Sashe 75
Namijin Zuma Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tanada mugun kwad ayi ko kisan Kai akayi a gabanta inde aka bata kudi zatayi shiru. Zaks yaja motar suka fice a gidan ya kalli Aeezad dake gaban motar yayi bending, duk jikinsa ya masa wani iri kewarta ta rufesa, Sam be iya fushi da ita komi zata masa, ji yakeyi kmr ya koma ya zauna gidan shima yayita kallanta, yariga yayi mugun sabo da ita a sati dayan dasukayi tare, ko zata dinga zaginsa Tana dukansa shi yana santa a haka kuma yanasan zama da ita. wani gida zamuje ? Zaks ya tambayi Aeezad din, ba tare daya kallesa ba yace Kaini gidana kawai, inaso doctor ya dubamin hannuna zafi yake maka? Zaks ya tambayesa aah,,,ba Ayimin allurata ta safe ba ai Zaks yace Okay inaga shiyasa doctor keta kirana se yanzu naga miss call ba tare da Aeezad ya kara cewa komi ba har suka isa gidansa, a packing space yaga motar naeema shi yana manta da ita se yanzu daya ga motar, tin randa tabar gidan taje gidan mommy sukaje gun boka a kan a musu aiki nabeelah tabar gidan boka yace an gama a bashi nan da 2weeks duk abinda ake ciki ze kirasu. Zaks nayin packing Aeezad ya fita a motar. Zaks ya karasa packing din motar ya fito yabi aeezad daya nufa falonsa,. Ba abinda kake bukata inaso in tafi gida ne Zaks yayi mgnr da Aeezad bayan sun iso falon, shirin hayewa upstairs ma Aeezad yake, sbda so yakeyi yayi wanka ya kwanta ya huta. Kaje ka dawo zuwa anjima after la asar ko after magrib sbda zaka kaini inga mommy Aeezad yayi mgnr byn ya taka matattala hudu, ya juyo ya fuskanci Zaks din. Fuska dauke da mamaki Zaks yace Wace mommy? Aeezad ya watsa masa wani kallo yace wacce kasani Zaks yace naga yanzu muka dawo daga gurinta, ka barta ta huta pls aboki, kodan sbda big hajiya tasa ido Ina ruwana da idon datasa ba abinda ya dameni ko hanci tasa wlhi bata isa ta hanani naje gun matata ba, Kai in duk duniya zasu taru basu iya su hanani zuwa ga mommy ba,,, Cewar Aeezad. Zaks yaja bakinsa yayi shiru Aeezad ya haye matattakalar yana fadin ka gayama doctor yazo ya jirani a falo, inyi wanka da sallah, se in fito yayimin allura Zaks yace toh, ya juya ya bar falon, ya nufa side din da doctor haphis yake ya isar da sako kana yaja motarsa yabar gidan. bajimawa Aeezad yayi wankan ya fito duk jikinsa ba ddh kmr an zare masa laka, ya shirya cikin kananun kaya marasa nauyi riga da wando iya guiwa kalar sky blue, yayi sallar azahar kana ya sakko falon kasa inda tini doctor ke jiransa hannunsa rike da charbi yana lazimi se zuba kamshi yakeyi, fuskannan tasa tayi fayau da ita. doctor ya gaidasa ya amsa, ya zauna kan kujerar 3ctr doctor ya duba hannun ya masa allura a baya ya koma ya kwanta kan kujerar 3ctr din idanuwansa na kan TV Amma zuciyarsa na kan mommy, da yanzu suna tare, tunawa yashiga jiya war haka yana tare da ita. "Ubangijine ya jarabceni da wannan azababben SON.." Aeezad ya fadi a ransa. doctor ya masa Allah sawake Sam be amsa ba sbda bejisaba, yanacan duniyar tunanin mommy. ftini doctor ya fice a falon da kayan aikinsa a hannu, a farfajiyar gidan yaga Hajiya naeema wadda ke tafe cikin isa sanye take da jallabiya nude color skin dinta na hutu se walwali yakeyi. Doctor haphis ya gaidata sbda yasan itace matar Aeezad din, sama sama ta amsa ta nufa part din Aeezad shi kuma doctor ya nufa part din da aka basa, yana tafe yana mamakin halin naeema tin tini in yana gaidata seta dinga amsawa da kyar, tin zuwansa gidan da 2days yaganta a gidan, wato ranar dasukaje gun bokan gidan hajiya mommy ta kwana har kwanaki biyu, tana gidan Alhaji sunusi ya gaya mata Aeezad ya kebance kansa sbda Yana bukatar hutu, Sam na'eema bata yadda da hutun da yaje yiba sbda baya daukar wayarta, Kuma gaskiya ba hk yake mata ba, ko a Wani hali yake yana daukar wayarta, daman ta tabajin kishin-kishin mijinta ya taba ajiye karuwa to Tasha gun karuwar yaje yanzu ma, Amma tayi shiru da bakinta seta tabbatar seta gayama hajiya mommy a dauki mataki, gabaki daya ma ya chanza mata, dace ada ne inya ganta jikinsa har rawa yakeyi yacita, Amma yanzu shiru,. Ta window dinta taga dawowarsa gidan yanzu. Ayi hkri da typing error. Saadatubintuabdullahi Big hajiya ta kalli nabeelah wadda keta sadda Kai kasa ta tabe baki tace ke daganin idanuwanki baki da gaskiya Ina ganinki kmr ta kirki ashe ina ohhh! nabeelah ta kuma sadda kanta kasa se taji wata kunyar ta kuma rufeta, ita yanzu batasanma da wata fuska zata kallesu ba, musammanma big hajiya, gabaki daya de Aeezad ne yaja mata wannan matsifar, dazata shigo falon ma kawai dakiya tayi ta shigo Allah kadai yasan ya takeji a zuciyarta. Aeezad ya kalli big hajiya da idanuwan rashin kunya yace me tayi na rashin gaskiya? Karki kara ce mata mara gaskiya wlhi in kinasan zaman lafiyata dani Big hajiya ta taso masa sannu ubana,tsinemin inbi duniya,,,ai kaine babban mara gaskiyar shege kayi da idanuwa kmr na yayan karuwai, gidan uban wa ka dauketa ka kaita? Kade ja mana abun kunya a dangi Aeezad ya amshe da Da nayi me? A kan wata karuwar aka kamani nasa al aurata? Dukkaninsu seda sukaji kunyar abinda yace amma shi ko a jikinsa, big hajiya ta amshe Tana kara taso masa to ita wannan ina ka kaita? Dan ubanka,. Har kanada bakin mgnr banza, Yarinya me tarbiya ka bata mata tarbiya, daman tin a jirgi naga wani al amari, kawai kallonka nakeyi wannan mgna dole a danganata da ubanka gaban nabeelah ya yanke ya fadi Jin abinda big hajiya ta fadi na karshe, har Zaks seda ya tsorata. Aunty hafsat ma haka sbda tasan karamin aikin big hajiya ne ta fallasa kowa yaji, daman kullum se mita takema Aunty hafsat kan wai Ina Aeezad yakai nabeelah , aunty hafsat tace bata sani ba itama, wuni big hajiya take Tana cancana maganar Tana cewa gaskiya iskanci Aeezad yajeyi da nabeelah, sbda taga wani abu a jirgi shikam Aeezad abinda big hajiya tace ko a jikinsa ya daga kafad a yace Se akayi me Inkin fad a ma daddy? Ya karashe yana kuma tabe baki shi ko wa zata gaya mawa ta gaya mada. Aunty hafsat de Tana gefe tayi shiru. Big hajiya ta sake hayayyako masa zakaci uwarka da ubanka ni kake gayama se akayi me? Kasa na hasala wlhi wannan mgna kmr a bakin Matarka da ubanka gaban nabeelah da aunty hafsat da Zaks ya kuma yankewa ya fadi ba kmr ma nabeelah seda ta hadiye wani azababben yawu. Aeezad dako a jikinsa ya bude baki zeyi mgna aunty hafsat ta rigasa dacewa yanzu in kika fadi kice me big hajiya? Kidena irin wannan abun gaskiya shaidar zirr haramun ne big hajiya ta dawo kan aunty hafsat ta watso mata harara Hadi dacewa SANNU kwankwasashiyar muna fuka, Yar shaidar zir din bura uba, kema kallanki nakeyi kawai nasan Kinsan komi,,,yaza ayi ace, namiji ya dauki mace tsawon sati daya, wannan kowa yaji ai yasan akwai lauje cikin nad i, wannan ai fasikancine Aeezad ya amshe da Aise ki nunamin inda nayi fasikanci, big hajiya sharrin Zina kikeso ki laqabamin kuma baze yuba sbda baki kamani Turmi Cikin tabarya ba aunty hafsat ta amshe da Ai shine, gaskiya big hajiya kidinga shiru a abinda baki sani ba aunty hafsat ta dage tana kare Dan uwanta. big hajiya ta amshe da Aise a hanani mgna bayan Allah ya tsagamin baki, munafukan banza, har Kai zakariyya tantirin munafuki ne kaine jagoran yan iska, shugaban fatsikai ta karashe Akalar maganarta da Kallan Zaks wanda yaketa kara makalewa a baya, Jin abinda big hajiya ta fadi ya karasa Zaks ya kara nokewa a baya duk mgnrsa yaki cewa komi. Big hajiya taci gaba dacewa Kana ciwo ashe ciwon karya ne na munafunci na makirci tinda ka iya iskancin big hajiya tayi mgnr Tana karewa nabeelah kallo dashi uban gayyar datayi mgnr dashi Aeezad kenan. Ba tare da Aeezad yabi ta kan big hajiya ba yaja hannun nabeelah suka nufa dakin nabeelah, nan ya kuma bawa nabeelah kunya taji ina zatasa ranta Gashi da karfi yajata ba halin ta turje. Big hajiya ta kuma binsu da idanuwa hadi da Jan salati, ita fa abun ya fara daure mata Kai, se ynzu ta kuma lura da tafiyar nabeelah ma ta chanza, abinka da tsoffi tini ta fahimci wani abu, aunty hafsat ma data Bisu da idanuwa tini ta fahimci meya gudana, a ranta de adduah take tayi Allah yasa da Auren akayi, tasan ma tinda yace ya aureta to tabbas ya aureta din sbda shi baya karya, komi gaskiya yake fad i duk d acinta. "Tayaya akayi auren?" Itace tambayar da aunty hafsat ke yawaitama kanta. Biri yayi kama da mutum, ohhh ni jikar ahmadu, yauni nashiga uku! Meke shirin faruwa a zuri ah ta, amma wannan yaran d an iska ne na gaske, wannan shine anyi amai an lashe, toh wlhi be isa ba, wlhi inde har ya lalata baiwar Allahnnan seya aureta , Kai daganin fuskarta kasan ba ruwanta ba a san ranta bane komi ya afku wannan yaro shine zakka a zuriahta,, ni wannan shaani ya dauremin Kai ohhh! aunty hafsat de tayi shiru dan ita bata sanar da big hajiya Cewar Aeezad yace ya auri nabeelah ba kmr yadda ya gargadeta. Big hajiya de Tana mita kuma Tana duba kayayyakin da aka shigo dasu, har tazo kan kayan ciye ciye ta bude wani chocolate tasha ta lumshe ido saboda dadih, Zaks ya kalleta suka hada ido da aunty hafsat sukayi m urmushi. Tsufa labari Cewar zaks. Big hajiya dake Shan chocolate dinta ta dago ta kalli zaks tace Uwarka da ubanka ne tsoffi.. Zaks yace godiya nake big hajiya, karde ki shanye chocolate din duka sbda kaf kayannan na mommy nabeelah ne tinda uwarka da ubanka ne suka siya ba,,,naga de ai jikana ne ya siya, shege munafukai kuna ce mata mommy, mommyn karya kou? Makirai aunty hafsat ta