Sashe 8
Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Zan je na kwanta. Na gode ,na ji daɗi da na tattauna da kai. Dama abubuwa sun cushe min da yawa a cikin raina yau na amayar da su i feel relieved. In sha Allah da safe zan tafi gida."
"Bai zama lallai ki tashi ki same ni ba. Kamar yadda kika sani ni matafiyi ne."
"Zan iya yi maka wata tambaya in ba zaka damu ba?"
"Allah sa ba raina zaki tambaya ba?" Ya faɗa cike da tsokana.
Dariya tayi tana kulle fuska.
"Tambaye ni na fara jin bacci."
"Me yasa ba ka tare da mahaifin ka,kuma mai yasa baka son a danganta nasarar ka da shi?"
Kusan sakan biyar ya ɗauka yana kallonta kafin ya kifta ido ya ɗan sauke ajiyar zuciya yace "Hah! Bana son a danganta nasarata da shi saboda na fi son duniya ta sani da ni kai na. A baya ma na faɗa. Bana tare da shi saboda ni ba mazauni ba ne."
"Ban gamsu ba amma ba zan tona ba."
"Oh! Ashe fa Maryam reporter ce."
Tayi murmushi. Har ya juya ta yi saurin katse shi tace "Am mahaifiyar ka fa? Ban taɓa jin ka faɗi komai a kan ta ba."
"Ta rasu!."ya faɗa da wani irin ɗaci a maganar har yana runtse idanuwansa biyu daga bisani ya buɗe su.
"Ayya! Allah Ya yi mata rahama ,ya haska makwancinta."
"Amin ,na gode." Ya faɗa ya juya da sauri ya shige ciki.
Bayansa ta bi da kallo. "Akwai boyayyen sirri a tare da kai. Kai ne tsanin da zan hau na kai ga nasara." Ta faɗa tana wani irin makirin murmushi. "Idan ɗan yatsan ka ya ƙarye ya zama dole ka kuma lanƙwasa shi kafin ya dawo daidai ya tsaya. Idan mutum ya kasa fahimtar naka yaren kai ma sai ka fahimtar da shi da na sa yaren."
*
Nimra Waziri ƴa ga shahararen ɗan siyasar nan da aka fi sani da Shamsu Waziri. Cikakkiyar ƴar boko ce kuma hamshaƙiyar ƴar kasuwa. Kusan rabin rayuwarta a turai tayi shi. Ƴar gatan mahaifinta ce domin kuwa ita kaɗai ya mallaka. Hakan ya saka bata san wani abu wai shi babu ba bare kuma kalmar "Aa". Duniya babu abinda take so da muradi irin Muhammad Sageer. A da suna soyayya kamar zasu cinye junansu sai dai wani munmunan al'amari ya afku,hakan ya sa suka ja baya da jununsu amma ban da Nimra ta kasa mantawa da Muhammad. Shi kuma ya fi ta taurin kai ya gaya mata ba zasu koma kamar baya ba.
Yanzun ma a zaune take kan wata ƙaramar kujera. Ko kayan kirki babu a jikinta wata ƴar ƙaramar shimi ce ta saka sai wani gajeran wando a hannta na dama tsakankanin yatsunta biyu kuwa sigari ce ta ke riƙe da ita. Cike da ƙuluwa ta saka a bakinta tayi mata wata doguwar zuqa har tana ƙware wa saboda yadda ta ja ta da yawa, tari ya sarƙe ta. Aikuwa ba kakautawa ta dinga yin tarin nan kuma ta kasa tashi daga wurin. Tuni launin idanuwanta suka sauya kala.
Da sauri Hajiya Zuwaira ta ƙarasa kusa da Nimra tana shafa mata baya a hankali tana hura mata iska akan fuskarta.
"Nimra... Ba za ki dain yiwa kan ki izaya ba akan wannan yaron mai shegen taurin kan ba?"
"Mum ,ba zan iya daina son sa ba. Kuna bani dukanin abinda nake so amma har yau kun kasa mallaka min Sageer. Yaya kuke so nayi da rayuwata ne wai? Ba ni na zaɓi soyayyar sa ba soyayyar sa ce ta zaɓe ni da kan ta kuma tana matuƙar wahalar min da zuciyata. Mum kuna gaf da rasani in ya so sai ku haifi wata ɗiyar bayan ni."
"Nimra bana son wannan banzar maganar. Ina ce mahaifin ki ya ce ki ba shi lokaci zasu yi magana da Uncle ɗin na ki?"
Da sauri ta jijiga mata kai tace "Mum kar ku yi wa kan ku ƙarya mana. Kun sani Sageer ba zai taɓa jin maganar Uncle ba." Ta kawar da kanta gefe tana murmushin taƙaici.
Hajiya Zuwaira kuwa jikin ta yayi mugun sanyi. Ita fa tana son ɗiyarta kuma ba zata iya naɗe hannunta biyu ta tsaya tana kallo a rabata da ita ba. Dole ne yau ta kai wa Hajiya Mujiba ziyara.
Kan Nimra ta shafa tace "I promise you my girl, Sageer zai zama naki ko yana so ko yana ƙi."
Rungume ta tayi tace "Mum yanzu na ji batu,shi yasa nake son ki!."
*
Aka ce su ɗawisu masu ado. In dai maganar ado da kwalliya ake to in ka kalli wannan baiwar Allahn sai ka ƙara kallonta.
A cikin ƴan mintuna na ƙare mata kallo tsab. Na gama gano isa da mulki a tattare da ita. Sai cika take tana batsewa.
Hajiya Mujibat bafulatana ce ta asalin jihar adamawa. Tana da kyau daidai nata fara ce tas mai ɗan ja-ja haka. Gashin girar ta sirara ne kamar an zana mata su. Fuskar ta mai ɗan faɗi ,hancin ta ya tsaya ɗas a kan fuskarta.Bakin ta kuwa kalar ja ne kamar an shafa musu janbaki. Hakoranta farare ne tas in tayi dariya kana ganin haƙoran makanta sama da ƙasa masu kalar gold ɗin nan.
Wuyanta sanye yake da wasu ubansu yari da sarƙa na gwal masu ɗaukar ido. Wata dakakiyar shadda ce a jikinta kalar shuɗi mai haske kamar dai kalar sararin samaniya. An yi mata ɗinkin zamani irin na manyan mata masu aji , ta kafa ɗaurin ɗankwalinta irin na turai ƴar'aduwa. Hannayenta sun sha jan lalle da yayi kalar maroon hannu da ƙafa sai farar fatar ta suka haska,ga zobbuna nan a hannunta su ma na gwal guda uku a jere. Iya wannan ya nuna mana daraja da dukiya ta Hajiya Mujiba. Falonta da jikinta wani irin ƙamshi suke fitarwa mai sanyayya ruhi.
[9/9, 11:27 PM] Ummulhair S Panisau: RUFAFFEN DUMA.
Ummulkhair S Panisau.
(Khairatup)
Wattpad:khairi_Muhd.
Arewabooks:Khairatup01
pg07
Hajiya Mujiba ɗawisu kenan sarkin ado. Ba a banza kika sace zuciyata ba.
Haj.Mujibat ta saki wani irin murmushi cike da gadara da kuma iyayi. "Nawan ni kaɗai,barka da fitowa annurin zuciyata gabaɗaya."
Alh.Barau da ƙaton tumbinsa ya samu wuri ya zauna kusa da Mujibat. Hannunta ya kamo yana murzawa sannan yace "An ɗauki tsahon shekaru bamu zaga ƙasashe ba matata. Abubuwa da dama sun sha min kai na. In har ba samun kujerar nan nayi ba ,hankalina ba zai kwanta ba nutsuwata ma ba zata dawo ba."
Hannunta ita ma ta ɗora kan nasa ta lumshe masa ido tayi alamar tabbacin ya kwantar da hankalinsa.
"Alhaji ai bana jin wannan lamari. Ni na sani da yardar Allah sai ka yi sai kuma ka je. Duk maƙiyanka sai dai su zama fadawan ka. Ai ba yau aka fara dama siyasar da kai ba wannan kafirar ƙwawalwar taka ai bata harbawar banza."
Ya kuma sakin wata iriyar dariya sannan yace "Bayan ke babu wanda ya san halina Mujiba. Shi ya sa nake ƙaunar ki,bainu ba kya tsufa."
A hankali ta jefa masa tambayar da take son jefa mai a siyasance.
"Ɗazu Ayan ya bugo mini waya ,yace ya kira ka baka ɗaga ba.Kamar dai akwai abinda ya faru yake son kuyi magana."
"Ban ga kiran nasa ba kuma. Dake hankalina na kan yaron nan Muhammad."
Tuni yanayin fuskarta ya sauya ta gyara zama tana muskutawa kaɗan tace "Shi ma ina da magana a kan sa ai. Yanzu haka zaka zuba masa ido yayi ta yin yadda yake so? Shekarunsa fa sun kai matakina ajiye iyali. Kuma ka kyale shi yana zaune can wani gida daban a wata unguwar,ba ka ganin cewa akwai wani abun da yake aikatawa? Sannan hakan fa zai iya zama illa ga siyasar ka."
Ya fitas da wani irin numfashi ya gyara zama yace "Kin fa san waye Muhammad! Kin kuma san halinsa tsab. Na rasa yadda zan yi da shi kuma na kasa lanƙwasa shi yadda nake so."
"Wai shin ma meya haɗa ku ne?"
Shiru yayi tsawon wasu lokuta kafin ya kalle ta yana murza zoben hannunta yace "Hajiya wasu labaran ba a tono su,idan aka tono su za a samu gagarumar matsala. Ki bar maganar kawai."
"Alhaji ai na ɗauka ni da kai babu ƴar wannan a tsakanin mu?"
"Haka ne,amma wannan ba zan iya faɗarsa ba. Ina fata za ki yi min uzuri kamar yadda kike mini a baya?"
"Haka ne. Amma dai ka same shi ka yi masa maganar auren sa da Nimra. Hajiya ta kira ni ina ganin kamar ma zuwa zata yi ne muyi maganar."
Alj. Barau ya miƙe tsaye yace "Kai haba! Ku bari a bi shi a hankula ni dai kun san haifar sa nayi kawai amma ban isa na saka shi ko na hana shi ba."
Hajiya ta buɗe baki cike da mamakin abinda ya faɗa.
"Kar kiyi mamakin hakan don hakan ba ɓoyyyen abu ba ne a wurin ki. Sunana ma don bai isa ya sauya ba ne da zai iya da kuma an yarda to tabbas sunan uwarsa zai saka "Maryam!"
Ambatar sunan Maryam kaɗai da aka yi sai da taji kamar an kwaɗa mata guduma a tsakar ka.
Har ga Allah ta tsani sunan matar ma. Duk da bata same ta a gidan ba kuma bata san ya akai Barau ya rayu da ita ba. A yadda ta ji kawai an wayi gari da rasuwarta ta kwanta lafiya amma aka tashi da rashin ta. An kuma ce wai zuciyar ta ce ta buga a cewar likitoci. Sai dai bayan matuwarta aka samu rashin jituwa da rabuwar kai tsakanin Muhammad da shi da Barau ɗin.Da kan sa ya nemi kuɗinsa da faɗi tashi da yana ma ɗan zama a gidan shekarun baya kuma ya kwashe komai na sa ya bar gidan ko da leƙe baya zuwa gidan. Yaranta biyu da Barau ƴan biyu ne ma da Ayaan da Ayra suna can Cairo suna karatu....tafi yayi mata a kan fuskarta yace "Ina kuma kika tafi Hajiya?"
Ta yi yaƙe tace "Ina nan kawai ina tuna baya ne."
"To a tuna lafiya sai na dawo ina da meeting da jama'a."
"Wai yau ne dama campgain din na ku ko?"
"Yau ne mana."
"Ai na sha'afa. To a dawo lafiya Allah Ya bada sa'a."
"Amin."