← Book details Namijin Zuma Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 107

Sashe 91

Namijin Zuma Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yau itace ta sakko da karfi, daga ita se riga mara nauyi doguwa har kasa, yanzu Sam batasan riga me nauyi sbda jin zafi gareta sosai... Ganin yadda ta gigice ta fita hayyacinta, ta tallabo kasan cikinta sbda azababben motsin da yakeyi kmr ze ballo mata mara ya fito sbda tashin hnkli da firgici. "Ki kwantar da hankalinki mommy, ba Wani Abu insha Allahu, in kikasa hijjabi bame gane akwai ciki jikinji insha Allahu..." Aunty hafsat ta fado mata cikin kwantar da hankali. Nabeelah tayi narai-narai da fuska na zallar tashin hankali, ta kasa motsin kirki, ji kake fatt fatt zuciyarta na bugu, ganin batada niyyar motsawa duk tabi ta daburce, aunty Hafsat ta bude drawer ta dubo mata hijjabi zumbulele, ta Mika mata,ta amsa ta saka kalar purple ne dark sosai, har kasan kafafuwanta hijjabin ya kai.. Nabeelah ta kallah uban tulun Cikin nata ta dago ta kalli Aunty hafsat tace "Ana gani kou?" ta fadi Kmr zata fashe da kuka, aunty Hafsat dake kare mata kallo ta girgiza Kai tace "Ba'a gani sosai,,Cikin naki ne tabar kallah yayi girma kamar ba Cikin farko ba, Amma ki dinga wasa da hannunki a Cikin hijjabi , kiyita innalillahi wa'inna ilaihirrajun,insha Allahu Khairan Aunty nabeelah,,," Nabeelah da zuciyarta keta tsananta bugu tana sauraran Aunty Hafsat ne Kawai Amma gani takeyi kmr dole a gane da ciki jikinta, ga face dinta ma duk ta kumbura. Karasawa tayi drawer dinta Cikin hanzari, ta dakko zani ta daure Cikin sosai wai yadda ze koma ya rage fitowa, Amma Sam ko gezau. Aunty Hafsat ta zaro ido tace "Kai ! Meyasa Zaki tamke cikinki har haka? Wannan aise ki kashe babyn, gaskiya ki kwance mommy, Wlhi bazan iya da haukar Aeezad ba in kika kashe masa baby, ai kwara ko wanne tashin hankali a kan nasa, ni Wlhi nafi tsoronsa a kn hajiya mommy, dande ita nata abun makircine da Kuma ta bayan gida za a biyo maka,,,ki kwance Kawai mommy Addu'ah ta kauda komai, wlhi ubangiji ya gama mana komi, shi muka roka Kuma ze rufa mana asiri..." Aunty Hafsat ta karasa wata zufa na karyo mata goshi dukda uban Sanyin AC dake falon Amma zufa takeyi sbda tunanin irin masifar dake gaba in Hajiya mommy da na'eema suka fahimci cikinnan na jikin nabeelah na Aeezad ne. Aunty Nabeelah data kama Nishi yayinda takeji kmr zatayi amai har bayanta ya dauki zafi sbda daure Cikin da tayi, ji tayi tana neman shidewa Cikin hanzari ta kwance zanin sbda itama bazata jureba, ta canza Wani hijjabi dayafi wannan na jikinta girma, suka nufo kofar fita a dakin zuciyar nabeelah kmr zata fito fili sbda tsabar bugu,.. Riko mata hannu aunty Hafsat tayi bayan sun iso kofar ficewa dakin cikin muryar kwantar da hankali tace "Mommy ki kwantar da hankalinki Dan Allah, ba abinda ze faru, Ina jiyo heart beat dinki in kika nuna tashin hankali za a gane, ki kwantar da hankalin ki dan Allah, ba asan tashin hankali game ciki da Aeezad na nan komi zezo da sauki, ki nutsu pls, kinji..." Aunty Nabeelah ta daga mata Kai alamar toh, amma batajin zata iya kwantar da hankalinta. aunty Hafsat ce ta bude dakin ta fara fitowa nabeelah na biye da ita a baya se wasa take da hannunta Cikin hijjabinta... Hajiya mommy dake zaune kan kujerar 3str ta daura kafa daya kan daya, hand bag dinta na side, se faman karkad'a kafa takeyi tana jijjiga kmr me iskokai, sanye take da jallabiya pink ta yane kanta da dankwalin abayar, hajiya mommy ba mummuna bace, daman normal tanada kyau Kuma ga kyawun hutu, sede bata da hanci, dande akwai gyara ne sosai, Amma tafi na'eema kyau nesa ba kusa ba, Kawai de na'eema tafita yarinta ne a jiki,. Aunty hafsat ta karasa ta zauna kasa, hajiya mommy nata binta da Wani Wawan kallo tace "Kinje kin dade daga kirawomin tsohuwar guzuma, Kai kace na aiki bawa garinsu, Kai yaran yanzu basu da tarbiya Sam Se kayi mgna a gaya maka mgna,,,ni inba ma kaddara ba me zanzo nayi a gidanki,..." Aunty Hafsat ta tabe baki daman ita Sam jininsu be hadu da hajiya mommy ba,tin sadda ta taba zaman gidan kafin tayi aure.... Kan nabeelah na kasa ta karaso ta zauna kasa nesa da hajiya mommy tinda ta shigo falon hajiya mommy ke kallonta, gani take Kmr nabeelah ce Kmr ba ita ba, itade taga tayi wata uwar kiba ne a lokaci kankani, kallon da take mata ya kara sa Nabeelah jin bugun zuciya, murya kasa kasa tace "Ina kwana hajiya mommy...." Ba tare da hajiya mommy ta amsa ba sbda mamaki Daya sake rufeta jin sabon muryar nabeelah dataji sak Cikin mamaki ta kalli Aunty hafsat tace "Hafsat Wannan Kuma yayar nabeelah ce tazo ko kanwarta ce" aunty Hafsat ta kalli Aunty nabeelah wadda kejin Kmr ta mutu Dan tashin hnkli. "Kmrya? Aunty nabeelah ce Hajiya mommy..." Hajiya mommy ta kara bude idanuwanta sosai a kan aunty nabeelah Baki sake tace "Yauni naga ikon Allah? Wannan shine Yar Aiki tafi me gida, itace tayi kiba haka nabeelah de dana sani tsohuwar kilaki, an jima ba'ayi Aure ba mazan waje sun gama cinki sun bar banza,,,a haka Zaki mutu ba aure, sede ki dawwama a bauta kina aikatau kina ciyar da uwarki,,Maza sun gama zurfafa gindin," aunty Hafsat taji zafin kalaman hajiya momny, a bangaren nabeelah ma taji zafi sosai, Amma sede ta saba da mafiyyin hakan da tana gidanta. Hajiya mommy ta tabe baki, ta jinjina Kai se kallon Nabeelah takeyi tana dawowa ta kalli Aunty Hafsat, tsayar da idanuwanta tayi a kan aunty Hafsat kana tace "Ke Kam kinyi asara Hafsa, yanzu kina gani Wannan kaskantacciyar tayi Wannan kibar..,,aaahhhh gaskiya lefinki ne, taya Zaki bama me aiki sake har haka, harma ki barta tadinga ci tana koshi har tayi kiba, aikin bauta tazoyi ko kuma cin abinci? Ahhh lallai , gashi daman Maza sun riga sun gama fafiketa, ko Ina ya bude a jikinta, duk Wani sassa kullalle mazan waje sun bude sun wangale, Allah wadaran naka ya lalace, uhm Allah de yasa ba mijin Hafsat bane ke cin gindin naki,danke Wannan daga ganinki k'arya ce ke, duk wanda kika samu wangale masa zakiyi yaci, yooo Daman meke baroku daga kasarku inba karuwanci ba, se Kuma in tsautsayi ya fada kun aurarma wata asararriya miji ku mallakesa, shegu Yan dangin asiri , dakun samu namiji nan da nan dakun kaishi gun teacher an wanke muku gindii kunzo kun bashi ya shanye, ku kwace miji ku kwace dangin miji, a haka dai ke zaki mutu ba aure...." Aunty Hafsat ta kumajin zafi da kalaman da take sukar mommy da ita, ba Kmr ma da take dangan ta ta da zina, zinar ma wai da mijinta, babbar masifar ma data dangan ta ta da shirka, aunty Hafsat bata tabajin ta tsani hajiya mommy ba Kmr yau, ji takeyi inama da yadda xatayi dase ta gayama hajiya mommy kalaman da harta mutu bazata mance dasu ba kilama bakin Cikin kalaman yazama ajalinta ita da yarta, Aunty Hafsat taso ace big hajiya na falon da hajiya mommy baza tayi wannan cin mutuncinba, koda big hajiyar ma ba komi take gareta ba Amma ta tabbatar da tana nan dole ma ta rage Wani abun.Nabeelah de shiru tayi zuciyarta na suya,. "Aunty Nabeelah ta muku nisan da babu me muryar daze kirata ta iya juyowa,,," Aunty Hafsat ta fadi hakan a ranta,.hajiya mommy ta kalli dankareren wristwatch din hannunta na zallar zinari, ta karkada kafa, ta kalli Aunty Nabeelah tace ''Kwana biyu karuwancinne ya hanaki kizo duk karshen satin da kk Zuwa kina min aiki? Yar iska, ko karuwancin naki yayi kaurin suna yasa kika dena zuwa gidana? " Aunty Nabeelah ta girgiza mata Kai alamar a'ah,Hajiya mommy taja kwafa, kana taci gaba dacewa "Yar iska! tin jiya nake kiranki waya kashe har yau waya kashe, ke harkin isa ki kashe waya kina yar aiki kaskantacciya, mara galihu, baki aje ba baki ba d'an daki ajiya ba, to kisani yadda kika sani wahalar zuwa gidannan haka zaki wahala da aikin gidana yau, nace ma Kar a gyara komi ke Zaki gyara ko Ina a gidannan yau, har sharar tsakar gida yau kece zaki yita, kina karyar bura uba ne, ni nan na fiki tashanci...harni zaki bawa wahala banzar bazara irinki, ke inbadan babban taronnan dazanyi na cikar shagona shekara goma ba, ai baki isa inzo ba, Amma yanzu ma danazo tabbas se jikinki ya gaya miki, yau duk wannan kibar taki ta asara seta zazzage, tashi mu tafi tsinanniya, waya sani ma ko uwarkima zina tayi ta haifeki Yar iska mara uba, dangin karuwai haihuwar ti-ti,,," ta karashe hadi da mikewa. Ba karamin zafi Nabeelah taji na kalaman hajiyar mommy ba musamman ma kalmarta ta karshe, seda ta lumshe idanuwanta ta bude, a ranta tana tunanin wai a banza banza ma tana mata wannan zagin ina maga ta fahimci akwai Aure a tsakaninsu da Aeezad mijin yarta, ta tabbatar daga ranar data sani kasheta big hajiya zatayi har lahira,. Ita kanta Aunty Hafsat abun ya mata zafi amma a ranta tasan koda goma ta lalace tafi biyar albarka, balle wannan goman ba lalatacciya bace. Ganin hajiya mommy ta mike yasa aunty nabeelah mikewa, Aunty Hafsat ma ta mike, hajiya mommy ta nufi kofar fita tana fadin "Wuce muje, ki daura tukunyar girki, ammayi wasu girke girken yanzu dai ke Zaki daura wasu , fried rice da jallof rice, se sauran ayyuka..." Nabeelah tace "Toh,,," a tsorace take gabaki daya, Aunty Hafsat se kallon aunty Nabeelah takeyi Cikin tausayi, tasan yau zata wahala ita da d'an cikinta. Hajiya mommy ta fice a palon, aunty Nabeelah na biye da ita, aunty Hafsat ma ta rakosu har bakin mota.. Bude hand bag hajiya mommy tayi ta zaro kudi dubu daya ta wurgama Nabeelah tana fadin "Kinde san bazan hau mota daya dake ba, kaskantacciya irinki, bana san karnin talauci, ga wannan Kya hau napep ki iso, karki sake in rigaki isa..." Nabeelah ta tsugunna ta dauka,tace "Toh mommy..."aunty Hafsat najin zafin kaskancin nan har cikin ranta, Aunty Nabeelah ta nufa gate aunty Hafsat na kallo tafice ji takeyi kmr ta dakatar da ita daga fita daga gidan, tabbas da Aeezad Na nan
Chapter 91 · 0% Book details