← Book details Nana Khadija Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 24

Sashe 15

Nana Khadija Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wani Numfashi ya dinga Saukewa mai dauke da tsantsan bacin rai yace wato yarinyar nan Abinda zatayi min kenan sai yaji duk masifaffiyar yunwar da ike ji ta kau wani daci yake ji a cikin bakinsa lailai ranta sai ya baci wallahi tunani yake kar shenta ma su malam Haruna da Sauransu sungama ganinta a haka lailai *D'ija ta cuceshi*

"Ummi kawai zuba masa Ido tayi tana so ta hasasu Wani Abu cikin kwayar idonsa amma ta kasa" lailai A kwai wani Abu a lullube

"Kanta a qasa ta karaso hannuta dauke da katon faranti ta aje gabansa tana kokarin zuba masa Abincin A sunkuye'

*innalilhi* kawai D'ija take Ambata ganin duk mamanta sun fito sakamakon sunkuyen datayi a gabansa kamar zasu fito daga cikin rigar"gashi babu breziya dama Hannu tasa ta dafe gaban rigar kana tayi zaman dirshan a gabansa A haka take zuba masa Abimcin da hannu daya "Ranta a mutukar bace

"Shiko kallonta yake da ido jazir yana faman tafka Mata harara ganin wai boye wa take kar yagani batasan tun shigowarta falon A karon Farko ya kare musu kallo ba ballanta sanda ta sunkuya babu Abinda bai gani ba ko shi zai'iya fada mata numbar breziyarta karewa ma

"Mtssss Dallah gafara daga gurin Wallahi tallahi duk Sanda na kara ganinki da wannan kayan saina illa ta ki saina fasa Abinda kike Nunawa a gani "yar iska kawai mara Hankali Duk A cikin Masifa yake fadin haka dama shi in ransa ya baci ba'iyaba dan ma taci sa'a bai kai mata duka ba Dan A kan matakin Ake in tayi wasa

"Kuka D'ija tafashe dashi Sosai tace Wallahi ni ba"yar iska bace mai nai maka dazaka kirana da sunan da na tsana Allah ya shigemin gaba Allah ya sakamin D'ijan tafada tana kokarin tashi a gurin cikin kuka"gashi haryanzu bata jin dadin jikinta daurewa kawai take ganin babu Wanda zata fadama taji dadi a ranta

"Mai da'ita yayi ya zaunar a zafafe yace waye Dan isaka to? Shiru babu Amsa ba dake nake ba Rashin kunya zakiyi min Dan Ammiki fadan gaskiya ko bazata!! taji saukar mari a fuskarta a fusace yace bani Amsa mana ?

"Shiru babu Amsa kanta A qasa tana shesheka kuka gashi haryanzu bai saki Dan tsanta da ya riqe ba

Ganin yana kokarin kara kaimata wani dukan ne yasa Ummi tasowa gami da kwace D'ijan A hannusa tace Allah yara baka da wannan zafin zuciyar Ali dama tunda ka shigo gidannan na fuskanci a kwai Abinda ke damunka zakazo ka sauke a kanta INA dalili nifa banason Neman fitina"

Da sauri D'ija tamike ta bar gurin cikin gursheqen kuka A fili tace wallahi nagaama xama a gidanan yau din nan a gaban Nene zankwana wannan masifa har INA da gudu tashige bedroom dinsu

"Shiko Ali A Fusace ya fice daga Falon yaje ya Bude mota ya zauna gami da kunna *Sigari* yana zuqa cikin bacin rai!!!

😊

*MUJE ZUWA*
💋

*MRS AHAMAD GWADABE*👌🏻👌🏻👌🏻
*NANA KHADIJA*
💜💜💜💜💜💜
💛💛💛💛💛💛

*STORY WRITTEN*
*BY*
*BINTA UMAR MM*
*ABDUL WAHABU*

*Pege*
*151*

Ka yan ta Hau zubawa cikin jaka tana kuka wani irin bacin rai take ji cikin zuciyarta Shi yayi mata Ummi tayi mata ina dalilin wannan masifa gwara kawai tabar musu gidansu

"Hijab ta zira bayan tasaka Atamfa Riga da zani ta ja jakar kayan tafito

"Babu kowa A falon Ummi ma tatashi tana kchin Dan haka waje kawai tayi ita a nufinta tasa malam haruna ya kaita

"Ali na zaune cikin mota yaga fitowarta tana Jan jaka fuska a hade ta wani Sha kunnu tana laluben inda malam Haruna yake

Fitowa yayi daga Cikin motar Hannusa riqe da karan *Sigari* ya durfafi inda take ransa A 6ace!!

"Gyara tsayuwa tayi tana jiran karasowarsa gurin idonta A kansa kamar yadda yasa mata nasa idon cikin zuciyarta tace duk Abinda kake ji dashi ina ji dashi dai dai nake dakai

"Riqe jakar yayi yace Ina zaki ?

"Dauke kanta tayi tana hura hanci hade da girgiza jiki

Dariya tabashi Amma sai ya share kawai bai yi ba

Yace batambayarki nake ba

"Nan ma Babu Amsa kan ta nacan na kallon wani gefen fuska a hade

Jakar kayan yake kokarin fizgewa gefe guda kuma yana zukar *Sigarinsa* yau babu 6oyewa ma A fili yake Sha sai hura mata hayaqin yake"
*lailai yau Ali A Shataransa yake*😃

"Riqe jakar tayi tamau yana ja tana ja "

"Toshe Hanci tayi jin warin *Sigarin* yana hautsina mata "ya"yan hanji rai A 6ace tace Dallah malam Sakar min jaka ina ruwanka da inda zanje me ya shafeka zan tafi inda nafi wayo ne in bar muku gidanku iheee!

Ta karashe maganar cikin tsiwa!
💜💜💜💜💜
💛💛💛💛💛

"Ni ne Dallah malam Alin yafada yana mamakin Rashin kunyarta

*Ni kam nace ka manta ne Dan dai kura tayi lafiya ne yanzu*

"Wani kallo take watsa masa taja Tsaki gami da dauke kanta tace wallahi yau babu Wanda ya isa ya hanani tafiya gurin Nene ihee!!

"To Anji Alin yace gami da Dan Sausauta Fuska Wuce ki koma gida yanzu magariba tayi zakiyi tafiyar dare ki bari gobe sai kitafi kinji ko"

"Mtsss taja tsaki gami da cewa wallahi bazan karya rantsuwata ba yau din nan zan bar gidanan zantafi inda nake da gado tunda Ubana ma yana dashi"

"Rai A mutukar 6ace yace wallahi kika sake kika kara yimin tsaki sai na fasa miki baki sosai har sai yayi jini kin san zan'iya ko

"Dan kinga Ana rarrashinki ni sa'anki ne da zaki dinga gayan magana kokuwa muma Ai bama nai manki kifi Ruwa gudu Ance bazaki tafi yau ba sai gobe sai muga yadda zakiyi Shashasha kawai"

"Fashewa da Kuka tayi A fusace ta Sakar masa jaka ta ruga da gudu tayi can han get tana kokarin Bude karamar kofa da niyar fita Cikin gursheqen kuka kamar wacce a yanka!

Da Sauri Ali yabi bayanta Yana kira Allah yasa baba mai gadi yana can waje kan banci sauran masu Aikin gidan kuma basa gurin

Dake sakatar kofar tana da tauri takasa budewa sai kici kici take takasa Anan ya Cimmata Ransa A bace ya hade ta da kofar ya tare da gangar jikinsa Suna jin bugun zuciyar juna

"Yana Sane yayi mata haka Sabida yasan jikinta zai mutu

Ai ko Jikinta lakwas yayi Sai faman kifkifta ido take tana turo baki gaba

Murya kasa kasa yace kinfasa guduwa ne mara kunya A she kina da wani gurin bayanan ko ? ba musani ba "

"Wallahi tallahi kinji rantsuwar Dan musulmi in kika sake raina ya 6aci bazaki je gurin Nene ba ma kwata kwata

"Kinsan zan 'iya hanawa kuma sabowar wayar ma nafasa bayarwa tunda ke baza'ayi miki fada nabawa Fa'iza ta hada biyu"

"Ni ka gafara ka matseni jikina ciwo yake zaka qaramin wani ciwon jiki Ai Abbah zai dawo Shine mai iko dani da kai nasan zai mayar dani gurin Nene"

"Tafada tana haki sai kace wacce tayi gudun fanfalaki''

"Cikin qasa da Murya yace Wallahi Nima bani da lafiya *Khadijatu* narasa meke damuna yafada baya ko tsoron wani ya fito ya gansu A haka!

"Satar kallonsa tayi kadan tana kokarin sunkuyawa ta qasanshi ta wuce tace kowa ma kayiwa Sannu a wannan zamanin Amsawa zaiyi *Allah yasawaqe*
💜💜💜💜💜
💛💛💛💛💛

"Qyaleta yayi ta wuce ta kasanshi Amma ya Riqe hannuta Sai da yabari tukkuna ya Saisaita kansa sannan ya jiyo yana lalaben glass dinsa cikin Aljihu Ayya yana cikin motarsa Ashe Kin kallonta yayi Dan karta ga halin da yake Ciki

"Har yanzu Fuskarsa babu walwala yace wuce ki koma cikin gida magana ta wuce zan shigo in baki wayarki yanzu

"Gyara Tsayuwa tayi tace Nifa yau din nan zan tafi ko ka ban waya ko baka ban ba"

Lailai ma Yaushe yarinyar nan ta gama rainashi haka yake fada cikin ransa

Sabida haka wata irin tsawa yayi mata wacce tasa sauran kadan Fitsari ya kufce mata

"Yace wuce daga Gurinan Dan Uwarki kin gama Rai nani ko zan zane miki jikinki Dan kinga ina kulaki ne

"Da Sauri ta bar gurin tana hararasa Cikin Ranta tace dubeshi Dan Allah babban kwabo Kaga ma zubar da girman Ai na kwashe
*lol Ali😃*

Jin Karan Motar Abbah yasa ta dakata bata shiga Ciki n gidan ba

"Baba mai gadi ne ya bude masa Get Sannan Haruna ya shigo ciki gami dayin parking

"Da Sauri Ali ya karasa ya budewa Abba motar ya fito yana masa barka da zuwa

"Amsawa Abbah yayi hannuwansu cikin na juna a haka suka jera zuwa Cikin gidan

"Malam Haruna na biye dasu A baya riqe da jakar Abba ta Aiki da Sauran kayayyakinsa

"D'ija na tsaye har suka karasu gurin Abbah yace Uwata yaya Akai ne ? Naganki riqe da jaka A hannu"

"Fashewa da Kuka D'ija tayi tace Sannu da Zuwa Abbah Andawo lafiya"?

"Lafiya kalau Uwata Abban yafada yana mamakin me Akai mata haka take wannan kukan

"Shiko Ali Ciki ya shige ya rabu dasu A nan domin yariga yagama sanin Halin D'ija zata iya yin Abinda yafi haka ma

"Abba yace me Akai miki ne Ali ne ko?

"Girgiza kai tayi tace A'a Abbah ina so ne naje gurin Nene Shine ya hanani tafiya

"Assha Assha haba Uwata Kinaso kije gurin Nene ba sai kifada munba sai in kaiki ko insa A kaiki wato da kina nufin da kanki zaki tafi kin ta6a ganin kin je ke kadai?

"Girgiza kai tayi yace to ki kwantar da Hankalinki zamuje in Sha Allah jibi zamu tafi zamuyi sati biyu hakan yayi miki ko?

"Daga kai D'ijan tayi Dan babu yadda zatayi ne kawai tana dariya tace Allah ya kaimu lafiya Abbah

"Yace Yawwa Uwata wuce muje ciki"

"Tana gaba yana Binta A baya haka suka shiga Falon,

*Mutara A gaba*

💋

*MRS AHAMAD GWADABE*👌🏻👌🏻👌🏻
*NANA KHADIJA*
💜💜💜💜💜💜
💛💛💛💛💛💛

*STORY WRITTEN*
*BY*
*BINTA UMAR MM*
*ABDUL WAHABU*

*page*
*152*

kai tsaye bedroom dinsu tashige ganin wani irin kallo da Ummi ta ke yi mata

"Abbah yace kina ina har D'ija tafita da jakar kaya wai zata tafi gurin Nene'
Chapter 15 · 0% Book details