← Book details Namijin Zuma Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 107

Sashe 97

Namijin Zuma Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan uwanta, Kuma tasan waye Dan uwanta, Sam bashi da sauki, bashi da saukin fushi Amma fa in ransa ya baci da mutum to ya barshi kenan har abadan. Suka isa bakin mota, Zaks ne ya sanar da sauran motocin gidansu Aeezad zasuje. Zaks ya budewa Aeezad murfin mota yashiga Jiri kawai ke kwasarsa, a zuciyarsa ji yakeyi kmr ma mommy Ta rasu. Bayan Aeezad ya shiga motar, Zaks ya xagaya yashiga other side site din kusa da AEEEZAD, ganin haka yasa big hajiya saurin shigewa gaban motar ita Kuma, dreva yaja motar suka ficd a gidan Aeezad ya kalli Zaks "Shikenan mommy ta mutu,,,wlhi in suka gane cikin dake jikinta nawa Ne kashemin ita zasuyi.. a zuciyata inajin Wani Abu na faruwa da mommyna wlhi naji a raina Wani Abu ya sameta...Wlhi in Wani Abu ya samu mommyna duk wanda yakeda sa hannu a ciki, wallahi sena zamo ajalinsa ko wanene!!!." Aeezad ya karashe Hadi da fashewa da kuka ya hade kansa da guiwa se kuka yakeyi me tsuma zuciya. Zaks yanata basa hkri kmr yadda de ya saba,. Big hajiya ta kada Baki tace " in Wani Abu ya samu jinina dake jikinta Nima bazan yadda ba..." Cikin matsifa tayi mgnr. Sam aeezad ma besan ta biyosuba seda tayi magana yaji,. Ba Wani nisa tsakani sosai gashi Aeezad Se Azalzalawa yakeyi kan suyi sauri, ba bata lokaci suka isa gidan hajiya mommy, a jere akayi packing motocin tin kafin a gama packing Aeezad ya fito daga cikin motar, dai-dai motar Hajiya naja'atu ta fita a gidan, Saboda Kiran da mijinta yayi Mata na Yana Airport ya dawo daga Lagos gashima ya kusa zuwa gida, Daman Kuma bata gaya masa bata gida ba, Dan haka ta tattare ta fice daga gidan, Amma taso ta tsaya tadinga bawa hajiya mommy hakuri ko Allah zesa taji ta sassauta bugun da takewa yarinyar, sun shafe awa Daya Suna bugun yarinyar tin tana ihu harta dena, Amma Sam ba tausayi azuciyarsu, hajiya naja'atu batasan rashin imanin kawarta ya wuce tunaninta ba se yau, a hanya tadinga Kiran sauran kawayensu da Basu samu zuwa ba ta shaida musu duk abinda ke faruwa a gidan hajiya mommy nande suka sata a fai-fai,Daman kawayen bariki ba amana. Direct Aeezad ya nufa falon hajiya mommy Zaks na biye dashi da big hajiya Amma sede Aeezad ya d'an musu nisa. Tinda ya nufo falon yake Jiyo zuciyarsa ba tsananta bugu Hadi da lugude, be tabajin irin bugun zuciyar da yake jiba yanzu,, Wani irin hayaniya yaji Yana tashi daga cikin falon nata, Dan haka cikin hanzari ya nufa falon nata, dai-dai ya Sako kafaduwa da Kai da jiki dai-dai saukar belt da bulalalar hannun na'eema data hajiya mommy a jikin Aunty Nabeelah, se zufa sukeyi su kansu sun gaji da dukan nata,ba inda basu fasa mata ba a jikinta, har fuskarta jini yakeyi tako ina sun fasa mata fuska, ba inda bulala bata samu ba a fuskarta, idanuwanta ta rufesu gam, ji takeyi kamar zata mutu, se kukan zuci Kawai takeyi Wanda yafi kukan Ido zafi, har yanzu ta kaMa ta kame cikinta gam ta kakkaresa da hannayenta, GAF take dajin fitar hayyaci wato sumewa. Idanuwan Aeezad Sukayi tozali da wannan matsifar, yayinda bawanda yaga shigowarsa falon sbda hankalin kowa na kan dukan da akema nabeelah falon ya rikice da zagin nabeelah gashi taf falon yake cike da bil'adama,ga Alhaji sunusi tsaye ba yadda zeyi."zaki gayamin waye ya Miki ciki ko semun karasa kasheki zuwa lahira...." Aeezad da zuciyarsa da idanuwansa ke kan aunty nabeelah dake yashe kasan tiles tako ina jinine a jikinta, kwallarsa suka yawaita cikin zallar tausayinta, zuciyarsa ta Kuma shiga halarar kuna, yasan duk shine sanadin sata a wannan matsifar, Daman yasan za a rina. "cikina ne.....!!" Ya fadi da karfi, yayin da a guje ya karaso ya janyeta daga dukan da suke mata, ya rungumeta a jikinsa Yana kallon uban shedar bulala a jikinta inda ya d'an bude sbda hatta rigar jikinta ta fara yagewa, tinda ya shigo falon taji sbda kamshin turarensa Daya cika mata hanci, ko a yaya in har zataji kamshin turarensa seta gane. Toh fa, Nan kallo yadawo kan Aeezad da nabeelah, hajiya mommy Kam mutuwar tsaye tayi, na'eema ma haka tinda yace cikinsa ne suka dago Ido suka kallesa duk se mutuwar jikkuna tasamesu a lokaci kankani, gani sukeyi kmr a mafarki,jamaah suka hau kus-kus, sbda ba Wanda be gane Aeezad din ba mijin naeema kowa ya sanshi a cikinsu. Hatta Alhaji sunusi Yayi mutuwar razana jin abinda d'ansa yace daga bayyanarsa. "cikinka kmr ya? Ni ban fahimta ba, Wani irin sakarai ne Kai zaka danganta cikin shege jikin Yar Aiki kaskantaccita da kanka,,,," cewar hajiya mommy, dai-dai big hajiya da zaks suka shigo falon, a guje big hajiya ta karaso inda take ganin Aeezad rungume da nabeelah, tini jinin jikinta ya gama shafarsa a jikin kayan jikinsa sbda rungumar dayayi mata Yana kuka kmr ransa ze fita, cikin zallar azabar tausayinta. Zaks de seyaja gefe ya tsaya shima Yana kallan abinda ya faru gasu hajiya mommy tsaitsaye da na'eema da bulala a hannu dagani su sukayi wannan aikin ko ba a gaya maka ba. Yaya de take ne?cikin jikinta de Wani Abu be samesa ba kou?'' cewar big hajiya, Nan kowa ya kara dimauta a zallar damuwa da tashin hankali. Hmmm seda na'eema ta zauna dabau a kasa sbda azabar tashin hnkli da kishi tana fadin "hajiya Mommy ban fahimta ba? Ki tambayesu me suke nufi? Bazan lamunta ganin mijina rungume da mazinaciya me cikin shege a jikinta ba bazan lamunta b...." Aeezad Daya dago red eyes dinsa ya kalli na'eema ya dawo ya kalli mommy ya katse na'eema cikin tsawa da kunar zuciya a ransa yanaji ko kashesu yayi duk baze fita daga mummunan bakin cikin dasuka dasa masa ba a zuciya, wata iriyar tsanar na'eema da hajiya mommy tana ratsasa, a halin da yake ciki Yana iya kashesu su duka,Kai duk Yan falon ma Yana iya kashesu, dabadan bakin duniya ba, da har ubansa dake cikin falon yana iya cinna masa wuta, Sam baya hayyacinsa For now. "kar wadda ta kara shegantamin ciki, duk wadda ta kara shegantamin cikin keda uwarki, zan ninka muku azaba kan azabar dazan muku, bana yafiya Kuma bana afuwa A kan mommyna, Kuma matata, matatace ta sunnah, Aurenta nakeyi, cikin jikinta cikinane, ni namata shi, ga shaidojina Nan..." Ya karashe Hadi da nuna big hajiya da zaks. Big hajiya tayi hanzarin amshewa da "Tabbas kuwa cikinnan na sunnah ne, kada Yar bakar macen data Kuma shegantamin cikin jika na, in ba haka ba duk se na hadaku na kwashi babbar bura ubaku, ba kmr make rafi'ah Yar gidan laure me fura da no-no, kina zaton yadda kike shegiya Ubanki yayima uwarki cikin shege a ti-ti haka jikana yake? To kinyi kuskure, nayima yarana tarbiya kuma Suma sunma nasu, mu ba sauran bokaye bane,, tsakanina dake rafi'ah sede in biki da Allah ya isa, tsinuwata gareki bazata kare ba, koda an dannaki a wutar jahannama,abinda kkyi na raba uwa da d'anta a tunaninki Zaki gama da duniya lafiya? To knyi kuskure..." Big hajiya ta karashe tana kwallah. Tabdijan rigiji gabji! Halin da hajiya mommy da na'eema suka shiga baze misaltuba tini belt din hannun hajiya mommy ya subuce ya fadi kasa, ta juya ta kalli dumbin jamaah dake falon wanda suketa kus-kus, hajiya mommy ta juya ta kalli alhaji sunusi Wanda kansa ke kasa. bala'i biyu kenan gana big hajiya dana Aeezad, komi nafilah ne a kn na Aeezad. . Na'eema kawai seta fasa Wani irin uban ihu Hadi da kuka kmr ranta ze fita. Cikin tsawa da matsifar tashin hnkli ita fa har yanzu hajiya mommy bata fahimta ba, kanta ya kwance. "karya kakeyi ba matar ka bace,sbda bamu da labarin aurenka, ga ubanka can tsaye,besan kayi aure ba, wannan cikin na jikinta cikin shege ne, can kwartayenta suka mata, Yar iska karuwa, kana danganta kanka da karuwa, da Kuma Cikin jikinta na shege, ita kanta shegiya ce mara asali, fatsika, sekin gayamin waye yau ya Miki cikinnan..." Ta karashe Hadi da tsugunnawa zata dauko belt din Daya fadi daga hannunta, kawai daurewa takeyi Amma tashin hnkli da take cikin ya isa, har bata gani sosai, tazama kmr mahaukaciya, sbda ta fuskanci akwai gaskiya a lamarin, sannan tasan Aeezad baya karya komin zafin gaskiya haka yake furtata, a kalamansa ba wasa a ciki. Ta daga bulalar zata saukewa nabeelah, Kafin bulalar takai jikin nabeelah, aeezAd ya rike bulalar ya ajiye nabeelah ya tashi tsaye, ya watsawa hajiya mommy Wani irin lafiyeyyen marirrika a kuncinanta duka biyu, seda falon yayi amsa kuwwar marin, ji kake fassssssssssssssssssssss! Fassssssssssssssssssssss!! Nan fa kowa ya dawo hayyacinsa Alhaji sunusi na gani yanaso ya dakatar Amma ya kasa, ji yayi duk jikinsa ya rike ya kasa katafus, Abu de Kmr a film ko a Hausa novels. Nan take Hajiya mommy tajiyo kukan karnika a kunnuwanta abun ya wuce tajiyo kukan tsintsaye, axabar zafin marin ya isa, kukan karnika kawai ke mata amsa kuwwa a kunnuwanta sbda tsabagen azabar marin daya gigitata, ya rudata, ya kid'imata, hakoranta na gefe da gefe suka ya dauka ji kake kauuuuuuuuu!! Nan take taji faduwar hakoranta hudu, sbda azabar zafin marin dayayi mata, seda hakoranta biyu-biyu suka fita daga gefe da gefen bakinta Kuma duka turame ne suka fita. Falon fa ya kuma rikicewa da gulmar siriki ya mammari uwar matarsa a gaban jama'ah. Na'eema ta tashi tsaye cikin zafin nama dai-dai Aeezad nacewa "Kar wadda ta Kara shegantamin ciki, saboda cikina ni nayisa da kaina Kuma banyi saa seda shari'ah musulunci ta aminta nayisa...wannan Marin Dana miki hajiya mommy somin tafi ne, ki jira sauran azabata keda yarki da duk wata halitta dake falonnan, bana yafiya a kan mommyna, sbda ban taba San wata halitta kmr ita ba, duk wanda ya tabamin ita wlhi sena tabasa ko waye shi..." Toh fa Nan take kowa yasha jinin jikinsa, tunaninsu ko binsu zeyi da mari, Aiko da Nan take dole wata ta fadi ta mutu. Na'eema ta karaso ta cakumi wuyan Aeezad tana fadin "Wallahi baka Isa ba, kaidin banza dazaka mararmin uwa a gabana, waye Kai? A Kan wannan karuwar banzar zaka mararmin uwa, anje an debo cikin waje an mako
Chapter 97 · 0% Book details