← Book details Namijin Zuma Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 107

Sashe 103

Namijin Zuma Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba Alhaji!!'' ta karashe cikin daga murya, na'eema Kam Dena cin abincin tayi, Ubangiji ne kawai yasan a Wani hali take ciki, data tuna da nabeelah matar Aeezad ce, sannan ga cikin jikinta ma na Aeezad din ne, se na'eema taji komi ya fitar mata a rai, ba ita ba har uwarta ma, ita abinda takeji ma ya wuce na Yar tata, a cikin azabar data tanadarma Aeezad harda nabeelah ciki,ta dauki alwashin inde tanada Rai cikin jikin nabeelah bazezo duniya ba. Alhajii sunusi yabi hajiya mommy da Ido, Ba tare dayace komi ba. Cikin fada taci GABA dacewa "Tukunna ma kayi bincike ka tabbatar Aurenta yayi?'' Alhaji sunusi yace "Eh tabbss nayi bincike hajiya, wlhi aurenta yayi...." Wani bakin ciki ya tokare hajiya mommy da na'eema wadda kejin kamar zata kashe nabeelah. "Tsintacciyar mage ai bata mage alhaji,,,Dan kudi ta Auresa kilama so take ta kashesa taci gado, da wuyama in cikin jikinta nasa ne, Alhaji kayi gaggawan sashi ya saketa Kuma ya mata korar kare zuwa kasarsu, shegiya ita kanta fa ta zina uwarta ta haifota...wannan abun ze taba maka martaba cikin abokanka Alhaji, ... " Hajiya mommy ta fadi cikin kissa da makirci. Alhaji sunusi ya jinjina Kai, shide yasan nabeelah ba Yar Zina bace. a zahiri yace mata "Za asan yadda za ayi, Nan Bada jimawa ba..." "Gaskiya Ayi gaggawan yin yadda za ayi. .Kuma ai yakamata ace shi Aeezad din yaxo ya bawa na'eema hakuri Nima ya bani hakuri kan cin mutumcin Daya mana a kan Wannan shegiyar yarinyar jinin karuwai Yar iskar yarinya! Yan kasar gadon asiri!" Alhaji sunusi yace "Dole zezo ya baku hakuri hajiya...." cikin sanyi yake mgna inde Yana gaban hajiya bashi da katafus. "Yayi gaggawar zuwa..." Cewar hajiya mommy. Alhajii sunusi yace "Toh yadda kikace haka za Ayi hajjajuna..." Murmushi hajiya mommy tayi a zuciyarta tace "Aiki na bugaka Alhajin Allah.." Alhaji sunusi ya kalli agogon dake manne a hannunsa kana yace "Zan fita YNzu Amma ba jimawa zan dawo..." Hajiya mommy ta hade Rai kana tace "Ina zakuje? Gaskiya ba yau ba sede gobe?'' "Pls meeting zamuyi da Abokina Bazan juma ba..." Cewar Alhaji sunusi, da yayi mgnr cikin magiya. Da kyar de hajiya ta barsa ya fita, dreva yajasa zuwa gidan Aeezad,. Alhaji sunusi na fita na'eema ta kalli mahaifiyarta tace "Mommy yadda daddy yake Miki Nima haka nakeso Aeezad ya dingamin, a maidaminshi se yadda nayi dashi Dan Allah mommy, ita Kuma Yar bura ubar Nan a haukatata, ita da Cikin a kaita can birnin seen ta karashe rayuwarta a can,ita da shegen cikin jikinta,..." hajiya mommy tayi murmushi tace "Me kikeci na bakinki na zuba? Fiye da haka na tanadar ma yarinyar Nan domin nafijin haushinta a kan Aeezad saboda na fahimci duk Dan ita ne ya mana wannan dibar Albarkar, Amma ki kwantar da hankalinki, yarinyar de dagani ta mori malami,,Ina me tabbatar Miki se tayi nadama ai ruwa ba sa'an kwand'o bane,ko kura ta rame ai tafi gaban raini ga Kar'e, sama Tayima yaro nisa sede ya tada Kai yayi kallo, yaro besan wuta ba seya taka, Wani ma yayi rawa balle d'an makid'a, sha ruwan sanyi y'ata kmr kin jika tsumma a ruwa..." Hajiya mommy ta karashe tana Jan kwafa, ko garwashi ta hada ta jefa nabeelah a ciki bata huce ba. "wlhi mommy hankalina baze kwanta ba Sam, bacci ma seda kyar nake yinsa har yanzu Ina San mijina, mommy wlhi bashi da lefi kawai Kiyi azabarki a kan nabeelah, duk asiri ne yasa idanuwansa ya kulle ya mana abinda ya mana, ni ko kashe yarinyar Nan akayi ban huce takaiba, mommy so nake Ayi mata DUk abinda zakiyi mata , ta d'and'ani azabar duniya taji, tinda harta aurar min miji ai dole in mata azaba mommy, gashi sanadinta mutumcinmu ya zube gaban masu mutunci, wlhi mommy kiyayyar da nakewa nabeelah bazata misaltuba.." hajiya mommy tayi murmushi mugunta kana tace "Ai duk kiyayyar da kike mata be Kai wadda nake mata ba naeema, Allah de ya kaimu gobe,in mukaje asibiti Kara duba jikinki, semu wuce gun boka kawai ba a bori da sanyin jiki..." na'eema ta amshe da Amin, kiyayyar nabeelah na Kuma ninkuwa a rayukansu ita da uwarta, sun rasa ma tayaya ta shammacesu. Seda Alhaji sunusi ya tsaya Yama jikokinnsa shopping sosai na kayayyaki na Alfarma a babban boutique din da Ake saida kayayyakin jarirai Wanda Ake kawowa daga kasashen waje. Seda ya cika akwatina uku da kayayyaki na Alfarma dreva dinsa ya tayasa zaba da wata me Aiki a gurin. Ya biya akasa a booth. Suka sake tsayawa yawa mahaifiyarsa siyayyar kayyan makulashi. t kana Suka nufo gidan Aeezad,. Alhaji sunusi na shigowa falon yaga ga kugun Aeezad gana nabeelah se kara shishige mata yakeyi ga yara duka ukun a kan cinyarta, zaune take kan carpet Kuma ta daura pillow a kasanta, ta zuzzuba duka yara ukun a kan cinya, ta bawa wancan nono ta dawo ta bawa wannan nono, yaran nada lafiyar tsotso Suna tsotso sosai, danma ana hada musu da madara, saboda tsotsonsu yayi yawa, yau kimanin kwanansu takwas da haihuwa Amma sun kware a tsotso. Big hajiya na gefe tana Jira a gama shayar da yaran a batasu, ummih na can gefe itama,Aunty hafsat bata Nan tana gidanta,se wata laure itama tana zaune gefe me Aiki ce, big hajiya tasa aka kawota dazunnan daga gidan hajiya Maryam wato matar d'anta Alhaji abubakar, Se Yau big hajiya ta shaida mata komi Aiko itama ma ta shaidawa mijinta, Abu kmr almara kowa yaji dadin wannan hadin, Daman ita hajiya Maryam ta fara fahimta kwanciyar Aeezad a asibiti. Alhaji sunusi ya gaida mahaifiyarsa ta amsa fuska sake, ya bata kayayyakin ciye-ciyen daya siyo mata, se godiya take masa dasa Albarka, tinda aka haifo yarannan take ganin sauyi a gurin d'anta, gashima tanata ganinsa akai-akai gaskiya haihuwar yarannan yazo da Albarka, haka big hajiya Ke cewa motsi kadan. Ummih ta gaida Alhaji sunusi ya amsa fuska sake, besan meyasa ba inya kalleta se yaji gabansa na faduwa. Daman nabeelah tini ta gaisasa tin shigowarsa Aeezad ma ya gaidasa, ganin yadda daddy keta zuwa Yana duba yaran yasawa Aeezad jin dadih ba kadan ba. laure me Aiki ta gaida Alhaji sunusin cikin girmamawa. Ya amsa Yana kallanta Yace "Wannan fa?'' yayi mgnar da Aeezad. Aeezad ya bashi amsa da "Big hajiya ce tasa aka kawota daga gidan Alhaji daddy,zata dinga taimakawa da Ayyuka..." Alhajii sunusi yace "Toh-toh...Amma an tabbatar ta iya wankan jarirai kou?'' ya juya akalar tambayarsa ga big hajiya. Big hajiyar tayi murmushi tace "kar aje a jefa maka jikoki a ruwan zafi kou?'' duk Yan falon sukayi murmushi ba karamin jin dadih sukayi ba musammanma Aeezad, dadih na nunawa yaran SO na tsakani da Allah Sam ma be iya boyewa. Alhaji sunusi ma murmushin yayi yace "Eh wallahi big hajiya, haka akayi da Yar Abokina ta haihu haihuwar fari aka dakko me wanka, garin gasa cibiya ta kona babyn, big hajiya satinsu uku a asibiti ana fama da babyn ba karamin kuna yayi ba,,, maganin Ayi ai kar a fara, kwara a bawa hajiya ta dinga musu wanka..." Ya karashe mmaganarsa Yana kallon ummih wadda kanta ke kasa. Aeezad yayi hanzarin cewa "Nima haka nace,Amma big hajiya taki, ita ke musu wanka daddy, da kyar take bari aunty hafsat ta musu wasu lokutan . " Alhaji sunusi ya zaro idanuwa yace "gaskiya big hajiya dakin bari an dinga musu saboda naga ke ba Wani gani kike sosai ba..." Big hajiya ta amshe da "uban bana gani! A haka de na raineka, Shima Aeezad din Dan Anki bani shine Amma Dani zan rainesa... Dan haka ni zan dinga musu wankan da gashin cibi har Ayi arba'in banga me rabani da yarannan ba sede mutuwa..." "Toh ai shikenan Allah de ya tsare min..." Cewar Alhaji sunusi big hajiya ta rike Baki tana mamakin ganin yadda d'anta be kawaici a kan yaran Kuma duk kawaicinsa. Duk Yan falon suka amshe da Amin Banda nabeelah data kasa cewa komi se gyangyadi takeyi Ma ita bacci takeji, so takeyi ta gama bawa yaran nono taje ta kwanta. " Hajiya me kula da jikokina, Jeki ce da dreva Dina ya bude Miki but ki kwaso kaya..." Alhaji sunusi yayi maganar da laure Cikin girmamawa bada raini ba wai Dan tana me AIKI. Laure tayi murmushi Hadi dacewa toh ta mike ta fice a falon, a kallah laure bazata wuce 45yrs ba. Ta kwaso akwatunan ta diresu a tsakiyar falon, Nan aketa kallon kayan arziki,. A haka hajiya Maryam da mijinta, da Saif da matarsa suka shigo falon, Daman big hajiya tasa aunty hafsat ta tura musu da address. Cikin murna suka karaso aka gaggaisa, duk hankalin kowa na kan baby's,har rige rige sukeyi gun daukar babyn, se Masha Allahu kawai suke cewa Alhaji abubakar yace "Ashe haka ya kasance,,,Toh Allah yasa Albarka..." duk falon suka amsa da Amin nabeelah de a zuciya take ta Amsawa da Amin de. Nan de falo ya kicime se ganin babys akeyi da kayayyakin Arzikin da Alhaji ya siyoma babys din duk sunyi kyau kmr siyayyar mace. Big hajiya taji dadin ganin iyalansa a hade, anata nishadi,matar saif ta dauke babys ta rike sun bata shaawah sosai ta taba haihuwa Amma yaran sun rasu har Sau biyu,ji takeyi kmr a bata babys din ta tafi dasu. "Kowa de ya hallara, banda tsatson tsiya, Allah de wadaran hali irin na Rafi'ah...Sanusi bakayi sa'ar mata ba, Ubangiji de yasa da raina na ga ka auri mace ta arziki.." Big hajiya ta Sako wannan maganar ana cikin Hira. Alhaji sunusi yayi Shiru kawai shida kansa yasan macensa bata kirki bace Amma ba yadda zeyi ne. "Dafatan de baka sanar da ita an haihun ba?'' tayi mgnr da Alhaji sunusi again. Ya daga mata Kai alamar Eh. "Toh kar inji kar in gani, domin kana sanar da ita wannan haihuwar,seta shiga ta fita ta kashesu, danma kullum se uwarsu ta musu Azkar An tofesu tako ina, bade mutum ba ko aljan be isa ba Insha Allahu, mun rike ubangijin da baya bacci, kema nabeelah ki dinga yawan askar din safe da rana da dare, koda Baki da tsarki, ki dinga zama da Alwala da''iman kinji kou?..." Nabeelah tace "Toh..." Daman kullum cikin Alwala
Chapter 103 · 0% Book details