← Book details Nana Khadija Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 24

Sashe 23

Nana Khadija Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yace Au kuka ma kike lailai kukan dadi kike yarinya dama nine!! Kawai kifadi ina sonka Ali shine Abin kuka ta66!!!
Da nine da tuni nafada Wallahi yafada yana kallon Fuskarta

"Cikin Mutuwar jiki ta Furta ina sonka Ali!!

"Kunnesa ya nuna mata yace matso da bakinki kifada min A nan yadda zan fi ji sosai"

Bayyada ta iya haka ta matsa da bakinta kusa da kunnesa ta furta ina *sonka Ali* wani irin yanayi ya shiga lokacin da yaji hucin Furucinta a kunnensa tsigar jikinshin ta dinga mikewa jiki Babu kuzari ya saketa yace kina iya tafiya!!

Kamar walkiya D'ija ta fita daga tsakaninsa tayi hanyar Waje tana Jan jakarta domin qudirinta na tafiya nanan gefe guda kuwa tanata wa Ali Allah ya isa da Abinda yayi mata

Ganin tayi hanyar Waje ne ya tuna masa Abinda take shirin yi da sauri ya tari gabanta ya riqe hannuta tamauu!
Fuska babu Walwala yace Ashe baki da Hankali ina zaki je da daranan iyi?

Kuka tafashe dashi tace babu ruwanka malami bayan duk kun tsaneni Nene har da cewa sai nabar gidan dadin Abin ma ina da sauran dangi badaga sama nafado ba!!

Dariya tabawa Ali Amma ganin tana kuka yasa bai yi ba tabashi tausayi sosai yarinyar yace to Munji ba daga sama kika fado ba yanzu dai ki aje maganar tafiya gefe guda kiyi hakuri ni da kaina zan kaiki can Ku gaisa shikkenan ko?

:A'a ni kaman yau bazan kwana cikin gidannan ba zan tafine kawai"

OK toum Muje kirakani In karbo Maganin zazza6i Sai ki tafi kinsan ni bako ne a nan ban San in da zan samu Camis ba"

Banza tayi Masa ta fincike hannuta tafita da Sauri shima da sauri ya bi bayanta yakara damqar hannuta a karo na biyu suka fara tafiya zugwi zugwi babu mai magana kasan cewar A kwai jama'a a waje Mussaman Matasa!!!!

*MRS AHAMAD GWADABE*👌🏻👌🏻👌🏻
*NANA KHADIJA*
💜💜💜💜💜💜
💛💛💛💛💛💛

*STORY WRITTEN*
*BY*
*BINTA UMAR MM*
*ABDUL WAHABU*

*page*
*162*

"Har sukaje suka dawo babu Wanda yayiwa Dan Uwanshi magana Hannuta yana cikin nasa yarike sosai shine dalilin da ya hanata tafiya tanaji kunya shi kuma yaqi ya gane haka Dan haka Sai faman zumbura baki take cikin jin haushi

Shi ko Ali zazza6in shi karuwa yayi domin daurewa kawai yake Amma shi yasan halin da yake ciki a halin yanzu

Da ido Nene tabisu da shi hannunta ruqe da ha6a tace A'INA ka ganta ni Hajara

Tafada tana kallon D'ija cikin Mamaki

"Yace A waje na ganta Wai kin ce ta bar gidan yafada yana kokarin shigewa bangarensa

Lai lai D'ija Nene tafada tace ai da kasani kabarta ta tafi kanta tayiwa ai tuntuni nace nafasa hada Auran tunda dama shine bataso

Da Sauri Ali ya dawo baya yace A'a Nene yaya kike dawo da hannun a gogo baya ne yanzu yanzu muka gama magana da ita tace ta Amince ko *khadijatu*

"Hararsa tayi Tace karya ne ban fada ba Nene"

Sororo Ali yayi yana kallonta yace Ni nake miki karya ?

Bata bari ya Nuffasa tace "E "

Girgiza kai yayi ya sha kunu yace babu Laifi yarinya zamu hade ne zakiyi min bayani a inda nake miki karya daga nayi Magana zakice karya nake Lailai kin girma da yawa
Ya Wuce yabarsu a gurin rai A 6ace

"Nene tace sai ki huce ciki ai ke ko kunya bakiji ba

Simi simi D'ija tashige dakin Nene tana zumbura baki

Bin bayanta Nene n tayi tasameta kwance a gado hawaye yana zubah!!

Zama tayi kusa da ita gami da kama hannuta tariqe sosai tace tashi muyi magana kinji *D'ija na*
💜💜💜💜💜
💛💛💛💛💛

"Mikewa zaune tayi tana share hawaye gami da cire hannuta cikin na Nene

"Nene tace ki kwantar da hankalin kinji 'D'ija kiyi hakuri ki Auri Ali Dan Allah ki rufamin Asiri nadade ina burin inga nahada Ku Aure kiyimin Wannan Alfarmar kinji diyar arziqi

*In Sha Allahu zaki ji dadin Abin nan gaba*

Ba Dan bana sonki ba nace ki Aureshi ba Asali ma shine son da nake miki duk wani Abin da yayi miki bayan Auran ki gayamin ni zanyi miki maganinshi kinji ko

Shiru D'ija tayi kanta a qasa takasa cewa Nene komai

Nene tace baki ce min komai ba 'D'ija idan kina ganin zan takurawa rayuwarki to sai in hakura kawai Allah yabaki wani mijin Wanda yafi Ali

"Kallon Nene tayi tana hawaye tace ki kwantar da hankalinki Nene na Amince kawai ina tunanin yadda zan zauna dashi babu so Asalima Abokin fada tane gefe guda kuma Siyama tana daga min hankali

"Ki kwantar da han kalinki kinji ko babu Abinda Siyama ta isa tayi miki Wanda Allah bai miki ba ki shiga da zuciya daya gidan Allah yabaku zaman lafiya in Sha Allahu zakiyi Alfaharin Auran Ali

Shiru D'ija babu magana Nene ko tanata zuba! Cikin Farin Ciki

********************

Washe gari a Dan sake D'ija ta tashi tana zaune gefen gadon Nene cikin wata doguwar riga mai taushi irin mai hular nan ce da Alama rigar ta bacci CE

Su N'aima suka shigo ita da Fa'iza ko kallonta Na'ima batayi ba taje ta zauna tana gaida Nene tace ina delu yau bata shigo da wuri ba?

E cewar Nene bayan ta Amsa gaisuwar tata tace yanzu zaki ganta ai tunda takwas tayi

Ya N'ima An tashi lafiya D'ija tafada"

"Lafiya lau lailai ne har kingama zagina Ashe kina Agaishi Mara kunyar karya kawai

Cikin Fusata Nene tace kinga Na'ima kar ki takalota Dan ma kin samu ta gaisheki ki kyaleta Dan Allah

Dariya Na'ima tayi tana ta6e baki tace Au na manta fa lallabata Ake humm D'ija Manyan kasa wato sai ma an rarrasheta akan ya Ali mata masu Aji a waje suna can suna Neman wannan damar da tasamu basu samu ba Amma ita tasamu tana wasa da'ita

"Eh din baruwanku cewar Nene. Ku kyaleta Ai ita ma macace mai Aji ehee!!

Cikin dariya N'aima tace kwarai kuwa naga Alama ai

Hararata D'ija tayi tana girgiza kai bataso tasata kara yi mata rashin kunya shiyasa tayi shiru

Wayar Fa'iza ce ta katse hayaniyar Nene da N'aima

Da Sallama ta daga wayar D'r Hashim ne

Nan da nan Fa'iza ta sanja murya Fuskarta dauke da Murmushi ta gaisheshi suka hau hira cikin so da kauna kamar sun jima da fara soyyaya ko kunya bataji. Amma wani Abin taken mayar masa da turanci sabida Nene

'D'ija sai faman hararata take tana jan tsaki!!!"
💜💜💜💜💜
💛💛💛💛💛

"Nene tace ooo duniya ina zakije damu yaran zamani sai a barku in kuna hira da samari har aro murya kuke ko makale ta Allah ya kyauta muku ummmm!!!!

Tashi Fa'iza tayi tabar dakin Kunneta makale da wayar ganin Nene tana Mata hayaniya taki ta kyaleta ta yi hira da habibinta

Na'ima ta kalli D'ija tace to kinga yadda A ke soyyaya ko yarinya babu Abinda kika iya sai shirme haka zamu kaiki Siyama ta mayar dake gora a gidan

A kull !! Bakinki ya sari danyan kashi inji Nene taci gaba da cewa Ai babban goro sai magogin karfe D'ija na baza tayi goranci ba a ko ina ballan tana a gidan Ali D'ija na Mowa ce a ko'ina to kaji!!!

Mtssss D'ija taja ta gyara kwanciya gadon Nene gami da lumshe ido ita kadai tasan Abinda yake damun zuciyarta

Da kallo suka bita Nene takama Baki tana kallon N'ima da ido tace tashi ma ni kinzo kin dameni kinga waccan kwallar ta aje kubude a kwai ganyan Magarya da kaikayi debu su ki tafasa ko wanne daban daban zaku fara Amfani dashi ne dukkaninku

Mikewa Na'ima tayi ta dauko ledar magungunan tayi waje dasu a hannuta ta samu babbar tukunya ta zuba ruwa sosai ta daurasu a kan wuta

Delu ce tashigo cikin Sallama suka gaisa da Nene cikin mutumci delu tace A,a Uwar masu gida har yanzu bata tashi ba ne ?

"Wai go wa D'ija tayi tana dariya kadan domin delu mutuniyarta ce tun tana yarinya tace tuntuni natashi delu ina kwana??

"Lafiya lao Uwata kun tashi lafiya"

Lafiya lau D'ijan tace ! Nan Delu ta zauna ta dinga kwantar wa da D'ija hankali har da yi Mata misalin su a lokacinsu su basa sanin miji ake daura maka Aure dashi

"Nene tace kwarai kuwa nima Abinda nake fada mata kenan tayi hakuri in Sha Allahu ita CE da riba

Nene tace yawwa Angama hada kayan gumbar nan ko delu!??

Eh duk an hada an ma fara Aikinta karshenta ma kiga anjima an kawo ta inji delu.

Tace Ai nasa Sallau yatafi can ruga ya samo mana nono mai kyau yanzu nan zaki ganshi ya dawo jarka biyu nace yasamo

Yawwa delu inji Nene tace maganar wannan bakar zumar fa ??

Eh itama za'ayi in Sha Allahu ni da kaina zanyi ta kin San yaran yanzu duk basu Santa ba tunda tamuce ta mutan da

Hakane cewar Nene tace Allah dai yasaka da Alkairi ya bar zumunxhi

Babu komai cewar delu ai duk an zama daya Allah dai ya sanya Alkairi yabasu zaman lafiya

*Amin Amin*
Nene tafada Fuskarta dauke da Murmushi

*MRS AHAMAD GWADABE*👌🏻👌🏻👌🏻
🏵🎗🏵🎗🏵🎗

🐾 *NANA KHADIJA* 🐾

🏵🎗🏵🎗🏵🎗

✍🏼 *WRITTEN BY*

_Binta Umar_
( _MAMAN ABDUL WAHAB_ )

🅿 *163*
Chapter 23 · 0% Book details