← Book details Nana Khadija Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 24

Sashe 9

Nana Khadija Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Cikin marai raicewa yace Ummina kinga haka zan fita gurin Aiki banci komai ba gashi na makara Dana karaso na Karya an an ya karashe maganar cikin shagwaba"

"Ummin tace duk kai ne mai laifi ai kace kai baza kaci abincin kowaba sai ka za6a yanxu me kakaso ai maka?

"Gyaran muryayi kadan yayin da yake kulle kofar dakinsa ya shirya staf sai tafiya cikin ransa yace yawwa

"A fili kuwa cewa yayi kisa ai min Abinci malam Haruna ya kawomin ofis Dan Allah kanji Ummina

Ca zakayi nayi maka abinci kwai abincin waka keci ko na Asabe mai aiki bakaci yadda take dai da tsafta ta iya girki maidadi da gamsarwa kama data namu na gida har na wajanma duk ta iya kalar Wanda kakeso

"Umum Ummina yafada kamar wani karamin yaro yace kisa dai daya daga cikin "yan matanki suyi min nafi yadda dasu. Yafada yana kokarin tada Mota"

"Ummin tace yau kuma yaran dakake kiran kazamai ne su zasuyi maka abinci kaci?

Yana dariya kadan yace Eh Ummi ai Dane yanzu naga sunayin tsabta kadan

Daga can 6angaran dariya Ummi din tasa kadan tace "hadair kenan manya to zansa wancan marakunyar yarinyar tayi maka badan halinka ba domin dai duk tafi su saurann "yan Uwannata kwarewa tana Nufin 'D'ija Kenyan

"Shima Ali ya fahimci D'ijan take nufi din dama haka yakeso yace ywwa Ummina godiya make

Murmushi Ummi din tayi kdan tana masa Addu'a sannan takashe wayar cikin so da kaunar danta

"Shima Aje wayar yayi gefe fuskarsa dauke da murmushi yace Ummi kenan dama nima haka nake so ai
Yacigaba da yin serving dinsa cikin kwanciyar hankali har ya isa gurin Aiki

*MRS AHAMAD GWADABE*👌🏻👌🏻
*NANA KHADIJA*
💜💜💜💜💜💜
💛💛💛💛💛💛

*STORY WRITTEN*
*BY*
*BINTA UMAR MM*
*ABDUL WAHABU*

*page*
*142*

"Dakinsu Ummi ta karasa dake safiya ce basu fito ba tace INA 'Dija Fa'iza tace tana toilet yanzu ta shiga tafada bayan ta gai da Ummi din tace in ta fito kice tashiga khicin tayi wa yayanku Abinci mai kyau yanzu malam Haruna ya kai masa"

"Abin mamaki yabawa Na'ima dake kwance kangado cikin bar go jin cewa wai D'ija tayiwa yaya Ali Abinci yaci ita dai iya saninta ko ruwa ne suka kawo masa baya Sha balle har ta kai ga yaci girkinsu

Bude ido tayi tana gaida Ummin Ummin tace au da idonki biyu Ashe gyara kwanciya tayi tace e Ummi baccin baizo tukkuna da gaske yaya Ali ne zai ci girkin D'ija kuma shiyasa tayi masa Ummi ?

Ummin natafiya tace aA nice nasata tayi masa bashi ba daga haka Ummin batakara cewa komai ba tafice daga dakin

"Duk Dija na jinsu sai da tatabbatar Ummin tafita sannan ta fito domin har yanzu Ummin bata sakar mata fuska ba

Tana fitowa Fa'iza take gayamata shiru tayi bata CE komai ba tana kokarin Neman guri ta kwanta

"Na'ima tace bakiji Abinda akace bane D'ija kiyi kokari kiyi Abinda ya dace tunda Ummin ke takeso kiyi dadin Abinma ai kin kware kanwata kar kikaraya mana tafada tana dariya

Ita ma D'ija dariyar tasa kawai Fa'iza tace qila yaci na jiyane da kikayi masa yayi masa dadi shine yanzu yakeso Na'IMA tace au jiya a'ina tayi masa girkin? A gidansq inji Fa'iza gyara kwanciya Na'ima tayi tace yanzu naji zance ya fito sai kitashi ai Aiki ya sameki"

"Mikewa D'ija tayi tana kallon Na'ima tace to ya Na'ima Dan Allah me zan dafa masa? Wallahi bansani ba kije dai kiyi masa Abinci mai kyau Na'ima n tafada"

"Ta6e baki Dijan tayi tafice daga dakin a ranta tace lallai ma wannan mutumin daba Ummi CE take masa Abincin ba sai yanxu rana tsaka yazo yace wani inyi masa Abinci da sanyin safiyar nan tafada lokacin data ke shiga kcin din

Asabe da Ummi ne A tsaye sun kammala Aikin kayan kalaci Asabae na faman gyarq guri yayin da Ummi take har hada kayan kalacin domin Asabe taji dadin fita dasu

"Tace Ummi mai zan dafa masa to? Wani kallo Ummin tayi mata tana kokarin fita daga kcin din tace kiyi masa duk Abinda ranki ya raya miki tafice daga kcin din

Asabe mai aki tace Uwar dakina girki za,ayi ne?

Eh wallahi D'ijan tafada bay an ta gaida Asaben tana karasawa kichin din sosai tace yaya Ali zanwa girki

"Lailai barbar magana inji Asabe n tace to kifara da yimasa Abu mai ruwa Wanda zai duma ma cikinsa Kafin Abincin tunda safiya CE yanzu Asaben tafada

'E D'ijan tace dama Abinda nake tunani kenan
Hakan yayi cewar Asabe kana tafita daga kcin din tabar D'ija a ciki tana nazarin me zatayi

*lafiyyan kunun gyada ta shirya masa Wanda yaji kayan kamshi sosai ta zuba a fulas mai kyau
Sannan tafara shirya miyyar Agushi wacce taji kayan miyi da waddataccan Naman rago da gyada batayi Amfani da Allayyahu ba sai miyar tayi kamar dage dage kamshi sai tashi yake

Gefe guda kuma ta kwa6a filawa finkaso take so tayi masa Kafin ta kammala hada miyar har ya tashi sabida haka Aikinshi tafara yi cikin nutsuwa

"Data kammala. Sai tayi tunanin yi masa farfesun kifi sabida haka cikin sauri taje ta Ciro kifi manya cikin frji tafara aikin cikin nutsuwa

"Sai da ta kammala komai tahada kayan Abincin cikin wani kwando mai kyau tsab sannan tafice daga kcin din

Duk suna zaune har Abbah Ana karyawa kamar ko da yaushe tazo zata shige tatsaya tana gaida Abban

"Abban yace yanzu nake tambayarki Uwata sai Umminku tace kina kchin yafada bayan ya Amsa gaisuwar datayi masa

Dariya tayi kadan tace e Abbah ai na kammala ma zanshi ga inyi Wanka sai in fito in karya Abbahn yace yayi kyau Uwata Allah yayi miki Albarka

Ameen tace sannan ta mayar da idonta kan Ummi tace Ummi nagama sannuki Ummin tace ko kalon D'ijan bata yiba taci gaba da cin Abincinta

Itama Dijan bata karacewa wani Abu ba tashige bedroom dinsu yanzu in da sabo tasaba da wannan halin ko in kula din da Ummi din take mata

"To 6angaran Siyama kam gari na wayewa bata jira kmai ba tayiwa Ummi waya cewar tanajira meye labiri ne?

Shine dalilin dayasa Ummi tayiwa Ali maganar

Ummin tace takwantar da hankalinta yace ya mayar da ita SBD haka ita kanta zatazo ta mayar da ita

Wani ihu tasa Wanda yatashi Rukyy daga baccin datake tana tsaki tace meye haka kin tashi mutane daga bacci

Nan Siyaman take gaya mata yadda a kayi

Gyara kwanciya tayi tace ba malam damayafada miki cewar baza'a kwanaba zakij zancan komanki ba

Kwarai kuwa haka yace inji Siyaman tace lailai malamin nan karshene Ayyada baudaddan mutuminnan ya rikice wallahi na dauka ya gama zama dani

Hannu Rukyyn tabata suka tafa tace shi din banza sai dai in ba'asa shi a Alon karfe ba

Sheqewa da dariya sukayi cikin farinciki

*Allah yasa mufi karfin zuciyoyinmu*

*MRS AHAMAD GWADABE*👌🏻👌🏻👌🏻
*NANA KHADIJA*
💜💜💜💜💜💜
💛💛💛💛💛💛

*STORY WRITTEN*
*BY*
*BINTA UMAR MM*
*ABDUL. WAHABU*

*page*
*143*

"To sai da malam Haruna ya kai Abbah offece sannan da ya dawu Ummi tabashi Abinci Ali ya tafi kaiwa bai Sha wata wahalaba maso tsaron gurin suka barshi ya shiga kasancewar sun sanshi lokaci zuwa lokaci yana zuwa wani'sa'in

"Wani Soja ne ya kar6i kwandon Abinci yacewa malam Haruna ya tafi kawai za'amika domin Oga Aiki yake A ciki shida baki ne A ciki

"Godiya malam Haruna yayi ya kama hanya yatafi. Abinsa kimanin Awa guda tukkuna bakin suka fito daga offece din Ali n sannan yashiga shi kuma hannusa rike da kwandon Abincin

Yana shiga ya hau kamewa tare da aje kwqndon gefe yana gaida Ali irin gaisuwarsu kana yace Oga kimanin Awa guda kenan da malam Haruna yazo yakawo wannan kayan

Kallon kwandon Ali yayi ya maida hankalinshi kan wata takkada dake hannusa yana dubawa yace OK Ajiye katafi To yace ya'aje Kafin yafita ma sai da yayi wannan gaisuwar sannan

Sai da yagama duba Abinda ke hannusa cikin nutsuwa sannan ya aje gefe domin wata irin yunwa CE take damunsa kasancewar yakwana biyu bai tsaya yaci Abinci yadda ya kamata ba

"Wayarshi ya dauka yana laluben no din Faruk bugu daya kuwa tashiga daga can 6angaran Faruk din yace yaya Akai ne mutumina?

Ali yace kafito muci Abinci gashi malam Haruna ya kawo faruk din yace ni A koshe nake fa wallahi

"Tsaki Ali yayi kadan yace malam in zakafito kazo Dan Allah INA jiranka yanzu ya kashewarsa Dan ma kar Faruk din yakara wata magana

"Shima Faruk din Aiki ne a gabanshi Amma sannin halin Alin ya mike domin yaje yaga wane irin girki ne da Alin hake wani masifa a kanshi
Domin dai shi kam A koshe yake Nafisa shi ta cika masa ciki

Tuni ya sauko daga kan kujerar da 'ike kai yana can kan wata shirgegiyar Sofa dake girke A Offece din gabanta wani wawakeken teble ne gefe kuwa wani qaramin friji ne cike da Ababedan Sha"

"A zaune anan Faruk din ya sameshi yana danne da danne A wayarsa

"Gani Faruk din yace kataso INA Aiki sai kace wani Ubana murmurshi Ali yasa kadan yace cika maka cikinka zanyi kafi jin dadin yin Aikin

Wai wane irin Abince ne wannan Faruk din yafada Yace nima bansani ba gadai kayan Abincin can dauko mana

Daukowa Faruk din yayi yana mamakin Ali wai zai aika sai da yazo tukkuna yace wallahi kara rai nani ni za,ka Aka ko Dan rainin hankali kawai kasan dai gaba nake dakai koba haka yarana biyu Ana shirin yimin ta Uku yafada yana zama gefen Alin yana kokarin fito da Abincin gami da bubbudewa
💛💜💜💜💛💛💛💜💜💛💛💛

Gyara Zama Alin yayi Sosai Fuska babu yabo babu Fallasa yace Au yau gorine ya tashi kenan

E Faruk din yace hankalinshi na kan Funkason da yabude su6usu6u dashi gashi sai kamshi yake da sauri ya bude miyar jin har miyanshi ya tsinke shi da yace a koshe yake wani irin kamshin dadi ne ya budi yancinsu shi da Alin tun kafin su sanya Abincin Abakinsu

Saurin kau da kai Ali yayi domin bayaso ya nuna zulamarshi daga baya in Faruk yasan girkin D'ija ne yasamu Abin fada da tsokana
Chapter 9 · 0% Book details