Sashe 93
Namijin Zuma Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mutane dayawa Nan gidan zasu kwana domin gobe ma akwai wata walimar Za a kira masu kida' a rakashe,. ba Wanda ya Kai Nabeelah aiki a gidan kaf jikinta ciwo yakeyi sallolin tama seda gaske tasamu tayi sbda aiki, a zaune tayi sallolinta,. Tana Aiki da daddaren tana gyangyadi, Wani mugun bacci tadingaji Wanda bata tabajin irinsa ba, kaf ilahirin jikinta ciwo yakeyi har Wani zazzabi ma ke neman rufeta, Motsin cikinta ma ya ragu, ko abincin kirki bata sawa cikinta ba sede ruwana Sanyi taketasha se ayaba data gani a kitchen taci Sbda duk cikin abincin gidan ba Wanda zata iya ci, jikinta yayi rawa harya gaji, babyn cikinta tin Yana mugun motsi, yazo ya denayi sede tana jiyo motsinsa Dan kadan-kadan.tanata Aiki tana tunanin Aeezad tasan Yana can Yana haukan kiranta, Gashi wayarta kashe take, tasan Yana can ze addabi aunty Hafsat da uban kira,. Basu suka kwanta ba ranar se karfe biyu da Rabi na dare Nabeelah tayi gyangyadi yafi Sau talatin, suna shiga dakinsu na masu aiki, Nabeelah ta kwanta ko wankan batayi ba duk uban gajiyar dake tattare da ita, haka ta kwana da yunwa cikinta ko motsin kirki beyi, sbda rashin abinci, ita har ynzu ta kasa cin komi sede abubuwan da takeci tin su take iya ci, ko kamshin abinci bataso sede dauriya kawai,. A gidan Aunty Hafsat kuwa, big hajiya na tashi ta tambayi Aunty Hafsat Ina nabeelah sbda tashiga daki bata ganta ba time din Aunty Hafsat na kitchen. Nan Aunty Hafsat ta sanar da big Hajiya kaf abinda ya faru. Aifa nan big hajiya ta dora masifa da bala'i tace meyasa aunty Hafsat bata tasota ba ta nunawa Hajiya mommy iyakarta. Aunty Hafsat ce tadinga bata hakuri kawai ganin big hajiya zata dawo kanta da masifar da bala'in,big hajiya ta rikice tadinga masifar, ta fita zataje gidan Hajiya mommy da kyar aunty Hafsat ta rikota tana bata baki, tadawo da ita falon suka zauna big hajiya de ranar ko abinci ta kasa ci se ruwan masifa takeyi knr yawun bakinta ze kare gashi tayi-tayi Aunty Hafsat ta tashi ta kaita gidan mommy taki sbda inta kaita seta lalata komi gashi abun kan Nabeelah ze dawo, duk fadan da big Hajiya keyi sbda cikin jikin nabeelah takeyi ita tsoronta kar aje a mata asara gashi tasawa ranta wannan cikin na jikin Nabeelah, a kullum se tayi Addu'ah Allah yasa Yan uku ne. Har dare nabeelah bata dawo ba, ga fadan big hajiya ga uban kira Aeezad na mata, sede ta masa karya tace kawai bacci Nabeelah ketayi yau sbda in ciki ya kusa shiga watansa bacci mace keyi sosai..." Itace karyar da Aunty Hafsat tayima Aeezad, Aeezad yace okay Amma badan hnklinsa ya kwanta ba daren ranar de gaza bacci Yayi sbda beji abar kaunarsa ba da Kuma ajiyar cikinsa dake jikinta. Big hajiya kanta duk mugun baccinta batayi bacci ba ranar, aunty Hafsat ma dake part din baban Noor gaza bacci tayi zuciyarta na kan tunanin ya nabeelah take da cikin jikinta? Jikinta ma kawai bata yakeyi asiri ya tonu. Seda baban Noor ya tambayeta meya hanata bacci tace masa ciwon kaine kawai. Daren ranar a bangaren Aeezad Da aunty Hafsat da big Hajiya bacci sede barawo, shi Aeezad Kam duk kwarewar satar bacci beyi galaba a kansa ba. Manage ba editing. This book is 1k 08101626484. NAMIJIN ZUMA 46.... kafin a kira Assalatu Hajiya mommy ta nufo dakin domin ta tashi nabeelah Sbda ta daura girki da wuri, jiya mutane nata santin abincinta, Sam ma sauran abincin ba a Wani cicciba anficin Wanda nabeelah ta dafa. Ta kira sunanta, bayan ta shigo dakin ta tsaya a kanta,kwance nabeelah take tana kallon Saman dakin ita kadaice kwanciyar datake iyayi, bata ita wata kwanciya bayan wannan. Idanuwa Hajiya mommy ta tsure cikinta nabeelah dashi wanda ya bayyana, Amma se Hajiya mommy Tasha ko idonta ne, dukda taji Wani mummunar faduwar gaba, ta lumshe idanuwanta ta kara budewa a kan cikin nabeelah,. "toko tumbine?" Hajiya mommy ta tambayi kanta da kanta, haka kawai ta tsinci knta da fadawa duniyar tunanin da bata San kona menene ba. Tafi karfin 5mnt tsaye kan nabeelah wadda keta sheka bacci batasanma hajiya mommy ta shigo ba, kaf maaikatan dakin bacci sukeyi kusab su hudu kowacce da d'an gadanta me daukar kafita waya sha biyu, dakunan masu Aiki a gidan tafi daki ashirin Kuma ko wanne da masu Aiki a ciki kusan mutum hudu, shida na Maza shida na mata. Hannu takai ta daki nabeelah a kafada, da karfi, a firgice nabeelah ta tashi zaune idanuwanta suka sauka a kan hajiya mommy, cikin hanzari nabeelah ta kalli cikinta a ranta tayi Addu'ah Allah yasa de hajiya mommy bata gani ba...'' "tashi kije Ki daura girki,,," nabeelah tace Toh ta diro daga kan gadon tana kallon Agogon dakin taga karfe uku ne da Rabi na dare, ko hudu batayi ba, Sam baccin be isheta ba, ji tayi kmr Yanzu ta kwanta aka tasheta, Wani irin azababben ciwo taji kanta nayi, ga azabar ciwon ciki da taji Yana taso mata, ji take kmr ta koma ta kwanta, Amma dole ta lumshe idanuwanta ta bude, ta karfafa jikinta ta fice a dakin hajiya mommy nata binta da kallo haka kawai taji a ranta bata yadda da nabeelah ba, yayinda kiyayyarta ta yawaita a zuciyarta, a sukwane hajiya mommy ta biyota kiching din, se kawai nabeelah ta ganta kwatsam seda gabanta ya fadi, yaga de se binta take da kallo tako ina, zuciyar nabeelah na bugu zuciyar hajiya mommy na bugu, dukkaninsu ba a natse suke ba ba kmr ma nabeelah ita tasan dalilin rashin nutsuwarta ita Kuma hajiya mommy bata sani ba, itade kawai taji ta kasa nutsuwa. "Ai nagaya Miki abubuwan daza kiyi tin Jira kin fahimtar kou? Akwai komi a kitchen din kasa dazaki bukata,..'' cewar hajiya mommy aunty Nabeelah tayi hanzarin amsawa da "toh...na fahimta..." Hajiya mommy ta shiga kare mata kallo, jikin Nabeelah ya fara Neman bari, kanta na kasa a ranta se Adduah takeyi zuciyarta nata fatt fatt fatt. Hajiya mommy ta juya xata fice a kitchen din se Kuma ta juyo ta sake kallon Nabeelah se kawai ta juya ta karasa ficewa a kitchen din haka kawai ta tsinci zuciyarta da saka da warwarar da batasan Kona meye ba a ranta de se tunani takeyi Kmr ciki tagani jikin nabeelah Kuma kamar tumbi,hakade Hajiya mommy tadinga saka da warwara. A ketchin din Nabeelah jiki ya mutu Se Kara adduah takeyi ta fara aikin tanayi tana layi kmr Yar maye, gashi ko Ina a jikinta azababben ciwo kawai yakeyi. Haka tadinga Ayyukan da kyar tanajin mararta kmr zata bude, inda ace da hali ma kwanciya zatayi , ji take kmr ta saka ihu, har akayi asubahi ta tsaya tayi sallar asubah, haka ta wuni tsaye yauma gashi cikinta ba komi se ruwa data sha, Aiko tanashan ruwan taji cikinta ya fara motsi, ada hatta tsorata, Dan haka ta dauki ayaba taci sosai Sbda tsoro takeji kar cikin ya dena motsi, a asibiti in taje awo doctor Maryam nace mata in ciki yadena motsi hanzari akeyi Azo asibiti wato da matsala, harga Allah batasan Wani Abu ya sameta koya samu d'an cikinta. Tukunya shida ta daura a wuta, tana Aikin ne da kyar, innah sadiya tazo ta tayata a tsorace take tayata gudun kar Hajiya mommy tazo ta ganu, sauran maaikatan nso su tayata Amma Suna tsoro. Haka suka gama aikin cikin temakon ubangiji, mutanen suka yawaita a gidan, hajiya mommy se shiga Ake ta alfarma ana fitowa it's a dole matar Alhajin Allah. Nabeelah da wasu Wanda aka dakko Dan serving mutane suke ta serving mutane, hajiya mommy na bakin cikin nabeelah ta zauna, duk inda tayi seta bita da Ido, a ranta kawai bata yadda da ita ba,, nabeelah kanta a tsorace take ga uban ciwo jikinta nayi kafafuwanta sunyi Wani him, sun kumbure, Cikin jikinta yayi lakur saboda azabar yunwa SE a hnkli yake wutsil wutsil Daman a gida haka takeyi in taci abinci se ya hau motsi Sosai in tanajin yunwa se yayi lakur. DUk abubuwan da takeyi hankalinta na kan tunanin Aeezad ta tabbatar yanacan ya kusa hauka,ko seconds yayi beji taba zarewa yake neman yi, Ina maga wuni da kwana gashi Amma Kuma Wani wunin. Allah-allah nabeelah take ta bar gidan Amma Ina ranar ma Nan gidan ta kwana sbda bakin Basu watse ba wasu se jibi zasu watse Yan nesa kenan, wasu ma Yan kusan ne Amma Nan zasuyi sati daya sbda duk sun gama da mazajensu ba yadda zasuyi, itafa Hajiya mommy bata kawance da macen da namiji ya Isa da ita, sede tayi kawance da macen data isa da namiji. Daren Wannan ranar ita knta nabeelah gaza baccin tayi Sbda tunanin halin da mijinta yake ciki, ga ciwon ciki, gana baya, gana jiki Sbda azabar gajiya, duk de jikin ma ya mata ba dadih kmr ba nata ba. A gidan Aunty hafsat Kam Aeezad nata kira, tin tana daukar tana masa karya, harta kashe wayar kawai Sbda ta rasa ma yazata ce dashi, harga Allah bazata iya gaya masa inda nabeelah take ba, Sbda tsoro, Se Yanzu take datasanima da gaya masa gaskiya tayi tin farko,tana kashe wayarta ya fara Kiran lambar big Hajiya, nanma Aunty hafsat ta dauki wayar ta kashe, big Hajiya se matsifa takeyi, da ace zata gane gidan rafi'ah da tini ta tafi, Sbda de kawai bazata gane bane gashi Kuma aunty hafsat taki kaita ko barinta ta fita ma taki,. haka suka wuni a falo jungum jungum, suna jiran dawowar nabeelah Amma Shiru har dare , gabaki daya se hankali ya kuma tashi, Daman 2days din takeyi in taje gidan ko 1day, Amma Yanzu se aunty hafsat ke gani kmr an gane cikin jikin Nabeelah ne,. Ranar ko part din baban Noor bata jeba, sede tace masa mgni zatasha ta kwanta kawai a part dinta. Nan falo suka kwana zaune, aunty hafsat ta rasa yazatayi tunaninta ya kasu kashi kashi. big Hajiya tasakota gaba da matsifa da bala'i, gani takeyi kamar lefin tane, se fadi takeyi "Meyasa Baki tasoni ba?ai da dakikaga zuwan rafi'ah ni dase ki tasoni Ina dai-dai da ita a Wannan Karan bazan daga mata kafa ba wallahi bazan