Sashe 3
Namijin Zuma Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
kwafa kawai yakeyi sau ba adadi. "Aikin banza kawai bani ga tsuntsu bani ga tarko,da yanzu beb na ajiye dana huta..." Ya fadi Yana me Jan tsuki se mutsu mutsu yakeyi a cikin kujerar, matsifa da bala'i na tsungulinsa, shifa sam beson damuwa, sannan yanada zakuwa, in yanasan abu kawai so yakeyi a lokacin ayishi ko yasamu a lokacin. Shadaya da minti uku dai-dai wata dattijuyar mata wadda a kalla zata iya Kai 45yrs ta turo kofar falon ta shigo sanye da doguwar rigar Abaya red, rigar ta amsheta Ainun kasancewarta fara sol me matsakaicin kyau Hadi da madai-daicin tsawo,. Tana shigowa yayinda Wani dattijo ke biye da ita a baya Sanye yake da manyan kaya, hannunsa rike da sandar dogarawa, da kyar yake iya tafiya kasancewar yanada ciwon kafa, sannan ya taba hatsari hakan ne sanadin mutuwar kafarsa, da kyar yake dogarawa. kallo Daya na masa na tabbatar yanada taddako a tattare dashi uwa uba ga cikar zati dogo neshi first class , ya manyanta sosai a kallah ya Kai 60yrs Amma yawan kudi baze bari a gano manyantar ba, nera ce kawai ke magana a skin dinsa, kyau kuwa se tsiyaya yakeyi ya fuskarsa ,a kallo Daya zaka fahimci kamanninsa da yaran dake kwance. ''A,S...." dattijuwar matar ta fadi yaynda kwayoyin idanuwanta suka sauka a kansa da yake kwance cikin kujerar, jin ta kira sunansa yasashi juyowa ya zubo mata manya-manyan jiga-jigan kwayoyin idanuwansa Masu cike da zallar kwarjini a bayanta yaga mahaifinsa biye da ita. "Haka de za a kare kullum yana gindin hajiya mommy...ban taba ganin mutum irin daddy ba shi gabaki daya from the bigining to ending haka ze kare, shiyasa kowa yasan shi mijin tace ne,ko a office .." Aeezad ya fadi hakan a ransa se Wani kara tamke fuska yakeyi ya zamo daga kan kujerar ya tsugunna ya shiga jero musu gaisuwa one by one. Hajiya rafi'ah ta amsa ba yabo ba fallasa, se wani tsumu tsumu takeyi irin na marasa gaskiya. Alhaji Sunusi ya amsa Hadi da zubowa d'annasa Ido cikin kallon SO da kauna yaketa binsa dashi,a kullum soyayyarsa ga d'an nasa baya boyuwa danma mommy tafi karfinsa ne se abinda tace ai da soyayyar daze samu a gun daddy seta ninka haka da ace babu hajiya rafi'ah. "Uban baba yau dirar sassafe kayi mana lafiya de kou?" Daddy ya tambayesa cike da kulawa da SO da kauna, a kallon dayayi masa ya fuskanci yanada damuwa. Hajiya rafi'ah ta kuresa da Ido kur tana jiran meze ce domin ita tasan tushen komi. Jin tambayar da daddy yayi masa ya dago ya kallesa a zuciyarsa yace "Daba Kai kayimin tambayar nan ba dakaji amsa zuku-ku ma kuwa.." ya hadiye Wani mugun yawu gani yakeyima ba karamin renin hankali daddy yayi masa ba da yayi masa wannan tambayar, dande kawai mahaifine,. "Wani abun ne ko Jarumi? " Daddy ya kara jefo masa tambayar batare daya damu da rashin amsa tambayarsa ta farko da beyi ba daman already yasan halin d'ansa ba kunya ce dashi ba akwaisa da tsiwa ga miskilanci. Aeezad ya bude baki zeyi mgna hajiya rafi'ah tayi caraf ta amshe dacewa "Haba Alhaji yazaka cikasa da tambaya haka, kusan 1week yayi fa a garinnan bezo ya ganmu ba se yau ai kaga be dace a cikasa da tambayoyi ba" cikin kissa da kisisina tayi maganar se juya baki takeyi Kai kace yarinyace yar 15yrs me tashen balaga, duk Wani me hankali kallo daya zeyima rafi'ah ya tabbatar ta taba bariki ko yayane domin idanuwanta tarr suke a tsakiyar Kai ga makirci da kisisina Ga kwarewa a iskanci. "Kwarai hakane..." Shine abinda daddy ya fadi kawai jiki na rawa dominshi in har rafi'ah zatayi magana toko yaya mgnr take zece haka ne kawai. "Shige mu nufa dainning mu barshi ya huta ..." Shine abinda hajiya rafi'ah ta fadi cikin zallar Iko da Mulki jiki na rawa Alhaji sunusi yayi gaba zuwa dinning room kmr wani wa-wa yadda kasan rakumi da Akala. Hajiya rafi'ah ta mara masa baya zuwa dinning room din cikin tafiyarta ta isa da takama,Aeezad ya bisu da Ido kawai inda sabo ya saba gani sam ba sabon abu bane a gunsa, dan haka ko a jikinsa, kowa a gidan hajiya mommy ta mallakesa Aeezad ne kawai be mallakun mata ba, shi kadai ne ya zaman mata gagarau. se yanzu yake kara nadamar Auren ma gabaki daya a rayuwarsa tinda ya Auri yar hajiya mommy be shiga kwanciyar hankali ba baya tunanin ze shiga ma har abadan, kuma ga Azabar san yarinyar yana dawainiya da ruhinsa, shi sometimes ma besan meke damunsa ba yakesan na'eema. Kmr an tsikaresa ya mike cikin hanzari ya fice a falon kmr ana ingizashi ko sallahma be musu ba yanaji Daddy nace mata tafiya zakayi Jarumi na? Yayi kmr bejishiba yayi ficewarsa. Direct motarsa ya nufa bakin ciki ya kuma cika masa zuciya yayi nadamar zuwa gidanma gabaki daya a rayuwarsa. Ba bata lokaci ya shiga motar tasa ya figeta fitt ya fice a gidan kmr tashin hankali haka yake figar motar. Wayarsa ya lalubo still Yana driving yashiga kokarin nemo lambar zaks har zeyi dealing se kuma ya fasa, ya Shiga lalubo Wani searching din sunan, JARUMA TA haka kawai ya tsinci kansa da sakin wani irin murmushinnan me tattare da zallar annashuwa Hadi da nishadi da nishadantarwa, ya manta when last ma yayi fara'a kmr wannan A rayuwarsa. Dealing number din yayi Ringing daya tayi ta dauka. "real mom dina good morning..." Ya fadi da azababbiyar zazzakar voice dinsa,se murmushi yakeyi kmr Wanda yaga wa-wan zama. ''Lafiya Lau Jarumi d'an gidan real mom dinsa..." Shine mgnr data fito daga cikin wayar cikin zazzakar murya me rikitarwa, dajin muryar zaka tabbatar me muryar tadabance maganarta ma cikinn nutsuwa da sanyi da zaki da gardi take yinta. Wani irin sanyi yaji daga tsakiyar kansa zuwa kasan tafin kafarsa, yana matsifar san yaji tace masa jarumi, already daman ita tasa masa sunan gashi sunan yabisa mutane da dama hakan suke ce mata, daddy ma jarumi kawai yake ce masa kuma a gunta yaji sunan shike nan ya koma ce masa JARUMI,. "Zanzo yanzu ki hadamin fruits pls..."Yana gama fadar hakan ya katse wayar ba tare daya jira cewar taba, ya ajiye wayar gefensa yana me sakin murmushi, tamkar uwar data kawosa duniya haka ya dauketa,inya jita se yaji kaf damuwarsa ta gushe, ita ta rainesa kuma itace bestynsa,a duniya bashi da wani makusancinsa kmr ita, ko damuwa garesa ita ce abokiyar shawarsa baya shakkar gaya mata komi daya shafesa , shi maraya ne Amma sam Bata taba barinsa yayi kukan maraici ba, Ta maye masa gurbin mahaifiyarsa dabe santa ba be taba ganinta ba, sometimes ma har maye masa gurbin mahaifinsa dayake raye takeyi, ita mace daya ce tamkar da millions, tafi dubu dubu a cikin dubbunnai, samunta zeyi wahala. "A kasan raina nake jinki real mom dina, kuma nanny na..." ya fadi Yana mejin Wani irin ruwan sanyin nishadi Na kara ratsashi,Nan take yaji damuwarsa dukta gushe,zuciya da ruhinsa suka cika da son ganin mommynsa.. Wannan book din na kudine 1k 0542703718 Saadatu Abdullahi gt bank 08101626484.