Sashe 1
Rufaffen Duma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[9/9, 11:27 PM] Ummulhair S Panisau: RUFAFFAN DUMA.
Ummulkhair S Panisau.
(Khairatup)
1.
(Kukan jirgin ƙasa a wata tsohuwar tasha.)
Ruwan sama ake yi kamar da bakin ƙwarya hakan bai hana shi jin sautin kukan jirgin ba. Duk da kuwa ya sani wanann tsohuwar tasha ce da ta jima da daina moruwa.
A hankali yake nutsawa ciki, ruwan sama na dukan tsohon rufin tashar da ya ɗauki shekaru bai yi aiki ba. Bishiyun daji sun rure kewayen ofishin, ƙofar shiga ta karye, tagoginta ma duk sun y duhu sun farfashe daga ɓarayi ɗaya ko ta sama ko ta gefe. Ana yawan cewa duk wanda ya shiga wanann wuri baya fita ba a ma sake jin wani labarinsa ko da wasa ko a ji wani bayaninsa. A cewar wasu ma akwai fatalwa a ciki wadda ke duk daren duniya sai an ji sautin kukan ta ko takunta shi yasa mafi akasarin lokuta ma ba a fiya yin hanyar ba.
Ɗansanda ne mai ji da kan sa kuma mai gaskiya mara tsoro inspeta Samir Ibrahim Gadanya wanda aiki ya dawo da shi garin Kaduna daga Kano. An san shi ne saboda jajircewar shi kuma an shaide shi bai taɓa cin hanci ba. Hasalima rashin tsoronsa da rashin bin umarni ya saka aka sauya masa wuraren aikin akai-akai. Ko yanzu ma an turo shi nan ne don a ga bayansa a faƙaice amma ta sigar aiki. Ta yadda mutane ba zasu zargi komai ba.
Inspeto Samir Ibrahim bai taɓa yarda da wannan sharhin da ake ta yi akan tsohuwar tashar ba. Ya ɗauki hakan ne ma a matsayin tatsuniyoyi. Mutum ne shi kamili,mai nutsuwa, ya saba ganin laifuka da dama a rayuwarsa ya kama manya-manyan masu laifi kuma baya ragawa ko wanne ɗan siyasa muddin yana aikata laifuka na cin amanar ƙasa.
Fitilar hannunsa ya kuma riƙewa da kyau sake haska ko ina yake yi ko zai ga wani abu da zai taimaka masa wajen gudanar da bincikensa. A zuciyarsa kuwa ya sani cewa wannan binciken ba ƙaramin bincike ba ne ba. Yau ma ya fito ne bayan samun wani rahoto daga mutumin da bai san waye ba ya sanar masa da cewa "A kullum da misalin ƙarfe goma na dare,kullum sai ya ji kuka a kan dandamalin tashar jirgin....amma babu kowa a wurin."
A hankali ya ci gaba da takawa yana kutsawa ciki. Ƙafafuwansa na taka ƙasa mai cike da laka.Fitilar sa ta haska kujeru da suka ƙarye,da tsofaffun hotuna na talla da aka rufe da fararen ƙyalle. Idanuwansa basu sauka a ko ina ba sai a kan wani bango ,kusa da wajen da ake siyar da tikiti a lokacin da wurin yake amfani.
"BAN TABA BARIN WANNAN WURIN BA. NAN DIN GIDA NA NE."
Da ganin rubutun ka san da wani abu aka rubuta mai kaifi.
Duk da ya ji ɗar amma cike da ƙarfin hali ya matsa jikin bangon kalmomin ya kalla da kyau ya saka hannunasa ya shafa rubutun. A fili ya furta "Wannan sababin kalmomi ne kwanan nan aka goga su ba tsofaffin kalmoni ba ne" ba kamar sauran tarkacen da ya gani ba kama daga kan tsofafun kujeru,tagogi,hotuna." Bai gama wannan nazarin ba kuma sai ya ji sautin kuka a hankali ƙasa-ƙasa alhalin shi kaɗai ne a wurin. Daga nesa yake jin sautin kukan kamar iska na kaɗo masa shi , cikin sakanin da basu wuce biyu ba kuma sai ya ji kukan ya ƙaru fiye da na baya. Kamar kukan mace tana ambatar wani suna amma ya kasa ganewa. Da sauri Samir ya juya da baya yana haska fitilarsa da kyau amma bai ga kowa ba. Ya haska hagu,ya haska dama,sam bai ga ko gilmawar kowa ba amma yana jin sautin kukan na ƙaruwa can kuma ya koma jin dariya. Ya sani sarai raina masa hankali ake so ayi wannan shiri ne so ake ya yarda cewa fatalwa ce amma ya sani ba haka ba ne mutum ne kamar shi mai numfashi ba shi kaɗai ba ne a cikin wurin.
Ƙasa ya kalla yana haska fitila nan ya hango taɓo a ƙasa. Ga sahun ƙafa ,shatin irin na ƙaramar ƙafa kuma takalmin mace ,takun sabo ne ,saboda akwai laka. Sahun ƙafar ya dinga bi a hankali har ta kai shi zuwa jikin wata ƙofa da take a kulle. Amma abin mamaki ƙofar ƙyauren a karye take amma ga kwaɗo nan jikin ƙofar. Zuwa sannan zuciyarsa ta soma rawa duk da haka cike da jarumta ya matsa ya sa hannunsa ya ɗaga ƙofar wadda ta yi ƙara "krrrreee..." Wani ƙamshi mai haɗe da ƙamshin ƙasa da ƙura ya bugi hancinsa. Fitilar ya saka ya haska sai ya ga ɗakin mai duhu ne sosai. A tsakiyar ɗakin wani ɗan ƙaramin tsohon akwatin ƙarfe ne , saman akwatin kuwa a rufe yake da wani jan ƙyalle da alamu ƙyallen ma sabo ne ba tsoho ba saboda babu wani ƙura ko alamun tsufa a jiki bare yagewa da ya taɓa ma sai ya ji shi a jiƙe da alamun ruwa a jiki. "Kenan yanzu aka shigo da shi wannan wanne irin wuri ne haka wai?" Ya faɗa a fili yana tambayar kan sa da kan sa.
Sai a lokacin wannan kukan ya tsaya cak. Zuciyar Sameer ta tsaya na wucin gadi. Zuciyarsa na duka da sauri-sauri.
Daga sama yaji ance.
"Inspector Sameer Ibrahim....kana da jinkiri..An riga da an riga ka."
Zuciyar Sameer ta bada wani irin bugu "Dum." Tuni hannunsa ya soma rawa fitilar hannunsa ta soma rawa. Bai taɓa cin karo da irin wannan abin a a tsahon shekarunsa na aiki. "Gif"fitilar ta faɗi daga hannunsa a lokaci guda kuma yaji wani irin ihu tare da faɗowar abu daga sama.....
*
"Maryam Kabir"
"Yallabai."
"Yau babban kamu fa kika yi. Na yarda ƙwarewar ki da basirarki shi yasa na zaɓe ki nace ke zan aika kiyi wannan hirar."
"Na gode Yallabai. Amma wa muka samu?"
"Muhammad Sageer Barau."
Hannayenta biyu ta saka ta rufe bakinta tana jin kamar zata yi tsalle don murna. Kallon Yallaban tayi tace "Yallabai muhammadSageer fa kake nufi?"
"Ƙwarai ma kuwa ,shi yasa na ce miki babban kamu muka yi. Kuma yace mintuna goma sha biyar kacal ya bamu duk abinda muke so mu tambaye shi a wannan mintuan. Kin san lokacinsa mai tsada ne."
"Kai Yallabai gaskiya nayi farinciki da wannan batu. In sha Allah ba zamu baka kunya ba dukanin abinda ya dace zamu yi. Yaushe zamu je?"
"Da yamma. P.A ɗinsa yace zai dawo daga Dubai a yau kuma a yau zai kuma yin wata tafiyar amma zai gana damu kafin ya tafi. Kar ki manta only 15 minutes."
"An gama Yallabai. Bari na haɗa team ɗin da zamu tafi dasu."
"All the best."
"Miss Maryam naga yau sai walwala kike shin me kika samo ne?"
"Yau Global times tayi babban kamu Smith. Ka san kuwa da wa zan yi hira yau?"
Wanda ta kira da Smith ya daga kafaɗarsa alamar bai sani ba. "Gaya min."
"The grate Muhammad Sageer Barau can you imagine?"
Ya ƙara girman idanuwansa yace "Eh! That big business man? And ke Yallabai ya bawa wannan damar ina Shehnaz?"
"Yes! Ni ya bawa damar. Wannan lokacina ne ranata ce kuma Allah ni ya zaɓa. Shehnaz ai ta fi ni samun manyan ayyuka saboda ƙwarewarta da hazaƙarta. In aka ce komai manyanmu ne zasu na yi ai mu ba za a san mu a duniyar jarida."
Ya sa hannayensa biyu yana tafi sannan yace "Da kyau,i must say it kina da sa'a."
"Sauri zan yi only 15 min ya bamu. Zan tafi da team ɗina. Sai mun dawo."
"All the best." Ya faɗa.
*
"Sir."
"Uhm."
"Sir kana da ganawa da Global times tv a yau nan da rabin awa."
Ya ɗan juya ya kalle shi. Ya manta da wannan ganawar amma shi mutum ne mai mutunta alƙawari. Kai ya gyaɗa mai kawai ya gaya mai adireshin da zasu same su. Ba gida za shi ba don zai bi jirgi zuwa London.
*
Kaduna Continental Hotel.
Ta ƙaranta sunan Hotel ɗin, ta kasa ɓoye ainihin irin farincikin da take ciki. Ta jima tana son a bata babban aiki amma bata san cewa ranar zata zo mata da wuri haka ba. Duk da ba yau ta fara aikin ba amma ba a taɓa aikata irin wannan hirar da babban mutum kamar SD ba.
Babban ɗaki ne mai cike da salo da iko.Teburin mahogany mai sheƙi a tsakiya. Gilashin tagar ke nuna shimfiɗar garin Kaduna,da ƙamshin turare mai tsada ya cika ɗakin.
A tsaye yake ,yana jira,hannunsa cikin aljihun baƙaƙen suit ɗin jikinsa. Muhammad Sageer wanda aka fi kira da SD. Ba kawai ɗan kasuwa a Najeriya ba ne,shahararen ɗan kasuwa ne da duniya ta san da zaman sa. London,New york,Dubai da sauran manyan birane suka san shi cike da kishi da girmamawa.Tsayinsa ya cika filin ,kayan jikinsa sun ƙara masa kwarjini.
P.A ɗinsa ya buɗe ƙofar ya shigo ya sanar masa da isowar Maryam Kabiru.
A karo na biyu aka kuma buɗe ƙofar. Baƙar bafulatana da kyawunta mai sanyi ne. Maryam Kabiru ƴar jarida daga Global Times da aka turo ta don tayi hira da SD. A hankali ta shiga hannunta ɗauke da littffi da biro. Ita kaɗai ta samu izinin shiga sauran abokan aikin nata tuni aka dakatar da su a ƙasa. Baya buƙatar kowa sai iya ita kaɗai kuma ba zai yi magana a gaban tv ba sai dai ta rubutu su wallafa a shafinsu na jarida kawai.
Wani irin kwarjini yayi mata na gaske. Tafiyarta ma tuni ta sauya jikinta na rawa . Cikin ranta ta ce da kanta "Kama kan ki Maryam wannan aiki ne ba shirme ba. "Sai dai idanuwnta na haɗuwa da na sa sai ta tsaya cak komai ya juya mata. Duk hotunansa da ta saba gani a jaridu ba su kai zahirin gaskiyar da take gani a yanzu ba.
Ba tayi aune ba taji yace "Ke ce Miss Maryam Kabir?".
Da sauri ta gyaɗa kanta. "ok. Only 15 minutes already ma kin ci minti huɗu. Shall we?"
Tayi sauri ta girgiza masa kai.
Ya kalle ta yaga duk ta rikice. Hannu ya saka ya ɗauko gilashin ruwa ya miƙa mata "Ƙarɓi ki sha. Calm down."