← Book details Nana Khadija Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 24

Sashe 18

Nana Khadija Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dariya Fa'iza tayi ita ma tabita su ka kwanta tare Suna dariya

"Tsaki Na'ima taja tace Sai kuyita Shirme Sai kace Wasu yara"

"D'ija Na birgima kan fado tace ta66 ya Na'ima yara ne mana kananu ma kuwa"
💜💜💜💜💜
💛💛💛💛💛

"Tsaki Na'ima taja ta zauna kan kujera gami da Fito da wayarta As'useal ta Makala eirpix

"Nene tashigo dakin da A zama ta gansu sun yi mata Rudu Rudu a kan gado Suna ta shewa babu Abinda ya damesu

Hararsu tayi tace maye haka zaku kwanta min a gado sai kun bata min

Dariya Suka dukkaninsu D'ija tace kai Nene Wannan gadon naki ma da bashi da dadi"

"Eh naji bashi da dadin A dai Sakko min Ehee

"Ta6e baki Na'ima tayi tace Sai kace Wani gadon Arziqi"

Duka Nene ta kai mata tace yafi dai Wanda bashi dashi " yar Nema kiyi zuciya kema ki mallaki naki

Dariya Suke tayiwa Nene Ita ko Sai Sababi ta ke tace Ku fito mushiga kchin tare domin baza Ku barni da kici niya ba

Gaskiya Yau girki kadai zamuci mufa baki ne yaya zaki ce muzo Mutaya ki D'ija tafada"

Rufe min baki Shasha Cewar Nene babu Abinda kuka iya sai Shirme haka za'a kaiku daki n miji babu fuss!!

"Kai Nene Wallahi D'ija tafi ki iya girki yanzu Fa'iza tafada taci gaba dacewa in kika ci Abincinta sai kunnanki ya gutsire"

Tunda yaya Ali yayi Santi Abinci D'ija Ai komai karshe ne

"Cikin Mamaki gami da kama ha6a Nene tace kina Nufin Ali ne yaci Abincin D'ija duk iyayinsa gami da tsamtsami n nasa?

Humm Nene kenan Sau nawa kuma Fa'izan tafada

"Wani dadi ne ya lullube Nene tana Hamdala cikin Zuciyarta tace Allah ya tabbatar Min da qudirina A kan yarannan"

Babu yadda Nene ta iya haka tai ta hidima su dam ma A kwai wata dattijiwa Delu dake nan makotansu take shigowa tana debe mata kewa gami da tayata Ai ke Aike

"Gajiya ta hana Ummi fitowa Sai da su Nene Suka kusa kammalawa sannan fito

Tayi tayi Nene ta tashi ta kar6eta Nene n taqi tace ta huttasheta

*MRS AHAMAD GWADABE*👌🏻👌🏻👌🏻
*NANA KHADIJA*
💜💜💜💜💜💜
💛💛💛💛💛💛

*STORY WRITTEN*
*BY*
*BINTA UMAR MM*
*ABDUL WAHABU*

*155*

Dukannisu guri guda suka hadu domin Cin Abinci har Abbah cikin Farinciki da Walwala
Jameel yanata Faman tsokanar D'ija kamar ko da yaushe sai dariya A ke musu

"Abbah ya gyara Murya yace Ai muhimiyyar magana ce Abaki na nake tafe da ita

"Cikin Farin Ciki Nene ta gyara zama tace Masha Allah Allah ya jishemu Alkairi

Jin Haka yasa Na'ima Mikewa da Sauri tabar gurin Domin ta San maganar

Bin bayanta Su D'ija sukayi duk da basu San ko wace irin Magana bace

"Shima Jameel tashi yayi yafita can waje gurin Matasan Anguwa suka cigaba da Hirararsu

Daga Abbah Sai Ummi a gurin Sai Nene n

"Abba yace Mutuniyarki ce tasami Miji duk da Cewa bata San da Zancan ba Amma ni nayi Murna da kasancewar dacen datayi domin yaron Dan kirki Sosai"

"Washe baki Nene tayi Tace Alhmdulilh Kaga Sai ka hadasu gaba daya kasa a daki kai nataya Fa'iza Murna Allah yasa za'ayi damu Ai sai ka fada masa yazo su daidaita kansu yaron"

"Cikin nutsuwa Abbah yace ba Fa'iza bace Nene D'ija ce Ai"

Kicin kicin da Fuska Nene tayi tace kamar yaya D'ija ita da take da Miji A Hannu

"Wallahi Abokin Ali ne Dr Hashim likitan da ya dubata lokacin tana wannan zazza6in gaskiya yana da hankali sosai

Gyara Zama tayi gami da Sake kwance daurin Dan kwali ta tasake daurawa tace bazai yiwuba yaje ya nemi Wata ni tuntuni nayiwa D'ija Miji domin Auran Zumunchi zan kulla to kaji !!!!

Gaban Abbah ne yafadi kadan jin wata Sabuwar rigimar ta Nene wai tayiwa D'ija Miji A'ina yake Dan waye shi duk da yaji tace Auran Zumunchi zata killa

Sai ya ba garar da Maganar Nene ya kara Sako Maganar Dr din dai A karo na Uku

"Yace Ai dan gidan Alh Salihu ne wannan Abokin nawa ina ji zaki san shima domin munsha zuwa nan dashi

Dama Muntsayar da daurin Auran Na'ima da Faruk nan da Sati Uku masu zuwa kinga in sun daidaita Kansu yaran sai Ahada kawai A huta
💜💜💜💜💜
💛💛💛💛💛

Hayyagowa!! Nene tayi Tace ka kyaleni da wannan zancan kai kasan wani Salihu ni bansanshiba ina maka maganar D'ija Nada Miji A hannu kanayi min wata maganar banza to D'ija bazata kai Wannan kwanakin da kafada ba ma zansa a daura mata Aure in Kai bazakayi ba"

"Cikin Kwantar da Murya Abbah yace kwantar da Hankalinki ne duk Abinda kikiso shi za'ayi yanzu Shi Mijin da kika zabarwa D'ijan Dan waye a cikin dangi?

"Kinga Sai mukulla magana Kafin mu koma Sai Su daidaita Kansu Allah dai ya Sanya Alkairi yafada Cikin Rarrashi domin bayason bacin ranta ko kadan

"Babu darr Nene tace Waye kuwa in ba Ali ba Shi nazaba mata A matsayin Miji ko tanaso ko bata so hakannan shima ko yana so ko baya so in Sha Allahu sai na idda wannan qudirin nawa to kaji"!!!

"Cikin Al'ajabi gami da Mamaki Abbah yace Kika CE Ali Nene??

"Kwarai kuwa Nene n tafada babu Alamun wasa A fuskarta"

"Ummi ko kusan daskarwa tayi a gurin dama tana zaune ne tana jinsu batasa musu baki ba Jin Abinda Nene tafada yasa ta dago kai a razane tana kallon Nene bakinta na rawa Ali Sam hadin ma bai yi ba!!

"A jiyar Zuciya Abbah ya Sauke yace Masha Allah hakan yayi Amma kina ganin Babu Cutarwa a Ciki idan A kai wa D'ija haka kin San halin Ali faa baudaddan Mutum ne zama dashi Sai mai hakuri gashi dama basa jituwa A tsakaninsu Sosai

"I Dan Sukayi Auran sa jitu babu Ruwa na ni Nene tafada taciga da cewa kai yanzu rashin Haihuwar yaron nan bata damunka duk da cewa Abin kamar gado yayi Amma jikina yana bani A kwai Alhairi a tattare da wannan Abin da nake shirin kullawa Sabida haka In Sha Allah D'ija da Auran Ali zata koma anan za'a daurashi Nagama yanke Magana. Shi kuma Masifaffen in Andaura An kai masa ita yasata A tsinken tsire ya tsire sannan ya soke A bango ta karashe Maganar har da dukan Cinya

"Saura kadan Dariya ta Subucewa Abbah ganin yadda Nene take hakilo shi bata San in zata tona zuciyarsaba tagani tafi Auduga haske sabida tsabar farin cikin hadin dama shima yana tunanin haka a zuciyarsa Sanin Halin Ali ne yasa ya bar maganar domin kwata kwata bayason Abinda zai sa ya shiga hakkin D'ija domin yana ganin in ya matsa ayi Abun D'ija zata Sha wahala da Ali kasancewarta yarinya karama babbar mace ma Siyama takasa dashi Shi dai yana ta Addu'a Allah ya zabawa ko wacce Miji Nagari

To Sai ga wannan Maganar daga bakin Nene hausawa nacewa duk Abinda babba ya hango yaro ko ya hau bishiyar rimi bazai zagani ba Amma yayi bala'in jin dadin Abin babban damuwarsa shine Abinda zai cewa da Alhjin Dr kasancewar ya Amsa masa da Cewar yabashi D'ija yazo kawai su dai daita Kansu Amma yasan Abinda zaiyi

*Tofa kaka kara kaka tsara*

😊

*MRS AHAMAD GWADABE*👌🏻👌🏻👌🏻
*NANA KHADIJA*
💜💜💜💜💜💜
💛💛💛💛💛💛

*STORY WRITTEN*
*BY*
*BINTA UMAR MM*
*ABDUL WAHABU*

*page*
*156*

Ganin Nene Sai fada takeyi yaqi karewa yasa Abbah yace Ai magana ta huce Nene na Aminchi yanzu Wacce Rana kika tsayar Domin daurin Auran?

"Sauke Nuffashi tayi tace mubarshi juma'a mai zuwa nan da kwana biyar ko"

"Hakan yayi Allah ya kaimu Abbah yafada"

"Kallon Ummi tayi tace ke munata Magana kin zauna bakice komai ba"

"Nene Mai zance Allah ya sanya Alkairi shine Abinda Ummi tace kawai Amma Cikin ranta tanaji bata Murna da Auran kwata kwata"

"Mikewa Abbah yayi yace Zan Dan Fita in zaga mu gaisa da "yan Uwa kin San munjima bamu hadu da juna ba"

"Ai kam Nene Tafada tace in yaso sai ka sanar musu da Abinda yake wakana"

Sama Sama Ummi da Nene suka dinga Hira Bayan Fitar Abbah Nene duk sai taga Ummin ta can zamata kamar Wata Mara lafiya Sai bata tambayeta ba tana dai Nazarinta. 'Ita ko Ummi wani sa'in haka take komawa jikinta sai ya dinga mutuwa ita kanta bata San dalili bah'

********************
To Atai kaice dai Sai da Suka Kwana Uku Sannan Ali ya biyo bayansu hakan Ma yace Shi baiyi kwanakin da zasuyi ba zai koma Sabida yabaro Aiki

Duk Wannan Abinda dake Faruwa Ali da D'ija babu Wanda ya Sani Na'ima CE kawai tasani itama Ummi CE tafada mata ita kan ta tajima tana Mamaki Al'amarin Wai D'ija zata Auri yaya Ali gashi bai sanar maganar ba yanzu in ya Sani wace tata burzar za'ayi domin ta San halin D'ija ba kanwar lasa bace ita ma

Abba yayiwa Maihaifin Faruk Waya yagaya masa Duk yadda Ake ciki Maihifin Faruk din yace Ai hakan yayi daidai Sai kawai A hada gaba daya A huta ko yaya kagani?

"Kwarai kuwa Abban yace nima Abinda nake tunani Kenan Amma A kwai wani Abu da nakeso in kulla tsakaninin Dr Hashim din da Fa'iza tunda bai Samu D'ija ina ganin yazo kawai nabashi ita Dan gaskiya nayaba da dabi'un yaron

"Masha Allah kayi tunani mai kyau Alh Bashir Na tabbata yaron bazaiqi Amuncewa ba Sai kawai kayiwa Alh Salihu Maganar Abinda ke A kwai Kaga sai mutawo da Shirimu Cewar Mahaifin Faruk din"

"Masha Allah yasaka da Alkairi Abbah yafada yana kokarin kashe waya yace yanzu. Zan kirashi in masa bayani n komai

Sannan sukayi Sallama yakeshe wayar"

Kamar yadda yayiwa mahaifin Faruk bayanin Abinda yake Faruwa haka ya zubewa Alh Salihu Magana

"Alh Salhu ya nuna Farin cikinsa A kan hakan domin Shi yana son hada zur'ia da Alh bashir yace Na'amice da hakan Allah ya tabbatar mana da Alkairi yanzu n nan zankira yaron in masa bayani dama wani baya Auran matar Wani Allah yayi ita *khadijatu* n ba matarsa bace

"Abbah yace Naji dad in Yadda ka Fahimceni Alh Allah yakara Zumunci"

"Ameen Alh Salihu yace Kana sukayi Sallama gami da kashe wayoyinsu Cikin Farin Ciki
💜💜💜💜💜
💛💛💛💛💛

To duk 6angarori biyu Sun Amice da Maganar jiran rana kawai sukeyi
Chapter 18 · 0% Book details