← Book details Nana Khadija Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 24

Sashe 17

Nana Khadija Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah yasawaqe Ai har indai izzarka bazata bari ka nunuwa yarinyar so ba babu wani bata lokacina da zanyi"

"Shawara daya zan baka tunda Shi Dr ya je gurin su Abbah kai mai zai hana kaje gurin Nene nasan ka nuna mata qudurinka kan D'ijan zata Rufa maka baya"

"Shiru dakin yayi wajan minti biyar

"Kana Ali yadago Fuska babu walwala yace bazan iya ba Wallahi kaji na rantse kai na mahakura da ita in dai har sai na Furta mata da baki na kana sane da halinta batada kunya ko kadan Rai nani zatayi!!

"Shikkenan Faruk din yace wannan yana nufin kabawa Dr damar ya cigaba da nemanta kenan?

"Mtsssss Do Allah ka Saurara min Alin yafada A fusace yace bakai ka daure masa gindi ba har ya samu dama irin haka gaka Kai ma Fice min A gida tunda baka da taimakon da zakayi min

"Mikewa Faruk din yayi yana Dariya Yace kwarai kuwa yanzu zan fita kaje ka kashe wutar kowa tashi ta fishsheshi Allah bawa mai rabo Sa'a kai da Dr din"
💜💜💜💜💜
💛💛💛💛💛

Ya fice yana kunshe Dariya ganin yadda Ali ya koma lokaci kankani

"Siyama Na zaune A falo taga Fitowar Faruk Dakin Alin dama tana dakinta ta dinga jin hayaniya kadan shine dalilin dayasa ta fito

"Gai dashi tayi tana qasqantar da kai Abin sai yabawa Faruk mamaki Amma bai nuna ba ya Amsa cikin Sakin Fuska

"Tace Dama ina son magana dakai kallonta yayi yana kallon Agogo kana yace OK Allah yasa lafiya dai?

"Fashewa da kuka tayi tace Wallahi A kan Abokinka ne Faruk yau tsawon Shekara Hudu da Auranmu nakasa shawo kansa Sai wulakanci yake min Abinda kasani dai Anayi har yanzu ba'afasa baya bani hakkina takowane bangare takarashe maganar Cikin kuka"

"Tabbas Yasan da Wannan to shi yanzu bashi da tacewa kan lamarin dan yanzu ko da wasa bazai tari Ali da wani zancan ba sabida ganin Halin da yake ciki"

"Sabida haka rarrashin Siyaman ya hau yi yace kikara hakuri kinji ko Akawai lokaci kici gaba da binsa kamar yadda Allah ya Umarci ko wace mace tabi mijinta inshi ne yake cutarki Allah zai sakamiki idan kuma kece kike cutarsa Allah zai sakamasa haka lamarin Aure yake"

"Kukan munafurci tacigaba dayi domin sai taji kamar Faruk yana gaya mata magana Akan Abin dasukeyi ne A kan Alin"

'Kasa dago kai tayi har Faruk din yafice daga Falon

"Shiko Faruk yana sane yayi mata wannan shagu6en domin ta San yasan duk irin Abinda sukewa Ali na cutarwa "

Faruk yana Fita yaji kamar yabishi yai maisa dukan tsiya Dan Wulakanci yana nufin bashi da taimakon da zaiyi masa A kan lamarin lailai zai hadu da Fushinsa Wallahi Shi kadai yake wannan zantukan A zuciyarsa Afili yace Wai ni yaya Zanyi ne?

*Gadanga manya kasa*😊

Kan Ya Ankara yaji An bude kofar dakin An shigo

Siyama CE tashigo da Sallama Dago kai yayi yana kallonta batare da ya Amsa mata Sallamar ba ya zuba mata ido kawai

Taku!! daya tayi ya tsayar da ita Shikanshi baya son irin Abinda yake Mata sabida darajar Dan Adam gami da kokarin Riqe Amana Amma yarinyar taqi ganewa""

Da Hannu ya Nuna mata kofa Alamar ta fita daga Dakin

Kin fita tayi ta zube a gurin tana Rusa ihu

Kallonta yake yana mamaki lailai kukan dadi take ina ma shine yake wannan kukan da yaji sassaucin Abinda yake cikin zuciyarsa

Jin zata Cika masa kunne ya mike yayo hanyar kofar da nufin fita daga dakin yabar mata

"Da Sauri ta mike domin tayi zaton zai mata Wani Abun ganin yadda ya dumfaro gurin Cikin A zama!!

Gifta ta yayi yabude kofar yafice Wani irin wari ya Ziyarci hancinshi lokacin da ya wuceta din Da Sauri ya karasa Fita yana toshe hanci!!!
💜💜💜💜💜
💛💛💛💛💛

Da Sauri ya Bude mota ya zauna yana haki wannan Masifa har ina
*innalillahi* yake ta nanatawa A fili ko ta ina babu Sauqi Allah ka yaye min wannan jarrabawar"

"A taikaice dai Ali nan cikin motarsa ya Kwana A ranar *Sugari* tayi kuka domin Shan hauka yayi mata Abinda ba yayi karkarinshi Kara daya wani Sa'in ma baya shanye kara dayan yake kashewa in Dan jin Shan ta ya bijiromasa ne babu yadda ya iya sai yasha yake jin dadi

*Sigari* tazama Wani 6angare a jikin masu ta Ammali da ita Bature mugun mutum wallahi Allah ya isar mana da kai Domin dai *Sigari* Ita CE Ajalin Wani Sakamakon Lalata kayan Ciki gami da babbaka huhu
*Allah ka karemu damu da zuri'armu masu Sha kuwa Allah kasa su daina*🤒

Misalin Biyu na dare Yafito Daga motar ya daura Alwala yashige massalaci domin yana jin tsoron komawa cikin gida yaji Wannan warin na Siyama Lailai yazama dole yayi nesa da Siyama in ba haka ba wataran Sai dai a zo a tadda gwarsa muddun zata ra6eshi""

Nafiloli yayi tayi gami da Karatun Al'kur'ani maigirma hade da kaiwa Allah kukansa Cikin qasqantar da kai zuwa ga *Sarki jalla wa Allah*

"Har lokacin Sallahr Asubah yayi yana zaune ladani anan ya tarar dashi kowa nan ya Sameshi

"Ana idar da Sallah ya mike ya fito daga masjid din ko sauraron Faruk yaqi Sabida Fushi yake dashi

'' biyo bayanshi Faruk din yayi yana magana tsayawa yayi yana jiran isowar Faruk din

Mika masa Hannu yayi Shima ya mika masa"nasa

"Yawwa Barka da Asubah daga haka Ali yazare hannusa cikin na Faruk din ya huce yana cicin magani

Sakin Baki Faruk din yayi yana bin qyeyar Ali da kallo cikin mamaki Auu Haushinshi yake ji kome?

"Girgiza kai yayi ya shige part dinshi yace Allah ya kyauta maka Ali Akiana zaka wuce ni mai ye laifina Hummmm

*Ni kam Nace kaida Abokinka babu mai shiga tsakaninku domin kaunar ta dabance daga Allah ne

*Muje zuwa*
💋

*MRS AHAMAD GWADABE*👌🏻👌🏻👌🏻
*NANA KHADIJA*
💜💜💜💜💜💜
💛💛💛💛💛💛

*STORY WRITTEN*
*BY*
*BINTA UMAR MM*
*ABDUL WAHABU*

*Malukal milki zuljalali wal'ikiram*

*page*
*154*

Da Wuri yagama Abinda zaiyi ya fice daga gidan Domin bayason Siyama tafito takara hada masa wani zafin da ya kwana dashi

Waya yayi wa Ummi yace don Allah tasa malam Haruna ya kai masa Abin kari yana gurin Aiki

"Wayar Faruk ce ta Shigo yana tsaka da duba Wasu takkadu kallo daya yayiwa Wayar da ya Fahimci Faruk din ne sai yaqi dagawa

Yakira ya kai Sau Hudu yaqi daga wa domin Fushi yake dashi Sosai Mai zai cemasa yanzu

"Shima Faruk Din gajiya yayi da kiran Yafito daga nasa Ofis din Domin yaji Wai mai Alin yake Nufi

Ko da Ya shigo Ofis din banza Ali yayi masa Yaki kulashi

"Cikin Mamaki Faruk din yace gaba ka dauka dani Sai kace ni najawo ma Ance maka ga yadda zakayi girman kai ya hanaka Sai ka tsiri Fushi da Mutane babu gaira babu dalili"

Nan ma Shiru Ali yayi baice Uffan ba

Sai ma ya dauki waya yana kiran Ogansu domin yakara yi masa bayani A kan 6arayin da 'A ka kama shekaran jiya Anyi Anyi Su fadi in da Sauran "yan Uwansu suke sunqi!!

Tsaki Faruk yaja ganin yadda Ali ya shareshi ya barshi A tsaye gashi shima yana da tarin Aiki A Ofis dinshi yafito Sabida haka bai kara cewa Ali komai ba yafice daga Ofis din nasa gami da buga kofa domin yaji haushin yadda Alin yayi masa

Yini Yayi A ofis dinsa Dan Sai wajejen goma da rabi ya bar gurin Aikin ya koma gida

Wanka yayi kana ya daura Alwala yafito ya Shimfida dadduma yayi nafilfiilunshi Kamar yadda yasaba Sannan ya Kwanta yana jin Sassauci cikin zuciyarsa da haka har bacci ya daukeshi

"Ba kwai Saura kiran Abbah ya shigo Wayar Ali A lokacin yana zaune yana kimtsawa duk da cewa Lahadi ce dole zasu Fita Aiki Sabida waddanan "yan Fashi da Suka kama

Daga Wayar yayi gami da Sallama
yace Abbah barka da Asubah Antashi lafiya?

Daga daya 6angaran Abbah n ya Amsa Cikin kulawa yace Ya Mu jira ka ne ko mutafi katawo daga baya?

"Ina Zamu je ne Abbah Inji Alin domin Shi har ga Allah ya manta da yau zasu zatafi gurin Nene

"A'a kar dai ka Manta Abbah yafada yaciga ba dacewa ba yau zamu tafi can Wurin Nene Ba"
💜💜💜💜💜
💛💛💛💛💛

"Ayya Wallahi na manta kwata kwata Abbah"

"Koda naji Abbah yafada"

"Mujiraka kokuwa?

"A,a Abbah kutafi kawai Na biyo bayanku muna da Aiki ne yanzu dole zan Dan nemi Alfarma'gurin Oganmu"

"To Masha Allah Sai kazo din Abbah yafada yana kokarin kashewaya

"Kwata Kwata Ali ya daina kula Faruk kiri kiri zasu hadu guri Sai ya shareshi Yau ma haka Suna tsaye a harabar bracck din nasu suna horar da kananan Sojoji Faruk din yana Masa magana A kan 6an garan Aikin nasu ya share shi

Ganin Mutane zasu An kara ne yasa ya rabudashi kawai in sun koma gida Sai yafada masa mai yake nufi da Abinda yakeyi

********************
To Siyama Fa tana Wani Hali domin yanzu Abin har yaci Uwar na da Domin yanzu bayan Ruwan dake Fita Wasu kananun koraje ne suke fesowa gurin masu bala'in qaiqayi Sabida Haka babu shiri ta kama Hanya ta tafi Gida Cikin tashin Hankali tana gayawa Momy'n ta gashi in kaikaiyin ya motsa ko ina sai tayi sosar take jin dadi

Hankalin Momy'n ta yatashi Sosai da Sosai Babu Shiri Sukayi Asibiti Tashin Farko likita da yaduba yace bai Fahimci komai ba kan lalurar domin har sparm din ta Sai da yasa A ka dauka domin yayi zaton ko Gloria ce Amma Abin Mamaki baiga komai ba

Haka Dai ya hada Musu magun guna yace taje tai Amfani dashi in suka kare bata dai naji ba sai tadawo

--------------------
"Nene taji Dadin Zuwansu Tadinga Murna ina A saka ina A je dasu tashin Farko ta ce Ina Muskili na Ali ko yayi Halinnasa Abbah yayi Dariya yace yananan tafe A kwai Aikin dasuke zaki Ganshi

"Tace Na dauka Ai bai zuwa ne Ai daya hadu da Fushi na" dama Ina nemansa

"Mikewa Abbah yayi ya nufi can 6angarsu ma'ana inda Suke Sauka in sunzo Ummi ma bayanshi tabi

"Yayin dasu D'ija Kuwa suka Shige dakin Nene Suna ihun murna D'ija tayi tsalle tafada gadon Nene tace Wallahi Nayi kewar gadon nan
Chapter 17 · 0% Book details