← Book details Namijin Zuma Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 107

Sashe 96

Namijin Zuma Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ajalinki wannan cikin sede ki haifo shegen cikin naki a kabari.., Cewar hajiya mommy. Yan falon se kara se zugawa yakeyi cikin sigar gulma, hajiya naja atu ita kadai ce keta aikin bada hakuri taki daddara, ita de gaskiya da sauran imani jikinta. Nan da nan falon ya rikice da hayaniya tako ina. Hajiya naeema da hajiya mommy se aikin dukan nabeelah sukeyi wadda keta ihu har yanzu, tini jikinta ya rufe da azabar zafi sbda sun faffasa mata jiki tako ina, har fuskarta ta fashe se jini kawai ke fita a fuskarta da wasu sassa a jikinta , rigar jikinta me Haske ce, dukta baci da jini,farar fatar nan tata tayi red sosai ba karamin duka suke mata ba, a zuciyar nabeelah ta kudirta ko kasheta zasuyi bazata gaya musu waye uban cikin ba, sbda ta tabbar in sukaji, tabbas wuta kawai zasu hada su sata ciki. Hayaniya Alhaji sunusi yaji wanda shigowarsa gidan kenan, ya fito daga mota yaji hayaniya tayi yawa, cikin hanzari ya nufo part din hajiya rafi ah sbda ya fahimci hayaniyar bata lafiya bace, yana shigowa falon yaga abinda ke faruwa, kokarin dakatar da hajiya rafiah yayi amma taki dakatawa tayi ma kmr bata San ya shigo falon ba, shi Sam bema kula dawa ake dukanba balle ya kula da cikin jikinta. Kawai de yaji hajiya nata fadin Sekin gayamin ubanwa ya miki cikin nan na jikinki? Sune kalaman dake fitowa daga bakin hajiyar, nabeelah kam tin Tana ihu ana ji har muryarta ta disashe yazamana tana ihun amma bame ji. daman kwance take kasan tiles din se kara rirrike cikin jikinta takeyi, har yanzu duk azabar da takeji ta kasa sakin cikin jikinta. Duk yadda Alhaji sunusi yaso Ya dakatar dasu abu yaci tura , yayi-yayi ma ta tsaya ta masa bayani amma ina, seda kyar naeema ta tsaya ta masa bayani se yanzu ne ya kallah yaga ashe nabeelah ce ga uban cikin yayi Totso a jikinta, naeema na gama masa bayani suka ci gaba da bugunta kmr wadda tayi musu wani mummunar kisan kai, Kai kace Ubangijine ya aikosu su daketa. Alhaji sunusi ya zubawa nabeelah ido cikin mamaki, shide dan bayadda zeyi ne amma a ransa yaji bayason dukan da Ake mata, dukda lefin datayi babba ne amma shi a ransa beji ya tsaneta ba,. Duk yadda yaso ya dakatar dasu abu yaci tura, yan falon de se kallonsa sukeyi daman duk sun San shi Mijin tace ne Sam basuyi mamakin danya Hana matarsa taki hanuwa ba a bainannassi. Hajiya rafiah bata taba bawa Alhaji sunusi rai ba kmr yau ganin yadda yayi-yayi ya hanata abinda takeyi ta masa bansa a karshe ma sede ta daka masa tsawa tace Ba ruwanka kaji kou!! In bazaka iya gani ba ka fita! Yaji zafin yadda ta masa hakan a gaban kawayenta, inda sabo yaci acee ya Saba Tasha masa hakan yafi a kirga a cikin mutane, ba kmr ma kawayenta, amma na yau ya masa zafi sosai. Paid book ne 1k 08101626484 NAMIJIN ZUMA 47..... Ba karamin gudu Aeezad yasa dreva dinsa ke shararawa ba a kan shantalelen ti-tin daga Kano zuwa katsina,. Duka motocin tawagarsa kawai gudu sukeyi a kan Ti-Ti. gabaki daya Aeezad Gani yakeyi ma Kmr basa sauri, yakagu yaga mommynsa, gashi zuciyarsa nata azalzalarsa a kanta, a jikinsa yaji kawai Wani Abu na samunta, ji yayi har jikinsa da komi na jikinsa ciwo yake masa, zuciyarsa se uban Zababbaka takeyi ya rasa dalilin hakan, cikin mummunan baccin Rai ya tsinci kansa mara misaltuwa, kawai kuka yakeso yayi sbda yaji sassaucin matsifar dake zuciyarsa a kanta, ji yakeyi daga zuciyarsa zuwa gangar jikinsa zafi rakayau Kmr ana zuba masa rushi. "Ya hayyu ya kayyum,,,!'' itace kalmar data fito daga bakinsa se Nishi yakeyi shi kadai yasan a Wani hali yake ciki. Zaks dake gefensa se Aikin kwantar masa da hankali yakeyi Yana fada masa kalamai masu sanyi Amma Ina be saurarensa sema yaji ya cika masa kunne Yana Neman hada masa tunaninsa biyu, shi Kuma yafi bukatar yayi tunani guda daya Rak a halin da yake ciki wato tunanin mommynsa shine ne abincin ruhinsa. Dasuka fara shigowa katsina suka tadda uban hold of, Aeezad ji yakeyi kmr ya sauka ya taka Zuwa gidan Aunty hafsat, harya fara kokarin sauka zaks ya rikesa da kyar ya hkra., sojojinsu suka sauka suka tsayar da kowa su suka wuce. Karfe biyar dai-dai motocinsu sukayi packing a farfajiyar gidan Aunty hafsat, a tafkeken packing space din dake gidan. Big hajiya da Aunty hafsat dasuke zaune jingum jingum a falon har yanzu ba Wanda yasawa cikinsa abinci har kwara big hajiya tasamu tasha tea, duk matsifar baccinta, yanzu baccin ya xamar ma big hajiya sede barawo. aunty hafsat taji karar shigowar motoci Cikin gidan, a matukar razane ta mike , ta lega Nan taga fitowar AEEEZAD daga mota, Daman tin kafin ta leka jikinta ya bata shine. "na bani yauni nashiga uku! Ina zansa rayuwata!'' itace kalmar data fito daga bakin aunty hafsat yayinda zanin atamfar dake cikinta ke niyar faduwa ta rikosa da kyar, daura zaninma ta kasa seda kyar se fama takeyi ta daurasa Amma Yana subucewa Sbda tashin hnkli , inside zuciyarta se azabar lugude kawai takeyi,ta tabbatar in Aeezad yazo bega Aunty nabeelah ba ita ze bawa lefi, big hajiya ta bata lefi ma Ina maga uban gayyar. "Meya faru kk fadin kin shiga uku? Me kika gano? Ko wani Abun ne yasamu Cikin jikin yarinyar?'' big hajiya dake zaune ta mike tsaye cikib tashin hankali take jeroma hafsat tambayoyin. "Aee.....za...d....ne,,,ya,,,da,,,wo"" aunty hafsat ta Fadi bakinta na rawa, ta cire dankwalin atamfa dake kanta ta ajiye kasa, azabar zafi da tiriri kawai taji brain dinta nayi, ta rasa Ina zatasa rayuwarta se Fadi takeyi ta bani, Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un Kam ta fadeta yafi a kirga, bata kai wata take daukat wata. Big hajiya a ranta taji dadin dawowar Aeezad, waNi farin ciki ya lullubeta, Daman kashe wuta seda ruwa, in ruwan beyi ba a Kasheta da wuta, Wani lokaci lalaman baya kashe bala'i, wuta seda wuta. Aunty hafsat na daga tsaye cikin mummunar fargaba da tashin hankali, big hajiya ma na tsaye,. Ya turo kofar falon da karfi kmr ze cireta, seda Aunty hafsat ta Kuma tsorata taci uwa zuciyarta zata buga, Nan take Wani zazzabi ya lullubeta, ta kama rawar d'ari, ko a iya Haka tashiga Azaba zazzabin da takeji bata taba jin irinsa ba se Yau. ya Sako kafafuwansa Wanda suke sanye da farin cilifas irin na Yan hutu, Sam ma besan silifas bane a kafarsa, a mota ya cire takalmin Daya sako, ya Saka slifas din ba tare ma Daya Sani ba. Zaks ke biye Dashi a baya. Idanuwansa suka sauka a kan Aunty hafsat, da big Hajiya dasuke tsaitsaye, tini ya hango uban rawar da jikin Aunty hafsat keyi, a fuskokinsu ya fahimci ba lafiya ga gidan yayi Wani silent kmr gidan mutuwa TV a kashe. "Ina mommy? Meya samu mommyna? A Wani hali momnyna take ciki? Meyasa kika kashe wayarki maman noor? Meyasa kika koma kika kashe wayar big hajiya Kuma ta mommy ma a kashe? Dan girman Allah Ayi gaggawan gayamin a Wani hali farin cikina na duniya take ciki Dan Allah na rokeku? Mommy na cikin wani hali inaji a zuciyata...a gayamin meya sameta? Ina take inaso in ganta? Jikina na bani bata gidannan ko ta gudu ne zuwa kasarsu? Dan Allah a gayamin" Aeezad ya jefo musu wannan tambayoyin masu rikita zuciyar Aunty hafsat, Hadi da magiya. , Nan take zuciyar Aunty hafsat tayi Wani mummunan bugu,. "Wayyoh na bani Na mutu yau ni hafsat!'' ta fadi a zuciyarta. Big hajiya ce ta kwashe Labarin komi ta gaya masa. Wani jiri luuuuuuuu ya nemi daukar gogan,seda Zaks ya rikosa, ya hadiye Wani yawu me mugun daci da kauri daga bakinsa zuwa cikinsa. ya tsurawa aunty hafsat idanuwa, ita kanta na kasa Daman tini. Cikin shauting da karadi da matsifa da tijara Aeezad ya fara cewa "Ni Zaki munafunta? Sannan kika kashe wayarki kika dawo kika kashe ta hajiya mommy? Wallahi kin zalinceni kin munafunceni, meyasa tin lokacin Baki kirani kin gayaminba, meyasa ba a gayaminba,Wani irin iskanci ne wannan, kika kashemin waya sbda Ke munafukata ce?!!!! Wlhi se kinyi nadamar dole zakiga another side of me, baruwana dake jininace, wlhi senayi maganinki!!!!! Kinci amanata, mena miki? Wlhi in Wani Abu yasamu mommyna bazan yafe miki ba, bana yafiya a kan lamarin mommyna!!!!...'' ya karashe kmr ze rufeta da duka seda kaf falon suka amsa da kalaman sa, Nan take kwallah suka wanke masa fuska, itama aunty hafsat kwallah tashigayi kalaman kaninta gareta sun matukar Yi mata zafi me tsanani. cikin kuka tace "Ka gafarceni blood , nasan zaka ga kmr na munafunceka, Ina Neman Afuwarka tsoro ne ya hanani Kiran k...." Kafin ta karasa kawai taji saukar Mari a fuskarta, seda ta zube kasa sbda azabar marin dataji ya shigeta shiga me tsanani, Yana Shirin kara Kai mata Wani irin duka harda dunkule hannu cikin zafin nama, big hajiya na shirin zuwa ta rikosa sede tasan bazata iya ba, Zaks yayi hanzarin ya rikosa Yana fadin "Sir kayi hkri dan Allah kasawa zuciyarsa salama, yanzu kamata yayi mu nufa inda Mommy take domin muga ya lafiyarta take..." Zaks ya jashi zuwa kofar fita a Falon sbda inya barsa Yana iya sumar da Aunty hafsat, domin Zuciyarsa a zafafe take, se turiri yakeyi shi kadai. se uban turiri kawai yakeyi, kmr ze hadiye zuciya ya mutu sbda axabar zafin zuciyarsa haka yakeji. Dai-dai suna Shirin ficewa a Falon Aeezad ya juyo ya kalli Aunty hafsat daketa faman kwallah ta dafe kunci yace "Allah ya isa wallahi bazan taba yafe miki ba!" suka fice a falon,big hajiya ta biyosu Daman sanye take da hijjabi. Wannan kalmar Daya fadi mata ta Allah ya isa ba karamin kara dagawa Aunty hafsat hankali tayi ba,Nan take tashiga tashin hankali, ta fuskanci kamar ma Aeezad Yana ganin da hadin bakinta hajiya mommy tazo ta tafi da nabeelah gidanta, Wani irin kuka ya subucewa Aunty hafsat, ita datasan wannan tashin hankalin zata gani wlhi da bata bar nabeelah taje gidan ba, kwara suyi bala'in daza suyi da ita, tasan de baze Kai bala'in data shiga ba yau ita da
Chapter 96 · 0% Book details