Sashe 14
Namijin Zuma Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
https://chat.whatsapp.com/FxikBhpweXTLMbrEVc6xdS Free page group. SAADATU BINTU ABDULLAHI (Writer of kyautar Allah) Free page6 Jin muryarta ya haifar masa dajin Wani irin sanyi me sanyaya ruwan jiki, ya sauke ajiyar zuciya 2tyms a jere ya lumshe Ido ya sake budewa kana yace. "mommy bani da lafiya wallahi..." Ya fadi a shhagwabe kmr me Shirin fashewa mata da kuka. Ya saba mata shagwaba Amma wannan Karan Se taji abun ya mata gatsal kmr bata saba ji ba. "Subhanallahi Meya sameka?" Ta fadi cikin sanyin murya sabanin farko data daga wayar. "Wani Abu nakeji mara dadih a jikina da zuciyata..." Ya fadi Yana mejin Sanyi a jikinsa kaso Dari na abinda ke damunsa ya ragu zuwa tamanin sbda muryarta kawai dayaji, shide be tabajin abinda yakeji ba a kanta kamar na yau,ada inyaji muryarta ba haka yakeji ba. "Kamar me babyna? Banason abinda ze dameka pls,, Ba munyi magana dakai ba a kan kan ka denasa damuwa a ranka Dan Allah kayi Adduarh itace maganin komi na rayuwar duniya, haba Jarumina!" Ta fadi tana mejin yanayi mara dadih a jikinta sbda ko a muryarsa ta tabbatar da Wani Abu na damunsa Amma setasha ko damuwarsa da na'eema ce. 'ajiyar zuciya kawai Aeezad ke saukewa yana me sauraronta kawai shi kadai yasan meke damunsa, shide yasan ba dmwar na'eema bace a wannan karon kuma besan meke damunsa ba. "kaji babyna !'' ta fadi jin yayi shiru sede ajiyar zuciyarsa kawai take juyowa ta cikin wayar. "Naji mommy insha Allahu zanyi Addu'ah kema kiyi min pls ....'' ya fadi cikin sanyi. Nabeelah ta jinjina tabbas yasa damuwa a ransa sbda muryarsa ta nuna alamar nadama a ciki duk yayi sanyi shida bakinsa be mutuwa Amma yau murus take jinsa, ko maganar batsa babu a bakinsa. "Zanyi maka kaji na mamansa..Amma se kayimin promise zaka denasa damuwar komi a ranka Dan Allah ka dinga sanyayawa a kan komi hkri fa maganin zaman duniya ne ..." ta karashe cikin muryar rarrashi da kwantar da hankali. "Thank you,,, proud of you ..." "Nima ina alfahari dakai na mamanshi...Ka kwanta kayi bacci kaga time ya tafi dare yayi sosai ko baka koma kanon bane?" "No na koma..." "Okay Allah ya bada sa'ah ya tsareminkai gabas da yamma kudu da Arewa..." "Amin ya Allah mommyna..." "Seda safe ka kwanta zuwa 3 or 2 katashi kayi sallar ka gayawa ubangiji damuwarka nima zan tayaka Kai kukanka , Allah shike mgnin damuwowinmu..." Aeezad ya kara sauke ajiyar zuciya yace "Insha Allahu nagode mommyna sweet dreams.." ya karashe badan ransa naso ba, haka kawai ya tsinci kansa da rashin San ta ajiye wayar. "Nagode babyna bye..." Ba tare data jira cewarsa ba ta katse wayar,. Bayan ta katse wayar ya kasa cire wayar daga kunnensa seda wayar tayi 5mnt a kunnensa yana mejin muryarta na masa gizo, ya cire wayar daga kunnensa ya kure Screen din wayar da Ido, ya shafa creen din wayar ta kawo haske, picture dinta ne kan lock screen dinsa, tana zaune a farfajiyar hutawar gidansu, sanye take da doguwar rigar atamfa tasha daurin ture kaga tsiya yayin datai murmushi har wushiryarta ta bayyana, ba karamin kyau tayi ba, sumar goshinta ta kwanta luf-luf. Wani irin murmushi ne ya subuce masa yayin dayake kallon picture din nata kamar Yana gabanta haka yakeji a zuciya da kwanjinsa. "Kinada kyau na matsifa mommy!" Ya fadi yana me kara kureta da idanuwa, be taba sanin tanada kyaun daya wuce lissafinsa ba se yau. Bude wayarsa yayi yashiga gallery dinsa ya fara duba picture dinta da yaketa mata ba tare data sani ba, kaf wayoyinsa itace take cika masa gallery kuma duk photos din da yake mata ba tare da saninta yakeyi ba, itace a kaf lock screen and home screen na kaf wayoyinsa, sunyi fada da na'eema yafi a kirga a kan hakan tayi tayi ya cire yaki cirewa, har hajiya mommy seda na'eema ta gayama, hajiya mommy ta kira Aeezad Ta tambayesa meyasa zesa kaskantacciya a screen dinsa..." Aeezad yayi mata banza, Nan ta rufesa da bala'i da matsifa tace dole seya cire kaf pictures din nabeelah a wayoyinsa, cikin Mulki Aeezad yace " am sorry hajiya mommy Wallahi bazan cire ba, ai kowa abinda yakeso shi yakeyi... Kuma in zaku lura ai a matsayin uwa mommy take a gurina..." Sam hajiya mommy bazata iya jaa da Aeezad ba Dan haka ta kyalesa kawai ita kanta Tsoronsa takeji wasu lokutan sometimes data gansa se taji zuciyarta na yawaita faduwa kwarjini yake mata, dole sede ta bawa na'eema hakuri a kan hakan. Dadin karawar abinda ya kara dasa musu kiyayyar Nabeelah a ransu kenan saboda ganin yadda Aeezad ya bata muhimmancin fin komi na rayuwarsa. Seda ya Kai 2:am Yana duba picture dinta haka kawai kallonta kesa masa nishadi,. Mikewa yayi ya nufa toilet ya dauro alwala ya fito ya fara jero sallolin dare Yana me Adduah Allah ya yaye masa abinda ke damunsa , danyafi tunanin boyeyyen ciwo yakeyi Wanda shi kansa besan Kona menene ba. Har seda yayi sallarh asubahi kana ya kwanta bacci ya barawo ya figesa, bashi ya tashi ba se 9:am, ya shirya ya tafi office 11:am. A office dinma yau kmr jiya se tunani tunani kawai yakeyi , ya kirata a waya yaci saah ta dauka bugu daya,, wuni sukayi suna waya, har ya bar office din, a voice dinsa nabeelah ta fara fuskantar kamar ya soma chanzawa, nutsuwar dole ta fara shigarsa. *Katsina state* Zaune suke a falon hajiya mommy kusan su biyar, hajiya mommy se kawayenta manyan mata su uku manyan mata ne kamar Hajiya mommy, Dayar ce karama wato na'eema . Duk kaninsu sunada kiba sosai, ba kamar ma ita karamar cikinsu, dukda a zaune take hakan be hanani gano itadin gajera bace, sede fara ce sol, bata da kyau kwata-kwata ga kananun Ido, gashi duk tayi kiba tako ina, irinsu ne akewa lakani da badan fari ba se bola. Zaune suke sun Sa table a tsakiya Wanda ke cike da kayayyakin motsa baki se sanyin AC da AC kawai keta ratsasu tako ina masu Aiki nata hidima dasu, sauran ukun duk Aminan hajiya mommy ne na bugawa a jarida, kallo daya zaka musu kasan sunci sun tada Kai, tinda hajiya mommy ta Auri Alhaji sunusi Ta dena kawance da talakawa sede Yan gayu masu kudi kawai. Hajiya mommy dake zaune kan kujerar 1ctr tana facing na'eema dake zaune da wayarta kirar iPhone 13promax a hannu tana kallon TikTok. "Ke tinda Allah yadawo dake lafiya ya kamata ki koma dakin mijinki Ko zuwa gobe ne..." na'eema dake kallon wayarta ta dawo da dubanta kan Hajiya mommy dake maganar ta tabe baki cikin mamaki tace "Ai benan mommy Na tambayi me gadi ta waya ya gayamin ya koma kano ai.. kuma ma ko Yana Nan gaskiya bazan koma yanzu ba. " Hajiya mommy ta amshe da "Dole ki koma saboda kinsan de mijinki ba hankali ne dashi ba, na fuskanci ya fara kosawa gaskiya, danma Allah ya rufamin Asiri uban a tafin hannuna yake .." Cewar hajiya mommy. Kaf kawayen hajiya mommy suka kwashe da dariya Hadi da hada baki gun cewar "Da kyau ta gurina ai bakya wasa..." hajiya mommy tayi Wani farr da Ido tace "ina zan tsaya wasa,,, ai kaf gidannan d'anne ya zamar min. Kadangaran bakin tulu....ita kuma wannan wawiyar tasha nono ta zubar Sam ta kasa maidasa kmr masa a tandaa." Hajiya mommy ta karashe mgnrta tana kallon na'eema. Hajiya naja'atu babbar Aminiyar hajiya rafi'ah ta amshe da "ta yaya zata maidasa kamar masa kullum kina kan aikata kasashen waje sarin kaya?" Na'eema ta amshe da "Gaya mata dai mama.. " cikin tsiwa tayi maganar daman bata da alamar kunya ko a Ido.. "A gayawa uwar ubanki me dattin talauci..." Hajiya mommy ta amshe da kundumoma na'eema manyan ashariya. Na'eema ta hade Rai tana kunkunai. "In ban aikaki kasashen wajen saro kayayyakin ba ubanki dake kabari zan aika ya saromin shigiya kawai! Yar bura uba, Nan dattin talauci ne ya kashe ubanki! shegiya Dan uban ubanki tashi ki barmin falona kuma gobennan ki shirya ki koma gidanki ,in mijinki yadawo ya taddaki gidansa,karki jamin yazo ya gayawa ubansa, tin uban be tafuka Wani Abu yazo ya tafuka a kansa, tinda azabar sonshi yakeyi kamar hauka.." cike dajin haushi da bakin ciki na'eema ta tashi ta bar falon ta cika fam ta batse, a rayuwarta ta tsani yarfi kuma mommy ta matsifar iya disga mutum a cikin friends dinta, ita kuma na'eema ga rashin kunya,ba tattausa harshe ko a kan uwa ne, a rayuwarta tana kaunar tafiye tafiyennan da takeyi , ko Dan pictures datakeyi tana nunawa duniya ta faso gari, uwa uba kuma tana facaka da kudi, ga yawon bude Ido tanayi tana ganin Yan Gayu da masu kudade. Hajiya wasila tace "wannan Karan kin matsawa yarinyarnan a kan seta koma gidan mijinta, bayan ke takema Amfani,saboda Allah fa yarinyar nan na Kokari ..." hajiya mommy tace "Eh nasani hajiya Amma ni tsorona kada yaronnan ya gaji ya gayawa mahaifinsa kinga de ko be mgna wata rana se yayi magana, ni shine kawai problem dina... " "Karki taba damuwa tinda kin riga kinsan hannunki..."cewar Hajiya najmu. Duk suka kyalkyake da dariya, hajiya nana ta nisa cikin nutsuwa domin duk tafisu nutsuwa da ilmi ita Dr ce, tace "Kawata gaskiya be kamata ace yarinyar Nan tayi wannan kibar ba Tari guda, alhalin ko haihuwar farko batayi ba,duba fa yadda tayi kiba duk gashi tafimu kiba, ke kanki uwarta tayi hudunki, mazan yanzu fa bawani So sukeyi mace tayi kiba ba, Nan da Nan seta narke inta cika kibarnan,.." Hajiya naja'atu ta amshe da "Ah Dr nana batta ta narka kibarta, yadda kowa ya kalleta zesan tana auran me kudi kuma babban soja Masu fada aji a Nigeria .." hajiya wasila ta amshe da "Wallahi kuwa a batta ta barbaza kibarta ...yooo taci tayi hani'an, uba kudi d'a kudi kaf dangi bana tsifa, a batta ta narka kibarta yadda zata kara bayyana a hajjajunta, Muma da kika ganmu Hana hajiya dande iya jikin kenan, Amma kiba ai kwarjini ce...." "Wannan de magana taku ce kune masu diya..."cewar hajiya rafi'ah, duk kaninsu duk suka murmusa .. hajiya nana ta rausayar da Kai tace "gaskiya de ni a ganina ya kamata ta rage,,