← Book details Nana Khadija Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 24

Sashe 14

Nana Khadija Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shima Dr shiru yayi bai sake magana ba yaciga da cin Abincinsa!!
💜💜💜💜💜💜
💛💛💛💛💛💛

"Asubah r Fari ya tashi bakinshi dauke da Addu'a kana ya mike yaje ya hada ruwan zafi sosai domin Akwai sanyin Asubah yayi Wanka gami da dauro Alwala yafito ya kimtsa sannan ya fice zuwa masjid hannushi riqe da carbi As'useal ' Musulman su suna ta fitowa daga part dinsu domin gabatar da Sallahr Asubah Sunata musabaha cikin mutumta juna!!

*Allah ka karema Musulunci da musulmai A duk inda suke Allah ka tabbatar da dugaduginmu A kan tafarkin musulumci da mu da zuri'armu Dan Ya rabbil A lamina*👏🏻

"Shida da Rabi Suka fito daga massalacin Shida Faruk suna hira Sama Sama Faruk din yace "Abokina naga kayi zuru zuru ko ka kwana kana tunanin D'ija ne ? Yafada yana kyalkyala dariya'

"Bani da Lafiya Alin yace ya bar waccan maganar da Faruk din yayi!!

Da gaske Faruk din yace'

"Serious jiya kwana nayi ina tafka Amai na dauka ma sa'i yayi?

"Wata Dariyar Faruk din yayi yace kaifa baka da mutumchi wallahi 'In lokacin ka yayi dole katafi ka daina naiman ta tana kan kowa qarkari kawai mu daka gumba mubika da Addu'a!!

"Da murmushi A fuskar Alin yace kai!!! Jiya nasha wahala wallahi najima banshiga yanayi irin na jiyaba Dr hashim fa mun dadeshi a jiya domin danaji Abin nanema ya wuce tunani sai na kirashi a waya ya kawomin magani"""

"Lailai Abin gaske ne inji Faruk yace wani Abin kaci yabata maka ciki ne nasan dai kai bai mai ciye ciye bane?

"Ko daya Alin yace yacigaba dacewa wani Abin tashin hankali nashaqa ya daga min hankali kasan dai yadda na tsani qarni ko wari !!

"Kwarai kuwa inji Faruk din kana yace Allah ya kyauta Sai ka dinga kiyayewa Ai"

"In Sha Allah inji Alin kana sukayi sallama kowa ya shige part dinsa domin kimtsawa zuwa gurin Aiki"

"Cikin Nutsuwa ya Shirya tsaff ya zauna kan dadduma ya bude Al'kurani yafara karatu sai da yayi izu hudu sannan ya rufe Al'kurani ya mike gami da dauke daddumar ya aje inda take"

Ya dau Agogo ya daura ya dibi sauran tarkacensa da wayoyinsa ya fice daga gidan bayan ya tabbatar da ya kulle dakinsa Sosai ko takan Siyama bai bi ba Domin yanzu kallonta ma zai iya daga masa hankali ko dako bai shaqi wannan mummunan warin da yaji tana fitarwa ba jiya!!

*lailai Siyama kin jawowa kanki masifa Allah ka karemu kasa mufi qarfin zuciyoyimu Amin*

*MUJE ZUWA*
💋

*MRS AHAMAD GWADABE*👌🏻👌🏻👌🏻
💜💜💜💜💜
💛💛💛💛💛

"Kwanciya yayi bayan yasha maganin. Yana ajiyar zuciya A fili yace wannan masifa har ina'mtsss yaja tsaki"

"Shima Dr da ya kammala zama yayi kusa da Ali n yana duba A gogon hannusa tara saura

"Yaya kaji yanayin jikin naka inji Dr din?

"Da Sauki dai Alin yafada Dr yace wai mai ya tayarma da wannan Abin naka ne?

"Yana daga kwance yana faman lumshe ido barci na fizgarsa kadan

"Yace kaifa kafiye tambayar kwakwa wallahi"

"Dariya Dr din yayi yace to Ai A kan Aikina nake dole na tambayeka"

"To babu Ruwanka Inji Alin Dr yace Ok toum naji yanzu sai tambaya ta biyu kamar kullum nasan in nayimaka ita baka bani Fuska

"Yaya maganarmu da D'ija wallahi da gaske nake Dan Allah kashige min gaba A kan Al'amarin A matsayinka na babban yaya A gurin ya rinyar Aboki na"

"Yafi minti uku bai ce komai kana murya irin ta maijin bacci ido A rufe yace wai duk wannan Abinda kake yarinyar tasani ma'ana tasan kana sonta kokuwa?

"Dr yace ina fa!!!

To wato Ni ka raina nine zanje yawon neman maka yaddata ko Sai kace wata 'Sa'ata. malam in zakaje kawai kaje da kanka zaifi ni babu Ruwana idan matarka ce Allah ya tabbatar da Alkairi"

"Abin Mamaki ya bawa Dr din ganin yadda Alin ya sakko sabida lokacin baya in yayi masa maganar da fada suke rabuwa

"Yace Nagode Abokina in Sha Allah A satin nan zanje Domin gaskiya ina son yarinyar dayawa wallahi"

"Wani matsiyacin tsaki Alin yaja yace naji Dan Allah tashi katafi ni ka hanani bacci kyoi ta zubar zubar da girmanku gurin kananan yara don Allah dubeka gemai gemai da kai Mtsssss!!

"Mikewa Dr din yayi yana dariya yace malam Dan dai ba kasan dadin Soyyaya bane kake wannan zancan"

"Banza Ali yayi masa har ya karaci surutunsa ya fice "bai ce masa komai ba

"Cikin Ransa yace wai ni zaiga yawa Yaya Soyyaya take yadda take wahalar da ni da Rayuwata"

"Ni kam bazan "Ta6a Furtawa yarinyar nan So da bakina Ai sai ta rainani in ita ta fahimci Son da nake mata Shikkenan Amma banzanyi wannan rashin Hankalinba irin nasu Dr da Faruk

"Da Sauri ya mike ya je ya kulle kofarsa Dan Abude Dr ya barta

"Ya murza key ya barshi A jiki Domin kar Siyama tashigo ta cuceshi yasan halinta da naci kamar wata mayya!!

"Kwanciya yayi gami da Addu'oi kamar yadda ya saba Ai kwan ko minti biyar baiyi ba bacci ya kwasheshi

*Asubah tagari Aliyu*
*NANA KHADIJA*
💜💜💜💜💜💜
💛💛💛💛💛💛

*STORY WRITTEN*
*BY*
*BINTA UMAR MM*
*ABDUL WAHABU*

*page*
*150*

"Ko da Suka tashi daga gurin Aiki kai tsaye can Family house ya nufa domin yinin yau din tunanin D'ija ya Addaba masa gefe kuma yana jin wata yunwa a zababbiya

Tun A mota ya dudduba wayar D'ija sosai ta fashe sakamakon buga ta da dayi da kasa sai da ya binkice ta tsaff babu Abinda ya gani na Assha aciki ko badala Asali ma duk numbobin dake cikin wayar basu fi biyar ba biyu nasu Fa'iza da Na'ima Sauran kuwa duk na mata ne yasan kawayenta ne sai numbar din jameel

"Cire layukan yayi ya aje sannan yayi parking ya fito yashiga wani gurin saida wayoyi yace su duba masa mai kyau "

"Ai kwan da Sauri suka duba masa sa gaidashi suke shi kuma yana Amsawa Cikin Sakin Fuska yana nuna musu kar su damu ba wani Abu waya kawai zai duba "su kuma masu gurin ganinshi cikin kayan Aiki ya tsora tasu gashi dama shi ba boyyeye bane

"Yana zama yace ma Ummi A kawo masa Abinci Ummi tace lafiya yau na ganka haka kamar Wanda ya tashi daga ciwo"

"Lafiya ta lau Ummi ka wai tsabar yunwace yinin yau babu Abinda naci wallahi. Yafada batare da ya fada mata mussabbabin Abin ba domin ko da can ma shi ba mutum ne mai yawan maimaita magana ba indai akai Abu a lokacin yake wucewa a gurinshi

"D'ija Ummi ta kwalawa kira Sai gata tafito da Sauri hannuta riqe da wani yanki Alamun daga kchin take"

"Tace gani Ummi

"Ali zaki kawowa Abinci

*innalillahi*!!
D'ija tace cikin Zuciyar ta domin kwata kwata bata lura da mutum A zaune a gurunba sabida kujerar da yake zaune a can loko take shiyasa bata ganshi ba

Satar kallon Jikinta take domin wasu riga da wando ne A jikinta rigar irin mai kamar Shimi ce Hammata duk a waje saman qirji sun fito sabida matsar da rigar tayi mata sai wando tree Quetar dinta Wanda yaza mar mata Ka'ida kullum a jiki inda Allah ya tai make tama ta daura zani Akai
💜💜💜💜💜💜
💛💛💛💛💛💛

"Dama in zata Shiga kchin haka takeyi sabida kwata kwata bata son zafi gashi yau Kusan girki kala Uku Ummi ta sasu duk su Na'ima ma suna kcin din tare da Asabe

"Kanta Akasa tace to taki yadda ta kalli inda Alin yake zaune Wanda ya zuba mata ido kirr ko kunyar Ummi baya ji

A tsarge tayi hanyar bedroom din su domin ta Sako Riga tana tafiya kamar zata fadi sabida sauri Tasan idon da Ali yasa mata ne kawai cikin ranta tace Allah ya isa wallahi

Wata muguwar tsawa ya da ka mata yace dawo Dan Ubanki INA zakije ko bakiji Abinda a kace bane munafuka

"Da sauri D'ija ta waigo har hular kanta na faduwa dalilin tsawar Ali ta hau inda inda yanzu yan kawo dama dama Ai Ai

"Dama Ai din me Uban me zaki yi A dakin Ni sa'anki ne ?

"Zan sako Riga ne tafada Saura kadan kuka ya kufce mata jin irin tujarar da Ali yake mata babu gyara babu dalili

"Wuce Dallah malama kije ki dauko mana Abinci da baki saka rigar ba sai da kika ganni Dan isaka ne ni iyi?

"Tayi Shiru bata tambayarki nake ba nan ma D'ija tayi shiru kai a sunkuye

"Yace indan ni zaki saka riga to baki da Abinda zaki daga min hankali Dan Ubanki wuce ko inzo nan wallahi ranki ya 6aci!!!
Kuma har in bar gidan nan a haka zaki zauna sai inga karyar iskanci yafada a zafafe sai kace Wanda akayiwa gagarimin laifi har zamowa yake daka kan kujerar tamkar zaifado sabida tsabar masifar datake cinsa

"Da Sauri D'ija ta wuce kchin din tana murguda baki tace Aikin banza Aikin wofiii "Mtssss
"Idonta taff da ruwan hawaye tana jin takaicin ganinta da yayi a haka

"Ita ko Ummi Abin mamaki ya dinga bata ganin yadda Ali ya hakikance sai zuba ruwan bala'i yake

"Tace wai meye haka Ali kaifa kafiya shiga Abinda bai dameka ba INA ruwanka da'ita

"A zafafe yace Ummi wannan Ai sakarci ne da rashin tarbiya yaya zata dinga yawo a haka sai kace ba diyan musulmai ba duba fa Ummi da kowane lokaci masu Aiki maza dake waje zasu iya shigowa wannan Sam bai daceba

Ummi tace Ayyo Ashe ban iya tarbiya ba ko Ali to bari kaji wannan yarinyar duk Abinda taga dama shi take a gidanan inyi magana kai da Abbah kuce ina matsa mata! Ka dai gani da idonka zakazo kana yimin tsawa Sabida ga Sa'arka!
💜💜💜💜💜
💛💛💛💛💛

"Fuska A murtuke yace Ummi kina Nufi dama tana sa irin waddan kayan a gida

"Kwarai kuwa in ji Ummi ba'ita kadai ba ma dukkanisu suna sawa sai dai ita tafisu sakawa to wai kai meye ruwanka ne iyi tafada cikin mamakin daga hankalin dataga Alin yayi!!
Chapter 14 · 0% Book details