Sashe 87
Namijin Zuma Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
farka aeezad ya fita ya siyo mata duk abinda yasan tana iya ci dama wanda bazata iya cinba, Sbda doctor tace a nemi abinci kusa, inta farka a bata Wani Abu tasa a bakinta ko yayane. Allah Allah yadingayi yadawo,Yana dawowa dai dai 11:30pm, ya tadda ta farka, se sannu big hajiya da aunty hafsat ke mata, har yanzu de kugun nata ciwo yake mata, Amma tasamu sassauci kadan, sannan taji dadin baccin datayi.. Ya karaso ya rungumeta Yana mata sannu, securities se shigowa sukeyi da ledojin Dayayo siyayyar ciki, suka gama suka fice a dakin Aeezad duk yabi ya kakkare nabeelah yadda bazasu ganta ba, Amma sun mata ya jiki aunty hafsat ta amsa da dasauki. "meke Miki ciwo ynzu mommy?'' Aeezad ya tambayeta. A hnkli tace "Kuguna da kaina..." Duk tayi ligi ligi kmr wadda tayi 1month tana jinya. Ya duba agogo yace "Yanzu doctor zataxo ta kara dubaminke mommy, in Bakiji yadda kkeso ba semu chanza asibiti, ko kuma bar kasarma in kaiki inda za a dubaminke sosai mommyna, ki kwantar da hankalinki Nima ciwon na tabani mommy, sannu mommyna mgnin kukana, sannu farin cikin rayuwar Ahamad Sunusi. ." Ko kunya beji yake mata wannan kalaman a gaban big hajiya da aunty hafsat, se tabasa nabeelah keyi alamar ya bari akwai mutane a dakin, Amma kmr tana Zugasa se famar rungumota yakeyi yana jawota jikinsa. Ya lallabata taci ayaba, se Kuma taji ayabar ta mata a baki Dan haka taci sosai, tana gama ci doctor Tashigo dakin, nurse na biye da ita da file din da aka budewa nabeelah a hannunta. Suka gaisa da Doctor , nurse ta gaidasu Hadi da tambayarsu yame jiki suka amsa da dasauki. Doctor ta matso kusa da gadon nabeelah ta tambayeta ya jiki nabeelah ta amsa da dasauki. Doctor ta tambayeta yanzu meke damunta? Nabeelah tace kugunta ke cowo..' doctor tace ze bari insha Allahu, yawan sex ne ya kawo haka, nabeelah tayi kasa da kanta, su big haiya aka kara bude kunne. Doctor ta kalli aeezad tace "Kaine mijinta?" Aeezad yace "A,..." Doctor ta bude wata yar takadda data rikota a hannunta se Kuma ta amshi file dn dake hannun nurse ta kalli nabeelah ta kalli Aeezad, idanuwanta na kan Aeezad din kana tace "Amma kasan tana dauke da ciki na tsawon wata hudu da kwana daya kou?'' nabeelah tayi hanzarin kallon doctor jin abinda tace cikin matukar kidemewar gigicewar fitar hankali me tattare da fitar hayyaci Wanda ke bayyane da tashin hankali karara a kan fuskarta, Nan da Nan ta firgice a zabure tace "CIKI!!!!!!????" da karfi tayi mgnr idanuwanta kaf a waje, takai hannunta na hagu ta dafe kirjinta yayinda zuciyarta tayi wani irin mummunan bugu har sau biyu. This book is 1k 08101626484 [7/18, 8:25 PM] SAFIYYA: NAMIJIN ZUMA Kowa ya ankare da yanayin da nabeelah tashiga amma babu wanda yabi ta kanta , sbda farin ciki, Aeezad yafi kowa farin ciki ji yakeyi kmr bashi ba, kmr a mafarki, ya kamo hannun doctor tace pls doctor are you serious nabeelah na, nada ciki? Doctor da fuskarta ke dauke da mamakin wai basu san da cikinba? Harshi me cikin, abun ya bata mamaki har tsawon 4month. Yeah sir cikine da matarka har tsawon wata hudu juyowa Aeezad yayi ya kalli nabeelah wadda bakin ciki ya turniketa kmr zata hadiye zuciya ta mutu sbda bakin ciki da kunya, ita Sam bata shirya amsar cikin d anda ta raina ba, kuma ma da wani ido zata kalli duniya? AlhamduLillah Aeezad ya fadi a bayyane, idanuwansa suka ciko da kwallar farin ciki mara misaltuwa, nan take ya zube yayi sujjadar godiya ga ubangiji , yana kuka yanama Ubangiji godiya daya bashi abinda ya jima yana nema., tako ina yasan Aurensa da mommy ya cika, daurin Auren da Akayi a babban masallacin sultan bello, inda Aeezad yace shine waliyyin amarya seda akazo daurin Auren Malam yace ai bazeyu wanda ze auri mace yazama waliyyintaba, a nan de babban malamin yazama shine waliyyin amarya a matsayinsa na babban me shari ah kuma babban malami a masallacin, Zaks shiya zama waliyyin ango, shi tamkar dan uwa na jini yake ga Aeezad. Bayan haka, kuma ya sanar da mahaifiyar nabeelah bayan tazo dubasa a asibiti dabeda lafiya, dayake ummih me fahimta ce kuma burinta nabeelah tayi aure, nan ta fahinta kuma ta amince, amma taace Dangin baban nabeelah sune damuwa zasu iya cewa basu amince ba Aeezad yasan su sbda ya taba zuwa gaidasu dayaje kasar shida mommy, dan haka ya bawa ummih kudade dayawa yace inta koma gida ta basu injisa duk sun sanshi sbda dayaje ya jikasu da kudi sosai, yanada alheri, shi a kn mommy ba abinda baze iya ba. Duk a boye sukayi hakan, kuma ya shaidawa ummih karta gayama nabeelah kuma karta nuna mata, ummih ta musu addu i sosai, dasa Albarka kuma ta barwa cikinta sbda batasan dalilinsa dayace karta nunawa nabeelah ba, ita a duniya sun gama mata komi shida mahaifinsa , ba abinda Aeezad Ze nema a gareta bata masa ba in har tanada iko da abun, kuma da abun kunya ai kwara irin wannan Auren dade a kawo mata abin kunya, kuma ta kula Aeezad nada rawar kai ze iya aikata komi, Gashi koda kashe nabeelah yayi basu isa su masa komi ba, saboda yanada kudi kuma yanada power ita a bangarsn ummih Aeezad ya gama mata komi sbda wannan tamkar rufa mata asiri yayi daya auri yarta. Da ummih zata tafi har lambar limamin daya daura musu auran ya bata kuma ya kirasa a gabanta ya tabbatar mata da tabbas shiya zama waliyyin nabeelah, kuma akwai shaidu dayawa. ummih taji dadih sosai,dana koma Niger ta sanar da yan uwan mahaifin nabeelah a fari sukace basu aminta ba, seda ta fada musu waye Mijin da kuma abun Arzikin daya basu kana suka amince da Auren suka sa albarka, daman Sam ba mutanen kirki bane su , basu taba taimaka mata dako Sisin kwabo ba bayan rasuwar Mijin nata, kuma suma tankar yan uwa suke a gareta, sbda Auren zumuncine tsakaninta da baban nabeelah. Shiyasa shifa Aeezad hankalinsa kwance a kn nabeelah babu wanda ya isa ya hanasa zaman Aure da nabeelah, yanzu de mahaifinsa ne matsala, shima kuma be maidasa matsala ba, sbda malamin babban me shariah ne, yasan daddy ma ba dmwa bane hajiya mommy da naeema suna babban case din dake gabansa. , big hajiya se washe wawulo takeyi tace Alhamdllh yafi sau ashirin, aunty hafsat kam baki har kunne, ita knta doctor da nurse din se murmushi sukeyi, suna Tayasu farin ciki, nabeelah kam ta hade rannan gam, se tunanin tunani takeyi, kan asirinta ya tonu a duniya, zuciyarta ta cunkushe Sam bata farin ciki ji takeyi daman cikin ya bare ynzu, babban tashin hankalinta yazata kalli mahaifiyarta da wannan abun? Uwa uba kuma Dangin mahaifanta da Alkhairi baya kawosu gidan. Se kallan big hajiya takeyi Tana kallon aunty hafsat su se murna sukeyi ba kmr ma uban gayyar da tinda yayi sujjada be dago ba, seda yayi 10mnt yana kuka, kana ya dago , AlhamduLillah taki barin bakinsa, ya karaso ya rungume aunty nabeelah se faman godiya yake mata cikin sambatu, be taba farin ciki kamar wanda yake ciki ba a yau. Nan take yayima doctor kyautar kujerar hajji, itama nurse ya mata kyautar kujerar hajji,. Suka dinga godiya nurse harda kwallah sbda farin ciki, daki de ya rikice da farin ciki Aeezad se murna yakeyi aunty hafsat da big hajiya ma ba a barsu a baya ba, nabeelah kam bakin ciki suke kara mata in suna murnar nan ta kasa hada ido da kowaccensu sede tayita satar kallansu kmr barauniya. Har wuraren 2;pm kana doctor ta fice a dakin ita da nurse se murna sukeyi kafin doctor ta fita tace da Aeezad ya sameta a office zuwa gobe. Ranar de kwana akayi ana farin ciki da murna, har seda sukayi sallar asubahi kana suka kwanta, drip din daman ya kare tin asubahi aka cire mata, ta kwanta ita kan ta kasa bacci, se kallan cikinta takeyi, tana ayyano yadda za ayi ta rabu da wannan cikin kaddarar dan ita bazata iya da wannan abun kunyar ba. Tini aeezad ya Kira mahaifiyar nabeelah ya sanar da ita, tayi farin ciki sosai, duk nabeelah bata sani ba, daman shi yana boyewa ne sbda iya wuya kar nabeelah ta gudu ta barsa, yasan akwai matsalolin a gabansu yana tsoron in komi ya bayyana kar nabeelah ta koma Niger ta barsa, ynzu kuwa yasan bazata iya barin gidanba sbda tana tsoron inta je can mexatacema mahaifiyarta. After 2days , Aeezad na bawa nabeelah kulawa ta musammanma ji yake da ita tamkar kwai, ya rasa Ina zesata dan murna, aunty hafsat da big hajiya sun fahimci nabeelah bata murna da samuwar cikin shide gogan Sam be fahimta na farin ciki ya hanasa ya fahimta a ganinsu Aunty hafsat kenan , basusan yana ankare da komi ba. Kwanansu uku a asibitin aka sallamesu bayan doctor ta jaddada ma Aeezad banda sex ya barta harnan da 1month, sannan Banda aiki dayawa, banda Yawan tafiya me nisa, sannan adinga barinta tana samun bacci sosai, a takaicede an bata bed rest. Aeezad har rubutawa yayi sbda beso ya mance ko abu daya gudun kar cikinsa ya zube ji yakeyi daman ana daukar Cikin ya dauki abinsa ya rike kayansa,. Zaks ma tini yasani shima yayi farin ciki sosai, dashi aka dinga jinyar nabeelah a asibitin, , kafin Subar asibitin Aeezad yayi kyauta kudi yafi millions of naira. kyauta kawai yadingayi kmr besan zafin kudi ba. Har gida seda yasa aka sake ma maman nabeelah sabo a niger ya zuba mata kayan alatu, bayan sun isa gida yau kawai nabeelah taga mamanta ta kirata ta tambayeta ya jiki, nabeelah tace dasauki, daman tasan bata da lafiya tin randa aka kaita asibiti Aeezad ya sanar da ita aiko se Kira takeyi dasuna asibitin nabeelah ta kula mahaifiyarta na Cikin farin ciki amma batasan Kona meye ba. , nunawa kawaj Ummih keyi kmr batasan komi ba. Ummih tace tayima Aeezad godiya.. se a nan nabeelah kejin ya chanza musu gida har mota yasiya ma ummih da dreva, ta kallesa se kimtsa dakin yakeyi tinda suka dawo yake tsaye sbda beso tayi aiki