Sashe 19
Nana Khadija Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Faruk ko Shida Na'imansa zubah soyyaya suke A waya kamar babu gobe
Yana sane yaqi Sanar da Ali zancan ganin irin Rashin mutumchin da yake masa har da zai tafi bai masa bamagana ba sai shafawa yayi yaga bayanan wannan Abu ya batawa Faruk rai mutuka Shiyasa shima yaqi kiransa a waya ya qyaleshi yaga iya gudun ruwansa
Dr Hashim ya Amince da maganar da mahaifinsa yazo masa da ita nacewar ya hakora da D'ija Anyi mata Miji in yana son Fa'iza Alh Bashir din ya bashi ita ma
Ya dade kansa a kasa domin bai so haka ba Dan yana bala'in son D'ija da gaske Amma tunda haka ta kasance zai kar6i Fa'izan bai San Abinda Allah ya hukunta
Kalar Fa'izan ya dinga tunanowa Wani Farinciki ne ya ratsa zuciyarsa domin yana son mace mai sanyin Hali gami da kunya in zai'iya tunawa ko gidan sukaje gurin Ali daga gaisuwa babu Abinda yake kara hadasu duk tsokanar ko da zai mata kanta a kasa sai dai tai murmushi ko tatashi tabar gurin
Wani Farinciki ne ya dinga ratsashi Dan haka mikewa yayi yayiwa mahaifinnasa sallma ya fita
"Yana Fita yayiwa Faruk Waya Suka dinga tattauna maganar da yadda Allah ya juwa Al'amarinsa
"Dr yace Dazu da Safe zan fita Aiki Ai naga Motar Mutuminnaka Sai Hon nake Masa ya qyale ni nasan yasan Nine tunda yagane Mota ta Har A Har danja ta tsayar da mu a titi INA Masa Magana yaqi kulawa Sai cin Magani yake
"Dariya Faruk yasa yace rabu dashi Nima ya dai na kulani yace Wai nine na daure ma gindi har kake shiga gonar da ba taka ba
Ai can Kano gurin Nene yatafi kasan duk family NASA suna can
"Shima Dr din dariya yasa yace rigima kenan na bar masa gonarsa Ai Allah yasa haka shifi Alkairi
Ameen Ameen Faruk yace kana sukayi Sallama kowa yakashe Wayarsa Cikin Walwala da Farin Ciki
💜💜💜💜💜
💛💛💛💛💛
Yana Zaune gaban Nene sai ina a saka ina a ka je take dashi an kawo masa kayyayaki an jere a gabansa sai wani lallabashi take yaci
Shi kuma Sai Wani dacin Rai yake yana latsa waya yayi kicin kicin da Fuska Maganar ma Sama Sama yake Amsawa
"Nene tace Wai ni ko baka da Lafiya ne naga duk kasanja min maigidana tafada tana Washe baki domin lallabashi take tana jin tsoro kar tazo masa da maganar dake A kwai yasakata A kwana tasan halin "yan kayanta
"Lafiya ta lau yafada idonshi kan Waya yana ya mutse Fuska ya kalli jerin kayyayakin Abin dake gabansa daya bayan daya kana ya dauke kai
"Yace Samin Wancan shi zanci yafada yana Nuna Fulas din bura busko Wanda yaji kayan hadi da Uban kifi hade da kayan lambu sai qamshi yake
Jiki na rawa Nene ta hau zubawa tana dariyar babu gaira babu dalili tace Dan Nema nasan dama shi zakace zakaci kai duk wani kyalekyalen Abinci baya burgeka
"A hankali yace in banda Abinki ina zan kai waddannan kayan Abincin da kika Aje min sai kace Wani Mai cikin zani"
"A'a wai ko zakayi sha'awa ne yasa nayi maka kasan kai na Mussaman ne Nene tafada tana tura masa plate din Abinci gabansa ta sanya masa cokali a ciki har lemo sai da Nene ta 'ajiye masa da su ruwa duk A Cikin kamfen ne😃
*Lol NENE*
Jin tace Wai shi na mussaman ne yasa shi sakin Murmushi yana gyara zama yace Abaki kike fada cewa ni na mussamanne dan kinga babu wancan yarinyar A kusa dake shiyasa data nanan Ai zaku hadu ne kuyita yi min Wulakanci San ranku"
"Habadai Wace D'ija kuma Ai kaine Shugaba a ko INA ita ma D'ijan bayanka take bi Ai naji dadi dakuka daina fada da ita Fa'iza take cemin har Abinci take dafa maka ko?
"Dan Allah ka dinga tausaya mata kaga marainiya CE ita takarashe maganar cikin kwantar da kai"
"Dariya yake kadan yana cin Abinchi sai yaji duk wani 6acin ran da ike dauke dashi yana raguwa domin dai yana jin dadin Rarrashin da Nene take masa
"Yace kowa ma maraya ne Ai Tace dake nayi mata Wani Abin ne ni meye ruwana da 'ita kowa sabgarsa yakeyi ki tambayeta kiji?
Da Sauri Nene tace A,a batace kayi mata komai ba Nice dai nafada"
Kafin ta rufe baki Ummi ta shigo dakin ido hudu sukayi da Ali yana zaune yana cin Abinci
"Tace A'a kai kuma yaushe kazo"??
*MRS AHAMAD GWADABE*👌🏻👌🏻👌🏻
*NANA KHADIJA*
💜💜💜💜💜💜
💛💛💛💛💛💛
*STORY WRITTEN*
*BY*
*BINTA UMAR MM*
*ABDUL WAHABU*
*page*
*157*
"Yace ban jima da shigowa ba Ummi nasameku lafiya"?
"Lafiya lau Ummin tafada tana zama cikin kujera tace ina Siyama na dauka Ai tare zaku tawo"?
"A,a Ummi tana gida batajin dadi ma Ai"
"Ai kam Nima yanzu nake tambayarsa ita Allah dai yasa Laulayi take naji kace bata da Lafiya Nene tafada tana washe baki"
"Tabe baki Ali yayi yana Cin Abinchi yace Eto bandai Sani ba"
Kamar yaya baka Sani ba cewar Ummi
Nan da Nan ya gyara maganar ganin Ummi har ta fusata
"Yace nabarta zata tafi Hospital da zan fito naso in kaita a dubata sai tace zataje Momy'n ta suje tare"
"To Allah yabata Lafiya Ummi n tace"
"Nene tace Allah dai yasa Ciki ne da ita"
Bai ce komai ba yacigaba da cin Abincin shi cikin kwanciyar hankali yana tunanin maganar Ummi wai ya tawo da Siyama Lailai kam Ai tun A mota zata karasa shi da warinta
Amma yaci Alwashin dole zai zaunar da ita ya tambayeta meye dalilin Wannan warin da take domin hakkinta dake Wuyanshi
Ummi da Nene ko hira suke cikin sakewa har delu ta shigo itama ta zauna a nayi da ita dake macace mai wasa da dariya nan taita jan Ali Wasa Yana Amsawa kadan Nene tace kayi kya gama indai wannan Muskilinne sai faman Hira kike masa sai kace wata tsohowar redio yana shareki Ummmm!! tafada gami da gyara zama
Dariya Ali yasa yace to ke ina ruwanki Har kin fara kishi kenan Ganin tana kula dani daga yau ma ita CE Uwar gida na sanja
Goro ta 6antara tana taunawa tace naji Kuje ina nan a zaune zanganku A rana
Dariya delu da Ummi suke ma Ali da Nene Yace Ummi ina Abbah ne da jamil?
"Nene tayi Sauri tace zama zasuyi jiranka Suna can suna gaisawa da "yan Uwa to kaji!!!
"Yace Nima zani ai sai dare tukkuna tace Sabida rashin son jama'a zakace sai dare sabida kar a ganka ko
"Yace babu ruwanki ki kyaleni haka don Allah"
"Dariya Delu take tace Ango da Amarya Ana fada Wai ina daya Amaryar take ne banji motsinta ba
Tana nufin *D'ija*
Qifta Mata ido Nene tayi Alamar tayi Shiro da Maganar dake Delu tasan komai Nene bata boye Mata Magana
💜💜💜💜💜
💛💛💛💛💛
"Nene tace Suna Can gidan indo kin San kawar D'ija ce tun a kuruciya jin nace mata yaranta Uku yanzu shine suka tafi gulma duk da ba a kauye muke ba ita ma inda a gabana take da tuni na Aurar da ita cewar Nene"
"Delu tace kwarai kuwa Ai D'ija a kwai San girma da kamar bazata girmaba Amma yanzu dubi yadda tazama babbar mace"
"Nene tabude baki zatai Magana su D'ija suka shigo Cikin Sallama
"Delu tace "yayan Halak yanzu muke zancanku a she kuna hanya"
"Iya Delu yaushe kika Shigo Cewar D'ija tana kokarin Tsallaketa tashiga dakin Sosai tace har muka tafi ina Cigiyar yau baki shigo da Wuri ba Kin bamu labarin Abinda dariya ko Fa'iza? Tafada tana dariya
"Fa'iza ko ta shiga taitayinta ganin Wanda ke zaune a dakin Nene cikin Nutsuwa tace Aikowa iya Delu INA kwana Allah yasa yau kinzo mana da labarai masu dadi
"Dariya D'ija keyi taji ta taka Kafar Mutum Taushi da Sanyi taji a tafin kafarta da Sauri ta kalli gurin jin tana kokarin Faduwa
Yana zaune ya gama Cin Abinchin kansa a kasa Sabida baya da D'ijan tabashi bazai iya kallonta ba A sabili da irin dinki dake jikinta Atampah CE a kai wai Riga da siket dinki yadan dameta ba sosai ba hakane ma yasa tayi Amfani da babban mayafi to mayafin mai shara shara ne a na ganin komai
Cikin Ransa yace Wai ita Wannan wace macece ne mara ji kowane kaya tasa sai sunfito mata da kiraaa jiki
Wato bata daina Amfani da mayafi ba kenan hijaban sun tashi a banza lailai zai bata Mamaki
Da Sauri ta Matsa ganin Wanda ta takawa qafa tana dan ya Mutse Fuska gefe guda kuma tana laluben inda ta cilar da Mayafin tun Shigowarta daki n sabida ita kanta tasan din dinkin jikinta ya Matseta yana can kan kyauran dakin A nan ta ratayeshi taje ta dauka ta lulluba tana wani Cin Magani
Dariya yake cikin Ransa Lailai yarinyar nan shi take rufewa jiki Dan iska ta Mai dashi ko me
"Fa'iza tace yaya Ali Sannu da zuwa ya Hanya?
"Alhmdullh Fa'iza na nasa meku Lafiya?
"Lafiya lau Wallahi tafada yace inaYa Na'ima dake Wataran haka yake CE mata kamar yadda Suke fada Mata
"Tace Sun tafi zaga dangi itada su Abbah"
"Cikin Kulawa yace ke meyasa baki bisu ba"?
Sunkuyar da kanta tayi batace Komai ba
"Yace ba tambayarki nake ba An jaki yawon gantali ko dama Abinda kikazo yi kenan to karkiqara bin Wasu yawo Har ki bar garin domin ba Abinda kikazo yiba kenan kinji ko
"To Insha Allahu Fa'izan tafada"
Kowa yayi zagi a kasuwa yasan da Wanda yake tsaff D'ija ta fahimchi da ita yake kawai Sai ta bagarar da shi
Cikin Izza tace yaya Ali Sannu da hanya kazo Lafiya?
Banza yayi Mata yaqi Amsawa
Ta6e baki tayi gami da ga kafadu ta shige can kuryar dakin ta Bude katowar siff din Nene tanaso ta Canja kaya
Cikin Ranta tace kayi kagama ba sai ka kara ganinaba Ma Ai nagama zaman gidanku
Duk yana lure da Abinda take Masa ta kasan idonshi yana Mamakinta wato Dan ta ganta a gaban Nene take wannan Abin tana nufin Nene zata hanashi Hukuntata ne ?