ummulkhair S Panisau.
(Khairatup)
Wattpad:Khairi_Muhd.
Arewabooks:Khairatup01.

04

Maryam na fita daga ofishin Shehnaz Ahmad zuciyarta sai tsuma take yi.Jikinta har rawa yake yi ta ko ina tuni kalar idanuwanta sun sauya daga farare zuwa jajaye. Smith da ya fito daga wani ɗakin ya bi ta kallon mamaki bai taɓa ganin fushi a tattare da ita ba sai yau duk yadda aka yi wani babban al'amari ne. A hankali ya isa kusa da ita yace "Miss Maryam" juyowa tayi ta ɗan kalle shi kawai sai ta ɗauke kan ta gefe ta share guntuwar ƙwallar da ta zubo mata daga ido.

"Kina lafiya?"

Ba tare da ta bashi amsa ba ta fice kawai daga cikin gidan.

Titi ta tsallaka da gudu ta samu jikin bishiya ta jingina tana jin wani abu na cin zuciyarta kamar zata yi ihu. Ta yi kusan mintuna biyu a tsaye a nan tana kuka. Bata yi aune ba kawai ta ga tsayuwar wata mota a gabanta. Baƙar mota ce mai gilashi baƙi,babu wanda ake gani a ciki bare a iya hango fuskar wanda ke ciki.  Tagar motar aka zuge a hankali. Cikin murya mai sanyi ƴar siririya aka ambaci sunanta.

"Maryam Kabir.." ta tsaya cak zuciyarta na yi mata luguden daka da ƙyar ta iya cewa "Na'am"
Chapter 4 · 0% Book details